Showing 129001 words to 132000 words out of 276165 words
Chapter 44 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ta,"
"Ko ɗaya,inshaa Allahu Hadiza ta gama shashanci Yah Abdul, amma dole ne sai na ɗana mata tarko kafin na kama ta ko?"
"Haka ne kuma,"
Suna nan zaune suna ta hira sultan ya zo kawo abinci, Mommy ta shiga d'aki har ya tafi basu haɗu ba, sai da ya wuce ne ta fita suka zauna suka ci suka sha.
Da rana bayan Abdul ya fita gidan su gaida iyayen shi, Sule ya je ya kai mata kayan ta, ita kuwa ta buɗe ta ɗakko ATM card ɗin ta ta sanar da Sule pin ɗin ta tace yayi amfani dashi a sai wa Ameerah kayan d'aki a yi mata jere na kece raini, kar ya sake ya baiwa kowa nera a hannu Ameerah kawai take so a yi wa kayan d'aki mai kyau, dan tasan halin Innoh da kud'in nan sun shiga hannun ta shikenan ba lallai ayi abinda ya dace ba.
Sule bai bar gidan ba sai da yaci ya sha ya qoshi sannan ya tafi gida dan isar da saƙon Hajiya Hadiza.
************************
Ihun murna mata da mazan dake tsaye a cikin wani madaidaicin gida ke tayi kamar qananan yara, Billy ce jingine da wata mota mai shegen kyau da tsada kalar maroon sai walqiya da ɗaukan idanu take yi,hotuna kawai ake zabga mata da video,nan da nan social media ta ɗauka ana haska ta, YouTube channels kala kala kuwa na bayyana shahararriyar 'yar TikTok ta samu kyautar gida da mota daga boyayyen saurayin ta.
Wasu irin matsattsun riga da wando ne farare tass a jikin ta, sai makeup da aka tsara mata da ya fitar da kyawun ta,ga wani uban kitson da aka yi mata har yana tab'o mazaunan ta, wayar ta mai tsada ta buɗe a kwali tana nuna wa sabbin ƙawayen ta da kuma tsoffin ƙawayen ta na TikTok, ihu wajen ya sake ɗauka da shi ana kyasce ta da hotuna da ɗaukan sabbin Videos ana watsawa a social media.
Drinks da kaji matasa ke ta d'iba suna guziri dashi a lokacin da taro ya tashi za su tafi gidajen su,da misalin qarfe sha biyu da rabi kuwa kowa ya watse an bar gidan babu kowa daga Billy sai halin ta, a dai-dai wannan lokacin kuwa da kowa ya tafi sai ta samu ta rufe ko ina na gidan ta kunna kiɗa ta fito da kayan shaye-shayen ta ta baje su a gaban ta tana kallon su, wani irin farin ciki take ji mara misaltuwa, da ta san haka rayuwar 'yanci take da daɗi ai da ta jima da barin Hajiya K'waisa ta sa Man ya sai mata gida,amma yanzu ma lokaci be ƙure mata ba ai zata shana ta wataya ta ji daɗin rayuwar ta tinda iyayen da suka haife ta sun gaza wajen wadata ta da abubuwan more rayuwar duniya.
Har ta zauna ta d'aga kwalbar Syrup zata kwankwad'e wayar ta ta fara ringing,kallon No ta sake yi da kyau dan ta tabbatar shin da gaske ita me wannan No ke kira ko kuma gizo idanun ta keyi mata?......................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 50:
Ɗaukan wayar tayi ta kara ta a kunnen ta sannan tace,
"Uhummm lafiya kike kira na a wannan daren?"
Daga can ɓangaren ne aka yi dariya da wata siririyar murya, kafin daga bisani mai kiran wayar ta furta,
'Lafiya ƙalou Billisious 'Yar sanata masu nerori gida da mota hajji duk sati, na ji irin abun alkhairin da ya same ki ne ya sanya ni zuwa har gidan naki na taya ki murna amma ina ga kamar nayi latti bari na juya..."
Cikin hanzari Billy tace,
"Noo baki yi latti ba, bari nazo na buɗe miki gate ɗin,"
'Ok ina jiran ki a waje,ina fatan gidan naki zai iya ɗaukan mota uku dan baby na a matsayin mota biyu take,'
"Har huɗu ma filin gidan nan zai iya ɗauka dan haka ki jira ni kawai,"
Koda Billy ta fita waje sai taci karo da wata hamshaqiyar motar da ta dame tata ta shanye,wata siririyar mace ce fara fat mai kyau a cikin motar, sai da ta samu wajen yin parking sannan ta yi ta fito tana kulle motar hannun ta riƙe da manyan wayoyi 'yan yayi, jaka ce mai tsadar gaske rataye a kafad'ar ta,ƙafafun ta kuwa sun coge a saman takalmi mai tsananin tsinin da ta sanya musu,gashin dokin dake kanta ta gyara ya kauce daga fuskar ta ta fara taku cikin yanga ta isa wajen Billy dake ƙare mata kallo, siririyar matar na isa gaban Billy sai ta rungume ta tsam a jikin ta cikin wani irin salo na 'yan bariki, jikin Billy ne ya karb'i saƙon da aka aika masa dashi dan kuwa kar ta san kar ce a tsakanin su, nan take ta rintse idon ta saboda bata so ta saki jikin ta da matar daga baya azo ana samun saɓani.
Ciki Billy ta ja matar suka shiga, banda kallon parlourn babu abinda matar keyi,a tsakiyar parlourn ta cire takalmin ta da ya dami ƙafafun ta da ciwo, sannan ta ajiye wayoyin ta da makullin motar ta tare da jakar ta a saman center table na glass dake tsakiyar parloun,zama tayi ta shafa cinyoyin ta dake waje da siraran hannayen ta da suka sha dogayen farata sannan ta harɗe ƙafafun ta waje ɗaya taa wani kwarkwasa,sake maida gashin ta baya tayi kafin cikin yanga ta karb'i glass cup ɗin da Billy ta zubo mata shampain a ciki ta miqa mata,baki ta yatsina sannan tace,
"Thank you, and congratulations 'yar uwa, kema da alama kan mage ya waye kin gane zaman kan ki ba tare da kin jingina da kowa ba ya fiye maki,na yi matuƙar mamaki da naji su Sally na maganar wai kun ɓata da K'waisan alheri kema kin kafu har ma ta nuna min gida da motar da aka yi maki kyautar su, to kin dai gani ko? Taya zaka zauna kana neman kuɗi da jikin ka amma ace sai ka raba da wani ƙaton da shima neman nakan shi yake yi? Yaci naka ya ci nashi duk shi ɗaya, ina taya ki murna da samun 'yancin kai sister,"
Cikin murmushi Billy tace,
"Lallai sai yanzu na gane dalilin ki na barin gidan Hajiya K'waisa Amy,amma dik da haka ba zan fasa faɗa maki gaskiya ba, ta yanda kika bar gidan be kamata ba saboda ko babu komai ya taimaka maki a rayuwa,ni kin ganni nan, garin mu suka je su taya ni faɗa aka rarako su yaji haushi ya kore ni, na tabbata da an kwana biyu naje na marairaice zai hakura, iyaka dai ba zan sake zama a ƙarƙashin shi bane kawai,"
Murmushin gefen baki wadda aka kira da Army tayi sannan tace,
"Uhumm ku kuka sani, ni dai na zama free daga cutarwar da ake yi min, ni nasan maƙudan milliyoyin da gardin nan yaci min,wataƙila bai taɓa sanar dake bane saboda kar a ga laifin shi,Allah dai ya kyauta, gaskiya gidan ki yayi kyau ba ƙarya,nima zan so na kai ki nawa ki gani watarana,ban ma jima da komawa cikin shi ba, tsohon sai na barwa ƙani na da yayi aure last 2 months,"
"Woww ! lallai kina wuta Amy,Allah ya kaimu watarana a nuna min gidan, ai ina jin yanda ake maganar gidan ki rannan a wani live da na hau na Sally,"
"Hummm ke ni fa bana son ƙaramar harka da kika ganni nan, dan kuwa yanzu ba safai ma nake harkoki da mutanen Africa ba, nafi son inda zan tsallaka masu jajayen kunne mata ko maza su biya ni da dollars,"
Ihu sosai Billy tayi ta jijjiga shampain ɗin hannun ta ta d'aga sama kumfa ta zube,miƙewa Amy tayi suka hau taka rawa suna shan shampain suna haɗawa da kayan maye,kayan cajin na fara faɗa masu gabas ta koma kallon kudu sai suka fara neman junan su kamar mayunwatan zakuna a daji,ina ganin haka nayi tir da wannan mummunar dabi'ar shaye-shaye da neman jinsi da ya shigo mana cikin al'ummar Annabi muhammad yaran musulmi suka maida shi ba komai ba,na bar gidan na koma gidan Mommy.
*****************************
Tinda suka dawo daga gidan Sarki Mommy ke kuka a jikin Abdul, yayi lallashin duniya taƙi shiru, sai ya samu ta rage sautin kukan sai ta sake fashewa da wani sabo,cikin muryar lallashi yace,
"Dan Allah Baby kiyi hakuri komai ai ya wuce ko? Bilal ɗin ma ya koma Kano yau kuma kin ga ban kyale shi ba sai da na yi masa tataa,sannan kin riga kin sanar dasu Innahta Billy bata gidan da kika santa a da dan kuwa da bakin ta ta sanar da ke bazata koma can ba sun kore ta to kukan na menene?"
Kallon shi tayi ta fyace majina da tissue sannan ta mele manyan leb'unan ta tace,
"Habaa baby...tayaya zaka ce bazan yi kuka ba bayan a gaban ka Innah ta gama kallo na tana harara ta tare da faɗa min baƙaƙen maganganun dake nuni da cewa bata so na ita da Umman Billy? Na tabbata sai an shiga rayuwar auren mu ba zamuyi rayuwar farin ciki ba ni da kai,shi kuma Bilal da har ya iya kallon ido na ya sanar dani baya so na baya ƙauna ta kara yake yi maka yaje na bar shi da Allah, Allah ya saka min,"
Kuka ta sake fashewa dashi ta kwanta a jikin Abdul ɗin da gaba ɗaya ya gaji da jin mitar ta, a hankali ya fara aika mata da saƙon da ya mantar da ita akan me ma take kukan,cikin sauri suka kashe fitila suka barni ina lalube a duhu ina neman hanyar fita.
Washegari da asuba Abdul ya tashi ya saisaita ruwan wanka ya ɗauki Mommy dake ta yi masa qananun mitar ya tashe ta tana tsaka da bacci ya je ya tsoma ta a kwamin wankan su, tana jin ta a ruwa ta buɗe ido ta hau kukan Shagwab'a, dariya yayi kawai ya shiga suka yi wanka tare kafin daga ƙarshe suka yi wankan tsarki suka fito daga band'akin.
Wajen kayan ta yaje ya ɗakko mata jallabiyya dan ya kula bata da hijabai sai dogayen riguna ya sanya mata ya bata d'ankwalin yace ta sanya dan bai iya ba, baya so ya tafi masallaci ya barta ta koma bacci shi yasa ya tsaya dan ya taya ta da kan shi.
Bai fita ba sai da ya ga ta tada kabbara sannan ya fita ya rufe gidan ya wuce masallaci, tana tabbatar da ya bar gidan ta cire kayan ta ta haye gado tana hamma, idanun ta har wani hawaye yake ji da yaji saboda baccin da take ji,cikin muryar bacci tace,
"Sallar nan fa koma nayi ta ance ba Karb'a za a yi ba tinda naje wajen mai duba,to ina dalilin wahal da gab'ob'i na bayan gajiyar da ka tara min jiya? Anjima idan na farka na haɗe su da azahar."
Baccin ta ta koma tasha dan kuwa da Abdul ya dawo ya ganta tana bacci shima sai ya cire rigar shi ya kwanta a bayan ta suka ci gaba da baccin tare.
**************************
Dik yanda Mommy taso Abdul ya bar ta taje a ƙarasa siyayyar kayan d'akin Ameerah ƙi yayi ya ajiye ta gidan su ya wuce nasu gidan dan gaida mahaifin shi, sanda tana sanar da Innoh abinda Abdul yayi mata sai Innoh tayi dariya tace,
"Ki kawo kuɗi anjima Naja ta koma maki wajen malam, ai an yi masa bita zai-zai ne shi yasa baya son kina yin nesa da shi, idan taje an sanar da malam ya dinga barin ki kina fita a sanda kike so ki koma a sanda kike so,dan idan aka sa maki ido abubuwa baza su na tafiya daidai ba."
"To ai shikenan bari Sule ya dawo min da ATM card d'ina,Innoh ina Baba ne? Ji nake yi kamar na jima ban gan shi ba,"
"Ai kuwa bai jima da fita ba ya shiga kasuwa sai dai muyi fatan Allah yasa a samu kasuwa mai albarka,kin san yanzu lamuran sun ƙara matsewa talaka na ganin rayuwa"
Da jin haka Mommy sarkin tausayi sai ta dakko jakar ta ta zaro dubu uku ta baiwa Innoh tace a ƙara a cefanen ranar,Ameerah kuwa tsaye tayi mata tace,
"Kin san dai har yanzu ban warke ba ciwon nan da ƙaiƙayi na nan na damu na,"
"Subhanallahi, to yanzu yanda za a yi Innoh ta sammana sabarar ta ki tafasa da kaninfari da ganyen bishiyar nim wato maina,wasu kuma su ce mata dogon yaro kiyi tsarki kuma ki sha kaɗan na tsawon sati daya zuwa biyu mu gani, ko an kai ki gidan ki ki dinga sa yana nemowa kuna sha ai magani ne,"
Cikin ikon Allah kuwa Ameerah na dafa maganin nan ta sanya gishiri kaɗan tayi tsarki sauƙin susar ya samu,kallon Mommy Ameerah tayi sannan tace,
"Ni fa Mommy ba zan yarda a kaini ɗakin miji babu lefe ba, yanda zamuyi musu kayan d'aki dole ne suma suyi min lefe ko babu yawa, idan babu lefen me zan d'aura idan na je gidan nasu har na yi masa kwalliyar da zata burge shi?"
"Haka ne kuma fa kema kin ce wani abu sister."
Haka suka dinga hirar su suna kitsa yanda za su sanar da shamsu suna jiran lefe kafin a kai masa ita ...................................[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 51:
Dik yanda Shamsu yaso Ameerah ta tare a cikin satin nan ƙi tayi, domin kuwa ta ƙeƙasa ƙasa tace dole sai yayi mata lefe kamar yanda ake yiwa kowacce mace lefe idan za a yi auren ta,hankalin shamsu ya tashi k'warai da jin wannan sabon lamarin da Ameerah ta tinkare shi da shi, cikin damuwa da tashin hankali ya wuce kasuwa shagon Baban su.
Sanda ya je ya tarar da mutane ana ta ciniki sai shima ya faɗa ya shiga karb'ar kuɗi yana ƙullawa mutane kalar dusar da suke son saye, ya kai azahar yana aiki bai samu damar keɓewa da mahaifin shi ba har sai da suka fito daga shagon domin gabatar da sallar azahar, anan ne ya matsa ya shiga cikin shagon ya sanar da Mahaifin shi abinda ke faruwa, murmushi yayi yace,
"Na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya,banza bata kai zomo kasuwa,yau kaga amfanin abinda nake faɗa maka ko? Shamsu babu irin bin kan ka da banyi ba akan ka dinga biyo ni shagon nan muna aiki tare duk wata ko ƙarshen sati na dinga fitar da kai kamar yanda nake yiwa su Idi ka ce kai Allah ya kashe ka ba za ka saida dusa ba,ka kama waya ka riƙe ƙam kamar ran ka, kai ne danne danne kullum wai kana kiristo/crypto,ko ka ɗauki wanka ka fita da yamma ba zaka dawo gida ba sai dare ya raba, to faɗa min tinda ka fara kiriston nawa ka samu? Ai na san zai ishe ka haɗa lefe tinda an jima ana fama,dan haka babu abinda zan ce maka da ya wuce Allah bada sa'a,sai kaje ka samu babar ku ta haɗa maka dan ni ba sanin kan atampa ko lehyi nayi ba,"
Mahaifin su Shamsu na gama fad'in haka ya wuce shamsu da baƙin ciki da takaici suka cikawa zuciya,alwala yayi ya shimfiɗa buhu a bakin shagon shi ya kabbara sallah,sallah ce dai irin ta 'wasu yan kasuwan da basa natsuwa a cikin ta,wato ana yi ana nuni da hannu da ido da baki,wani lokacin ma sai ya kauda kan shi daga alƙiblah sai ya gama kallon abinda yake so ya kalla sai ya tafi ruku'u ko sujjada, raka'a huɗu yayi ya miƙe,gani yayi shamsu ya fita daga inda yake ya bar wajen,girgiza kai yayi cikin jin takaicin halayyar ɗan nashi,a zaton shi Shamsu ya tafi kenan ya bar kasuwar ba zai yi aikin sayar da dusa ba.
Har ya manta da Shamsu ya zo ya tafi ya ci gaba da harkokin sana'ar shi, sai ga Shamsu ya dawo da alama masallacin kasuwar yaje yayi sallah,tare da su Idi yaran shagon Baban nashi suka dawo, koda ya dawo sai ya shiga cikin yaran shago suka ci gaba da hidimar saida dusa,murmushi mahaifin su kawai yayi ya na zaune yana hutawa yana kallon yanda ake gudanar da shagon nashi.
Su Shamsh bai tashi a kasuwar nan ba sai goma na dare, cikin jin daɗi mahaifin shi ya ƙirga dubu hamsin ya bashi yace,
"Alhamdulillah Shamsu na ji daɗin yanda ka sauke girman kai ka morawa jikin ka aka amfana da kai yau,dan haka ga tawa gudummawar haɗa lefen,idan ka dage kana zuwa nan kullum muna aiki tare da kai, dik sati ko wata zan dinga biyan ka dubu goma zuwa sama da haka ma, kaga sai a samu na cefane ko? Allah yayi maka albarka,"
Cikin sosa ƙeya Shamsu yace,
"Ameeen Baba na gode, amma Baba dubu hamsin zata haɗa lefe kuwa a yanda abubuwa suka yi tsada yanzu?"
"Ina zan sani tinda ban ƙara aure ba nan kusa balle na san darajar kaya? Rabona da siyan atampa wa uwar ku ma ai yau shekara biyar kenan,yarinyar nan ita ke siya mana kayan sallah ka sani dan haka ban san ya darajar kaya suke ba a yanzu,"
Godiya shamsu yayi wa mahaifin sa suka rufe ko ina tare da kashe kayan wuta suka koma gida, tinda suka koma gida Shamsu ke nazarin inda zai samu cikon kud'in saiwa Ameerah kayan da take so.
Ya jima yana tunani kafin dabara ta faɗo masa, cike da murna da farin ciki ya kwanta yana addu'ar samun nasarar yin komai cikin rufin asiri.
A daidai lokacin da shamsu ke farin cikin samun nasara akan samun mafita dan haɗawa Ameerah lefe,ita kuwa Ameerah na nan na fatan kar Allah ya sa ya samu nasarar samun kuɗin da zai haɗa mata lefen hakan ne zai bata damar yakice auren shi ta huta.
***************************
Mommy ce zaune tana danna wayar ta tana kallon account ɗin Billy na TikTok daga nan ta koma Facebook tana ta tinanin yanda zata rama abinda Billy tayi mata,ganin Amy da Billy suna tare mamat kamar gum a koda yaushe sai ta ɗigawa abotar su ayar tambaya, dan kuwa Billy bata taɓa ƙawance da mace bata neme ta ba.
Mota da gidan da taga Billy ta mallaka sun gigita ta,mamakin inda ta samu wannan kyautar take yi dan kuwa a iya sanin ta Man bashi da kud'in da zai sai mata irin wannan abubuwan a lokaci ɗaya dole akwai wata a ƙasa.
Zama taji anyi a gefen