Showing 15001 words to 18000 words out of 276165 words

Chapter 6 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

ka ke hana wa zuwa aikatau birni,tun daga qofar gidan su Balki za ka san yarinyar nan ta dangwalo arziki,ka wa Allah malam ka bar yarinyar nan ta tafi Itama ko mun samu a dena wulaqanta mu dan za a bamu zakka,ka duba ka ga muqamuqi na yanda ya kumbura saboda kawai na yi hausar da ba a gane me na ce ba"

"Ga aboniki na siyo maki an ce ya na ɗauke zafin ciwon da ya danganci qashi da tsoka, ke Mommy karb'i murza mata wajen ya sauka,dangane da zuwan ki birni aikatau kuma zan sake duba lamarin,dan kuwa yau da na ga suturar da ke jikin ja'irar yarinyar nan sai na ji dama ace Mommy ce ta saka,se wani walwali take ta na sheqi kamar 'yar wani hamshaqin,nan kuwa daga Saida dusa uban ta bai wuce kowa ba,ke ki ma fara haɗa kayan ki zuwa birni ya kama ki, yarinya mai tausayi irin haka za mu tauye a gida?"

Cike da murna Mommy ta ɗauki aboniki ta hau lafta wa Innoh ta na yi ta na qara lasa masu duk wani labarin jin daɗi da za su samu a gaba idan suka barta ta tafi birni,wani uban ihu Innoh ta kurma ta miqe tsaye zumbur kamar wadda cinnaka ko kunama ta ciza,waje ta fita da gudu ta yi hanyar randunan su,ta na zuwa ta buɗe ta yi rashin sa'a babu ruwa har wani bushewa suka yi saboda rashin ruwan da ba a zuba ba taqamar suna da rijiya.

Rijiya ta nufa a guje ta zura guga ta na ihu hawaye na bin kumatun ta,jin fuskar ta take yi kamar ba a jikin ta ba, jiki na rawa ta janyo ruwan ta kwara a fuskar ta sai ta ji wani sanyi mai daɗi na ratsa ta,a hankali zafin ya sake dawo mata sabo dal, Yadiko da su Saddiqa da Ameerah duk sun fito sun yi cirko-cirko saboda rashin sanin abinda ya gigita Innoh,Sule ne ya fito daga d'akin shi ya na hamma ya ce,

"Baba mun shiga uku kar dai Aljana 'yar shanono da ke kan Baaba ce ta sake dawo wa Innoh,"

Baaba wadda zuwan ta kenan ta d'aga siraran hannun ta ta ce,

"Haram, kar ka yi wa bakanuwa Jinin Fulanin kanawa sharri, ita dai ta san Allah ya isan waye ya ciyo ta ta haukace"

Cikin tsananin masifar zafin da Innoh ke ji ta kalli Baaba ta ce,

"Ban ga hauka ba, sai dai ki gan shi a kan ki,wayyooo Allah aboniki zai qona ni"

Ruwa Ameerah ta sake janyowa Innoh Sule kuwa ya zaro tabarya ya ce,

"Ina abonikin yake na sheme ɗan wahala?"

Cike da dariya Mommy ta ce,

"Ba fa mutum bane Yah Sule, man zafi aboniki na murza mata a muqamuqin ta da ya kumbura ka san shi akwai zafi,in banda abun Baba ma ai Robb kaɗai ya isa amma ya kwaso aboniki"

Ɗan liti dai sai zare ido yake yi bai ce komai ba, dan kuwa maganar Mommy gaskiya ce da ya sani da Robb ya shigo mata da shi, yanzu dai aikin gama ya gama sai dai ta yi hakuri Allah ya kiyaye na gaba. Zamewa ya yi ya bar gidan dan kar ma ta yi masa tijarar ta da ta saba.

Yadiko ce ta d'akko wani kyallen yadi mai laushi ta bawa Innoh ta ce ta goge wajen zai rage zafin, ta na sakawa zafin ya haɗe mata ya mata yawa, ga zafin kumburin da kuncin ta ya yi,ga na aboniki,ga kuma na goga tsumma da take yi a wajen, wani nishin wahala ta sauke ta ce,

"Kwad'ayi mabud'in wahala,ina zaman zamana a d'aki daga jin za a bada zakka na tashi na hau rawar jiki,gashi nan na ci kud'in zakka da azaba"

"Innoh magana ki ke yi ne?"

"In ce uwar me to ni ina a wannan halin na tsakanin rayuwa da mutuwa?"

Baya Ameerah ta ja ta bar ta a wajen ta na ci gaba da goge muqamuqin ta tare da zuba ruwa mai sanyi a wajen,a haka Yadiko ta wuce madafin su ta hau sharewa dan kuwa ita ce za ta karb'i girki a ranar, duk halin da Innoh ke ciki bai hana ta zabga tsaki ba tare da hararar Yadiko da bata san ma ta na yi ba.

Bayan wasu awanni fuskar Innoh ta saɓe daga kumburin da ta yi, shatin kaqoran Baaba ma ya baje, sai zazzaɓi da ciwon kai mai zafi ya rufe ta sakamakon kuka da shiga tashin hankali da damuwa da ta yi,ta na nan kwance ta hau tunanin ya zama dole su bar Mommy tafiya birni aikatau ko babu komai duk wata za ta dinga samun 'yan kud'ad'e irin yanda Mahaifiyar Billy da Baaba ke samu, nan take ta ga wautar ta da ta biye wa Ɗan liti suka hana Mommy tafiya birni, a cewar shi ita mace sai ana saka mata ido, an saka mata ido ma ya ta qare ballantana ba a saka mata ba?

A can d'akin Mommy kuwa ta riga da ta gama sanar da Billy amincewar iyayen ta game da tafiyar su tare,nan take suka dinga murna,wani videon da suka yi a gidan mai gari Billy ta yi posting a status d'in ta a qasa ta rubuta (Gidan grandma akwai daɗi amma hutu ya qare, guys ina nan dawowa Abuja nan da wasu kwanaki, na yi missing ɗin ku qawaye na).

Mutanen ta da ta ke zabga wa qaryar ita 'yar sanata ce tuni suka hau yi mata comment, ana yaba wa kyawun da ta yi, wasu har tambayar ta suke yi a wanne gari grandma ɗin ta take ita kuwa ta karkace ta ce a cikin garin Kano take da zama.

Albishir ta yi wa Hajiyan ta da zuwan Mommy, nan take ta tura mata dubu hamsin ta account ɗin ta sannan ta ce ta tabbata ta kawo mata Mommy kar a samu wata matsalar da za a ce an fasa zuwa, nan take ta yi mata alqawarin zata kawo mata Mommy har gida.

Kayan ta ta gama haɗawa a akwati sannan ta wuce tasha ta ciro kud'in da aka tura mata ta yi gida, mahaifan ta ta baiwa dubu biyar biyar sannan ta ware wasu dubu biyar ɗin da niyyar ta baiwa Mommy ta qara wa iyayen ta dan su yarda ana samun kuɗi ta hanyar aikatau.

Da yamma liss ana daf da Kiran magariba ta isa gidan su Billy,a tsakar gida ta tadda Yadiko da ta fito daga wanka Saddiq ya na mata shagwab'ar yunwa yake ji ta yi ta gama girki ta zuba masa miyar da ke ta dahuwa a Saman garwashi a hankali,in dai girki ne Yadiko ta ciri tuta ta wannan fannin fiye da Innoh, dan kuwa in ba alale da dambu ba Innoh bata k'ware a girki ba,hasali ma ita sam bata qaunar yin girki musamman tuwo idan ta tuqa kafin safiya a yi d'umame ya sake, shi yasa lokuta da dama sai dai kowa ya ji da kan shi da safe ranar girkin ta. Billy durqusawa ta yi ta gaishe da Yadiko kamar wata ta Allah, sannan ta ce,

"Ina mutuniya ta kuwa ko ana ciki ana sallah?"

"Ko ana ciki ana latsa waya ba? Ke yanzu da magaribar nan ana ta Kiran sallah aljanu na ta gilmawa shine ki ka fito a haka ki ka zo gidan su ƙawa? Dibi kayan jikin ki fa ki na d'aga hijabin ki na ga babu wata suturar arziki a haka ki ka banka uban hijabi,yanzu ba kya jin tsoron iska ta d'aga ko wani tsautsayi ya faru a ga jikin ki?"

Cikin kosawa da maganganun Yadiko Billy ta ce,

"Wanda ya gani shi ya jiyo, ni ba wa'azi na zo ki yi min ba,ki je can ki yi ta zuba wa 'yar ki wa'azin naki wataqila ya yi mata amfani, gata nan kullum cikin hijabi bamu san me take b'oyewa ba, wa ya sani ma ko ta d'akko na shege a waje?"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, Balkisu daga yi maki nasiha Zaki jefi 'ya ta da wannan mugun alkaba'in? To ba ita ba ma ke kan ki da dikkan musulmi ina nema maku tsari da wannan mummunar jarabawa Allah ya baki hakuri qawar ki na d'aki,"

"Tun farko da haka ki ka ce min da baki b'ata mana rai ba da ni da ke"

"Humm duniya ce ta fi bagaruwa iya jima, Allah ya kyauta"

D'akin ta ta shige ta bar Saddiq na kallon Billy kamar ya je ya make ta, ita kuwa d'akin su Mommy ta afka ta na shiga ta gan ta kwance a rufe da zani ta na ta latsar waya,zube wa ta yi a jikin ta ta na d'aka mata duka ta ce,

" 'Yar duniya ana can ana sallah ki na nan ki na kallon harkar duniya,mu ga me ki ke kallo,yanzu na haɗu da wannan kishiyar uwar taku mai shegen kinibibi kamar ta fi kowa tsoron Allah a duniya"

"Hummmm Yadiko ko? Haka take ai duk ta bi ta ishe ni ko ganin ta bana qaunar yi a gidan nan ita da waɗannan shegun yaran nata"

"Humm ai kin kusa tafiya ki basu waje qawata, kin ga ga wannan ki sake qara wa su Innoh gobe da sassafe zamu bar garin nan, ina so mu isa da wuri ido na ganin ido saboda lalacewar hanya"

"Tom Allah ya kaimu, na gode sosai qawata akan irin wannan qoqarin da ki ke yi min a gaskiya banda masoyiya kaff garin nan sama da ke"

Murmushin gefen baki Billy ta yi sannan ta ce,

"Babu komai ai yi wa kai ne"

A haka suka kwanta tare babu sallah babu salati suka ci gaba da kallon fina-finan da aka tura masu na turanci wanda anan ne suke qara gogewa da yaren turanci,sai dai kashh kusan rabin film ɗin bashi da kyan gani,amma su ko a jikin su, suna gani suna qarin bayani akan abinda suke kallo. Billy bata bar gidan ba sai bayan isha'i,ta bar gidan ɗauke da kayan Mommy da ba su fi kala bakwai ba wanda a ciki biyu ne kawai na sallahn ta sauran dika Billyn ce ta bata. Billy kuwa ta tafi da su ne a cewar ta ba za a ɗaukar mata jakar buhu a bi ta Kano da shi ba, za ta je ta yi wa kayan waje a akwatin ta tun da ta rage kaya ta babbayar,godiya sosai Mommy ta yi mata sannan ta koma d'aki ta kwanta.

Da dare Ɗan liti ya siyo wa kowa tsiren ɗari uku-uku har Baaba,hakan da ya yi ya hasala Innoh ta dinga masifa ta na fad'in ai kowa na da kud'in shi me zai sa shi kashe kuɗi a banza? Bai kula ta ba ya ɗauki nasu shi da Yadiko da yaran ta zai tafi wanda kafin hakan sai da Innoh ta qirga shi tsaff tsoka bayan tsoka dan kuwa a cewar ta kar a yi rashin adalci.

D'akin Yadiko ba shi da wadatar kayan d'aki daga gadon ta da sif sai ɗan qaramin madubi shikenan ledar tsakar d'akin ma ta yi yagewar da ta fi rabi amma a haka ta gyare d'akin ta tasss,Saddiqa ce zaune a gaban Mahaifiyar ta ta na jin haddar ta Ɗan liti ya shiga bakin sa ɗauke da sallama, murmushi ya sakarwa Yadiko gaba ɗaya dasorin shi suka bayyana itan ma sai ta sakar masa murmushi sannan ya qarasa shiga ya ajiye leda ɗaya a gaban ta, ya miqa wa Saddiqa nata ya ba wa Saddiq nashi sannan ya ce,

"To maza a tashi a je makwanci a kwanta ko? Sai da safe,"

"To Baba Allah ya tashe mu lafiya"

"Amin"

Yaran na fita Yadiko ta fita Itama ta je rijiya ta kindimi ruwa ta kai wa Ɗan liti na wanka, sabulun ta irin koren nan na wanki ta sa a kwandon wanka duk ta kai masa ta cika buta da ruwa ta ajiye ta koma d'aki.

"Mata ta 'yar aljannah,shi yasa fa idan mutum ya tashi aure malamai suka ce Annabin rahama ya bada shawara da maza su auri mai addini,yau kwana na biyu rabo na da wanka tun wancan zuwan da na yi na tafi da wanka na sai yau zan sake wani, yo ita kan ta uwar garken wato uwar awaki wajen rashin son wanka ba ta yi ba balle mijin ta ya yi,"

"Hummmm malam kenan"

Shine kawai abinda Yadiko ta ce, dan bata son halin shi na son a d'akko zancen Innoh a yi ta zagin ta, dan kuwa yin hakan ba dai-dai bane,Hakan kuma na tabbatar mata da cewa Shima idan ya koma wajen Innoh suna yi da ita. Jin ba za ta ce masa komai bane ya sanya shi tashi ya na fad'in,

"Bari na je na dawo akwai labari, da kuma neman shawara da za ki bani"

"To malam Allah ya sa na baka mai amfani da albarka"

"Ameen"

A haka Ɗan liti ya tafi wanka ya gama ya yi alwala dan kuwa bai yi isha'i ba ya na can wajen me nama aka shiga masallaci ya qi barin abinda yake yi ya tafi sai da aka gama yanka masa sannan ya yi gida.

Bayan ya gama shiri har sun ci abinci ya kishingid'a a gefen gado ya ce,

"Dama shawara nake nema game da yarinyar nan Mommy, kamar yanda ki ka sani ta jima ta na so ta tafi birni na ke hanawa,to shine d'azu ta zo min da jawabai na gansuwa kuma na gamsu na amince ta tafi, uwar ta ma ta amince amma har yanzu na rasa me ya sa na kasa haƙuri na kwantar da hankali na,ke wace shawara ki ke ganin ya dace a bi?"

Gyara zama Yadiko ta yi sosai ta buɗe baki ta ce...........
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI*








RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)








PAGE 7:








"Malam a zato na mun riga mun gama da wannan shafin tinda jimawa amma kuma na ji yau ka sake d'akko maganar,na riga da na san tinda ka kawo maganar a yau kuma a yanzu to fa tabbas kun gama yanke shawara akan mommy za ta tafi kano aikatau ko na bada shawara ba za ku sauya ra'ayin ku akai ba da kai da mahaifiyar ta da kuma ita kan ta yarinyar, ƙarshe ma zagi zai iya biyo baya a zarge ni da yi musu baƙin ciki da hassada wataqila har a zagi yarana a tsine musu tinda ba yau aka saba irin haka ba,abu ɗaya zan sanar da kai wanda bai wuce na ce maka ka yi k'ok'ari ka fi ƙarfin gidan ka kafin gidan ka ya fi ƙarfin ka,sannan ina so na baka shawara akan yanda ka ke son abin hannun 'ya'yan ka da mu matan ka, idan baka ɗauke ido akan haka ba tabbas ina jiye maka ranar qin dillanci..."

Cike da wani irin yanayi mara fassaruwa ya katse ta da fad'in,

"Dakata dan Allah Yadikon Sule, ke kuwa daga neman shawara sai ki yi ta surutu irin haka? Me ya kawo maganar qin dillaci kuma? Allah ya raba ni da ganin ranar nan,yanzu dai ba wannan ba miko min ruwan nan na karasa sha, tuwo ya yi daɗi Allah ya biya"

"Ameeen"

Kawai ta ce ta miƙa masa ruwan shan da ya buqata, ta samu waje ta yi shirin bacci ta yi addu'a ta shafe jikin ta tas ta kwanta ta na ta tunanin irin halin da Ɗan liti yake so ya jefe ƴar shi a ciki, ta jima da sanin wasu daga dabi'un Mommy da sule har ma da Ameerah, ta yi magana akan a gyara aka hau yi wa yaran ta fatan tsiya da tsinewa da masifa da bala'i ranar ce nara ta farko da har suka dambace da Innoh ta yi sa'a ta yi wa Innoh jahilin duka tin daga ranar Innoh ke shakkarta sai dai a yi cacar baki amma banda gwada 'yar k'ashi,dan haka dole ne ta ja bakin ta ta yi shiru bazata sake magana akai ba,tinda gashi ya na so ya tabka babban kuskuren barin Mommy ta tafi wata duniyar da sunan aikatau bayan sun gama maganar da ita da shi da jimawa akan mommy baza ta je birni aikatau ba,shine yanzu za su sauya shawara,wanne irin kwad'ayin abun duniya ne wannan ke damun shi?

Da wuri mommy ta yi wa shamsu sallama ta waya har da yi mata kukan soyayya na zai yi kewar ta sosai, ita kuwa ta yi masa alqawari da cewa kar ya damu za su kasance tare ta waya a kullum ai kamar basu rabu ba, da haka ta samu ya hakura ya dena koke-koken da yake yi mata suka ajiye waya.

Baccin ta kalilan ne domin kuwa tunanin ta duk ya qare ne a kan yanda zata samu garin kano shin ya na da kyau kuwa kamar yanda ake ta zuzuta shi? Ko kuma dai yanda ake kiran akwai mutane da yawa ba wani kyau gare shi ba saboda cunkoso? Anya zata haɗu da had'ad'd'en saurayin da zai aure ta ya cire ta daga qangin babu da wahalar rayuwar da suke ciki ita da iyayenta kuwa kamar yanda take karantawa a littafan hausa? Da ire-iren wannan tunanin ta samu bacci ya ɗauke ta.

Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na asuba Saddiqa ta farka domin yin ibadun ta kamar yanda ta saba har zuwa a yi sallar asuba sai ta ga mommy ta tashi itama a dai-dai wannan lokacin da bata saba tashi ba, in fact wani lokacin ma a sannan take ajiye wayar ta ta juya ta yi bacci,abun ya bata mamaki sosai amma haka ta danne sai zuciyar ta ta kawo mata cewar wataqila fitsari zata je ta yi ta dawo ta ci gaba da baccin ta dan su basu yin sallar asuba sai rana ta fito rangad'ad'au a sama sannan suke yin ta.

Ga mamakin ta sai ta ga mommy ta ɗauki soson wanka da sabulun wankanta ta tatsi toothpaste a brush ɗin ta ta rataya zanin wankanta ta fice daga d'akin, ɗauke kanta ta yi daga kallon ikon Allah ta koma ga ibadar ta tana kyautatawa yayar tata zato.

Mommy kuwa wankan minti shabiyar ta yi ta yi brush sannan ta yo alwala ta nufi d'akin su ta na rawar sanyi saboda kad'awar da iska ke yi irin ta yanayin nan na farko-farkon shigar sanyi.

Tsane jikin ta ta yi sannan ta shafa mai sosai da turare ta sanya sabuwar doguwar rigar da Billy ta bata sannan ta fara doka sallah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login