Showing 147001 words to 150000 words out of 276165 words

Chapter 50 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

ni? Banda abun ka sai kace mata abinci muke so ba ruwan zafi ba,"

"Ke tafi can ana neman yanda za a rufawa kai asiri kina hauka,da an kawo ruwan zafi an kai maki ki samu kiyi wanka ko ki zubar bayan kin jima a band'akin,idan ba kiyi haka ba zata gane, kuma ki dinga tafiya kina dingishi kin dai ji na faɗa maki, ba dan asiri na zai tonu ba nima yasin kyale ki zan su gane, ke ana gabar kina yamma wai abinci, mtswww."

Harara ta zabga masa sannan ta juya masa baya,can ta jiyo shi yana faɗin,

"Aikin banza mamalam, da an kawo ki da gara yanda ake yiwa kowacce yarinya da zaki zauna da yunwa ne? Ko nima da ban fita kunyar abokai na ba?"

Cike da masifa Ameerah ta sauka daga saman gadon ta tsaya a gaban shi ta kama ƙugu tace,

"Kai fa ba tsoron ka nake ji ba, idan ka kuskura ka faɗa min cuta zan faɗa maka mutuwa,nawa ka bani kud'in sadakin da za a yi maka gara? Gara kuma ai ka riga ka gama kwasar ta a soron gidan mu idan ka manta na tuna maka,"

Shiru Shamsu yayi kamar ruwa ya ci shi, shi sai yanzu yake mamaki da tunanin ma ya aka yi ya dinga jin abinda yaji akan Ameerah kafin ya aure ta, wani irin abu yake ji a kan shi da zuciyar shi mai nauyi a baya,ji ya dinga yi idan bai aure ta ba numfashin shi zai iya tsayawa,har daren jiya da ya shiga ɗakin yana jin shauƙin son ta da ƙaunar ta sai dai ya rasa me yasa suna gama kusantar junan su yaji kamar an zare masa wannan abun akan shi da zuciyar shi, mamakin yanda aka yi ya nace zai aure tane ya mamaye shi a wannan lokacin, dan haka dik masifar da take yi ma bai ji ta ba, har ta gama ta gaji ta koma ta zauna tana maida numfashi kamar wata kumurcin maciji.

Suna nan zaune har gari ya waye basu da niyyar fita suyi alwala suyi sallah,Ummahn Billy ce ta yi musu sallama ta buga d'akin,cikin zumb'ura baki Ameerah ta miƙe zata fita, da sauri Shamsu ya fizge ta ya miƙa mata mayafi yace,

"Ki yafa akan ki mana ko a haka zaki fita ƙandar-ƙandar gaban surukar ki? Sauran kuma ki dinga tafiya kamar doki ki rusa mana shirin mu,"

Hararar shi tayi ta zabga masa tsaki sannan ta buɗe ƙofa ta fita kanta a ƙasa,murmushi Ummahn Billy tayi tace,

"Muje na raka ki bayin na nuna maki yanda za kiyi, sannu ko?"

A hankali Ameerah ke tafiya kamar da gaske,suna shiga bayi Ummah ta nuna mata yanda zata gasa kanta, tana gamawa ta fita ta bata waje dan ta shiga ruwan zafin.

Sai da Ameerah ta b'ata lokaci sosai sannan ta fito tana jin kunyar Ummahn Billy, wanda a wannan lokacin kallon da Ummahn ke yi mata ne ke sanya ta jin kunyar tata, d'aki ta shiga ta tarar da Shamsu ya fita baya nan, cikin sauri ta sauya kayan jikin ta ba tare da ta shafa roll on ba ta fesa turare ta shafa mai, zama tayi ta tsara kwalliya dai-dai iyawar ta ta zabga hoda,tana gamawa ta kashe d'auri da ɗankwalin doguwar abayar da ta saka,tunani ta fara yi shin me ya kamata tayi ne? Yunwa take ji kamar taci babu.

Tana nan zaune shamsu ya dawo ɗauke da food flask d'in da ta tabbata a wajen mahaifiyar shi ya same shi tinda ita bata da kayan kitchen, ajiyewa yayi a gaban ta yana ɓata rai, bai ce mata komai ba ya samu waje ya zauna ya buɗe,masa ce da miya da nama a ciki, cikin sauri Ameerah ta sauka itama ta saka hannu suka fara ci tare.

Tin shamsu na b'ata rai sai ya dawo yana sakar mata fuska, a haka suka gama cin masar nan suka zauna zaman hira, gud'a suka ji an zabga ana yi wa Shamsu da Ameerah kirari irin na yabo saboda kama mutuncin su da suka yi kafin aure.

Ameerah ce ta ƙunshe dariya Shamsu ya doka tsaki yace,

"Ke fa naga alama baki da hankali,gani kike yi abinda kika aikata ba komai bane ko?"

Cikin ɓacin rai ta kalle shi ta qanqance ido tace,

"Kasan Allah ka sake kira na mara hankali se na yi maka haukan gaske, da alama baka san wacece ni ba hyi yasa kake ta kira na da mara hankali,"

Tsaki yayi ya tashi ya fita ya bar gidan gaba ɗaya, yana fita tsakar gida dangin mahaifin shi da na mahaifiyar shi da suka samu halartar gudanar da bikin al'adar tasu ne suka hau tsokanar shi, har d'akin Ameerah suka shiga suka fito da ita aka dasa tabarma da kujera,mayafin ta aka rufa mata aka buɗe mata shi kowa ya shigo ya jefa kud'in shi na taya su murnar kare mutuncin su da suka yi.

Nan take wasu mata suka hau ƙusƙus suna faɗin,

"Kin ga ana zaton wuta a maƙera sai gashi an same ta a masaƙa, kin ga yayarta da kowa kewa kallon ta Allah itace ta tara mana karuwai da 'yan daudu a ƙauyen nan, tinda aka kai ta shiru kake ji babu wanda ya gudanar da al'ada tinda ai gidan Sarki fulani ne,sai gashi 'yar talla ta kawo mutuncin ta gidan miji,"

Dayar ce tayi ƙasa da murya tace,

"Ai dama haka Allah ke lamarin shi,Allah dai ya basu zaman lafiya,"

Haka aka dinga jefawa Ameerah Hamsin ɗari, masu bayarwa da yawa ne suka jefa dari biyu, abu kamar wasa sai gashi an tara kuɗi masu tarin yawa.

Taro na watsewa Ameerah ta tattara kuɗi cikin ladabi ta kaiwa surukar ta ta durƙusa har ƙasa kamar ta Allah ta miƙa mata tace,

"Ummah gashi,"

Murmushi Ummahn Billy tayi tace,

"Ah ah ai wannan naku ne ke da mijin ki, maza tattara ki kai muku Allah yayi muku albarka,"

"Ameeen"

Ameerah tace ta tattare kuɗi tayi gaba dasu zuwa d'akin ta, ƙanwar Billy Faridah da ta san Ameerah sosai sai mamaki take yi da aka ce Ameerah ta kawo mutuncin ta gidan miji lafiya.

*************************

A can Australia kuwa Billy ta sha mamakin ganin irin gidan da Amy ta mallaka ba wai haya ba kamar yanda da yawan turawa ke hayar gida da motar hawa da sauran abubuwan more rayuwa, hakan ya nuna mata cewar Amy fa ta kama ƙasa da nerori har da daloli,wani murmushi ta saki dan tunawa da plan ɗin ta..........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI












RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨





*SANARWA !*

*Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....*

*MAZAUNA GIDA 300*
*ƳAN ABUJA 300*
*A GARIN MU 300*
*KAI NE JARUMI 300*
*KUN MAKARO 300*
*TAUBASHI 300*

*KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻*
*IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.*


PAGE 58:





Tafe take a makeken gidan dake da sama da ƙasa ko ina a gyare fess kamar da mutane a cikin gidan,tinda Billy ke yawon ta daga gida Nigeria zuwa ƙasashen Africa da ta taɓa zuwa bata taɓa ganin gida mai kyan wannan ba.

Komai na gidan kalar brown ne da fari, hatta da kujerun dake gidan kalar brown ne,wani irin ƙamshi ke tashi na musamman wanda ya sanya ta jin wani irin yanayi mai sanya nishad'i,wayar ta ta d'akko tana yi wa kanta da gidan video, a dai-dai jikin table ɗin da aka kunna wasu candles masu kyau ta tsaya, ɗaukan kwalbar tayi ta shinshina, wani irin ƙamshi ne ya ziyarci hancin ta, cikin sauri ta buɗe idanun ta da ta kulle ta hau juya candle ɗin tana mamakin jin ƙamshi na tashi a jikin shi, Amy ce ta fito bayan ta ajiye musu kayan su a bedroom ta samu Billy na mamakin ƙamshin da take ji a jikin candle, cikin sauri ta kashe videon da take ɗauka ta kalli Amy tace,

"Kin ga wani magic candle anan me ƙamshi?"

Murmushi Amy tayi ta rungume Billy ta baya sannan ta ce,

"Ba magic candle bane wannan romantic candle ne,kin san nawa ake siyar da shi kuwa? Wannan na musamman ne, ni da kaina na sa campanin dake kula da gyaran gidan nan su saka min shi, na san zaki so ƙamshin,"

"Woww ! Ban taɓa sanin kina da wannan capacity ɗin ba, yanzu da gaske kina nufin wannan gidan da motar da aka kawo mu nan dika naki ne?"

Murmushi Amy tayi ta saki Billy ta isa gaban makeken fridge ɗin da ke manne a jikin gini irin mai ƙofa biyun nan ta buɗe,tsayawa tayi tana kallon abinda zata d'akko can idanun ta ya sauka akan wata kwalbar lemo, dakkowa tayi ta buɗe locker ta d'akko glass cups guda biyu ta tsiyaya musu ta miƙawa Billy sannan ta kurɓi nata sau biyu ta ajiye, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Billy dake jiran jin amsar ta tace,

"Billy ba abun mamaki bane dan ina da irin waɗannan kuɗaɗen,a lokacin da na bar gidan k'waisa na fara zaman kai na anan na haɗu da wani Alhaji wanda ya so cutar dani ta hanyar siyar dani ga wata ƙungiyar matan dake yin lesbianism dake a Miami, kuɗi ya samu ba na wasa ba  a lokacin saboda sun yaba da kyawu na da diri na sosai,kin dai ganni kyakkyawar bafulatana ce bani da makusa a jiki na sai dai idan baka ra'ayin irin jiki na ne kawai zaka ga ban yi maka ba. Wannan dalilin ne yasa mata da yawa suka dinga bina a ƙungiyar har daga ƙarshe wata da ta fi kowa kuɗi a cikin su mai suna Arica ta aure ni muka gina gidan mu cike da soyayya mai ƙarfi cike da gaskiya da riƙon amana,Arica na matuƙar sona nima kuma ina son ta sosai,saboda tana kyautata min, ta shagwab'a ni da dukiya sosai komai nake so shi nake samu, kullum cikin saya min gifts take masu tsada,Arica itace shugabar ƙungiyar da aka saida ni,ita ke kula da komai na ƙungiyar, kama daga ci gaban ƙungiyar da fafutukar samarwa da matan dake cikin ta 'yancin kai,a haka muka ci gaba da rayuwa har muka dawo Austaraliya, wannan gidan nata ne da ta siya na musamman saboda ni,rayuwa muke yi cike da so da ƙauna har muka fara shirin adapting yara mu riƙe a matsayin 'ya'yan mu,muna haka kwatsam Arica ta fara rashin lafiya,abu kamar wasa daga ciwon ciki muka je asibiti aka duba ta wai tana da lung cancer,ashe Arica ta jima da sanin tana da wannan ciwon amma bata sanar da kowa ba,wannan dalilin ne yasa muka tattara muka koma asibiti domin bata kulawa kafin lokacin ta yayi.

Bayan mutuwar Arica ne na gaji dukiya mai yawa a wajen ta, ciki har da wannan gidan da muke ciki da wani gida dake ƙauyen su amma na barwa iyayen ta shi dan bani da buƙatar shi ni,ina da kuɗi kud'in da suke da matuƙar yawa Billy,daga baya mun dawo muna mutunci da wannan Alhajin sosai wani lokacin ma nakan haɗa shi da yaran da yake ɗauka ya siyar nima ya bani wani abu a ciki, shi yasa kika ga ko a Nigeria bana cikin matsalar kud'ad'e."

Baya Amy tayi sannan ta durƙusa a gaban Billy ta zaro zobe mai ɗauke da dutsen diamond a jiki ta kama hannun Billy dake cikin shock tace,

"Billy ina so ki yi min alfarmar zama matata wadda zamu rayu cikin so da ƙaunar juna har mutuwa ta raba mu,"

Cikin wani irin shauƙi Billy ta hau tsalle ta manta da tunanin da ta fara yi akan Amy da Alhajin da ta bata labari a yanzu sai ta hau cewa,

"Na amince zan aure ki,"

Rungume juna suka yi, Amy ta sake buɗe fridge ta ɗakko musu shampain suka jijjiga tare da buɗe kwalbar nan take kumfar ta hau zuba suna ihu suka zuba a cups suka hau sha.

A ranar Billy da Amy sun raya daren cikin nuna wa junan su yanda suke son junan su sosai. Washegari da safe kuwa bayan sun yi wanka sun shirya sai suka wuce restaurant dan cin abinci,sai da suka ci suka ƙoshi ne Amy ta ɗauke su suka wuce wajen aski, suna zuwa Billy taga yanda matan dake askin suka sha wata iriyar kwalliya da shiga kamar ba mutane ba, kawunan wasun su babu gashi, wasu kuma rabi da gashi rabi babu, wasu kuma kan sol babu ko ɗigon gashi,ga piercing sun sha a harshe da kumatu wasu har a leb'unan su,dik yanda Billy ta zaci zata ga turawan sai abun ya wuce tunanin ta, cike da ƙauyanci take bin su da kallo har ma ta kai hannu ta taɓa abinda taga tana da buƙatar tabbatar da ingancin wanzuwar shi a jikin 'yan Adam ɗin dake gaban ta.

Wata magazine Amy ta ɗauka ta samu kujera ta zauna tare da yi wa Billy nuni da ta zauna a cinyar ta su zaɓi kalar askin da za a yi wa Amy ɗin,zaman su ke da wuya ɗaya daga cikin masu askin ta kula da zoben dake hannun Billy, cikin ihun murna ta kalli Amy tace,

"Oh my God are you two engaged?"

Cike da murmushi da nuna farin ciki Amy tace,

"Yes we are engaged."

"Awwww ! Congratulations."

Nan da nan matan dake wajen suka dinga taya su murna, wanda suka yi aure a cikin su da junan su sai suka hau surutai suna sanar da Amy yanda idan suka yi aure za su ji daɗin rayuwar su da sauran surutan da already Amy ta riga da ta san su, wata ce ta zo ta tsaida hirar ta hanyar sanar da su Amy fa ita ce tsohuwar matar Arica,nan take suka dinga mamaki, kowa ta bar wajen suka hau aikin dake gaban su.

Wani aski Billy ta zab'a a yi wa Amy wanda za a aske kanta ta baya sosai ta gaba a gyara shi a ƙara masa gashi a d'aure mata shi, babu musu kuwa Amy ta zauna aka hau yi mata gyaran kai ana gamawa aka hau aski,sanda aka gama yi mata Billy sai ta rungume ta suka dinga yiwa junan su hotuna da videos kafin daga baya su sallame su su tafi.

Shopping Amy ta kai su suyi na abubuwan da za su buƙata na gida, da siyayyar auren su da suke su suyi shi nan da kwana uku, dan kuwa basa son su jima ba tare da sun mallaki junan su ba ta hanyar aure.

Rabbi najjina wa ahluna mimma ya'amaloon, tabbas rayuwar generation ɗin nan namu na cikin babban hatsari, 'yan uwa na kuna yi wa kawunan ku addu'ar neman tsari daga zama cikin ɗaya daga lalatattun wannan zamani da wanda zai zo a gaban mu? Zuri'ar ku fa? Idan kuma kuna yi to ku dage ku ƙara akan nada, sannan a haɗa da dikkan musulmi, Allah ka shirya mu ka yi mana tsari da mummunan farko tsakiya da ƙarshe da bayan rayuwar mu Amin.

Haka rayuwar su Billy ta kasance cikin kashe kud'ad'e da jin daɗin rayuwa, Amy tayi wa Billy register da ƙungiyar su ta mata masu auren jinsi da wajen da take zuwa motsa jiki,sun kammala da siyayyar kayan da za su saka ranar auren su har ma sun yi booking wajen da za a d'aura auren nasu wanda mad'aura auren arna ne. (Inda zaku tabbatar abun bana hankali bane sab'on Allah'n ake so a aikata da gasken-gaske kenan my beautiful fiful)

A washegarin ranar d'aurin auren sune Amy ta ɗauki Billy a mota dan ta kai ta saloon domin a yi mata gyaran gashi hannu da kuma ƙafafun ta, a hanyar su ta tafiya ne Billy tayi shiru tana nazarin irin rayuwar da ta taso a cikinta ta talauci, da kuma lokacin da mahaifin su ya fara sana'ar saida dusa har Allah ya sanya wa kasuwancin shi albarka yake iya ciyar da gidan shi har ma ya taimaka wa wasu, dik daren duniya idan za a yi abinci sai an saka nama ko kifi, amma dik da haka ita dai hakan bai yi mata ba tana buƙatar ƙari,a haka ta samu Baban ta ya siya mata waya har ta fara WhatsApp, daga shiga groups na batsa da tura videos na batsa ta haɗu da wata da ta hilace ta ta koya mata yanda ake neman mata har da maza ma,a hankali ta kwad'aita mata zuwa kano dan ta haɗa ta da manyan mutane su dinga bata kuɗi sosai,da wannan ta samu ta yiwa Baban ta ƙaryar da ya barta zuwa kano aikatau.

Ranar da ta isa kano a gidan karuwai ta sauka ta fara karuwanci irin na ƙazaman karuwan nan ana biyan ta kuɗi kaɗan har ta haɗu da K'waisa ya ɗauke ta a gidan,tin daga nan ta shigo gari take babbar harka.

Man shine saurayin da ta fara jin tana so ba wai iya son bariki ba kawai,saboda tafi jin daɗin mu'amala da shi sannan yana sakar mata kuɗi, daga baya samun shi ya ragu ba kamar da ba amma dai still yana bata dik abinda yake da shi, tana tsaka da tinanin taji mota ta tsaya, kallon wajen da suke tayi sai taga a gefen titi ne basu isa inda za su je ɗin ba,kallon Amy tayi taga damuwa sosai a saman fuskar Amy sai ta saki murmushi ta ce,

"Lafiya naga mun tsaya anan?"

"Ke zan tambaya lafiya naga kin shiga tunani mai zurfi har ina ta yi maki magana baki sani ba? Are you having second thoughts about this....."

"No i am not ! na yarda na amince zan aure ki,idan har kin amince kema zaki biya min dikkan buƙatuna da na nema a wajen ki,kin san menene matsala ta, kuma daga dikkan alamu da yanda kike shagwab'a ni na san ba zan yi dana sanin auren ki ba,"

Murmushi Amy tayi ta duƙa ta sumbaci Billy sannan ta tada mota suka ci gaba da tafiya, suna isa wata mata gajera siririya fara tass mai dogon gashi ta isa wajen su ta nuna masu inda za su zauna, babu b'ata lokaci ta hau wanke gashin Billy da bashi da tsaho sai cika, cikin awanni biyu da rabi aka gama gyara mata gashi da hannayen ta da ƙafafun ta, kallon ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login