Showing 108001 words to 111000 words out of 276165 words
Chapter 37 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
da mutane da ɗan yawa dik da dai ba wasu baqin fuskoki bane amma ganin mutanen ya sanya Saddiqa jin ta a takure, Munir na ganin haka ya shiga gaban ta ya kare tafiyar ta har sai da ta samu wajen zama sannan ya matsa shima ya zaune kusa da Ɗan liti,tinda suka shiga Munir ke kallon inda Abdul yake dan ya ga ko yana kalle masa mata sai ya ga gaba ɗaya hankalin shi na kan Mommy ne,shi dai hamdala yayi da ya ga hakan be damu ba koma me yake faruwa kar kowa ya rab'i matar da zai aura suje can su qarata.
Bayan gaishe-gaishe da gabatar da kai a gaban Sarki, Sarki yace,
"Alhaji Baban Gida mahaifiyar ka ta kawo koken ta gare mu akan musgunawa da ake yi wa yarinyar da jikan ta zai aura, wadda mun san mahaifiyar ta tinda da sa hannun mu mahaifin ta ya karb'o auren ta daga Sarkin rigar Hard'o,muna da labarin rasuwar ta domin kuwa anan fada aka sallace ta aka kai ta gidan ta na gaskiya, yanzu muna so mu san da amincewar ka a matsayin ka na uban yaro za a yi wannan auren ko babu amincewar ka?"
Cikin girmamawa Alhaji Baban Gida yace,
"Ranka ya dad'e sarkin mu mai adalci da amincewa ta a wannan aure da muke so a qulla a yau dan kuwa har dukiyar aure na zo da ita gashi,"
Hannu ya sanya a aljihun shi ya zaro kuɗin da za su kai dubu ɗari ya ajiye a gaban Sarki,murmushi sarki yayi yace,
"To Alhamdulillahi dama mun samu qorafi daga yarinyar wajen Ɗan liti mai suna Ameerah tace babu sa hannun iyayen yaro tirsasa su aka yi su amince a yi auren,dan haka yanzu za a yi maganar d'aurin auren yarinyar wajen Ɗan liti da yaron wajen Baban Gida ina waziri da Liman?"
Matsawa suka yi gaban sarki suka kai gaisuwa tare da faɗin,
"Allah ya baka yawan rai gamu gaban ka umarnin ka kawai muke jira,"
Qoqarin d'aura auren Saddiqa da Munir ake yi cikin wani irin yanayi na gaggawa muryar Abdul ta katse su,
"Allah ya baka yawan rai nima ga nawa sadakin a taimaka a d'aura aure na da Hadiza saboda ita na zab'a zan aura bisa doron soyayya da ke tsakanin ni da ita da kuma amincewar ta gata nan a gaban ku,"
Cike da ladabi Abdussaboor yayi maganar,Sarki bashi da dalilin qin amincewa da maganar auren Abdussaboor dan kuwa da safe mahaifiyar shi ta sanar da shi komai kuma ya tabbatar mata in dai yaro da yarinya na son juna kuma iyayen su sun amince to fa tabbas za a d'aura aure dan haka Sarki sai ya nemi Ɗan liti da ya yi magana, cikin fara'ar da kowa ya kasa gane ta mecece Ɗan liti ya furta,
"Ran Sarkin mu mai adalci ya dad'e ai ni yau ji nake yi kamar an yi min albishir da babbar mota na zama babban direba,wannan aurarraki da za a yi ina mai farin cikin sanar da kowa dake wajen nan na amince da auren yarana mata gaba ɗaya su har Ameerah da Shamsu Ɗan Gidan Mai Dusa,"
Kuka Ameerah ta saka tace,
"Alqur'an in ka amince ni ban amince ba dan ba kai zaka zauna min da shi ba, yasin ni bana son shi Manniru nake so, kwarankwa..."
"Hattara dai yarinya ki iya bakin ki kina gaban mai martaba sarki mai adalci, hattara 'yar talakawa,"
Yanda dogarin ya zaburo wa Ameerah yana zaro idanu ga wata sharb'eb'iyar dorina a hannun shi ne ya sanya ta kame bakin ta da hannayen ta tayi gum ta ci gaba da gunjin kuka, shamsu kuwa ido ne ya raina fata dan kuwa bashi da kuɗin da suka wuce dubi huɗu a aljihun shi, zaro su yayi ya hau kallon mahaifin shi, nan take kuwa Mai Dusa ya zaro kuɗin aljihun shi shima ya qirga,dubu goma sha shida ne kuɗin sai ya karb'i na hannun shamsu ya haɗe waje ɗaya ya d'aga sama yace,
"Ga sadakin Shamsun waje na shima, Allah ya sanya wa auren albarka,"
Babu b'ata lokaci Liman ya dinga d'aura auren da Sarki ya umarce shi yayi, inda aka fara d'aura auren Mommy da Abdussaboor kan sadaki dubu ɗari, sannan aka d'aura auren Saddiqa da Munir suma a bisa sadaki dubu ɗari cif,daga nan aka d'aura auren Ameerah da Shamsu bisa sadaki nera dubu ashirin cif,kuka Ameerah ta dinga yi tana yi wa Shamsu Allah ya isa a ranta dan kuwa dogarin nan tinda ya tsaya a saman kanta be motsa ba har aka gama, Hamdala Saddiqa da Munir suka yi a tare wanda a dai-dai wannan lokacin suka d'aga kai suka kalli junan su cikin tsananin farin ciki.
Bangaren Abdul da Mommy ma murna ce fal cikin su, Abdul har da kashe mata ido yana yi mata magana daga nesa da labb'an shi, cike da jin kunya Mommy ta sauke kan ta, nasiha sosai Sarki ya gabatar a wajen Baabaa sai gyad'a kai take yi cike da gamsuwa da dik abinda sarki ya faɗa, bakin ta sam ya gaza rufuwa saboda farin ciki,bayan kammala komai ne sarki ya sallame su suka frfito bakin fada mazan na ta gaishe da junan su da taya juna murna Baabaa da Innoh sai hararar juna suke yi Ameerah na ta kuka kamar zata rasa ranta Shamsu na bata hakuri tana zagin shi, Ɗan liti kuwa jin shi yake yi kamar an yi masa albishir da zuwa makka saboda farin ciki.
Abokan shi su Malam Jibo na zaune a bakin fada suna jiran fitowar su dama,aiko suna hango Ɗan liti suka taso suna taya shi murnar siyan hatsi ya ragu a wuyan shi,haqoran shi ya washe gaba ɗaya ya maida kan shi baya ya tsage da wata iriyar dariya, suna nan tsaye Abdul ya kirawo Sultan ya bashi umarnin a je a buɗe gidan shi a gyara dan kuwa a so samun shi ne a daren yau a kai masa matar shi dan kuwa komai akwai a gidan hatta da kayan kitchen ya zuba ashe rabon Mommy ne,in ji cewar Abdul,
"Da zafi-zafi ake dukan qarfe,"
Gaba ɗaya Sultan baya farin ciki da wannan aure da aka daura amma babu yanda zai yi duba da yanda Yayan nashi ke ta farin ciki da auren.
Suna nan tsaye suka jiyo qarar motoci da kid'a na tashi kamar za a tsaga garin, cike da mamaki Alhaji Baban Gida ya hau kallon mutanen wajen yana son sanin shin wa ya kirawo masu DJ daga d'aura auren da ba kowa ne ma ya sani ba?
Munir ma kallon su Ɗan liti yake yi dan a zaton shi daga wajen shi ne da abokan shi dan ya kula babu abinda Ɗan liti ba zai iya aikatawa ba a yau duba da farin cikin da yake ciki na rabuwa da yara har uku da yayi a yau.
Wata qatuwar mota ce fara irin bus ɗin nan ta 'yan makaranta ce ta doso fada sai qananu guda biyu dake take musu baya, kowa tsayawa yayi yaga ikon Allah, cikin masu kallon har da fadawan sarki dake can cikin fada dik sun fito waje dan ganin daga inda kiɗan ke fitowa.
Wani wawan burki bus ɗin nan da qananan motocin suka ci a gaban su Ɗan liti da gudu Ɗan liti da abokan shi suka dare suka bar wajen suka koma gefe suna ganin ikon Allah.
Mata ne suka dinga fitowa daga cikin bus ɗin da 'yan daudu wanda za su kai kimanin mutum goma ko sama da haka, wani hatsabibin Ɗan daudu ne da ya fi kowa zaqewa da iya rawa da kwarkwasa ya je gaban motar Hajiya K'waisa ya buɗe baya, cikin isa da qasaita da iyayi Hajiya K'waisa ta fito tana kallon mutanen wajen a d'age a wulaqance, gefen ta kuwa Samuel ne ya fito dan kuwa yace ba zai taɓa yarda masoyin shi ya je wani qauyen ba tare da shi ba dan be san me zai wakana ba kar a illata masa masoyi.
Motar dake bayan su kuwa Billy ce ta fito da kyar idanun ta duk sun yi luhu-luhu saboda kukan baqin cikin samun labarin auren Mommy da Abdul da aka d'aura wajen Ta Annabi mahaifiyar ta, Man ne ya fito ya tsaya a gefen ta yana bata haƙurin da take ji kamar ta shaqe shi kowa ya huta.
Bayan kowa ya bayyana ya hallara ne Hajiya k'waisa ta d'aga wa DJ hannu, nan take waje yayi tsit kiɗa ya ɗauke muryoyin 'yan daudu da karuwai ta kacame da taya Mommy murnar auren ta da aka d'aura, wannan Ɗan daudu mai rawar kan ne ya tafi da gudu zai rungume Mommy yana faɗin,
"Ahayyyy ragasssss dole ne yau mu raqashe mu bushe da rawa saboda taya ki murna 'yar uwa Allah ya tsamo ki cikin dubun 'yan bariki ya wanke miji daga fadar sarki ya baki a hannu ki yi yanda kika so da shi, hahaiiiii Ragassss,"
Wani wawan mari Abdussaboor ya kafe masa a kunci wanda ya sanya shi ɗauke wuta ya kwasa da gudu ya ɓuya a bayan Hajiya K'waisa yana kyarma cike da tsoro da tashin hankali.
Sarki ne ya fito da kan shi ba aike ba fadawan shi na gyara masa alkyabbar shi har ya iso bakin qofar fadar ya tsaya yana bin kowa da kallo, mutane ya gani danqam a gaban fadar shi kamar ranar hawan Sallah, dan kuwa a wannan lokacin mutanen gari dik sun hallara saboda kiɗan da suka dinga ji na tashi a fada.
Hajiya K'waisa na ganin Sarki ta isa gaban shi ta wani kame guiwa ta rausayar da kai ta kwashi gaisuwa sannan tace................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 42:
Mommy ce ta yi wa Abdussabour rad'a a kunnen shi jikin ta na wata iriyar tsuma hawaye na karakaina a kuncin ta, cike da b'acin rai ya ɗauki waya ya kira sarkin yaqin garin Ba mugu ya bada umarnin a turo masa matasa majiya qarfi da manyan makamai idan da hali a had'o har da mafarauta da karnukan su, yana gama wayar shi ya koma gefen Mommy yana tambayar ta dalilin ta na son a gayyato waɗannan mutanen, cikin kuka tace masa,
"Ka tina sanda ka taimaka min a qasar waje? Ka tina labarin da na baka akan sace ni da aka yi da abinda aka yi min bayan an sace ni? To wancan ɗan daudun shine ya sa komai ya faru,dan Allah Yah Abdul kar ka bari a rabani da kai, idan aka raba mu mutu....."
Cikin sauri Abdul ya rufe mata baki da hannun shi yana jin yanda zuciyar shi ke wani irin bugawa da qarfi,cikin sarqewar numfashi ya kama hannayen ta dika biyun ya riqe idanun su na kallon junan su yace,
"Dan Allah Hadiza ki dena maganar mutuwa, idan kina kiran zaki mutu ji nake yi kamar numfashi na zai tsaya,ba zan taɓa iya ci gaba da rayuwa ba idan babu ke Hadiza, ina son ki,ina qaunar ki, dik wanda zai cutar dake ya shirya faɗa dani,"
Dik abinnan dake faruwa idanun Billy na kan su tana jin wani irin kishi na taso mata, gaba ɗayan su tana son su me zai hana su raɓa ta a cikin rayuwar tasu,su so ta su zauna lafiya dikan su? Ah ah saboda mugun son kan su se suka ware suka yi aure suka barta, ina zata kai dakon soyayyar su dake cikin ranta? Dan haka in dai baza ta samu ɗaya daga cikin su ba to dole ne su tarwatse kowa ya rasa.
Hajiya K'waisa na gama gaishe da sarki ya karb'i abun magana a wajen DJ ya yi gyaran murya zai yi magana, nan take muryar shi ta namiji ta bayyana amma dik da haka sai ya maqale murya kamar mace yace,
"To ni dai ban saba magana gaban sarakai ba balle kuma malaman gari, osshhheee mutanen garin Ba mugu ina miqo gaisuwa,Sweet H baki gayyaci dangin ki na bariki auren ki ba amma dik da haka mu ba za muyi fushi dake ba, gamu mun zo a yi biki a gama damu muna fatan za a karɓe mu hannu bibbiyu hahaiiiii Ragassss !"
Yayi wani fari tare da maqale hannu a hammata ya sake watsa su gaba ya rangad'a guda a cikin abun magana da qarfi 'yan uwan shi 'yan daudu na taya shi rangwad'a da gud'a tare da shewa,Abdul na ganin haka ya isa wajen Hajiya K'waisa ya kife shi da wani gigitaccen marin da yayi sanadiyyar cirewar d'ankunnen shi guda ɗaya gashin idanun shi na bangaren damar da ya karb'i marin ya cire,nan da nan muryar shi ta asalin namiji ta bayyana yace,
"Ya zaka mare ni daga taya ku murna?"
Murmushi Abdul yayi sanda ya hango sarkin yaqin garin Ba mugu tafe da gungun matasa da adduna da gorori har da barandami suna tafe sai bushe-bushe 'yan farauta suke yi da fito kamar za su je daji farauta, karnukan su kuwa sai haki suke yi suna zazzaro harsuna waje da ganin su kaga mayunwatan karnuka.
Idanun 'yan daudu da karuwai ba sai ya hau rarrabuwa ba tsakanin jiran Umarnin Hajiya K'waisa da kuma fusatattun matasan dake tafe fuskokin su na nuna rashin tausayi ko imani.
Cikin ihu ɗan daudun nan mai zaqewa yace,
"Manya da qananan asshohi kowa yayi ta kan shi rai da lafiya shine jarin kowanne mai numfashi,mu kuwa karuwai da 'yan daudu jikin mu shine jarin mu duk wadda ta bari karnuka suka yaga ta kasuwarta ta samu tasgaro"
Ai kafin kace me 'yan daudu da karuwai sun fara d'uruwa a mota suna ihu da kiran sun shiga uku, Hajiya K'waisa na ganin wanda take taqama da su sun fara guduwa ta kalli Billy dake neman taimakon su tana kuka tana faɗin,
"Hajiyata dan Allah kar ku tafi ku barni baku warware wannan tsinannen auren ba, wayyoo Allah na na shiga uku zan yi biyu babu, dan Allah ku taimaka min,"
Wata harara Hajiya k'waisa ta b'alla wa Billy dake jan hannun shi ya fisge yace,
"Ki tabbata baki sake dawowa gidana ba dan kuwa se mun yi gunduwa-gunduwa dake idan kika dawo, shegiya matsiyaciya me qashin tsiya ashe haɗa baki kuka yi da mutanen qauyen naku ku kashe ni da jama'a ta? Matsiyaciya me muguwar hassada to kuwa hassada ce zata kashe ki auren Sweet H ya d'auru kenan mutuwa ce zata raba su,"
Yana gama faɗin haka ya juya dan ya shigewa motar Samuel da ke ta danna masa oda akan su gudu wani kare yayi wufff ya cafke qasan skirt ɗin Hajiya K'waisa, ihuuu ta kurma ta hau yarfe hannu ita a dole korar karen take, ganin wasu karnukan na tafe zuwa wajen ta a guje sai ta zuge zip ɗin skirt ɗin ya faɗi qasa se ga K'waisan alheri daga shi sai ɗan kamfai a guje ya afka motar da tini Samuel ya buɗe masa mazauni ya rufe ta yana haki kamar numfashin shi zai tsaya.
Bus ɗin 'yan daudu kam har ta kusan wuce qofar gidan Ɗan liti dake kan hanya,Samuel na taka motar zai gudu wani mafarauci ya samu gaban motar ya doka mata gorar hannun shi ya qara dukan gilashin motar nan take kuwa ya fashe, ihu Samuel da Hajiya k'waisa suka tsala ya figi motar shi ya bar wajen a guje,yara da manya da mafarauta da mayaqan garin duk sun kwasa da gudu sun bi bayan motocin 'yan daudu da Man ɗin Billy dan kuwa shima be tsaya ba,banda ihu da sowa baka jin komai kowa na faɗin albarkacin bakin shi.
Dattijan da Billy ta taba soyayyar shan minti da Man ɗin ta a gaban su ne suka juyo suna kallon ta suka hau faɗin,
"Amma dai ke 'Yar gidan mai dusa ba 'yar albarka bace,kuma albasa bata yi halin ruwa ba, ana tsaka da abin arziqi ki zo ki kawo mana gungun karuwai da 'yan daudu su tarwatsa mana waje?"
Wani dattijo ne ya karɓe da maganar da faɗin,
"Ahhh ai dole tayi ba tare suka tafi birni ba suke yawon iskanci ai takaicin ta ita Hadiza ta samu miji na nunawa sa'a ita bata samu ba dole ta yi hassada da baqin ciki mana,"
Abdul be gama jin me mutanen nan ke faɗi ba ya kai Mommy wajen Innoh yace su wuce gida kuma da dare zai zo ya ɗauki matar shi,suna tafiya ya shiga cikin gida ya nufi turakar mahaifin shi dan kuwa yaga sanda ya shige ranshi a matuqar bace.
Sultan ne ya sha gaban shi da sauri yace,
"Yaya zan baka shawara kar ka je wajen mai martaba a yanzu, ka jira ya neme ka da kan shi, sannan ka jinkirta tarewar Mommy har sai kaji daga wajen su Innah yanzu kaje ka sallami Sarkin yaqi sun dawo da jama'ar shi suna ta yi maka kirari a waje,"
Cike da damuwa Abdussabour ya zira hannun shi a aljihu ya deb'o kuɗi masu yawa ya baiwa Sultan yace,
"Je ka sallame su,"
Fita Sultan yayi yana tausayawa yayan nashi bisa abubuwan dake faruwa a game da rayuwar shi cikin kwanakin nan,shi kuwa Abdul d'akin shi ya wuce yana jiyo kukan Billy Innah Laminde na lallashinta tana so tayi shiru ta sanar da ita abinda ke faruwa.
Sai da Billy ta sha kukan baqin cikin abinda ke faruwa sannan ta zaro wayar ta cike da mugunta ta shiga file ɗin da ta yi saving hotuna da videos ɗin Mommy da tsohon accounts ɗin ta na social Media da ta dinga screenshot tana ajiyewa a wayar ta ta miqa wa Innah Laminde wayar tana nuna mata hotuna da videos ɗin Mommy, wasu tsaye take tsirara babu ko ƙyalle a jikin ta,wani tana wanka kwance cikin kwamin wanka, wani kuma tana shafa mai, wani kwance take tana kallon videos ɗin banza tana biyawa kanta buqata, Innah Laminde na ganin haka ta saki wayar ta faɗi qasa jikin ta na rawa hankalin ta a tashe tace,
"Wannan yarinyar dama haka take shine Abdul ɗina ya aure ta? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,wannan wace iriyar duniya muke ciki? Wannan wacce iriyar rayuwa muke ciki? Na shiga uku ni Laminde me na gama gani yanzu?"
Hanci Billy ta ja ta qara goge idanun ta tace,
"Ai baki ga komai ba game da Hadiza Innah, yarinyar nan aikatau na sama mata a gidan mutanen kirki amma taqi zama ta koma rayuwa da 'yan daudu da karuwai, har qasar waje ta tafi ta hanyar karuwanci,ai a can