Showing 84001 words to 87000 words out of 276165 words

Chapter 29 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

masoya,shi yasa ko maza ne ke son yin suna to fa hotuna da videos ɗin mata kawai mutum zai saka ya dinga trending ko ina.

Tana nan zaune taji qarar mota a qofar gida, ba tare da ta yi tunanin ko Abdul bane ta ci gaba da abinda take yi,ba jimawa Bilal ya riqo Abdul suka shiga ciki suka zube a kujera ba tare da sun kula da Billy ba.

A hankali Mommy ke tafiya tana shiga cikin gidan riqe da jaka tana tsiyayar da hawayen da suka qi tsayawa,parlourn itama ta shiga ta zauna a qasan carpet kanta a qasa, cikin mamaki Billy ta nufi wajen mommy da gudu ta rungume ta tana faɗin,

"Alhamdulillah Mommy ina kika shiga muka dinga neman ki? Hajiya saida ta bada cigiyar ki wajen mutanen mu saboda Alhaji ya kashe wayar shi ya goge accounts ɗin shi da za a iya samun ku,Mommy na shiga damuwa da tashin hankali har bacci nake kasawa idan dare yayi saboda ina tunanin halin da kike ciki"

Janye jikinta Mommy tayi daga na Billy ta koma gefen qafar Abdul ta zauna ta ci gaba da kuka, wani irin mamaki ne ya shanye Billy a wajen ta qame tana kallon ikon Allah,Bilal ne yace,

"Alhamdulillah Mommy sunan ta dama?"

Cikin kuka Mommy tace,

"Suna na Hadiza Ɗan liti,"

"Hadiza? To wacece Mommyn?"

In ji Bilal da ya zama confused,cikin sanyin shi da natsuwar shi ya tashi zaune daga kashingid'ar da yayi yace,

"Dik sunan ta ne idan na fahimta, yanzu ku bar wannan maganar har iyayen ta su iso a je gaban mai martaba a yi wannan case ɗin bana son hayaniya ki dena min kukan nan da kike yi dan bashi da wani amfani a wajena,"

Gimtse bakin ta mommy tayi har da saka hannuwanta biyu ta riqe shi, hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta, ga tsoron ance Innoh da Babanta na nan tafe,Billy da ta daskare a wajen ce ta samu damar magana cikin rud'anin da ta shiga tace,

"Mommy wai meke faruwa ne haka ki yi min bayani na sha wahala Mommy wajen neman ki,na azabtu da rashin ki Mommy please ki yi min magana mana,"

Qala Mommy bata ce ba dan kuwa yanzu tunanin ta ya tafi wajen zuwan iyayen ta da Saddeqa tare da tunanin yanda case ɗin zai kasance.

Suna nan zaune suka sake jin qarar mota, ba tare da Abdul ya kula kowa ba ya leqa d'akin Innah Laminde da ke nad'e abin sallah ya gaishe ta, kallon shi tayi da kulawa tace,

"SARAUTA lafiyaa kake kuwa? Kaga yanda idanun ka suka zurma ciki kodai ka yi jinya ne?"

Da jin kalaman mahaifiyar shi sai zuciyar shi tayi rauni, tinda aka fara maganar bai samu k'walla ta taru a idanun shi ba sai yanzu hawaye suka samu damar ɓalle masa kamar da bakin ƙwarya,cike da matsanancin tashin hankali Innah Laminde ta isa gaban shi ta dafa kafad'ar shi, da sauri ya ɗora kan shi a kafad'ar ta yana ci gaba da kukan shi kamar wani qaramin yaro.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeelu Abdussaboor me ya same ka haka kake kuka?"

A can parlour kuwa tini Sultan ya sanar da su su je fada wajen mahaifin su iyayen Mommy sun iso, bayan kowa ya tafi ne ya leqa d'akin Innah Laminde ya sanar da su a haɗu a fada yanzu iyayen Mommy sun zo.

"Kai sultan me ya sami yayan ku yake kuka haka? Yaron da rabon shi da kuka har na manta"

Cikin tausayawa Sultan yace,

"Innah magana ake ta zuciya da yarda da amana da aka yi wa rugu-rugu kin ga ko dole zuciya ta karye idanu su yi tsartuwar ruwa, ɗan ki dai daga qarshe ya faɗa soyayya amma da baragurbin k'wai me wari"

"Allah ya fitar da kai Babana,Allah ya sassauta maka, lallai kana cikin jarabawa, Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar, maza jeka ka wanke idon ka, ko 'yar wacece ta sanya min gwarzon ɗa na kuka itama sai ta yi kuka,idan ka gama ka same mu a can fadar,"

Hijabin ta ta ware ta sanya ta fita ranta a matuqar b'ace, dan kuwa bata ɗaukan lamarin Abdussaboor da wasa a kaf yaran ta,yau zata ga wacce mara rabon ce ta sanya mata shalelen ta kuka.

Suna fita Abdussaboor ya shiga band'aki ya wanke idanun shi sosai da sabulu sannan ya sa zanin Innah dake jikin qofar ya goge fuskar shi ya tsane gemun shi da kyau sannan ya fita ya nufi fada inda kowa da kowa ke jiran shi.

Yana shiga ya tarar da wajen a cike da mutane wanda da gani iyayen Mommy ne da 'yan uwan ta, idanun shi akan fuskar Saddeqa da ke zaune kusa da Billy suka sauka,kanta na qasa tana wasa da yatsun ta, tabbas wannan idanun ya gani ranar da yaje makarantar su Saddeqan, tabbas gashin idanun su da girar su da Mommy na matuqar kama, nan take ya gane dalilin da ya sanya shi shiga rud'ani har ya ɗauki mommy a matsayin Saddeqa, a ranar da ya ga Saddeqa iya idanun ta da girar ta ya gani ta sa qur'aninta ta kare hancinta da bakin ta,wannan shine dalilin da yasa sanda ya ga mommy na leqe ya ga iya idanun ta da girar ta yayi zaton saddeqa ce, to amma me yasa da ya ce mata Saddeqa bata sanar da shi gaskiya ba ta yi shiru ta bar shi ya kamu da mugun son ta irin haka? Me yasa ta ha'ince shi? Me yasa ta ci amanar soyayyar shi?????..........

*To amsa na wajen Gimbiya Mommyn Ɗan liti*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI















RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨












PAGE 32:












A jikin ta taji ana kallon ta, dan haka cikin sanyin jiki ta d'aga kai dan taga waye yake yi mata kallon qurilla take jin ta a takure, ido huɗu suka yi da Abdul dake kallon ta cike da tsantsar so da qauna, da sauri ta kauda kan ta tana jin wani irin tsoro da fargaba na shigar ta, cikin wata murya mai dattako aka ce,

"Babana samu waje ka zauna mana, Mai dusa da iyalin shi na hanya dan kuwa har su na aika a kirawo zaman ba zai cika ba sai an haɗa dika bangarori dan jin ta bakin kowa,"

Zaman shi ke da wuya aka yi sallama, izinin shiga aka bawa mahaifin Billy da mahaifiyar ta, suna shiga Billy ta hau turo baki ita ga shagwab'ab'b'iya,gyaran murya mai martaba yayi sannan yayi musu sallama ya ɗora da faɗin,

"Abinda yasa na tara ku anan shine ina son sanin me yake faruwa ne a garin nan namu mai albarka da har yara mata kamar waɗannan za su bar gari su ƙetara wani garin dan yin aikatau, shin talaucin dake cikin wannan qasar har ya kai ga a bar yaran da suka isa zama iyayen wasu su bar gaban iyayen su su tafi wata uwa duniya? Kai Mai dusa iya sani na dakai Allah yayi maka rufin asiri ko zan iya sanin dalilin aika 'yar ka ta cikin ka aikatau birni?"

Cike da jin kunya da nauyi mahaifin Billy yace,

"Allah ya baka yawan rai ni kaina yanzu bana ce ga dalilin barin wannan 'yar zuwa birni ba, sai dai in ce qaddara, dan kuwa alhamdulillahi Allah ya bani cin yau da na gobe har ma da na jibi da gata,wasu ma suna samu su ci a qarqashi na ranka ya dad'e,"

"Alhamdulillahi tinda ka yi wannan bayanin da kan ka, kai kuma ƊAN LITI zaka iya yi min bayanin dalilin barin 'yarka budurwa kamar wannan ta shiga duniya aikatau?"

Da hannun rigar shi Ɗan liti ya goge zufar saman leb'en shi na sama da karan hancin shi ya laso leb'en shi da basa iya rufe haqoran shi sannan yace,

"Allah ya bawa sarkin mu mai adalci yawan rai babu ce ta jawo na amincewa yarinya ta ta tafi aikatau,ranka ya dad'e ka san sana'a ta ba wani samu ake yi ba, qarshe watarana mata ne za su ci da kan su da yara har nima a tsakura min,Allah ya baka yawan rai tin ana maganar tafiya aikatau ina qi har dai watarana Bilkisu 'yar gidan Mai dusa tayi nasarar jan ra'ayin Hadiza, Hadiza kuma ta ja ra'ayin mu ni da mahaifiyar ta muka amince mata,"

"To alhamdulillahi idan dai na yi dai-dai a hasashe na gaba ɗayan ku rashin godiyar Allah ce ta janyo kuka aika yaran ku inda baku sani ba, garin da baku taɓa takawa ba kawai dan su kawo muku kuɗi kuka bar su suka tafi,kun san wanne irin aiki suke yi? Haqqin ci da ku da sama maku yalwatacciya kuma ingantacciyar rayuwa akan su dama ya rataya ko akan ku ku iyayen su? Me yasa ku iyayen su idan kun ga kulawar da kuke baiwa yaran ku ta gaza ku ku fita ku qara da wasu sana'o'in dan yalwata iyalan ku? Mata kuma da suke ci da kan su da yara da miji dik ba a cikin arziqin da ubangiji ya azurta ku da shi bane? Yanzu misali ace kai ka fita baka samo komai ba, suma da suka kasa tallar su a gida ba a siya ba,to dame zaku ci abincin? To amma Allah ba azzalumin sarki bane sai ya hore maku idan kai baka samo ba matan ka nada shi, sai ku haɗu ku rufawa kai asiri.

Masu zuwa aikatau ma saboda neman kud'in saiwa yaran su kayan d'aki talakawa ne tuluf da basu da me yi musu, kai Mai dusa yanzu idan auren 'yarka ya tashi ba zaka iya sai mata kayan gado biyu da kujeru seti ɗaya ba?"

Cikin jin kunya da nauyi Mai dusa yace,

"Zan iya Allah ya taimaki sarkin mu mai adalci,"

"Kai Ɗan liti idan auren Hadiza ya tashi idan kai baka da na siya mata gado kana tunanin ɗan ɗan uwan ka ba zai taimaka maka ba ne? Ko kafff dangin ku babu mai taya ka yi mata kayan d'aki dole sai ta fita aikatau? A nan fadar akwai tallafi da ake baiwa marasa qarfi idan za a aurar da su wanda yake fitowa daga dukiyar talakawan garin nan namu da aljihu na da na Abdussaboor,kun san da hakan amma kuka aika yaran ku aikatau, to yanzu ke Hadiza ina so ki sanar dani garin yaya aka sace ki?"

Cikin kuka Mommy ta d'aga kai ta kalli Billy dake roqon ta da idanun ta akan kar ta tona masu asiri, rasa yanda zata yi da ranta tayi sai kawai ta qara fashewa da kuka, cikin takaicin ta Bilal yace,

"Ke ba kuka zaki yi wa mutane ba mai martaba da kan shi yake tambayar ki a garin yaya aka sace ki har aka kai ki qasar turawa SARAUTA ya taimaka maki kika ha'ince shi kika ci amanar shi,"

Kallon Bilal Innoh tayi ta banka masa harara sannan tace,

"Bawan Allah ya da daka mata tsawa ai ka bari Mai martaba yayi mata magana da kan shi ko?"

Abdul ne ya d'aga kai da jajayen idanun shi da suka sake rinewa ya kalli mommy cikin bada umarni yace,

"Ke muke saurare,"

Da sauri Billy ta karɓe maganar da faɗin,

"Ranka ya dad'e laifi na ne da na kai Mommy gidan aikin da suke maha'inta, a can ne aka rud'e ta suka yi safarar ta zuwa qasar waje suka saida ita,ni kaina ban sani ba sai daga baya, lokacin da na sani kuwa ba abinda zan iyayi akai shi yasa na bazama neman ta ko ta ina amma ban same ta ba, wannan dalilin ne ya sa na shirya na shigo garin nan dan in ga ko ta dawo gida sai kuma naga ba haka ba,"

Kallon ta Innoh da Ɗan liti suka yi Innoh tace,

"Amma dai Bilkisu an yi shegiyar yarinya, shine har da bani atampa da leshiri da dubu goma ki ce inji Mommy? Ashe kuna can kun sayar min da 'yar tawa?"

Kuka mommy ke yi sosai dan tunawa da Alex da azabar da ya gana mata, babu wanda ya san meke cikin zuciyar ta na qunci da damuwa,Innoh ma kukan ta saka tana kallon yanda gaba daya Mommy ta koma jaaaa saboda kuka,daga sama suka jiyo muryar Abdussaboor na faɗin,

"Ko zan iya sanin dalilin da yasa kika yi qarya da sunan 'yar uwar ki?"

Da rarrafe Mommy ta isa gaban Abdul tana kuka tace,

"Dan Allah ka yi hakuri da abinda na yi na qin sanar da kai ni ba Saddeqa bace a farkon haɗuwar mu, na yi haka ne saboda gudun kar ka fasa kub'utar da ni daga cikin tashin hankalin da na shiga, jin cewar ka san qanwata ya faranta raina har na ji be kamata na sanar da kai asalin suna na ba har sai na kub'uta gaba ɗaya, da na san zan kamu da son ka a zuciya ta da ban yi maka qarya ba, da na san zaka kamu da soyayya ta har haka da ban ci amanar yardar ka ba, dan girman...."

"Kan uban can, wai Yah Abdul da gaske kana son wannan abar?"

Billy ta katse Mommy tana jijjiga idanun ta na tara k'walla,cikin wata iriyar muryar da ke nuna tsananin danasani Abdul yace,

"A da ba ! dan kuwa a yanzu babu wadda na tsana bana so na buɗe ido na gani da ta wuce wannan yarinyar maha'inciya, kin ha'ince ni Hadiza, na fara son Saddeqa tin kafin na bar qauyen nan na koma bakin aiki na,na sa a yi min bincike akan gidan su dan na sanar da iyayen ta ina son ta, ban kai ga aikata hakan ba kika shigo rayuwa ta kika gurɓata komai, ba zan yafe miki abinda kika aikata wa zuciya ta ba,"

Munir da tinda suka shigo yana danna waya be d'ago ba sai da yaji ana zancen Saddeqan shi ya d'ago yana bin su da kallo, dan har ya fara qosawa da wannan zaman da yake ganin be shafe su ba shi da Saddeqa amma an kirawo har da su an hana shi tafiyar shi dake gaban shi, cikin sauri ya kalli Abdul dake magana cike da b'acin rai yace,

"Ah ah fa ranka ya dad'e Saddeqa na da mijin da zata aura da zarar ta kammala sakandire,"

Ko kallon Munir Abdul be yi ba ya kalli mahaifin shi dake kallon kowa yana jin abinda suke faɗa baki ɗayan su,

"Allah ya baka yawan rai ni yanzu amsar tambaya ta ta samu,dan Allah ina so ka nema min auren Saddeqa gata ga ka ga kuma mahaifin ta anan ina tare da kuɗi a jiki na ko yanzu a d'aura mana aure da ita,"

Murmushi Sarki yayi irin nasu na manya sannan ya kalli ɗan nashi da tausayawa domin kuwa Abdul bai taɓa shiga irin wannan halin da yake ciki ba a yanzu,amma dole ne ya bashi hakuri dan kuwa ba zai zama sarki mara adalci ba.

"Abdussaboor ba haka ake yi ba ai, ita yarinyar ai ya kamata a ji ta bakin ta akan wanda take so ko? Ba za a yi mata auren dole ba tinda ga masoyan a gaban magabatan ta dan haka ke yarinya ko zaki iya yin alamar da zata nuna zaɓin ran ki a cikin waɗannan mazan guda biyu dake son ki da aure?"

Cike da jin kunya Saddeqa ta sake sunkuyar da kan ta qasa tana wasa da yatsun ta, gefe ɗaya na zuciyar ta na tinanin alamar da zata yi a gane ita Munir take so,Munir kuwa zuciyar shi banda bugawa babu abinda take yi tsoron shi kada Saddeqa ta ji tsoron ganin suna fada ta zaɓi ɗan sarki ta bar shi, Abdussaboor kuwa har ya cire rai da jin wannan maganar da mahaifin shi yayi, ya tabbata Munir zata zab'a saboda da dikkan alamu sun nuna shi take so, yaso kawai yau a karo na farko mahaifin shi yayi amfani da mulkin shi a aura masa Saddeqa, tunanin shi ne ya katse a lokacin da Saddeqa ta tashi zaune ta koma gefen Munir ta zauna ta na rufe fuskar ta,murmushi Ɗan liti yayi wanda ya bayyana farin cikin shi, dik da cewa har yanzu baya kula Saddeqa da Sadeeq hakan baya nufin baya son farin ta, cikin b'ata rai Innoh tace,

"Amma dai kin san 'yar uwar ki Ameerah na can kwance babu lafiya saboda yanda take son Manniru ko? Yanzu ke baza ki iya hakuri ki bari ta aure shi ba ko dan ta tsira da rayuwar ta?"

Daga yanda take magana Abdul ya gane ba itace mahaifiyar Saddeqa ba, dan haka kafin Sarki yace wani abu ya riga shi magana,

"Kin san kuwa zafin rabuwa da masoyi? Ita idan aka raba ta da nata masoyin kika san wanne hali zata shiga? Tinda har suna son junan su ba wanda zai raba su,Saddeqa ina yi miki fatan alkhairi na ɗauki qaddara ke ɗin ba rabona bace, nayi nauyin baki gashi na rasa ki,ina fatan Allah ya baku zaman lafiya ni kuma yayi min zaɓin alkhairi,"

"Shikenan magana ta qare Babana ya gama magana, dan haka ina rokon ku da kowa ya zauna yayi wa kan shi karatun ta nutsu, ku iyaye maza da kuma iyaye mata ku sani yaran ku amana ce daga wajen Allah ta musamman wanda ba kowa yake baiwa ba, mutum ma ya baka amana yana tsammanin kar ka wulaqanta amanar shi balle ubangiji mu Allah? Dan haka komai kyawu da kuma munin yaran ku,komai fasaha da rashin fasahar yaran ku, komai arziqi da rashin arziqin yaran ku ku so su daidai, sannan ku basu tarbiyyar islama, kuma ku dage ku ɗauke dikkan lalurorin su, mata a haɗa kai da mazaje dan kula da iyali, babu ruwan ki da ai haqqin shi ne ba zan taimaka masa ba bayan kina da halin taimakawar,kar ki manta idan asirin mijin ki ya rufu naki ya rufu,idan kuma asirin shi ya tonu dan nema maku abinda zaku ci to fa naki kema ya tonu, dan haka a zauna bisa gaskiya da amana,Allah ya yi wa kowa zaɓin mace ta gari ya shiryar mana da zuri'a da dikkan musulmi,daga yanzu bana son na sake jin wai an samu wata a garin nan da zata qetare ta tafi aikatau na soke wannan maganar, wanda duk be ji ba ba zai qi gani ba,na sallame ku,"

Da sauri Billy tace,

"Baba ya zaka sallame mu baka sanar da auren mu ni da Yah Abdul ba, ni fa shi nake so, indai ana so na zauna a garin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login