Showing 234001 words to 237000 words out of 276165 words
Chapter 79 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ai, dan na san bata ɗaukan shaƙiyanci."
Dariya suka sake yi, Mommy ta saɓi mayafinta dan ta raka Naja,sai da suka fita daga gidan suka ɗan yi nisa Mommy ta riƙe hannun naja ta tsaida ita,cikin damuwar da tai ta dannewa ta ce,
"Aunty Naja ya haka? Yanzu ke kina nufin idan ban aikata haka ba ba zan iya komawa gidan Abdul ba har abada?"
"K'warai da gaske, sharaɗin da malam ya bayar kenan,kina dai ganin wancan satin irin rashin mutuncin da kakar yaron nan ta yi mana saboda ba a kai mata shi ba,da yana gidan ubansa haka zata faru ne? Dan haka idan kina son ayi komai a gama cikin ƙanƙanin lokaci to ki amince da abinda malam ya ce kawai."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Mommy ta sauke,da wannan maganar suka yi sallama da Naja ita kuma ta kama hanyar gida zata koma,tafe take tana tuna irin dokokin da Innah Laminde take gindaya mata akan Amir,wata iriyar tsana Innahr take yi mata kamar bata taɓa zama surukar ta ba a baya,me yasa Innah Laminde ta kasa gane dik abinda tayi akan kishin mijinta ta aikata shi? Zuciyar ta cike da tunani ta koma gida,dole ne ma ta amince da wannan shawarar saboda ta samu ta maida auren ta da Abdul.
*******************************
Billy da Any sun maida rayuwar su ta koma abun sha'awa ga dik wanda bai san su ba a baya,domin kuwa sun tattare gaba ɗaya dukiyar su sun kyautar da ita ga gidan marayu,hisbah kuwa ta yi musu ƙoƙari ta basu kyautar kud'ad'e,da jin labarin su kuwa gwamna ya bada kyautar sabon gida da motar hawa,tare da jarin million uku aka basu,sanda wannan kyautar ta riske su sun yi kukan farin ciki kamar ba za su dena ba,a yanzu suka tabbatar da cewa idan bawa ya yi tuba na gaskiya zuwa ga ubangijin shi,to lallai Allah zai musanya masa da abinda yafi saɓon Allah'n da ya bari a baya,a baya Billy ta damu da kyautar zunzurutun kud'ad'en da Any ta bayar masu matuƙar yawa, ga kadarori da gidajen su da suke ciki dik ta haɗa ta bayar wa mabuƙata ta bar su babu komai,Billy gama tunanin shikenan za su afka rayuwar tagayyara da ɗimuwa da talauci,sai Allah ya kawo musu taimako cikin gaggawa.
Hukumar hisba da manyan ƙungiyoyin kula da haƙƙin dan Adam na garin kano sun yabawa su Any da Billy akan sadaukarwar da suka yi saboda Allah,ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba har da suka iya barin dukiyar su mai tarin yawa saboda sun san basu same ta ta hanyar halal ba. Tin daga wannan lokacin hukumar take jan su Billy a jiki,dik inda za a je wa'azi za a saka su a gaba a je da su,hakan ba ƙaramin ƙara musu imani yake yi ba,a dik sanda suka je suka dawo daga wa'azi jikin su kan yi sanyi,suna shiga damuwa idan suka tina rayuwar su ta baya,sannan suna godewa Allah da ya basu ikon gane gaskiya kuma suka gyara.
Haka rayuwar su take ta gudana kafin daga baya Any ta zaunar da Billy ta kawo musu shawarar fara kasuwanci,a cewar ta zara bata barin dami,idan basu fara kasuwanci ba kud'in hannun su ya ƙare basu da wanda zai ɗauki nauyin lalurorin su na yau da gobe,Billy ta yi na'am da shawarar sai dai sun jima suna saƙa da warwarewa akan wace iriyar sana'a za su yi?
Watarana Any na WhatsApp tana duba wani group da bata jima da shiga ba,group ne da ake tura littattafan hausa a cikin shi,sai taci karo da wata baiwar Allah marubuciya tana tallan wani littafin ta da ta rubuta me suna MAIDA TSOHUWA YARINYA tare da No wayar ta a jiki (09031416423), kamar wasa sai ta ɗauki No dake jikin rubutun da matar ta tura ta yi mata magana ta private chat,bayan sun gaisa ne tace mata tana son littafin da taga tana tallatawa na MAIDA TSOHUWA YARINYA,nan take matar ta tura mata account No ta saka dubu ɗayan ta aka bata document ɗin littafin.Billy ta nunawa yanda suka yi da matar,nan take Billy ta yatsina fuska ta ce,
"Ke yanzu Any da wannan shirmen ne zamu zuba jari mai yawa mu kama sana'a? Haba dan Allah,ki dinga yin abu da tunani mana please."
"Menene abun rashin tunani anan Billy? Kin kuwa ga irin abubuwan dake cikin littafin? Tinda na shiga group ɗin naga matar na tallata kayan gyaran jikin da take siyarwa na san lallai littafin nada amfani,kuma na nuna maki hirar mu ta sanar dani yawancin abinda take siyarwa ɗin nan akwai su a littafin,muma ba sai mu duba muga wanne zamu iya yi a ciki ba?"
"Gaskiya ni ba zan tsaya shiririta da wasan yara ba,idan gyaran jikin ne mu je mu siyo na shago mu zuba muyi mu samu kuɗi,kowa fa yanzu ya raja'a akan kayan nan na shafe-shafen zamani,waɗannan abubuwan nata dik wahal da kai ne,ko kuma mu fara saida kayan sawa kamar su leshi,atampa,materials da mayafai,ga kuma jakunkuna da takalma dik ana ya yin siyarwa,shagon ƙofar gida kawai zamu gyara mu watsa komai tinda kan hanya muke ba zamu yi wahalar samun masu saya ba."
"Humm ban ƙi shawarar ki ba,amma wannan ɗin ma mu gwada Billy,yanzu ba a zama waje ɗaya,raba ƙafa ake yi saboda zaman banza ba namu bane,kar ki manta wahalar da muka sha a baya muka tara dukiyar haram,idan muka yi haƙuri da wahalar da zamu sha a yanzu watarana sai kiji ana kwatance da mu."
Ajiyar zuciya Billy ta sauke sannan ta ce,
"To wanne suna zamu sanyawa business ɗin namu yanzu?"
"Me zai hana mu saka A&B BEAUTY PALACE?"
Kyab'e baki Billy tayi,dan ita har yanzu shawarar amfani da wani ɗan ƙaramin littafi su kafa sana'a bai zauna mata ba,sai dai bata son hakan ya zame musu matsala ita da Any da ta ɗauke ta kamar babbar yayar ta,da taimakon Allah da addu'a duk wata muguwar soyayya da suka ɗora wa zuƙatan su a baya duk ta kau,har kunyar junan su suke ji idan suna tina rayuwar da suka yi a baya.
Da wannan shawarar Any da Billy suka fara neman kafinta dan ya gyara masu shago,sai da suka kashe sama da dubu ɗari uku wajen ƙayata shagon nasu ta yanda zai jawo musu kwastomomi,ana gama buga kantoci da sanya wall paper su Any suka zuba kujeru masu kyau, ƙarshe sai da ta dinga shiga internet tana ganin yanda masu shagunan gyaran jiki suke haɗa nasu shagunan,sannan suma suka ƙarasa haɗa nasu,dik wanda ya shiga shagon nan sai ya jima yana mamakin yanda akai matan da basu taɓa saida ɗan kunne ba suka ƙirƙiri irin wannan idea ɗin,a cikin satin Any ta shika kasuwa ta siyo kayan haɗin sabulai da ta ga an koyar,ta siyo na body scrub, da man skin da na gashi,da haɗin dilka da halawa,bata baro kasuwar nan ba sai da ta siyo dik wani kayan haɗin gyaran jikin da taga suna da buƙata,a hankali da taimakon matar da ta sayi littafi a wajen ta ta fara haɗa kayan gyaran jikin,bayan sun gama komai Billy ta dinga murna tana tsalle,cike da farin ciki Billy ta ce,
"Ashe dai wannan shawarar mai ɓullewa ce Any,ni fa da dik a tsorace nake kar mu narka kuɗi masu yawa komai ya kwaɓe mana,wa muka ajiye da zai sake ɗora mana jari?"
"Kamar yanda bamu san zamu samu wannan ba Allah ya bamu, Allah zai sake bamu wani Bilkisu,kar ki manta a kasuwanci akwai riba da fad'uwa,dole ne mu sa wannan a ran mu kafin kasuwancin mu ya samu ci gaba,dole ne mu sanya a ran mu cewa komai na Allah ne,shine ke azurtawa ba zafin neman mu ba,eh tabbas ana so ka tashi ka nema kafin ka samu,amma mu sani sai Allah ya nufa zamu samu ɗin,dan haka dan Allah Billy mu sa zuciyar mu da jikin mu a kasuwancin nan,da yardar Allah watarana zamu ji daɗi."
"Inshaa Allahu zan yi dik abinda kika ce, yanzu kawo robobi na taya ki sanya sticker mu zuba abubuwan da aka gama, gobe da sassafe sai mu je mu jera a shagon,zuwa ranar Juma'a sai mu buɗe shago ko?"
"K'warai da gaske, wannan shawarar taki ta yi kyau,Allah yasa mu buɗe a sa'a,zan zauna na tallata mana komai a online idan mun gama,ta hakan ma naga ana samun kwastomomi."
Nan da nan suka haɗu suka dinga saka sticker suna zuba kayan sana'ar su a mazubi suna kullewa,kamar yanda suka tsara kuwa washegari suka zuba kaya suka jera a shagon, nan da nan waje ya haska,Any ce ta zauna a kujerar da ke da table a gabanta,Billy na yi mata dariya ta yi mana short video,kamar abun wasa ta ɗora a shafin ta na TikTok da Instagram,sannan ta saka a status ɗin ta,tana tallata shagon nasu,daga nan suka ƙara share wajen suka goge,Any ce ta ce,
"Sauran mu mu siyo bokitai da babban mazubin da za ana adana ruwa saboda kinga ba kullum ake samun na famfo ba,ina ganin da ragowar 200k ɗin nan na business mu siyo atampa ko leshi mu ɗan gwada zubawa a gefe mu gani?"
"Ah ah yanzu an fi yayin dogayen riguna, ko materials ɗin da ake rigunan dasu sai kig ga mutum ya siya ya kai tela ya dinka masa."
"To ai sai mu gwada materials ɗin mu gani ko?"
"Allah ya kaimu goben mu je tare,wataƙila ma mu samu wasu abubuwan da zamu siyo."
"Amin."
Da haka suka ci gaba da gyare-gyaren da za su yi suka rufe shagon suka koma cikin gida.
**************************
A cikin watanni bakwai da auren Abdul da Huzaimah,babbar yayar su taje gidan ya fi a ƙirga,kullum taje da kalar sauyin da take gani a tattare da Huzaimah,hakan ke saka ta yi mata tambayoyi masu cike da hikima da dabara dan ta gano dalilin rama da lalacewar ta,ita kuwa Huzaimah dik kalar wayo da dabarar da za a yi mata bata faɗin gaskiyar matsalar ta,daga ƙarshe sai yayar ta ta ɗauka ko ciki ne da ita shi yasa ta lalace haka,domin ba kowa ne cikin fari ke yi masa kyau ba,nan da nan kuwa ta baza magana a dangi,ƴan'uwa da iyayen ta da abokan arziƙi sai suka dinga murna Huzaimah nada juna biyu.
Dik abunnan da ake yi Huzaimah bata san maganar da ake bazawa a dangi ba,sai watarana da Abdul ya kai ta ganin gida,tinda ta je mahaifiyar ta ke nan nan da ita,motsi kaɗan zata tambaye ta ko da abinda take marmari a yi mata? ita kuwa sai ta biye mata ta dinga lissafa dik abinda take so,haka Ummahn ta ta dinga jigilar shiga kitchen da kanta tana samar mata dik abinda ta buƙata,kwanan su huɗu suka baro garin Katsina ta koma ɗakin mijinta.
Tinda ta koma Abdul ke rawar kai kamar wani sabon ango,ba dan komai ba sai dan shan wani maganin gargajiya da Innah Laminde ta aiko masa da shi daga ƙauye ya yi,a hankali yake jin jikin shi yana motsawa,dan haka ya ƙudirta a daren ranar da Huzaimah ta dawo zai ƙara shan maganin ya gwada ko zai samu ci gaba.
Ita kuwa Huzaimah tin da ta dawo take d'aure fuska,gaba ɗaya hirar da suka dinga sha da ƙawayen ta da yayyen ta ne ke yi mata yawo a kwanyar kanta,yanda kowa ta buɗe baki take yabon gwarzantaka da ƙwarewar mijin ta wajen gamsar da ita a gado abun ya burge ta,duk yanda suka so su bugi cikin ta dan itama ta bada nata labarin ƙi tayi,sai dai kawai ta dinga dariya tana sunne kai,babbar yayar su ce ta ce a ƙyale ta,da dikkan alama kunya take ji watarana da kanta zata zo tana basu labari.
Hawaye ne masu zafi suka fara gangaro mata, ba tare da ta damu da zubar su ba ta samu waje ta zauna a bakin gado tana karasa sanya wandon baccin ta,Abdul ne ya shiga ɗakin sai ƙamshi yake bazawa,sanye yake da zallan boxer a jikin shi babu ko vest,ɗaga kai tayi ta kalle shi daga sama har ƙasa,gashi nan dai a ido namiji ne mai ƙirar mazantaka,babu abinda Abdussaboor ya rasa daga kyawun jiki zuwa kyawun fata,sai dai ta inda ya kamata ya nunawa mace shi jarumi ne an kassara wajen,lokuta da dama idan ta fara jin haushin shi sai ta danne zuciyarta ta bashi uziri,tinda ba da kanshi ya illata kanshi ba,sannan ko babu komai ta dalilin zai aure ta ne aka illata shi.
Hawayen ta ne suka ƙaru saboda yanda take ji a jikin ta sakamakon magungunan matan da yayar su ta dinga ɗirka mata,idan ta ƙi sha sai ta hauta da faɗa tana faɗin,
'Ke yanzu haka zaki zauna babu gyara? Kar ki manta fa mijin ki ya taɓa wani auren,kika san ita wanne irin gyara take yi da suna tare? To idan zaki gyara ki gyara,idan ba haka ba akan idon ki zai dawo da ita ko ya sake yin wani auren, tinda baya samun yanda yake so a wajen ki.'
Kuka ta rushe dashi sannan ta kifa kanta a saman gadon,nan take jikin Abdul ya yi bala'in sanyi,dik wani karsashi da ƙwarin guiwar da ya shiga ɗakin dashi ta kashe masa shi,cikin hanzari ya isa gaban ta ya tsugunna ya kama hannayen ta dika biyu cikin nashi,muryar shi a matuƙar sanyaye ya ce,
"Dan Allah Baby ki tashi zaune ki sanar dani abinda ke damun ki,ko dai na yi maki wani laifin ne ban sani ba?"
Girgiza kai Huzaimah tayi tana zubar da hawaye tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi,sake rikicewa Abdul ya yi ya ɗauke ta gaba ɗaya ya ɗora a cinyar shi,a hankali ya ke shafa bayan ta da sigar rarrashi,cikin sauri da zafin nama Huzaimah ta tashi daga jikin shi ta tura shi baya sai da ya kwanta a saman gadon ba tare da ya shiryawa hakan ba,kuka take yi kamar wadda aka yi wa dukan tsiya,cikin kukan ta hau nuna shi tana nuna kanta ta ce,
"Dan girman Allah ka dena taɓa ni,ka dena saka min rai akan abinda ba zan taɓa samu ba, na amince zan yi rayuwar aure da kai,amma ba zan sake yarda ka dinga jagwalgwala ni kamar ka samu mage ba,bana son abinda nake ji a jiki na, bana son abinda kake yi min ka kasa ƙarasawa,ban san yanda ake ji ba,amma zuciya ta na kwaɗaita min abinda ƙawaye na ke faɗa ana ji idan ana mu'amalar auratayya tsakanin miji da mata,dan Allah ka sama min mafita na gaji,na gaji Abdussaboor ba zan iya jurewa ba."
Zubewa tayi a ƙasan wajen ta ci gaba da rusa kuka mai ban tausayi,cikin hawaye Abdul ya miƙe ya bar ɗakin da sauri ya faɗa nashi,wasu zafafan hawaye ne ke kwaranya a idanun shi kamar an kunna famfo,Hadiza ta cutar da shi,me ya yi mata a rayuwa mai muni da zata illata shi haka? Ya so ta a lokacin da kowa ke yi mata kallon ƴar iska,ya rufa mata asiri ya aure ta dik da ya san ita ɗin ba budurwa bace,sannan ta yi yawon karuwanci,shine zata saka masa da nakasa shi irin haka? Yanzu shikenan duk duniya Amir ne kawai ɗan shi? Cikin kuka ya zauna a bakin gadon ɗakin shi ya furta,
"Ban taɓa ganin butulu a duniya sama da ke ba Hadiza,na so ki,na ƙaunace ki,na zauna dake a yanda kike,na kyautata maki a zaman da muka yi,na maida ke sarauniyar mata,babu abinda bana baki kafin ma ki tambaya,ke da kan ki kika sani na ɗaukar maki alƙawari a lokacin da zuciyata bata so,me yasa zaki nakasa ni akan na zaɓi na raya sunnar Annabi dan gujewa zina?"
Rashin samun amsar tambayar shi ne ya sanya shi ɗaukan wayar shi ya kirawo Bilal,Bilal na zaune ya na karatun ƙur'ani bayan ya idar da sallar isha'i ya ga wayar shi na haske,hannu ya miƙa ya ɗauka sannan ya saki murmushi,yana amsawa ya fashe da dariya ya na faɗin,
'Allah ka aurar dani a wannan shekarar na huta da wannan rawar kan da ake min, tin jiya ka ƙi.....subhanallahi kuka kuma? Me yake faruwa? Dan Allah ka dena kuka habaa sai kace ba namiji ba? Me ya yi zafi haka?'
"Bilal bani da amfanin komai a matsayina na ɗa namiji,Bilal ka bani shawara kamar yanda ka saba bani, ya zan yi da matsalar dake tattare da ni akan auren Huzaimah? Yarinyar nan ta yi haƙurin zama dani,a yanzu kuma haƙurin nata ya ƙare,dan Allah ka bani shawara kamar yanda ka saba................."
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
*Masu tambayar novel daga farko ina mai sake baku haƙuri,ku diba wattpad ko WhatsApp channel d'ina za ku samu,an kai wata kusan uku ana tura maku novel a group ɗin da kuke baku fara bi ba sai yanzu da aka kai page har 95? Ai ko kun san ba zai yu a sake tura maku daga farko ba,ku jira a haɗa document amma fa ba kyauta bane.*
PAGE 95:
Gyara zama Bilal ya yi da kyau kafin ya rufe ƙur'anin dake hannun shi ya mayar dashi ma'ajiyar shi,cike da natsuwa ya ce,
"Abdul ka kwantar da hankalin ka dan Allah,ka yi alwala kayi sallah sannan ka roƙi Allah ya yi maku zaɓin alkhairi a rayuwar auren ku,domin ni kaina yanzu ban san kalar shawarar da zan baka ba, addu'a kawai zan taya ku,Allah zai kawo maku mafita,zuwa da safe zan zo gidan daga nan sai mu wuce office."
"Na gode Bilal,har ka sa na ji sanyi a zuciya ta,inshaa Allahu zan yi yanda ka ce,Allah ya shiga lamuran mu,sai da safen zan jira ka inshaa Allahu."
Da wannan shawarar suka kashe waya,Abdul bai ɓata lokaci ba wajen zuwa ya yi alwala ya tada sallah,sai da ya yi nafila raka'a shida kafin ya zauna ya yi addu'a sosai ya shafa,yana idarwa ya naɗe abun sallah ya ajiye a inda ya dace sannan ya haye gado,ya jima a kwance yana juyi kafin ya samu bacci ya ɗauke shi cike da tunanin Huzaimah.
Tinda ya kwanta bai motsa ba sai takwas da rabi na safe, wayar shi dake ta ƙara saboda kiran da ake zabga masa ya jawo,lamabar Bilal ya gani, cikin sauri ya kalli lokaci,a guje ya sauka daga gadon shi ya faɗa banɗaki brush ya fara yi sannan ya watsa ruwa ya yi alwala ya fito,sai da ya yi sallah sannan ya fita zuwa parlour,a saman dinning table ya tarar da Bilal yana kwasar girki,zama shima ya yi sannan