Showing 195001 words to 198000 words out of 276165 words

Chapter 66 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

musamman mahaifiya ta wadda bata son ko ƙuda ya taɓa ni,ta ɓangaren mahaifina kuwa dik irin soyayyar da yake yi mini bata rufe masa ido ya tsawatar min idan nayi ba daidai ba sannan ya bani ilimi na addini gwargwadon iyawar shi.

A lokacin da na cika shekara goma sha ɗaya a duniya mahaifina ya rasu,ƙannen mahaifi na bayan arba'in suka zo dan su karɓe ni daga hannun mahaifiya ta sai taƙi amincewa,bana taɓa mantawa tana kuka take cewa Baffana ya bar mata ni zata iya kula dani, tinda tana sana'ar saida kayan gwanjo,idan yaso sai su dinga zuwa suna gani na akai-akai tinda bamu da nisa da juna,amma sam suka ƙi amincewa da roƙon ta,daga ƙarshe ƙanin mahaifina Baffa Iliyasu ya samu nasarar karɓata daga hannun mahaifiya ta, ina kuka tana kuka aka raba mu, ya kai ni gidan shi mai mata biyu da yara bakwai.

A hankali Baffah Iliyasu ya karɓe gado na daga hannun Mamana da zummar shi zai ci gaba da kula da cina, shana, makaranta ta,da dik wani abu da zan buƙata na yau da gobe, idan mahaifiyata na son gani na zata iya zuwa dik ƙarshen mako ta ganni, idan kuma aka yi hutun term sai naje nayi hutu a wajen ta,ba dan mun so ba haka muka haƙura na fara zuwa makarantar da yaran shi suke zuwa yana biyan kud'in makaranta na da dik abinda za a buƙata na yau da gobe a cikin gado na kamar yanda ya faɗa.

Kowa dai ya san zara bata barin dami,dan haka a hankali kud'in gado na ya tasamma ƙarewa gashi ko sakandire ban gama ba, a wancan lokacin dika-dika a JSS2 nake,Mamana na yawan kawo min ziyara, idan zata zo zata kawo min dik wani abu da take dashi da ta san zai faranta min rai,wani lokacin tana yin kara ta yowa yaran gidan tsaraba,bani da matsalar komai da matan Baffah na,dan kuwa babu mai saka ni ko ta hana ni,ko aiki ne yaran su suke sakawa,dik yanda Mamana ta dinga roƙon su akan su dinga sanya ni aikace-aikacen gida saboda ni macece watarana za su yi min amfani, sai su ƙi da nufin kar ace suna zalintar marainiya ko shara na ɗauka zan yi masu sai a karɓe wanke-wanke kuwa dama ko sau ɗaya ba a taɓa barin nayi ba,iyakaci na naci na sha, na je makaranta na wanke uniform d'ina da kaya na shikenan aikin da nake yi.

Ana haka har na shiga JSS3,a wannan lokacin ne dik wata siffar ƴa mace da ƙira irin ta budurci ta bayyana a jiki na, dik inda na shiga sai mutane sun tanka kyauna da ƙira ta,kin dai ga yanda nake,to a baya na fi haka kyau da tsawon gashi, alhamdulillah jikin Mamana nayo ban baro ta ba a komai,tinda Baffah na ya ƙyalla ido yaga irin kyawun da na taso da shi, sai ya janye maganar shi na dena zuwa na makarantar boko da ya yi,yace na ci gaba da zuwa zai ɗauki nauyi ai da shi da Malam dik ɗaya ne.

A baya ya cire ni a islamiyya yace tinda na sauke ƙur'ani da hadisai sai dai ma na koyawa wasu ai, ba zai ɓarnatar da kud'in shi a banza akai na ba, ban san ya aka yi ba ya sanya ni a makarantar dare da kanshi wai ilimi baya kaɗan,ba ni kaɗai ba hatta mahaifiya ta abun yayi mata daɗi sosai,haka ta taho ƙafa da ƙafa dan yi masa godiya,Baffah kuwa ya nuna mata ai babu komai yiwa kai ne,kula dani ne kawai zai yi ya riƙe zumuncin dake tsakanin shi da Malam.

Haka na dinga zuwa makarantar boko da islamiyya,wanda gaba ɗaya nafi bada ƙarfi na akan ilimin islama, wannan shine dalilin da yasa na sake dawowa baya ina tisa haddata dan nima in samu damar shiga gasar musabaƙa da ake yi dik shekara,ina jin daɗi da sha'awar yara ƙanana dake shiga gasar musabaƙa kuma suyi nasara,dan haka sai na maƙale wa wani malamin mu malam Isa ba dan komai ba sai dan yanda yake da tarin ilimin addini, nayi imani da Allah zai taimaka min wajen cikar buri na.

Tin daga nan idan an tashi zan ƙara minti goma in bawa Malam Isa hadda ta sannan na koma gida,ana haka watarana da dare mummunan al'amari ya afku akai na,baƙin daren da ba zan taɓa mance shi ba har abada a rayuwa ta, na fito daga Islamiyya bayan mutane sun ragu sosai, sai tsirarun da ba a rasa ba, na kama hanyar komawa gida ina tafe ina muraji'ar karatuna,sai naji an yi sama dani an damƙe min baki na, ƙur'ani na da sauran littattafai na a wajen suka watse,ba a dire ni a ko ina ba sai a wani kango da babu kowa,a wannan baƙin daren mutumin da na baiwa mahimmanci a rayuwa ta ya cire tsoron Allah a ran shi yayi min fyad'e,a wannan daren na rasa budurci na,a wannan daren nayi sallama da farin ciki na faɗa rayuwar baƙin ciki."

Kukan da Any bata taɓa zaton zata sake yi ba a rayuwar ta ta fashe dashi,ta jima da sallama rayuwar da ta wuce a baya, ta yanda ko ta tuna bata kokawa, sai gashi a yau zuciyar ta tayi rauni,ta karye har tana zubar da hawaye,cikin share hawaye Billy tace,

"Kina nufin Malam Isa shine yayi maki wannan aika-aikar? Lallai duniya babu yarda."

Cikin wani irin murmushin takaici Any ta kurɓi juice ɗin dake glass cup ɗin gaban ta,kafin ta ajiye ta miƙe tsaye ta taka zuwa kujerar dake fuskantar Billy ta ce,

"Ai da Malam Isa ne yayi min fyad'e da da sauƙi Billy,kin san wanda yayi min fyad'e kuwa Billy?"

Girgiza kai Billy tayi alamar bata sani ba,murmushi Any ta sake yi sannan ta ce,

"Baffah Ilyasu shine yayi min fyad'e Bilkisu,yana gama abinda zai yi dani sai ya jawo ni ya fito dani tsakiyar hanya ya yar dani,idanu na sun kumbura saboda kukan da na sha,cikin hawayen dake zuba mota tazo wucewa a wannan daren ta haske min Baffah na da suke uwa ɗaya uba ɗaya da Malam mahaifi na yana ƙoƙarin buga machine ɗin shi ya gudu.

Kar ki manta fa yana da yara mata sa'anni na da wanda suka girme ni, da wanda na girma,saboda dika yaran shi mata ne bashi da namiji ko ɗaya,ya manta girman zumunci da alaƙar dake tsakanin shi da mahaifi na, ya manta haƙƙin maraici da amanar da mahaifiya ta ta damƙa masa,ina nan kwance cikin mawuyacin hali wata dattijuwa dake a layin mu tazo wucewa ita da jikan ta ta taso daga wajen da take saida kayayyakin ta na tsofaffi irin su daddawa kuka da sauran su,suna tsaka da hira da jikan ta ta ganni a cikin wannan mugun halin ta taimaka min ita da jikan ta suka kai ni gida.

Tinda aka kaini a wannan halin matan Baffah na suke min faɗa da masifa tare da kira na da sunaye kala-kala na karuwanci da bin mazan banza,cikin rashin tsoron Allah Baffah na ya fito daga ɗaki kamar bashi ba, da alama ma yayi wanka ne ya sauya kaya dan kuwa sai ƙamshin man shafi yake ya fito yana muzurai tare da cin alwashin washegari sai na faɗa masa inda naje yawon iskanci.

Dik yanda tsohuwar nan taso ta nuna masu fyad'e aka yi min sun ƙi fahimta,banda zagi da cin mutuncin iyaye na babu abinda suke yi, hatta yaran su ba a bar su a baya ba wajen zagi na da zagin iyaye na, tare da faɗin dama Malam ne ke yabo na ba tare da yasan mugun iri ya haifa ba.

A cikin daren nan tsohuwar nan ta aika yaro wajen Mamana ya sanar da ita tazo gidan Baffah babu lafiya, cikin abinda bai kai minti ashirin ba ta iso gidan,tinda tayi ido biyu da abinda ya same ni ta yanke jiki ta faɗi bata sake shurawa ba, wannan ne yayi sanadiyyar da ni kaina na suma saboda yanda naji mata sun fasa ihun Mamana ta rasu,ban sake farkawa ba sai washegari a gadon asibiti.

Ko da na farfaɗo sai na kula babu kowa akai na, ni kaɗai ce a kwance a asibitin bani da kowa sai Allah na,likitar da ta duba ni ce ta tausaya min sannan tace zasu sallame ni tinda na farfaɗo kuma an yi min ɗinki a kasa na,sai na tafi gida wanda ya kawo ni ya biya kud'in komai,a lokacin da aka sallame ni na fito harabar asibitin Billy kallon dika mazan wajen nake yi a matsayin azzalumai,kallon su nake a matsayin mazinata,kallon su nake yi a matsayin maciya amana,na kasa goge fuskar baffahna a cikin kai na, sai a wannan lokacin nake tuna sanda yake yi min fyad'e da irin kalaman da yayi akan ya jima yana son mahaifiya ta bai samu ba, to yanzu gani nama fi mahaifiyar tawa kyau da komai dan haka shi ya samu wajen hutawa.

Kuka na durkushe a wajen ina tayi kafin daga bisani na mike na bar asibitin,na gama yanke hukunci ba zan koma gidan baffah ba, zan shiga duniya na ƙarasa abinda ya fara, ba kuma zan manta da shi ba zan dawo gare shi domin ɗaukan fansa, wannan shine dalilin da ya sa na faɗa bariki,har na haɗu da Hajiya K'waisa a gidan karuwai ta taimaka min,daga ƙarshe da na haɗu da Alhaji ya nuna min hanyar safarar mata da maza zuwa turai da dukiyar da ake samu,sai na bar gidan K'waisa na dawo na kafa tawa daular,kin san da waɗanne mata na fara kasuwanci na na farko Billy?"

Gyad'a kai Billy dake ta matsar k'walla tayi alamar bata sani ba, cike da wani irin nishad'i irin na wanda ya ɗauki fansa Any tace,

"Da babbar ƴar Baffana na fara samun kuɗin safarar mata,na sace tane a ranar da aka ɗaura auren ta da dare za a kai ta gidan miji,ƙasar Columbia na kai ta na siyar,da suka gaji da ita suka dirka mata ƙwayoyi ta sheƙa ƙiyama,bayan ita sai na sace autar shi,daga ita na sace mai bi wa babbar ƴar shi,a haka sai da na sace yaran shi mata kafff,kuma a shekarar ne aka haifa masa yaro namiji,a shekarar ne na baiwa wani yaro mai shaye-shaye a unguwar kuɗi ya nemi jaririn ta baya ya farke shi ya gudo waje na na aika shi ƙasar waje,yanzu haka ya zama babban yaro na,sai daya girma sosai ya zama gawurtacce na sake aika shi ya yi wa Kawu na dake jinya saboda damuwa da tashin hankalin abinda ke faruwa da rayuwar shi fyad'e,yayi masa kaca-kaca, dake Allah bai yi a lokacin zai rasu ba,sai yayi tsawon rai har sai da naje na same shi a d'aki yana jinya,na cika matan shi da kuɗi da kayan abinci,suka bamu waje na zauna na bashi labarin dik abinda yayi min da irin fansar da na ɗauka akan shi,sannan na tabbatar masa idan har yana raye sai ya yi shaidar ɗauke matan shi biyu da suka rage na sayar da su suma.

A wannan lokacin ne ya fara wani irin nishi kamar wanda ake zarewa rai,ina ganin haka nayi musu sallama na wuce,Baffah Iliyasu bai rasu ba Billy sai da ya ƙara wata uku da sati biyu da kwana ɗaya a duniya yana shan azaba.

Wannan itace Any Billy,bana jin tsoron kowa,bana shakkar kowa,ina da ilimin addini da na zamani dai-dai misali,ni ba jahila bace na san Allah,na san irin azabar da ya tanadar wa dik wanda ya aikata aiki irin nawa, Allah da kan shi yace kar mu kusanci zina, balle mu aikata ta,ni ban kusance ta ba, jefa ni aka yi cikin ta ta karfi da yaji,dan haka zunubin abinda nake aikatawa zai koma zuwa ga wanda ya jefa ni cikin ta."

Ajiyar zuciya Billy ta sauke,cikin sanyin murya tace,

"Amma kuma ai kin balaga,kema zaki karb'i naki sakamakon zunubin Any,me yasa kin san irin ayoyi da hadisan da kika dinga jawow waccan baiwar Allah'n kuma kika zama haka? Da ace ni ce nake da ilimin da Allah ya baki da ban kawo haka ba,labarin ki ya taɓa zuciya ta ya sa na fara tunanin shin wai menene ma silar fara nawa karuwancin? Kwad'ayi ko son zuciya? Butulcewa Allah da rashin gode masa ko kuma tsananin sha'awa ce da gasa? Dai-dai misali Allah ya horewa mahaifi na abinda zamu ci,ba a taɓa girki a gidan mu babu nama, musamman a tuwon dare,idan ba a saka nama ba za a saka kifi,ke watarana ma Baba na siyo mana kaza gasasshiya ko tsire ko balangu ko kilishi.

Daga zuwa aikatau Hajiya K'waisa ta haɗa ni da Man,daga nan ne rayuwa ta ta sauya na fara bin maza da mata kamar karya,a hankali na dena aiki na zama ta hannun daman Hajiya,iyaye na basu taɓa tambayar dalilin daya sanya kud'in aiki na yin yawa ba,da ace sun bi diddigi a lokacin da sun gano inda matsalar take sun yi wa tufkar hanci,da ace ko sau ɗaya sun wanke ƙafa sun je sun ga gidan da nake aikatau da ban zama international karuwa ba."

Kuka sosai Billy keyi wanda za a iya kiran shi da kukan nadama,ganin haka ne ya sanya Any tashi ta faki idon Billy ta jefa mata ƙwaya a lemo,sai da ta hau lallashin ta tana yi mata magana mai daɗi sannan ta bata lemon ta sha,tana gama sha babu jimawa wata iriyar sha'awa ta taso mata,rasa inda zata saka kanta tayi,dik yanda taso ta bijirewa jikin ta dan kar ta komawa babban zunubin da suke aikatawa sai ta kasa, dole ta sake wa Any jiki suka gurji junan su son ran su.

Basu suka rabu da junan su ba sai tsakiyar dare,bayan komai ya lafa ne Billy ta tashi daga saman kujerar da suke ta kalli Any da tayi bacci,ta wuce d'aki zuciyar ta na yi mata saƙe-saƙe kala-kala.

Wanka ta fara yi sannan ta haye gado ta jawo wayar ta,direct Facebook ta shiga dan kuwa anan ne take ganin shamsu lokuta da dama,yau ma kuwa ta ci karo da sabon posting ɗin shi shi da babyn su da Ameerah,sun sha kwalliya sun yi kyau sosai abun su, nan take kuka mai tsananin ƙarfi ya ƙwace mata,kuka ta dinga yi har bata san sanda ta nemo No Mahaifin ta ba ta danna masa kira...........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI













RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨












PAGE 80:










"Babaa."

Billy ta furta cikin wani irin matsanancin kukan da bata san sanda ya taho mata ba,cikin yanayi na damuwa Mai Dusa ya sauke wayar shi daga kunnen shi ya kalli sababbin lambobin da bai sani ba,sannan ya sake mayarwa kunnen nashi, tabbas muryar Bilkisun shi ce ya jiyo a cikin wayar,cikin sauri ya furta,

"Bilkisu ! Bilkisu ke ce ke magana? Bilkisu ina kika shiga? Dan Allah ki dawo gida mun yafe miki dik abinda kika yi,ki dawo ki zauna a cikin dangin ki,ki samu miji kiyi aure Bilkisu, aure shine mutuncin dik wata ƴa mace a duniya da lahira Bilki."

Kukan da Billy keyi ne ya tsananta har sai da ta sa mahaifin ta zubar da hawaye shima,cikin kuka ta furta,

"Baba ku yafe mini,ku yi hakuri akan dikkan baƙin cikin da kuka ƙunsa ta sanadina,Baba ku taya ni da addu'a Allah ubangiji ya bani ikon dawowa gare ku a raye cikin ƙoshin lafiya, Baba ina cikin wani irin mawuyacin halin da ni na jefa kaina da kai na a cikin shi saboda kwad'ayi da son zuciya, dan...."

Cikin sauri Billy ta latse wayar ta sanya ta a flight mood saboda kar a sake kiran ta Any ta ji,hawayen ta ta hau gogewa tare da rufe jikin ta har kan ta, Any ce ta shiga ɗakin ta tsaya tana kallon Billy dake cikin bargo tana goge hawaye, murmushi Any ta saki wanda ita kaɗai ta san ma'anar shi sannan ta shiga banɗaki ta hau wanka.

Ta jima tana wanka kafin ta fito ta tarar da gadon wayam babu kowa akai,ba tare da damuwar komai ba ta gama shirin ta sannan ta buɗe wata jaka a ƙasan gado ta ɗauki abubuwan da take buƙata ta bar ɗakin,direct ɗakin karatun ta ta shiga,anan ta tarar da Billy ta haukace tana mata bincike,jingina tayi da bakin ƙofa ta harɗe hannayen ta a ƙirjin ta tana ci gaba da kallon Billy dake dube-dube a tsorace,rashin ganin abinda take nema ne ya sanya ta zama a ƙasa ta haɗe kanta da guiwar ta ta fashe da kuka mai tsanani,tafi Any ta hau yi da hannayen ta,cikin abinda bai fi taku biyar ba ta ƙarasa shiga ɗakin,Billy ce ta miƙe tsaye a tsorace tana ja da baya,wani irin tsoron Any take ji wanda bata taɓa zaton zata ji tsoron wani mahaluƙi a duniya irin haka ba.

"Looking for this young lady?"
(Wannan kike nema Young lady?)

Passport ɗin Billy Any ta d'aga tana kad'awa a gaban fuskar Billyn,cikin azama da zafin nama Billy ta yunƙura zata karɓe passport ɗin nata,wani irin naushi Any ta sakar wa Billy sai da jini yayi tsartuwa ta yi katantanwa kafin ta kife a ƙasa,durkusawa Any tayi a dai-dai fuskar Billy ta zaro bindigar da ta soke a bayan wandon ta ta saita kan Billy da ita, cikin wata iriyar murya ta kece da dariyar mugunta kafin tace,

"Yarinya kin riga da kin siyar min da kan ki da hannun ki,dan haka banga dalilin da zai saka ki neman passport ɗin ki ba,ina kike tunanin guduwa to? Ko kin manta ke matata ce? Kin manta kin saka hannu a takarda kin saida min da kan ki akan maƙudan kud'ad'e masu yawa? Kin manta kin saka hannu a contract ɗin aiki da kamfanin mu na porn? Idan kika gudu babar ki kike so mu ɗakko tayi mana aikin mu? Baki da wajen guduwa a yanzu nan ne madakatar ki, kuɗi kike so ai ko? To ai kin samu,zaki ci mai kyau, zaki sha mai kyau, zaki kwanta a wajen mai kyau kalar wanda kike so,zaki tuƙa mota ko ki hau jirgin da kike so,abinda nake so kawai a wajen ki shine biyan buƙata ta a wajen ki da ta kamfanin mu,kar ki mayar dani mutuniyar banza a ƙungiyar mu ƙarƙashin reshen Arewa mana,ko kin san ni ɗin madubi ce a wajen wasu? A matsayin da na taka a yanzu kina nufin zan bari ki zubar min da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login