Showing 204001 words to 207000 words out of 276165 words

Chapter 69 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

rana Ɗan liti da Sadeeq suka bar garin Abuja ba tare da sun yi wa Baaba sallama ba, sun tafi cike da abubuwan arziƙi masu tarin yawa,tin da suka tafi Sadeeq ke dariya har sai da ya baiwa Ɗan liti haushi ya daka masa tsawa,cikin faɗa Ɗan liti yace,

"Wai Sadeequ dariyar uwar me kake yi ne haka? Ko ni ne nake baka dariyar ne ban sani ba? Talabijin na zame maka?"

"Baba ba da kai nake ba fa,kawai ina tina tashin hankalin da Baaba yau zata yi a gidan nan idan ta buɗe ido taga bama nan mun tafi."

Murmushi Ɗan liti ya saki sannan yace,

"Ɗanneman matsokani,ai sai tafi cin ƙaniyar ka tinda ɗaki ɗaya kuke kwana."

Ba karamin daɗi Sadeeq yaji ba da ya ga mahaifin sa ya sake masa fuska, nan take ya tuna da nasihar Saddiqa akan yin addu'ar matafiyi, addu'a ya dinga yi akan Allah ya sa mahaifin su ya dawo da son su da nuna masu kulawa fiye da yanda ya yi musu a baya.

A can Abuja kuwa Hajiya Baabaa ta ga magariba tayi kowa ya watse Anisah da Khaleesat na ƙara gyara gidan,sai Baaba ta ɗakko jakar kayan ta ta dawo parlour ta hau ƙwalawa Sadeeq kira, Anisah ce ta fito ta zauna a kusa da ita tace,

"Baaba ai su Sadeeq yanzu sun kusan isa kano,tin bayan azahar suka tafi,ke fa yanzu kin zama ƴar Abuja,dan kuwa ke zaki dinga yi wa jinjiri wanka har su yi arba'in."

Nan da nan ran Baaba ya ɓaci ta miƙe tsaye,cikin masifa ta ɗauki jakar ta tayi hanyar waje ta na faɗin,

"Allah yasa ni ba cima zaune bace da uwar kuɗi na a jiki na zan iya biyan na mota na koma ɗaki na,mutuwa kuke so ta riske ni a inda ba a nan miji na ya ajiye ni ba to kun yi kaɗan,matsa min na wuce kafin na yi kutubal dake Anisah."

Da sauri Anisa ta matsa saboda damƙar da Baaba ta yi wa damtsen ta,ji tayi kamar an d'aure mata damtsen da waya tsabar ƙarfin da Baaba ta sa mata,da gudu Anisah ta yi ɗakin Ummi dan ta sanar da ita dramar da Baaba ke son tada musu.

Kafin Ummi da Anisah su fito Baaba ta fita bakin gate ta zauna da ƴar jakar kayan ta a gefe wai tana jiran me adaidaita sahu ya zo ya kai ta tasha,dik wata magiya da roƙo da ban baki da su Ummi suka dinga yi wa Baaba ta ƙi sam ta saurare su balle ta koma cikin gida.

Kiran sallar magariba ne ya sanya su Ummi sake shiga damuwa, cikin hawaye Ummi tace,

"Baaba ko dai laifi na yi maki ne ban sani ba shi yasa baki son zama a inda nake? Dan Allah idan akwai laifin da na taɓa yi miki a tsawon rayuwa ta da Abbahn su ban sani ba ki yi haƙuri ki yafe min,zama da mu ba yana nufin zaki mutu bane anan Baaba, dikkan mai rai baya mutuwa sai a inda ajalin sa yake,da ace zaki shekara hamsin ko ɗari baki taɓa barin ɗakin ki ba, a duk ranar da ajalin ki yazo sai Allah ya nufe ki da fita daga ɗakin ki tafi can inda Allah ya hukunta anan ne zaki mutu,kina zuwa sai Allah ya ɗauki ran naki a wajen,dan haka na fi yarda da cewa laifi nayi miki shi yasa kike hukunta ni ta hanyar ƙin zama da ni Baaba."

Jikin Baaba ne ya yi sanyi laƙwas,nan take taji bata kyauta ba akan abinda tayi,surukar ta ta da jikokin ta basu nufin ta da komai sai alkhairi,nan take tunanin wata kawar ta ya faɗo a ran ta,ita surukar ta ma ke korar ta a gidan ɗan ta,dik da cewa basu kai Baban Gidan ta arziƙi bama,tashi tayi daga tsugunnon da tayi ta kama hanyar shiga gidan tana faɗin,

"Kai Manniru ɗakko min jaka ta tinda uwar ka na so ta dabaibaye ni da kalaman ta,zan zauna amma ana yin arba'in zan koma ɗaki na dan ba zan dawwama anan garin ba ah toh."

Cike da farin ciki suka tattara suka koma cikin gidan,bayan wucewar su ne mai gadi da driver suka hau gulma,driver ne yace,

"Ka ji gigitacciyar tsohuwa dan Allah,kowa na so yaje Abuja ya huta ya ci mai kyau ya sha me kyau ya kwanta a waje mai kyau,amma wai ita a maida ita kauye,kaiii amma tsohuwar nan bata yi ba."

Suna nan suna gulma Abbah ya dawo,tinda mai gadi ya buɗe masa gate ya fara tsakura masa labarin abinda ya faru,murmushi Abbah ya yi sannan ya ƙarasa fita a motar shi ya na faɗin,

"Ai ni nama yi zaton zan dawo na tadda su a bakin ƙofar gidan nan,to Alhamdulillah tinda ta amince za ta zauna ɗin."

Ko da Abbah ya shiga gidan a daƙile Baabaa ta amsa masa gaisuwar shi, murmushi ya yi ya wuce ɗakin shi dan ya zaci ma zai samu abinda ya fi haka daga gare ta,a haka Baaba ta ci gaba da yi wa Saddiqa da jinjirin ta Suhail wankan jego cike da kulawar da Uwa zata baiwa ƴar ta.


****************************


Da misalin tara da rabi na safe Shamsu ya isa gidan Ɗan liti da mai adaidaita sahu,fita ya yi ya je ƙofar gidan yana ta zabga sallama,cikin sauri Ameerah dake jiran shi ta fara fitar da kayan ta,sai da ta gama tsaf ta sa zani ta goya yaron ta sannan ta hau yi wa Innoh da ke baccin safe sallama,cikin magagin bacci ta fito tana faɗin,

"Ameerah yanzu hura iccen ne baza ki iya ba ko me? Ina kwance ina huce gajiya zaki tada ni saka ruwan wanka se kace wata baiwar ki."

Ganin Ameerah da goyo ga kaya ta fitar ne ya sanya ta sauke hannayen ta da ta ɗage sama tana miƙa tace,

"Ke lafiya ina zaki da kaya haka da sassafen nan?"

"Gidan miji na zan koma,gwanda na koma can ya dinga taimaka min yana saka min ruwan zafin tinda banga amfanin dawowa ta nan gidan yin jego ba."

Kuka Innoh ta fashe da shi tare da faɗin,

"Ameerah yanzu har na yi lalacewar da zaki koma gidan mijin ki baki yi arba'in ba?"

"Ni dai ban ce ba, amma kam ba zan zauna ina jego ina aikatuwa ba, babu wata kulawa ta musamman,rabo na da na samu hutu a gidan nan tin zuwan Kaka da ta kawo min farfesun kaza ta mana wanka ni da yaron nan,sannan ta bar mu muka yi bacci isasshe,ke me kike yi mana? Sai dai idan an kawo mana abun ƙwalama a cinye da ke, to gaskiya ni na gaji, yana waje yana jiran mu kar mu ɓata masa lokaci."

Baki Innoh kawai ta saki tana bin Ameerah da kallo, dan kuwa ta kasa ƙaryata ta tinda gaskiya ta faɗa,amma a ganin ta ai be kamata Ameerah ta koma ɗakin ta ba ba tare da ta kammala wanka ba.

Ko da Ameerah ta fita sai ta miƙawa Shamsu kayan su ta wuce ta zauna a adaidaita sahu ta kame tana jiran shi,yana zama kusa da ita ta buɗe baki zata yi masa magana wani warin baki ya ziyarci hancin shi........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨














PAGE 83:







Shamsu na shaƙar warin da Ameerah ta feso masa sai ya juyar da kan shi gefe tare da ɗauke numfashin sa,sai da ya ji iskar saman hanya na dukan fuskar shi sannan ya sauke numfashin da ya riƙe,sake kallon Ameerah ya yi ya ga alamun ko wanka bata yi ba ballantana wanke baki,tsaki ya ja kafin ya ce mata,

"Dan Allah ki yi haƙuri ki dena yawan mitar nan da kike yi,a saman hanya fa muke, ki bari mu je gida kiyi wanka ki wanke baki, ki ci abinci ki huta idan yaso sai mu tattauna."

Tura baki tayi tana ƙunƙuni,suna isa gidan ta ɗauki handbag ɗin ta ta shige ciki ta bar wa Shamsu sauran kayan ya kwashe,sai da ya sallami mai adaidaita sahu sannan ga kwashe kayan ya shiga gidan,a tsakar gida ya tarar da Ameerah da Ta Annabi suna hira, Ta Annabi ta rungume jinjirin tana sauraran ƙaryar da Ameerah ke shirgawa akan Shamsu ne ya matsa ta dawo,amma ita taso ace sai da tayi arba'in sannan ta dawo ɗakin ta, Ta Annabi ce ta kalli Shamsu ta ɗan harare shi sannan tace,

"Yaran yanzu baku da kunya ko kaɗan,yanzu Shamsu ka bar ƴar mutane ta yi wankan ta cikin salama shine ka lallaɓa ka dawo da ita? To Allah ya kyauta, karɓe shi ku shiga d'aki bari na ɗora maku ruwan wanka a wanke mai gida."

Karb'ar yaron Ameerah tayi tana sunne kai ƙasa kamar ta k'warai,Shamsu kuwa mamakin tane ya kulle masa baki ya kasa cewa komai,ganin kowa ya kama gaban shi an barshi tsaye da kaya a hannu ne ya sanya shi bin bayan Ameerah,suna shiga ya ajiye kayan ya na hararar ta, dariya tayi ta ce,

"To idan ban faɗi haka ba me zan ce? Ko so kake a ga rashin kunya ta ace na kasa haƙuri na biyo miji ban yi arba'in ba? Uhumm na tuna dalilin dawowa ta ma,jiya da wata shegiyar kake waya da tsakar dare?"

Cikin sauri ya juya ya bar mata ɗakin yana dariya,nan take Ameerah ta gano akwai wata a ƙasa,ranta kuwa ba ƙaramin suya ya hau yi ba, ta rasa da wanda zata yi wannan hirar ta samu salama, Mommy ce ta faɗo mata a rai, nan take ta samu bakin gado ta zauna,wayar ta ta ɗauka ta hau kiran Mommy,ba jimawa Mommy ta ɗauki wayar murya a shaƙe ta amsa sallamar Ameerah,cike da mamaki Ameerah tace,

"Yah Mommy lafiya naji muryar ki haka ko dai mura kike yi?"

Mommy ce ta ja majina kafin ta ce,

'Ai da mura nake yi Ameerah da na sha mata magani ta tafi,halin da nake ciki Ameerah idan ban samu mafitar shi ba ina ga mutuwa ce kawai zata sassauta min shi.'

Miƙewa Ameerah tayi tsaye ta hau safa da marwa a ɗakin nata, cike da jimami tace,

"Ke kuwa Yah Mommy wannan wanne irin hali ne kika shiga da mutuwa ce zata zame maki sauƙin shi?"

'Ameerah na rasa gane kan Abdul kwana biyu,da na matsa da bincike a wayar shi na gano yana soyayya da wata yarinya a nan unguwar tamu,gida uku ne tsakanin mu,ki duba fa ki ga yanda nake ƙoƙarin biya wa Abdul duk wasu buƙatun shi,amma har yanzu na kasa cike masa gurbin kowacce mace da zai yi sha'awa.'

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,ki ce dodo ɗaya muke yi wa tsafi dani dake ban sani ba,ni kai na matsalar shamsu ce ta sa na kirawo ki dan na samu mafita, Shamsi waya yake yi cikin dare da wata ƴar iskar ni ina can gida zaune ban sani ba sai jiya da na kira shi na gane hakan, shine na sa ya maido dani ɗaki na,yanzu Yah Mommy ya zamu yi?"

Shiru Mommy tayi kafin tace,

'Ai ni yanzun nan ma zan je ɗaukar nawa matakin,dan kuwa da Abdul ya yi min kishiya gwanda na kashe dika matan garin nan a sani a gidan yari har ƙarshen rayuwa ta,dika-dika yaushe na haihu? Yaushe na gama da kashe wutar yarinyar da ya yi zina da ita amma ya ke ƙoƙarin kwaso min wata lalurar? Ke Ameerah ina zuwa, mun yi waya anjima idan na dawo daga cin uban yarinya,ni ba wadda zata ɗauki iskancin ɗa namiji bace.'

Kashe waya Mommy tayi ta miƙe ta bar Ameerah da zullumi da tunanin anya itama ba haukace wa shamsu zata yi ba?

Ruwan wankan da aka sanya musu ita da jinjirin ta ne ya yi,dan haka Fadila sai ta sallama ta sanar da ita,miƙa mata yaron tayi da kayan da za a sauya masa sannan tayi shirin wanka ta fita zuwa bayi, tafe take tana saƙa da warwarar irin rashin mutuncin da za ta yi wa Shamsu.

Mommy kuwa bayan ta kashe wayar ta,sai ta kira Aunty Naja ta miƙa mata yaro tace mata zata shiga maƙota yanzu zata dawo, idan Abdul ya dawo ta sanar da shi taje gidan Maman Khadija,yanayin da Mommy ke magana da shi ne ya ɗarsawa Aunty Naja zargin babu lafiya, dan haka tana fita sai ta ɗauki waya ta kirawo Abdul ta sanar da shi abinda ke faruwa,cike da tashin hankali Abdul ya ce,

"Dan Allah Aunty kar ki barta ta isa gidan nan, ki tsaida min ita dan Allah, innalillahi Aunty dan Allah ki tsaida ita gani nan zuwa yanzun nan.'

Da jin haka Aunty Naja ta gane Abdul bashi da gaskiya, dan haka sai ta ƙi fita, cikin yatsina fuska tace,

"Namiji ɗan kunama, baya zama waje ɗaya sai ya yi harbi,mace daga haihuwar ta ka hau dasa mata baƙin ciki? Wacce iriyar kulawa ce yarinyar nan bata baka? Allah yasa idan abinda nake zargi ne ta ci uban yarinya,ta haka ne matan unguwar za su kiyayar mata miji."

Mommy kuwa na isa gidan Maman Khadija bata bata lokaci ba ta hau yi musu watsi da dik abinda ta gani a tsakar gidan,girki ne aka ɗora na rana a gas a tsakar gida Mommy na isa gaban tukunyar ta tintsirar da ita ƙasa,nan take shinkafar dake zaɓalɓala a wuta ta antaye a ƙasa,tukunyar miyar da ta ji nama zuƙu-zuƙu ta kifar tana faɗin,

"Da kud'in miji na ake wannan girkin ai,dan haka dole na zubar,ina yi maku kallon mutanen kirki ke da ƴar ki saboda baku yawo irin na sauran matan unguwa, daga makaranta sai gida,ashe kuna nan ƴar ki har ta iya turawa miji na hotunan ta babu mayafi ko?To miji na yafi karfin ƴar ku, ku je can ku sama mata masaki irin ta, tana tafe tana cogala ƙafa kamar ta Allah ashe shaid'aniya ce."

Mahaifiyar Khadija ce ta fito ta kalli ɓarnar da Mommy tayi musu,cikin ɓacin rai tace,

"Ai mijin naki shine ya nace akan yana son ya auri mai irin sunan ki,yana so ya cika gidan shi da mai suna khadija,kuma ya tabbatar mana da cewa kin amince da yawun ki zai ƙara auren,mijin ki shi ya kawo kan shi ba nemo shi muka yi ba."

"Ke tsohuwar banza ba maganar miji na ake yi ba yanzu,na san da mijin nawa ai na tsallake shi na zo wajen kwaɗayayyu masu son abun duniya, wato kun ƙyalla ido kun ga ina walwala a gidan miji na, shine zaku aura masa cogal ɗin ƴar ku ko? To sai dai ku nemo mata masaki irin ta, idan kuwa tayi gigin shiga gida na na rantse maku sai dai ku je ku ɗauki gawar ta, iyaka dai a kai ni gidan yari ko?"

Ba tare da sallama ba Abdul ya afka gidan, yana zuwa ya hau jan Mommy yana faɗin,

"Baby mu je gida, zan yi maki bayanin komai."

"Kutu.....uban...bayani zaka yi min Abdussaboor,jiya na ga chatting ɗin ku da wannan matsiyaciyar gurguwar,da kyar na yi haƙuri na danne zuciya ta har ka fita kafin na zo,ashe dama shi yasa kake cewa a kai musu buhun shinkafa kana tausayin su? Ina hankali na yake tin farko ban gano ka ba? Abdul yau sai ka yi daka sanin sanin yarinyar nan a duniya."

Fisgewa daga riƙon da Abdul ya yi mata tayi ta nufi kan ƴar mutane ta hau duka,dik yanda Abdul yaso ya kwace khadija daga hannun Mommy ya kasa, ƙarshe ma juyawa tayi kanshi ta hau jibgar shi da muciyar da ta ɗauka a cikin kwandon wanke-wanken gidan,hauka tuburan Mommy ta dinga yi sai da ta yi wa gidan kaca-kaca, sannan ta juya cikin haki ta ƙura wa Khadija ido tace,

"Idan kika fasa auren miji na Allah ya tsine maki albarka, ina nan ina jiran ki,dan Allah a d'aura auren nan gobe ko yau ma idan kuna so, Allah ya baiwa mai rabon shan duka sa'a."

Bangaje mahaifiyar Khadija Mommy tayi sai da ta faɗi ƙasa sannan ta wuce gida mayafin ta a hannu kanta babu ɗanƙwali,Abdul kuwa rasa abinda zai ce wa bayin Allah'n ya yi sai kawai ya sa kai ya bar gidan,ya tabbata shi ke da laifi ɗari bisa ɗari akan dik abinda ya faru,ya rasa me yasa yake da burin ƙara aure dik da kulawar da Mommy ke bashi,gashi ta dalilin son faranta ran shi ya jawowa wadda bata ji ba bata gani ba duka da wulaƙanci da ƙasƙanci ita da mahaifiyar ta,banda asara da Mommy tayi musu wanda bai san ya zai yi ya wanke kanshi ba a wajen Khadija.

Ko da ya isa gida ya tarar da Mommy zaune a ƙasan carpet tana ta rusa kuka tin ƙarfin ta,idanun ta sun yi wani irin jan azaba da masifa,Aunty Naja ta yi lallashin duniya taƙi shiru,Abdul na shiga ta zabura ta miƙe tayi kan shi,cukume rigar shi tayi tace,

"Abdul ka sake ni ba zan iya ci gaba da zama da kai ba,na tsane ka na tsani zama da maci amana,yanzu duk irin kulawar da nake baka bata ishe ka ba sai ka nemi wata macen? Me yarinyar nan take da shi wanda banda shi? Yarinya a ƙyarmashe a bushe ga nakasa amma wai ita ka ke bi tsabar akuyanci...."

Wani irin mari mai tartsatsin wuta Abdul ya sakar mata,cikin fushi ya hau nuna ta da yatsa yace,

"Ni kike kira da nayi akuyanci saboda zan raya sunnar Annabi? Na nemi macen banza na aikata zina kin yi masifa, na nemi aure kin yi masifa,kina nufin da ke kaɗai zan rayu ba zan sake wani auren ba a duniya?.."

"Eh da ni kaɗai za ka rayu Abdul ! Alƙawari kayi min akan hakan kuma dole ne ka cika shi."

"Ba zan cika maki alƙawarin ba Hadiza,zan kara aure dan Allah idan kin so ki yi bindiga ki fashe ki mutu."

"Ba zan kashe kaina ba Abdul amma zan kashe ka, zan kuma kashe matar da zaka aura,idan ka cika ɗan halak haihuwar uwar ka da uban ka ka ƙara aure a cikin satin nan Abdussabour."

"Ni kike faɗa wa wannan maganar Hadiza? Ni kike yi wa rashin kunya haka? Zan kuwa shayar dake mummunan mamakin da ba zaki manta da ni ba har abada,aure kuma kamar nayi na gama sai dai ki mutu da baƙin ciki."

Kuka Mommy ta kwanta a ƙasa tana yi kamar wadda aka yi wa mutuwa,dik yanda Naja taso ta lallashe ta ta nuna mata za su koma wajen malam,sam Mommy taƙi fahimta,ƙarshe ma masifa ta fara yi tana faɗin,

"Ni ki rabu dani Aunty Naja,wannan karon ba boka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login