Showing 159001 words to 162000 words out of 276165 words

Chapter 54 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

amarya ta zamo a gajiye a jigace, tana son ayi komai cikin tsari da ƙayatarwa.

Ba ƙaramin daɗi su Abbe suka ji ba dan ganin yanda Ummi ke gudanar da komai kamar ba matar ɗan ta na fari ba,ta ajiye kunya ta rungumi Saddiqa da irin rungumar da ya kamata kowacce surukar kirki tayi wa surukar ta musamman marainiya irin Saddiqa,dan haka suma suna idar da sallah sai suka koma baccin safe abun su tinda babu abinda za su yi a gidan akwai masu aiki.

Da misalin ƙarfe 3:11pm mai kwalliya ta zo, a wannan lokacin kuwa amarya ta sake wanka ta yi brush tayi alwala tayi sallah, dan haka zaman tsara mata kwalliya aka zauna yi a kyakkyawar fuskar ta da ta sha gyara, jikin ta yayi wani irin haske mai kyau yana sheƙi da k'yalli wanda bature ke kira da glowing,sun kai kusan awa guda ana tsara mata kwalliya kafin ta sanya kayan fulanin da aka d'inka mata na musamman kalar blue da ratsin ja a jikin rigar da zanin,gashin ta aka gyara mata aka zubo shi ta gaba, cikin sanyin murya tace,

"Dan Allah in babu damuwa ina so a rufe min gashi na, bana so a buɗe shi saboda na tabbata idan aka yi hotuna za su iya fita duniya kuma hakan ba dai-dai bane haramun ne."

Murmushi mai yi mata kwalliyar tayi tace,

"Masha Allah, gaskiya na jima banga amarya mai irin tunanin ki ba,Allah ya albarkaci auren ku, yanda kike so haka za a yi miki,"

Maida mata gashin ta baya aka yi aka daure shi,sannan aka kafa mata d'aurin ɗankwalin da yadin kayan fulanin, nan da nan sai gata tayi kyau sosai kamar ba ita ba,baƙar rigar da ta saka a ciki mai dogon hannu sai ta ƙara fitar da kyawun farar fatar ta, mayafin kayan fulanin aka yafa mata a saman kan ta aka manne shi da pin da jikin d'ankwalin ta,Anisah ta bata Ƴar ƙaramar jakar da zata riƙe ta taya ta sanya takalmin ta baƙi mai k'yallin silver stones wanda yake mahaɗi ne na jakar hannun ta.

Tsabar kyawun da tayi basu jira mai ɗaukan hoto ya iso ba Anisah da Khaleesat da ƙawayen su da suka zo cikin shigar kayan fulani suka hau ɗaukan ta a hotuna tare da yi mata videos.

Ko da Ummi ta shiga ɗakin cikin shigar wani leshi mai tsananin kyau da tsada kalar purple mai haske ta sha d'auri mai kyau ta yafa mayafi sai tayi turus dan ganin yanda Saddiqa tayi mata kyau,tasbihi tayi ga Allah da ya halicci kyakkyawar yarinya mai natsuwa kamar Saddiqa, da kanta ta isa ta d'aga ta tsaye tana sake kallon ta, a hankali ta dafa kan ta ta hau yi mata addu'a kamar haka,

"U'idhuki bi kalimatillahi tammat min kulli shaidhanin wa hamma wamin kulli Aynin lammah, Anisah ku rako ta waje mu tafi bana son b'ata lokaci saboda bana so mu kai magariba ba a fara ba."

"To Ummi gaskiya sai kin tsaya mun yi muku hoto amma."

Babu musu ta tsaya aka yi musu hoto da Saddiqa dake ta jin daɗin yanda suke nuna mata so da ƙauna, ana gama yi musu hoto su Anisah ma suka tsaya suka yi wa junan su hotunan sannan suka fita, a motar da za a kai amarya wajen taron ta tarda shi tsaye yana ta latsa waya yana jiran fitowar su,gefe kuma abokan shi ne mata da maza suna ta hira.

Fitowar ta ce ta sanya abokan shi ɗaukan sowa da yabon kyawun da Saddiqa tayi,nan da nan mai hoto ya hau ɗaukan dik wani takun ta da na su Anisah da ƙawayen su dake kewaye da ita suna taku cikin yanga, kafe ta yayi da idanun shi yana jin wani magaɗisun ƙaunar ta na fizgar shi,da kyar ya iya buɗe mata mota ya taimaka mata ta shiga ta zauna sannan ya zagaya cikin sauri ya faɗa gefen ta ya zauna, babban abokin shi mai suna Suhail ya ja motar suka bar gidan sauran motocin abokansa da qawayen Anisah na take musu baya.

Basu jima da tafiya ba Ummi da tawagar ta suka shirya suka bi bayan su,basu tsaya a ko ina ba sai a wani babban hall da ake yin biki na masu ido da k'walli, kiɗan da ke ta tashi ne ya sanya Saddiqa fata da addu'ar Allah yasa kar a sanya ta yin rawa a wajen nan dan kuwa ba zata iya ba.

Waƙa ce ta fulani saboda Ummi bafulatana ce shi yasa ta shirya fulani dinner saboda a ƙawayen ta ma akwai fulani sosai. Taro yayi taro nera ta koka sosai dan kuwa an watsa ta ma ango da amarya, Saddiqa na gani babu damar magana, tinda ta san dik wannan watsi da kud'in da ake yi haramun ne.

Basu tashi daga wajen dinner ba sai bayan magariba, a gajiye kowa ya koma gida cike da kayan ƙwalama da aka raba a wajen biki,dik yanda Hajiya Sa'a taso ganin gazawa ko kasawar wannan bikin ta rasa, ƙarshe ma sai ta hau yiwa Suhail fatan ya samu mace irin Saddiqa kuma a raƙashe ayi wadaƙa da nera kamar yanda aka yi a bikin Munir.

Alhaji Baban Gida yayi matuƙar farin ciki da wannan auren dan haka da kan shi ya fito parlour bayan sun dawo sun yi sallah suna hira ya hau gaisawa da mutane yana tsokanar ƙannen shi da suka kawo amarya, a haka suka sha hira har dare yayi Ango ya shigo yana mamakin ganin yanda Ummi ke wani kanainaye masa mata ta hana shi,dan haka ya riga ya ƙudurta idan ba a bashi matar shi ba to fa sai dai ya zauna su ci amarcin a nan gidan dan kuwa babu inda za shi.

Amarya ƙawayen Ummi suka shirya ta sha wanka da gayu aka turare ta da turaren wutar HUMKAM banda ƙamshi babu abinda ke tashi a jikin ta, fruit salad Ummi ta sake bata irin haɗin da tayi mata tin farkon zuwan ta ta Karb'a tana sha,sai kawai daɗin shi yasa taji dama da Munir take shan shi dan kuwa yayi mata daɗi sosai,a haka ta gama sha su Hajiya Sa'a sune a gaba-gaba wajen tasa amarya a gaba suka shiga motoci aka kai amarya ɗakin ta.

Suna kai ta basu jima ba suka dawo suka baro ta daga ita sai angon ta, domin kuwa ko da suka shirya zasu kai amarya shi kuma har yayi gaba ya riga su isa gidan, tafiyar su ke da wuya Munir ya rufe ko ina sannan ya shiga d'aki kallon Saddiqa yayi dake nad'e a cikin laffaya, wani irin farin ciki ne ya lullub'e shi ya sanya shi durƙusawa a guiwowin shi ya kafa kan shi a ƙasa yana sujjada domin godewa Allah da ya mallaka masa matar aure irin Saddiqa, ga kyau, ga ilimin addini, na bokon ma ta yi dai-dai ita wanda yake fatan nan gaba zata ci gaba.

Murmushi kawai take ta dokawa a cikin mayafin da take ƙunshe a cikin shi,yana tasowa sai yace,

"Ke kin ga tashi ki gani mu yi alwala mu godewa Allah da ya nuna mana wannan rana mai albarka."

Babu musu ta miqe tsaye tana gyara mayafin ta cikin muryar da Munir bai taɓa sanin tana da ita ba tace masa,

"Ina da alwala sai dai idan kai ne zaka yi sai na jira ka,"

"Alhamdulillah nima ina da alwala,na tsaya siyan kazar amarci naga suna sallah a wajen sai na tsaya nayi alwala nayi sallah sannan nayo gida."

Sallah ya ja su suka yi raka'a biyu sannan ya karanto addu'ar da dikkan ango ya kamata yayi wa amaryar shi a daren farko kamar haka,

"Allahumma inni as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha  alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha  alaihi"

Yana kammalawa ya zauna kusa da ita ya janyo naman da ya kawo da fresh milk ya buɗe yana tayi mata hira domin ta sake da shi,gaba ɗaya sai yaƙi nuna mata maitar shi a fili saboda baya son ya sa taji ta a takure har ta kasa cin abinci ta ƙoshi yanda ya kamata.

Ai kuwa ya samu yanda yake so dan kuwa ta saki jiki suna hira suna cin abinci, banda labarin wajen dinner da yanda ta dinga jin kunyar yin rawa babu abinda suke yi, a haka suka ci suka ƙoshi sosai sannan daga baya suka sha madara, Munir ne ya fara shiga band'aki ya wanke bakin shi sannan itama ta shiga ta wanke nata ta sake tsarkake jikin ta sannan ta koma ɗakin,tana shiga taga baya nan ya tattare ledar da suka ci abinci da kwalin madarar ya fitar da su, sai kawai ta buɗe wardrobe ɗin da ta gani, kallon kayan dake ciki a goge a jere take tayi cike da mamakin wannan dik suturar mutum ɗaya ce?

Da kyar ta tsaida idanun ta a kan bangaren kayan bacci ta ɗauki wata maroon rigar bacci mai santsi ta sauya sannan ta ninke wanda ta cire ta saka a can ƙasa inda taga babu komai a wajen ta rufe.

Bata jima da shafa Shu'umar Humrar HUMKAM da ta gani a saman madubi ba ta tsaya tana shaƙar ƙamshin tana lumshe idanu tsabar yanda ƙamshin ke ratsa ta,gado ta kad'e sau uku tana bismillah sannan ta buɗe bargo ta shiga tare da zama ta kara hannayen ta a bakin ta tana karanto ayatul kursiyyu uku,ikhlas uku, falaƙ uku, nas uku, sai amanarrasulu uku, tana gamawa ta shafe dika jikin ta ta kwanta ta rufu da bargo, tunawa tayi bata kashe fitila ba sai ta dan yi gajeran tsaki zata sauka tana faɗin,

"Kashh na manta ban kashe fitila ba na kwanta,"

Munir ne ya ziro kanshi ɗakin yace,

"Kar ki damu Amaryar Mannirun Baabaa zan taya ki kashewa ke dai ki koma kawai ki kwanta ki jira zuwan angon ki gare ki."

Wata iriyar faɗuwa gaban ta yayi nan take ta hau karato addu'o'in samun natsuwar ruhi saboda kar ta bari tsoro ya hana ta sakewa mijin ta da ya jima yana dakon wannan ranar mai mahimmanci a gare su sakewa,cikin wani ɗan ƙanƙanin lokaci Munir ya kashe fitilar tare da kulle ƙofar d'akin yayi duhu dinɗim,ganin haka ne ya sanya ni sake buɗe ƙofar ina ƙunƙuni na kulle su na koma parlour na kunna kallo ina cinye ragowar kazar ango da amarya ina korawa da laban..................

*Cassss ana yi ina jin nayis...albishirin ku mutanen k'warai masu albarka, marasa yin comment ko liking a groups ɗin da nake turawa kuna yi kamar baku ganni ba, aradun Allah aski yazo gaban goshi nima ina shan wahala dama wajen sharing, zan dena sharing duk group ɗin da ba a acknowledging ɗina sai in dinga turawa masu so,kar kuma daga baya na dena turawa group ɗin ku ki bini ta PC kice kina so, zaki biya kuɗi kafin na tura maki daga farko zuwa inda na tsaya tabbas.*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI










RUBUTAWA:HAERMEEBRAEH ✍️✨





*SANARWA !*

*Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....*

*MAZAUNA GIDA 300*
*ƳAN ABUJA 300*
*A GARIN MU 300*
*KAI NE JARUMI 300*
*KUN MAKARO 300*
*TAUBASHI 300*

*KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻*
*IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.*

*KAR KU MANTA AKWAI KAYAN GYARAN JIKI A KANO, KADUNA DA KEBBI STATE.*

*FACE OIL*
*SKIN OIL*
*BODY SCRUB*
*HAIR OIL*
*HAIR CREAM*
*HAIR MASK*

*GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423*


PAGE 63:








Washegari da safe Saddiqa ta tashi da wata iriyar shagwab'ar da ni kai na da na san ta tun tana ƙarama ban san ta da ita ba, ko taɓa ta Munir yayi sai ta mere baki alamar zata yi kuka,nan da nan shi kuwa jiki na matuƙar rawa da mazari zai hau ririta ta yana lallashi tare da ban baki, a yanda yake jin ta a cikin zuciya tsokar jiki da ɓargon jikin shi zai iya yi mata komai dan farin cikin ta. Wani irin so yaji yana yi mata tare da girmamawa wanda a baya bai yi mata su ba na musamman,bai taɓa zaton yanda ake ta bada labarin lalacewar Ƴan matan yanzu zai samu Saddiqa a yanda ya same ta daren jiya ba,dik wani sharri da zagi da kiran lalacewa da Innoh ta dinga yi mata ashe dik sharri ne? Nan take yaji ƙaunar Yadiko da ta zuri'arta ta samu masauki a zuciyar shi, addu'a kuwa ranar Saddiqa da iyayen ta sun sha ta babu adadi.

Shirye take tsaf cikin wani leshi wanda ta dinga mamakin yanda aka yi kayan suka yi mata dai-dai a jikin ta kamar an auna ta duba da cewa ko ganin ta telan be yi ba, kalar purple ɗin ta karɓe ta saboda kala ce dake yi wa kowacce kalar fata kyau, d'aurin ɗankwali ta yi mai kyau da ta kafa a goshin ta kamar hula, sai gashin kanta dake nad'e a bayan ta ya zauna a dogo cikakken dokin wuyan ta, duk yanda zan misalta maku yanda Saddiqa tayi kyau ba lallai ku gane ba sai idanun ku sun gan ta,Munir kuwa zama yayi ya sanya ta a gaba yana kallo ko ƙiftawa baya son yayi, cike da shagwab'ar da ta tsiro da ita daga sama ta hau karya jikin ta tana wasu 'yan koke-koke dake rikita lissafin Munir tace,

"Ni dai dan Allah ka daina kallo na haka, sai in dinga jin kallon ka na fasa ƙirji na yana shiga zuciya ta,"

Da sauri ya dawo gaban ta ya zauna tare da ɗora hannun sa a saitin zuciyar tata yace,

"Dan Allah da gaske kike? Muga iya inda kallon nawa ya tsaya,matso in gani,"

Da gudu ta tashi ta koma parlour tana dariya, hannun shi zube a cikin aljihun wandon shi mai faɗi wanda ya ɗan tsuke daga ƙasa kaɗan,sai vest da ta manne a jikin shi ya fito yana zuba murmushi yana binta da kallo,

"Ai da ki tsaya naga inda kallon nawa yake zuwa, dan sharri yanzu ace kallon ɗan mutum na huda ƙirji ya shige zuciya sai kace wani maye?"

"A tsakanin jiya da yau idan aka ce min kana lashe mutane har ɓargon su ba zan yi musu ba,"

Dariya suka fashe da ita a tare ya sanya hannun shi na dama ya shafi kan shi mai tattausar suma irin ta fulani mai nannad'ewar nan,lashe leb'en bakin shi yayi na ƙasa sannan ya kalle ta yana wani lumshe ido, yanayin da ya ke kallon ta dashi yayi matuƙar tasiri wajen jefa ta cikin ƙaunar shi dumu-dumu fiye da yanda take ji a baya.

Da kanta ta tashi daga mazaunin ta ta zauna a saman cinyar shi ta rungume shi, murmushi yayi ya hau shafa bayan ta, a hankali tace,

"Ruhina yunwa nake ji,"

"Yi hakuri Ruhina bari na sama nana abinda zamu ci ko?"

A hankali ta miƙe daga jikin shi, shi kuwa ya kamo ta ya riƙe fuskar ta yana sumbatar ta, sai da ya gaji dan kan shi sannan ya sake ta ya tafi da baya da baya zai shiga kitchen yana yi mata dariya, dan kuwa ya shanye lipstick ɗin da ta saka gaba ɗaya.

Murmushi itama tayi ta samu waje ta zauna da ƙafafun ta da suka yi sanyi saboda kashe mata jiki da Munir yayi,door bell ɗin gidan ce ta fara bugawa tana zabga sallama, cikin sauri Munir yayi hanyar fita dan ya ga ko wanene ke sallama musu.

Da sauri Saddiqa ta sha gaban shi tana cije baki saboda zafin da take ji a jikin ta,mamakin saurin shan gaban shi da tayi Munir yayi, cikin tura baki tace,

"A haka zaka fita? What if mace ce mai sallamar fa?"

Sunkuyar da kanta tayi ta hau wasa da yatsun ta,wani irin kishin shi ne ya taso mata lokaci ɗaya,shi kuwa Munir ji yayi kamar ya taka rawa saboda murna,rungume ta yayi ya manna mata kiss kafin ya ɗaga murya yace,

"Wa'alaikumussalam ! Ana zuwa."

D'aki ta shiga da sauri ta ɗakko masa jallabiyya ta sanya masa kamar yanda ya taya ta sanya kayan ta,kallon ta yayi yace,

"Zan iya fita yanzu gimbiya?"

D'aga kai tayi tana dariya ƙasa-ƙasa tare da noƙe kanta,da sauri ya nufi ƙofar ya buɗe sai yaga drivern gidan su riƙe da basket ɗin abinci, cikin girmamawa ya karɓa tare da gaishe shi, amsawa drivern yayi tare da yi musu fatan zaman lafiya da samun zuri'a mai albarka.

Bayan ya koma sai ya ajiye basket ɗin a dinning table sai ya wuce kitchen ya d'akko plates da spoons da serving spoon ya dawo, zaune ya ganta gaban abinci tana buga hannun ta a table ɗin tana faɗin,

"Yahhh Munirrr yunwa nake jiiii....Yah Munir zan ci abinciiiii."

Murmushi kawai yayi ya buɗe food flask d'in farko dan yaga me zai zuba masu, karo yayi da farfesun naman kan rago, daga ƙamshin dake tashi yasan yaji kayan ƙamshi, amma an saka daddawa kaɗan a ciki ɗaya food flask d'in ya buɗe yaga an soya dankalin bature da ƙwai,sai ɗayan kuma fried rice ce da ta ji kayan lambu da naman rago,kunun gyad'a ne a dogon flask ɗin ruwan zafi ya ji kindirmo fari ƙal da shi.

Yawu Saddiqa ta had'iya ta ci gaba da shagwab'ar da ke samun mazauni a zuciyar Munir na musamman ta zauna,yana gama zuba musu ya ja kujera kusa da ita ya hau bata, sai da taji yunwar cikin ta ta lafa sannan itama ta hau d'iba tana bashi a baki, a haka suka gama ciyar da junan su abincin sannan Munir ya tashi zai tattare wajen, murmushi Saddiqa tayi ta kama hannun shi tace,

"Ai kai kuma ka gama naka aikin, yanzu nawa zai fara,"

Sakar mata yayi ya nad'e hannayen shi yana binta da kallo,sai da ta gama kwashe komai zata wuce sai ta kalle shi da wani irin salon jin kunya tace,

"Ruhin Saddiqa cire rigar nan ta sama nafi son in dinga ganin ka da irin shigar d'azu,"

Tana gama faɗin haka ta wuce kitchen da sauri tana dariya, shi kuwa Munir wata ƙara ya saki ra farin ciki ya tashi da sauri ya cire jallabiyyar yayi wurgi da ita saman kujera ya bi bayan ta kitchen yana faɗin,

"In dai kuwa haka kike son gani na kin samu Ruhina,dik abinda kike so shi zan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login