Showing 207001 words to 210000 words out of 276165 words

Chapter 70 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

babu malam Abdul zai ga zallan haukan da bai taɓa gani ba a garin nan,har ni zai yiwa kishiya bayan alƙawarin da ya yi min? Inaa ba zata sab'u ba, ba zai yuwu ba, dole ne ka haƙura ka zauna dani ni kaɗai."

Abdul kuwa na shiga ɗaki transfer ɗin dubu ɗari uku ya yi wa khadija, sannan ya yi mata message ya bata haƙuri tare da fatan alkhairi,dan ya kula Khadija bata da tashin hankali,ko ya auro ta wahala zata sha wajen Mommy,dan haka wata zai nemo a cikin satin a d'aura masa aure da ita ya ga ta ƙarshen rashin hankalin Mommy,yaso yanda ya fara soyayya da khadija babu wanda ya sani sai dai daga baya a ji auren kawai,sai gashi garin binciken wayar shi ta gano abinda yake ta ɓoyewa, iskar bakin shi ya furzar yana dana sanin alƙawarin da ya ɗaukar wa Mommyn tin tana amarya,tsaki ya ja sannan ya ɗauki wayar shi da makullin motar shi ya fita daga ɗakin.

A parlour ya tarda ita tana shayar da Amir tana kuka, tausayin ta ne ya ɗan kama shi kaɗan cikin sauri ya kauda kan shi ya bar gidan, kuka ta fashe da shi tana ayyana abubuwa da yawa a ran ta game da fitar tashi,kallon jaririn nata tayi sai taji gaba ɗaya haushin yaron ya kama ta,ta tabbata dan ta haihu ne ya sanya Abdul tsanar ta har ma yake ƙoƙarin yi mata kishiya,dangwarar da yaron tayi a kujera ta wuce ɗaki,kwantawa tayi a gado tana ta rusa kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa.

Naja ce taji kukan yaron ya ƙi ƙarewa sai ta fito, sauran ƙiris ya faɗo daga kujerar ta tafi a guje ta tare shi ta ɗauke shi tana lallashi,kishin Mommy yana firgita Naja ba kaɗan ba,wannan wanne irin mahaukacin kishi take nunawa?

Abdul yaso neman Bilal ya sanar dashi abinda ke faruwa amma sai ya fasa,tinawa da hirar da suka yi da Bilal ɗin ya yi a daren ranar da aka yi sunan Amir.

'Man yana da kyau fa ka dinga tsananta addu'a da kuma yin azkar,wai ni kam kana ma tashi yin sallahr nafila da dare ma kuwa?'

'Gaskiya ni bana yi kullum sai dai can ba a rasa ba na kan yi watarana.'

'To karatun ƙur'ani fa?'

'Rabo na da yi tin last Ramadan,kai ina buƙatar addu'a fa,lamura na sai a hankali Bilal.'

'Gaskiya mana, shi yasa dik wani yajuju da majuju da aka yanko maka suke afka maka,haba Abdul? Kar ka manta daga gidan da ka fito, gida ne na sarauta da malanta da sanin addini,me yasa ka saki addinin ka kake wasa da ibada? A wannan zamanin da muke ciki wanda ya riƙe ibada ma yake fuskantar jarabawar masu sihiri da shirka balle kai da ka saki ibada? Tashi ka gani.'

A wannan daren basu kwanta ba sai da Bilal ya yi wa Abdul ayoyin ruƙya a ruwan sha ya bashi ya sha, ya wanke jikin shi,sannan suka raya daren da nafila da karatun ƙur'ani,tin daga nan Abdul ya ke jin shi cikakken mutum,wani kasala da nauyin jiki wajen yin ibada dik ya tafi,a cikin satin kuma ya haɗu da Khadija ta dawo daga islamiyya yaji ya na so ya aure ta,daga nan ne suka fara soyayya ta waya har yakan tura masu da kuɗi da kayan abinci,sai kuma gashi hamshaƙiya Mommy ta gano su ta tarwatsa abun a tashi ɗaya.

Ajiyar zuciya ya sauke ya wuce wani joint na shan iska,abinci yasa aka kawo masa ya hau ci kamar wanda ya yi kwanaki be ci ba,wata matashiyar budurwa ce tazo ta zauna a gefen table ɗin shi tana masa dariya,cikin ƙasa da muryar ta tace,

"Ran ka ya jima dan Allah ka rage saurin nan da kake yi, ka ga can ni da Ƴan'uwana ne ke zaune muna hango ka, sai dariya suke yi maka,ni kuma ban ji daɗin hakan ba, shine na ce bari nazo na faɗa maka ka ci a hankali akwai ƴan sa ido ba kai ɗaya bane a wajen."

Tin da ta fara magana Abdul ya kafe karamin bakin ta da ido yana kallo,baƙa ce kyakkyawa ajin farko,irin baƙin mutanen katsina mai kyau da ɗaukar hankali,daga jin hausar ta ya gane ba bakanuwa bace,da ƙyar ya rufe bakin shi ya gyara zaman shi ya kalle ta yace,

"Na gode sosai,inshaa Allahu zan gyara,kin san idan mutum ya fito daga ƙwadago yunwa ta cinye masa ciki sai a hankali,"

Murmushi tayi ta miƙe za ta bar wajen ya yi saurin cewa,

"Ammm baiwar Allah nace ba."

Juyawa tayi ta kalle shi tace,

"Na'am?"

"Nace dan Allah ko zan iya samun No wayar kyakkyawar?"

Babu ɓata lokaci ta karanto masa lambar wayar ta ya saka, har zata tafi ya ce,

"Da wanne suna zan yi saving?"

"Huzaimah"

"Masha Allah,what a nice name you have dear,ammm nace ba tsaya in kira kiyi saving tawa, dan ban gama yarda da no gaske kika bani ba, na san halin ƴan matan yanzu idan basu son ka basu bada No mai kyau"

Dariya tayi sannan tace,

"To gwada ka gani mana."

Kiran No yayi sai ya ga wayar ta na ringing, murmushi suka yi a tare yace,

"Ki saka Abdussaboor a sunan."

Daga haka ya koma mazaunin shi ya ƙarasa cin abicin shi,ba jimawa ya ga ƴan matan sun bar wajen zaman nasu sun shiga wata mota sun bar wajen gaba ɗaya,shima be wani jima ba ya tashi ya shiga tashi motar,yawo ya dinga yi a gari dan baya son komawa gida ya tadda mommy da masifar ta.

Da misalin sha ɗaya na dare ya kira No Huzaimah,babu jimawa ta ɗauka da alamar bacci ta fara ma,bayan yayi mata sallama sun gaisa ne,ya tambaye ta ko tana da tsayayyen mijin aure? Cikin dariya tace,

"Haba malam, daga haɗuwa d'azu zai zancen aure? Ni fa baƙuwa ce gidan yayata nazo hutu daga katsina, jibi ma zamu koma gida."

"Da dikkan alama Allah ya nufe ki da zuwa Kano ne dan ki samu mijin aure shi yasa ya haɗa mu Huzaimah................."
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨








PAGE 84:








Motsi Abdussabour ya ji a bakin ƙofar ɗakin shi ya yi saurin kashe wayar ya ajiye a gefen shi,Mommy ce ta buɗe ƙofar ta shiga sanye da kayan bacci mai kyau riga da wando,kanta babu hula sai sheƙi yake yi alamar ya sha gyara,cikin zuciyar ta baƙiƙƙirin take jin shi saboda baƙin cikin abinda Abdul ɗin ya yi, amma hakan bai hana ta shanye damuwar ta ba dan ta faranta masa,Amir ta ajiye a ƙaramin gadon shi dake ɗakin ta wuce zata hau gado ta kwanta,a hankali Abdul yace mata,

"Ya zaki ajiye yaro baki yi masa addu'a ba? Kullum idan kika ajiye shi sai na yi maki magana akan yi masa addu'a sai kice wai kin yi masa,a gaskiya bana son irin abinda kike yi Hadiza."

Idanun Mommy ne suka tara k'wallar baƙin ciki,amma sai ta shanye ta koma ta tsaya a saman kan yaron ta yi a'u'ziyyah kawai ta tofa masa zata koma saman gado da niyyar kwantawa,tsaki Abdul ya ɗan ja kafin ya tashi ya ɗauki yaron ya rungume shi a ƙirjin shi,sai da ya karanta ayatul kursiyyu,sannan ya yi falaƙi,nasi da iklas zuwa amanarrasulu ya shafawa yaron sannan ya ajiye shi ya koma ya kwanta, shi kanshi bai kwanta bacci ba sai da ya yi wa kan shi addu'a ya shafa sannan ya juya mata baya,dik abinnan da yake yi da ido kawai mommy ke bin shi, sai da ya natsu har bacci ya fara ɗaukan shi sannan ta tada shi,yana farkawa sai ta fashe da matsanancin kuka,dik yanda Abdul yaso ya kyale ta ta ci kukan ta ta gama tai bacci kasawa ya yi,a hankali ya dafe kan shi ya rintse idanun shi,cikin sassanyar murya ya ce,

"Ya isa haka kukan, matso ki faɗa min me kike so ayi yanzu."

Babu kunya babu tsoron Allah Mommy ta hau share hawaye tana jan majina ta ja jiki ta kwanta  a saman cinyar Abdul tana ci gaba da matsar ƙwalla,cike da shagwab'a ta mirgina ta yanda za su dinga kallon junan su sannan ta ce,

"Ni dai so nake ka jaddada min alƙawarin da ka yi min,Abdul ka sani ina son ka bana son kishiya,dan Allah kayi min alƙawarin ba zaka yi mini kishiya ba."

Janta ya sake yi jikin shi ya sumbace ta a goshin ta sannan ya ce,

"Baby baki ga alƙawarin dana yi maki na farko ma na kasa sauke shi ba ballantana na sake yi maki wani? ki yi tunani da kyau mana, ta yaya lafiyayyen namiji kama ta zan iya zama da mace ɗaya? Idan kina period da ƙyar nake iya bari ki kammala,kafin ki gama dik inda hankalina yake ya gama tashi, bani da natsuwa bani da sukuni,yanzu kin haihu jinin nan kafin ya tsaya sai da kika yi sati biyu currr,a haka ma an ce kin yi sauri,to ki faɗa min haka zan ƙare rayuwa ta zuciya ta na hango min wasu matan bayan Allah ya hore min arziƙin da zan iya ƙara aure? Sannan ina da gidan da zan iya saka matar dik da na aura saboda ko gidan nan zai iya ɗaukan mata biyu,dan haka ki yi haƙuri ki taimaka min na kare kaina daga aikata zina,na yi kafin aure na, na kuma yi bayan aure dan Allah kar ki jawo ya zamo ɗabi'a a gare ni."

"Ai kuwa in dai ni Hadiza Ɗan Liti ina raye babu kai babu wata mace a duniya Abdul ! dik wannan bayanin da ka zuba ba shiga ta ya yi ba,kai na na sani,kai nawa ne, ka aure ni,kana so na nima ina son ka,babu wata ƴar iska ƴar karuwa jinin karuwan da za ta raɓe ka ban sabauta ta na illata ta ba,Abdul ko a aure ko a zina ni kaɗai ce matar ka,kai yanzu baka ji kunya ba dan Allah? Ko dake ba abun kunya bane bama wannan, sai dai nace baka da godiyar Allah,a rana sai ka neme ni sama da biyu,yaushe na taɓa hana ka? Idan ina period bana barin ka haka,ni na san dabarun da nake yi maka har ka samu gamsuwa,to me kake nema wanda bana yi maka?"

"Ke Hadiza na gaji da yin abu ɗaya da ke ke kaɗai ne shikenan? Ina ta yi maki kara ina boyewa bana so na faɗa maki kiji babu daɗi amma kina matsa min dole sai na bayyana maki abinda zai dame ki,ba fa ke ɗaya Allah ya halatta min ba,Allah ya halatta min zama da mata huɗu ne,dan haka ke baki isa ki hana ni ƙara aure ba, idan kika ga ban ƙara aure ba sai dai idan Allah ne bai nufa ba,haba! Ayi mace sai masifa da bala'i,to akan ki zasu ƙare."

Masifa Mommy ta dinga zazzagawa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,ƙarshe sai ta fashe da kuka kamar wadda ake duka,ganin abun nata ba na ƙare bane sai kawai ya ɗauki pillow da wayar shi zai bar ɗakin,ƙofa ta tare ta hau jijjiga jiki tana ci gaba da kuka tana kiran Allah ya saka mata akan abubuwan da yake yi mata,tsabar ma mamakin da ta bashi kawai sai ya fashe da dariyar takaici,tin yana dariyar takaici har dariyar gaske ta maye gurbin haushin dake cikin zuciyar shi,kallon yanda take ta zumɓura baki ya yi,sai ya ajiye pillow da wayar shi ya ɗauke ta gaba ɗayan ta ya wurga ta a gado,kamar wadda take jira kuwa sai ta zira hannu ta kashe fitilar ɗakin ganin duhu ya mamaye wajen ne ya sanya ni haska waya ta na buɗe ɗakin na bawa masoyan waje.

Da safe haka suka tashi kamar basu ne suka yi rikici da masifa da bala'i ba da dare,Abdul sai wani nan nan yake yi da Mommy ita kuwa tana masa shagwab'a,hatta da wanka da shafa mai shi ya yi mata.

Dik yanda Aunty Naja taso ta baiwa Mommy hakuri su bari ta yi arba'in kafin su je wajen boka ƙin yarda tayi, ganin ta ƙi yarda ne yasa ta ce mata,

"Ke yanzu a wannan halin da ake ciki ina kika ga na yin tafiya? Ai bari zaki yi sai kin jiƙa shi da ruwan ƙaunar ki kafin nan kafin kiyi arba'in,ta yanda ko kwana ɗaya kika yi baki nan zai gigice ya yi kewar ki,ta haka ne zai gane kowacce mace zai nema in dai bake ba to fa ba wata gamsuwa da zai samu,sannan shi wannan aikin da za a yi maki da nayiwa boka bayani yace za a ɗauki kwana uku ana yi,kin ga a yanzu kina tafiya kika yi kwana uku baki nan sai dai ki dawo ki ga ya yi maki abinda baki so,tinda na kula a shirye yake ya yi auren nan ko kina so ko baki so."

Shiru Mommy tayi tana nazari kafin tace,

"Maganar ki gaskiya ne Aunty Naja,zan yi haƙuri har nayi arba'in,inshaa Allahu dik sanda naje gida sai an yi min zazzafan aikin da zai cire masa ra'ayin kowacce mace a rayuwar shi."

"Yauwaa ta waje na ko ke fa? Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya."

Tinda su Mommy suka yi wannan tattaunawar sai ta samu natsuwar zuciya, gaba ɗaya ta maida hankalin ta akan kula da mijin ta da yaron ta,ita ce shan magugunan mata ita ce gyaran jiki da dik wani abu da ta san zai riƙe mata Abdul gam a hannu.

A gefe ɗaya kuwa Abdul na yaba mata matuƙa akan ƙoƙarin da take yi akan shi,shi yasa yake sakar mata kuɗi take yin yanda take so,amma hakan bai hana shi ci gaba da soyayya da Huzaimah ba,dan kuwa har Katsina sun je wajen ta shi da Bilal sau biyu,Bilal ya yaba da tarbiyya da kamun kan yarinyar dan haka sai ya dinga baiwa Abdul goyon baya akan ya aure ta kawai,idan yaso ko can garin Ba Mugu sai ya ajiye ta dik ƙarshen sati ya dinga zuwa wajen ta, tinda yarinyar da iyayen ta suna da fahimta,zuwan su na farko sai da ta ce ya gaishe da Yayar ta da ɗan ta tinda ya sanar da ita yana da mata da yaro ɗaya, hakan da ta yi ba ƙaramin farin ciki ya dasa wa Abdul a ran shi ba,sanda suka koma kuwa har rigar yara da atampa da turare ta bashi tace ya kai wa Yayar ta da ɗan ta.

Abdul kuwa da ya dawo sai ya kaiwa Mommy ya yi gum da bakin shi bai faɗi daga inda kaya suka fito ba, Mommy kuwa da ya bata kayan sai ta dinga murna tana godiya dan kuwa kaya ne masu kyau da tsada,da dare da ta yi wa Amir wanka sai ta sanya masa riga guda ɗaya a cikin kayan da Huzaimah ta bayar a kawo,tinda Abdul yaga kayan a jikin yaron ya hau ɗaukan shi a hoto yana murmushi, Mommy na fita ya tura wa Huzaimah hoton Amir yana godiya sannan yace ɗanta da Yayar ta dik suna godiya da kyautar da ta aika musu dashi.

Haka soyayyar Huzaimah da Abdussaboor ta ci gaba da gudana cikin sirri ba tare da Mommy ta san da zancen ba, har dai wata rana Abdul ya samu dama yaje ƙauye ya sanar da su Innah Laminde maganar ƙarin auren shi,Innah ta yi farin ciki da maganar sosai sannan ta sanya albarka ta kuma bashi goyon baya ɗari bisa ɗari,Sarki ma ya sanya albarka sannan ya yi masa nasiha sosai akan zama da mace sama da ɗaya, da yanda zai gudanar da adalci a tsakanin su.

Iyayen Huzaimah sun amince zata zauna a ƙauyen Ba mugu tinda ya nuna mata gidan a waya,ta ga haɗuwa da tsaruwar shi,dan haka ko da aka je tambaya Abdul da Uncles ɗin shi biyu da waziri sai suka bada har da sadaki sannan suka roƙi kada bikin ya wuce sati biyu,iyayen Huzaimah dake ba ƙananan mutane bane,suna so ƴar su tayi aure da mutum na gari sai suka amince da hakan, already dama suna nan suna ta ƴan siye-siye da ba a rasa iyayen da ke da budurwa yi ba,musamman abinda ya ƙunshi kayan kitchen da abubuwan da ba a rasa ba.

Nan da nan maganar auren Huzaimah ya yaɗu a dangin su da dangin Abdussaboor,dik abinnan da ake yi ko da suɓutar baki Abdul bai taɓa sanar da Mommy zai yi aure ba.

***************

Wataranar laraba Shamsu na zaune a parlour riƙe da kunu zai sha maganin ciwon kai,saboda yanda yake jin kan shi na tsananin sara masa saboda damuwar da yake ciki,Ameerah kuwa na zaune da yaron ta tana bashi abincin shi tana sheƙa dariya kamar mahaukaciya sabon kamu,cikin dariya tace,

"Sannu Shamsi na Allah ya baka lafiyar zuciya da jiki,gaskiya wannan bazawara bata kyauta ba,Allah ya kiyaye gaba idan kwaɗayi be sake janka ba,nan gaba a dinga gina soyayya domin Allah ba dan son zuciya ba."

Ƙwafa shamsu ya yi sannan ya ce,

"Ke har kin isa ki yi wa wani wa'azin yin abu domin Allah? Ita kuma da ta guje ni saboda wani dama can ƴar iska ce,Allah ne ya cece ni ba zan sake auro mugun iri ba shi yasa ya kai ni shagon na ga komai da ido na."

"Oho muku can ta matse muku, ni yanzu na dena damun kai na akan ka Shamsu,tinda baka ɗauke ni da mahimmanci ba ni ma ba zan kahye kai na akan ka ba,daga yau idan kaso ka yi soyayya da mata sama da dubu ma ruwan ka,sannan mugun iri ai ba a mugun iri ɗaya sai biyu."

"Dama na jima da sanin ba ƙauna ta kike yi ba ai."

"Ka ji da shi wai ciwon ajali a ɗan yatsa,idan na yi kishin ka kace min mahaukaciya,idan na ƙyale ka kace bana son ka,ni dai kawai abinda na sani shine na dena damun kai na akan ka, na riga na san ko mace aka baka sadaka sai dai ka kalla kace baka so,tinda baka da wajen aje hatsi ma balle mata biyu."

Suna nan suna ciwa juna mutunci Azizah ta yi sallama ta shiga gidan,Ta Annabi da Fadilah ne suka amsa mata,har ƙasa ta kai tana gaishe da Innar ta ta kafin su tafa da Fadilah su gaisa,zama tayi ta ajiye babbar ledar da ta shiga gidan da ita a gaban Innah Laminde sannan ta ce,

"Innah ce ta aiko ni tace na kawo maki goron saka ranar Yah Abdul,sannan tace na sanar dake nan da sati


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login