Showing 135001 words to 138000 words out of 276165 words

Chapter 46 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

dawo zan nemi mai siyan wasu kaya a siyar na kawo miki kud'in ki had'o lefen ki da kan ki, dan naga yanzu hakan ake yayi ko?"

Nan take Ameerah ta washe baki, haƙoran ta yellow shar da ratsin brown a saman su suka bayyana,fari tayi masa da kyakkyawan farin idanun ta tace,

"Ohhh da kai kasan kana ta fafutuka irin haka ka ƙi ka sanar dani? Shikenan ni ma an yi min kayan d'aki dik ranar da ka kawo lefe washegari sai aje ayi jere na tare ko?"

"Hakan ma yayi, Allah ya kaimu wannan rana mai dumbin tarihi a rayuwar mu masoyiya ta,"

"Ameeen"

Ameerah tace tana wani laƙwashewa kamar taliyar da aka zuba a ruwan zafi,hira suka ɗan taɓa da zai tafi ya bata dubu biyu yayi mata sallama, murna ta dinga yi ta soke kud'in ta a zani ta koma ciki ta zauna tana baiwa Innoh labarin abinda suka tattauna da shamsu, sai da ta gama zuba labarin ta Innoh tace,

"Uhumm sai kuma ki miƙo kud'in da ya baki kika ɗaga fatari kika soke a nan ba,"

A zabure Ameerah ta kalle ta, nan take ranta ya ɓaci ta tura baki tana murguɗawa tare da fari tace,

"Alqur'an ba zan baki ko sisi ba, ai dai naga miji na ne, kema jiya ba kud'in Baba kika amshe ba da ya dawo da daddare ko ji kike ban sani ba,"

"Laaaa Ameerah laɓe kike yi mana dama? Tabbas kin riƙa dole ki zo ki tafi gidan mijin ki dan uban ki,"

Tura baki tayi tana tuna daren jiya da ta fita fitsari taji ƙusur-ƙusur a ɗakin Innoh, kasa kunne tayi taji yanda Baban nasu yake roƙon Innoh akan ta amince dashi amma taƙi sam tace sai ya bata kuɗin hannun shi sannan ta amince masa, dik abinda ya faru tsakanin iyayen nata a kunnen ta ya faru,sai da taji motsin Ɗan liti zai fito sannan ta gudu ɗakin ta.

"Ke wai ba dake nake magana ba? Ba zaki bayar ba dai kenan? To ai shikenan ki riƙe kud'in ki zaki zo nema na da buƙatun ki ne ai,shi yasa bana jin ƙyashin kashewa Mommy ko nawa ne a rayuwa saboda tin kafin ta kai haka take kyautata min balle yanzu da kuɗi suka samu wajen zama a rayuwar ta,"

"Ba wani nan dama dai kin fi son ta tin kafin ta fara baki kuɗi, kuma lalurata ta tashi ai dole kiyi mini saboda dolen ki ne ki ɗauki d'awainiya ta,"

Sakin baki Innoh tayi tana kallon Ameerah dake faɗa mata maganganu son ran ta tashige ɗaki tana ci gaba da ƙunƙuni.


Shamsu kuwa na barin ƙofar gidan su Ameerah hanyar kasuwa ya nufa, yana tafe yana kiran lambar Billy, ta jima tana ringing kafin a ɗauka,cikin wata narkakkiyar murya Billy tace,

"Yah shamsu meye kake kira na da sanyin safiyar nan?"

Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya kalli time yaga ƙarfe 10:30am, sannan ya mayar kunnen sa cikin dakewa da shanye baƙin cikin wulaƙanta shi da Billyn ke shirin yi masa, a hankali ya furta,

"Ayyaa yi haƙuri ƙanwata yanzu kika tashi kenan?"

"Eh meye?"

Haɗiye wani abu yayi mai ɗaci a wuyan shi kafin yace,

"Dama na kira ki ne dan na nemi alfarma, dan Allah zan iya samun aron dubu ɗari biyu ke ko ɗaya ne ma a wajen ki zan haɗa lefe,idan na samu sai na maido maki,"

Sai da ta gama yatsinar ta tana ta zabga tsaki sannan ta sauka daga gado tace,

"Dubu ɗari biyu, tabdijam banda su nikam gaskiya,zan dai baka dubu goma gudummawa ta Allah sanya alheri,"

"Ba komai na gode,sai anjima."

Ba tare da ta furta komai ba ta kashe wayar ta tana zabga wa wayar harara kamar tana ganin shamsun,cikin masifa take faɗin,

"Wato ga ƴar iska ta tafi sayar da jikin ta ta kawo muku kuɗi ko? Ai wannan karon zaku ga wulaƙanci daga waje na,kowa ya samu ya zuba a rumbun sa kawai,"

Hannu Amy ta sanya ta ja Billy ta kwantar da ita a saman gado sannan ta yi mata rumfa tana sumbatar ta tace,

"Love ke da waye ne kike ta mita kika barni ina jiran ki?"

Murmushi Billy tayi sannan tace,

"Ba kowa bane, mu ɗora daga inda muka tsaya Sweetheart."

Billy na fad'ar haka suka ci gaba da aikata masha'ar su da suke ganin dik duniya babu abinda ya kai musu ita daɗi,Amy na samun ƙololuwar gamsuwa da Billy shine dalilin daya sa ta dage ta manne mata har take wani tunani akan Billyn, ta riga ta ƙudirta sanar da ita abinda ke zuciyar ta game da ita sai dai tana jin tsoron amsar da zata bata.

Suna nan manne da junan su bayan sun dawo cikin hayyacin su Amy ta sumbaci Billy a kafad'a tace,

"Baby ina so na yi maki wata tambaya, dan Allah ki bani amsa tsakanin ki da Allah,kin ga dai gidana, kin ga motocin da nake da su maza da dama basu da irin su,sannan kin ga yanda nake samun kuɗi ta hanyar Youtube channel d'ina da kasuwanci na, ɓangare ɗaya kuma na nuna maki takardar yarjejeniyar dake tsakani na da turawan da suka ɗauke ni aikin yaɗa wannan ƙungiyar tamu ta auren jinsi, kuɗi suke sakar min manyan da zan iya maida wanda naso mai kuɗi cikin kwana ɗaya,dan haka na tabbata ba zaki yi danasanin kasancewa dani ba idan nace ki aure ni,"

(channel ɗin littafan batsa ake karantawa shi yasa take da subscribers da yawa a sati daya idan aka yi posting tana samun wanda suka gani sama da mutum dubu dari biyar,abun takaicin kuma akwai channels da ake karanta littattafai masu ma'ana da faɗakarwa mutane basu cika bin su bama balle su saurare su,Channels ɗin malamai kuwa su aka fi rainawa sai idan malami ya kai malami ne yake samun mutane dake kulawa da channel ɗin sa. Allah yasa mu dace mu gane gaskiya mu gyara kurakuren mu)

Maganar Amy ta zo wa Billy a bazata,dan haka cikin sauri ta d'aga kai ta kalli Amy dan ta gasgata maganar da ta sanar da ita a yanzu,cikin rawar baki da nuna ita ɗin ashe iskancin nata bai kai ko ina ba ta furta kalmar,

"Auren Jinsi fa kenan?...............
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨






*MAHREEN 1K*
*MAIDA TSOHUWA YARINYA 1K*
*KYAKKYAWAR FAHIMTA 500*




PAGE 53:



Shiru Billy tayi tana tunanin irin daular da ta ga Amy na da shi, kama daga kan motoci, gidaje da tsabar nerori da daloli,ta tabbata dik macen da zata mallaki gida a kasar turawa nata na kanta ba ƙaramar mace bace.

Wata zuciyar kuwa Ƙauyen Ba mugu ta hango mata,iyayen ta, ƴan uwan ta da rayuwar da taso tayi bayan ta gama yawon ta, a baya ta tsara da ta gama bariki zata koma gida ta tuba tayi aure, amma yanzu da ta tina mijin da take so Mommy tayi mata shigar sauri akan shi, sai kawai taji bata da wani burin da ya wuce na ta amincewa Amy da buƙatar ta na su yi aure,ko babu komai zata yi rayuwa ta ƴanci da jin daɗi,abinda take nema na dukiya, suna da ɗaukaka a harkar tasu zata same shi.

Juyawa tayi ta maida Amy ƙasan ta ta sumbace ta sannan tace,

"Na amince zan aure ki,amma da sharad'i,"

Murmushi Amy tayi cike da jin daɗin nasarar da ta samu na dulmiyar da Billy da tayi tace,

"Ina jin ki my love, ki faɗi sharad'in ki ko menene na ma amince tin kafin na jishi,ke kaɗai nake so a yanzu, bayan ke babu abinda yake da mahimmanci a rayuwa ta a yanzu,"

Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Billy, dama akwai wanda zai so ta har haka? Wataƙila dan babu Mommy a kusa ne, da tana nan da ta k'wace mata Amy ba yanda za a yi a yi mata irin wannan son Mommy na kusa, lallai rabuwar su ma alkhairi ne a wajen ta,kwantawa tayi a saman gadon ta tallabe kan ta tana fuskantar Amy kafin tace,

"Sharad'i na ba wani abu bane mai wahala a wajen ki, ina so idan za a yi wannan auren a yi shi a can ƙasar waje ba a Nigeria ba,sannan ina so idan an yi mana auren na zama ina da wani kaso a cikin dukiyar ki, bayan haka idan mun dawo zaki haɗa mana party da mutanen mu zan kuma gayyato Hajiyata,"

Tinda Billy ta fara tattab'a sharad'in ta Amy take zabga murmushi tana nuna amincewar ta akan hakan,sanda taji Billy tayi zancen gayyatar Hajiya K'waisa sai ta sauka daga gadon tana fad'in,

"Hell no babe ! Ba za mu gayyaci wannan zindiƙin ƙaton ba,ki sauya wani sharad'in amma banda wannan,"

"Haba Sweetheart ki manta komai mana,ki duba fa ki ga yanda ɗaukaka ta same ki, ai ko dan ki kirawo shi yaga yanda arziki ya mamaye ki kin gayyace shi,"

Shiru Amy ta yi zuwa wani lokacin tana nazari kafin daga baya tace,

"Na amince yanzu yaushe kike so mu tafi a d'aura mana auren? dan ni fa ban ƙi ki ce mu tafi yau ba,"

"Mu bari zuwa wani satin mai zuwa ina so na gyara passport ɗina,"

"Ok wani satin then,I love you,"

Murmushi Billy tayi sannan ta mayar mata da martani da,

"I love you too,"

Hira suka ci gaba da yi da tsare-tsaren yanda za su gudanar da shagalin auren nasu da Allah yayi haramci akai,ya la'anci masu aikatawa, yake tsananin fushi akan wanda suke aikata irin wannan zunubin.

************************

Shamsu ne tsaye wajen masu kayan gado suna ta ciniki, mamaki nake yi shin bayan kayan d'akin da aka yi wa Ameerah me kuma ya kawo shi nan wajen saida kayan d'aki?

Ciniki suka gama tsafff tare da alƙawarin gobe za su je suga kayan idan yayi musu a yanda shamsu ke son siyarwa sai su bada kuɗi,idan bai yi musu ba dole ya rage musu wani abu, nan take na gane ashe shamsu ba siya zai yi ba, shi ne zai siyar,sallama yayi musu ya kama hanya ya nufi wajen masu saida tsire ya siyi ƙulli biyu, ɗaya na dubu biyu ɗaya na dubu ɗaya, ana gama ƙulla masa ya wuce shago ya siyo lemon roba na fanta ya sai dangin su sweet da chewing gum har ma da biscuit sannan ya wuce gidan su Ameerah.

Yana aikawa a kira ta ta fito tana wani yatsina,tana ganin shi da ledoji a hannu ta washe baki tana yi masa sannu da zuwa sannan ta koma cikin gida ta samo masa tabarma a ɗakin Innoh ta koma soron ta shimfiɗa masa.

Gaishe shi tayi sannan tayi shiru tana jiran ya bata abinda ya kai mata, Shamsu kuwa daɗin yanda ta saki jiki dashi ne ya sanya shi miƙa mata ledojin dika bai ware nashi ba, karɓewa tayi ta hau yi masa godiya, kallon ta yayi cike da shauƙi yace,

"Gobe iwar haka muna tare da junan mu masoyiya ta,na matsu na gan ki a d'aki na a matsayin mata ta Ameerah,"

"Hummm"

Kawai ta furta tana wani abu kamar mai jin kunya,a haka hirar su ta ci gaba har dai shamsu ya samu damar tattab'a jikin ta ya wuce gida,abinda Shamsu yayi mata yayi matuƙar jan ra'ayin Ameerah, kusan abinda kullum take fatan taga tana aikatawa kenan saboda kallon fina-finan batsa da ya zame mata jiki a yanzu,wata irin buƙatar kasancewa da shamsu ke d'awainiya da ita musamman da yanzu ta rage biyawa kanta buƙata da take yi saboda wahalar da ta sha ta ƙuraje da warin gaba,nan take ta hau addu'ar Allah yasa goben a kai ta gidan mijin ta itama ta ji abinda ake ji a gidan aure.

Karo suka yi da Innoh dake jingine a jikin gini tana jiran shigar Ameerahn dan kar ta shammace ta ta shige bata bata komai ba,a tsorace Ameerah ta kurma ihu ta falfala da gudu zuwa ɗakin ta, tana shiga ta rufe ƙofa tana ci gaba da ihun a kawo mata agaji ta dunguri aljani.

Cikin tsananin jin haushi Innoh tace,

"Ke dan uwar ki Naja buɗe ƙofar nan ba aljani kika dungura ba ni ce,ki fito ki kawo ledar da ya kawo miki mu raba ko nayi miki ba daɗi ,na san halin ki na rowa tsaff shi yasa na lab'e dan in ga me zai kawo miki,"

A hankali natsuwa ta fara shigar Ameerah haushi da takaici tare da baƙin ciki na maye gurbin tashin hankalin da ta shiga,wannan wace iriyar rayuwa ce haka Innoh ke yi? Yanzu kenan akan idon ta shamsu ya gama jagwalgwala ta har ya biya buƙatar shi? Bata buɗe ƙofar ba sai da ta boye babban ƙunshin me ɗauke da nama, lemo, chewing gum,da sweets sannan ta ɗauki ƙasaramin ƙunshi me lemo ɗaya nama ƙunshi ɗaya, tana bud'ewa Innoh ta afka d'akin tana muzurai tare da zagin Ameerah, cikin fushi Ameerah tace,

"Yasin Innoh idan baki dena lab'e ba babu ruwa na idan Allah ya sa ki a wuta,miji da mata ne mu fa ni da shamsu ba wai saurayi da budurwa ba balle ki lab'e ki ga me muke yi,haba Innoh haba Innoh, yanzu kenan fa dik abinda muka yi kin gama gani,"

(Abun takaicin kuma ɗanta na can na iskanci a d'aki ta waya bata taɓa yi masa lab'e ba dan ta san me yake aikatawa,balle ta yi masa gyara)

Kunya ce ta ɗan kama Innoh ta hau susar diddigar kan ta,cikin borin kunya tace,

"Haram ! Zuwa na kenan naga ya miƙa miki leda shine na tsaya ki zo a raba ko ki sammin abinda aka kawo miki, sannan ni ba zuwa nayi na musamman dan na leƙa ku ba, b'uruntu naji na zaci awaki ne suka shigo, gudun kar suyi b'arna shine na leƙa,ni dai buɗe muga menene dan na ji ƙamshin ƙuli,"

Maida ledar bayan ta Ameerah tayi tace,

"Ai kuwa idan dan kin ga sanda ya bani ledar nan kin jima a lab'e,ina fita kema kika biyo ni, dan kuwa ba sai da zai tafi ya bani ba,"

Cike da borin kunya Innoh ta hau zage-zage ta bar ɗakin tana faɗin,

"Shegiya marowaciya, inda Hadiza ta fiki kenan,nan nan abincin gidan ta ta zubo tace a kawo mana mu ci, amma ke gaki a gidan ma an baki kina b'oye wa kar na ci,to gaki ga ƙunshin nan ki ci ke kaɗai kiyi zawo ke kaɗai matsiyaciyar yarinya me shegiyar rowa kawai,"

Ita dai Ameerah ta ji daɗi da Innoh ta tafi bata karb'i ledar hannun ta ba, kuma ta tabbata gobe ba zata sake yi mata lab'e ba, sai da ta rufe ƙofar ta sannan ta samu waje ta baje dika kayan daɗin da Shamsu ya kawo mata,murmushi tayi da ta tina da abubuwan da yayi mata, nan take taji tana iya zaman aure da Shamsu indai zai dinga faranta mata rai irin haka.

Babu b'ata lokaci ta hau lodar nama tana shan lemo,kamar wata mayya haka ta dinga cin naman nan tana zare ido, da ta ji motsin Innoh a tsakar gida sai ta rage taunawa,ita kuwa Innoh tana can tana masifa tare da jiran Ɗan liti ya dawo ko da masifa da bala'i ne sai ta ci tsire zata kwanta bacci.

Tana nan tana sintiri a tsakar gida kamar ƴar ƙato da goran unguwa Ɗan liti ya dawo,adaidaita sahun shi ya shigar saman barandar ƙofar gidan ya kulle sannan ya shiga gidan, ya kama ƙofar gidan zai rufe kenan Innoh ta kwasa a guje mazaunai na rinjayar ta ta isa wajen shi tace,

"Kar ka kulle gidan nan yanzu Malam !"

A tsorace Ɗan liti ya qame a jikin ƙyaure yana zaro ido, ganin ya tsorata da bazatan da tayi masa ne yasa ta sassauta murya tace,

"Malam na roƙe ka da Allah ka taimaka ka siyo min ƙunshin tsire, idan ka kawo min zan baka labarin abinda ke faruwa har nace ka siyo tsiren,yanzu lokaci na ƙurewa kar su tashi,"

"Innoh babu wasu isassun kuɗi a waje na, wannan kuɗin na karin safe ne,idan aka siyo nama ɗari biyar ce zata saura min,"

Kuka Innoh ta fashe da shi ta wuce cikin gida ba tare da ta ce wa Ɗan liti komai ba, ganin Innoh na kuka ne ya sanya Ɗan liti barin gidan jiki a sab'ule ya wuce bakin kasuwa dan siyo mata tsire.

Dariya Innoh ta saki sanda ta koma d'aki ta ji shiru be bi bayan ta ba, ta tabbata ya wuce siyo tsiren kenan, zama tayi tana nazarin yanda zata ci wa Ameerah mutunci zuwa safiya.

Tana nan zaune Ɗan liti ya dawo,ledar ya miƙa mata ta Karb'a ta raba musu naman ta zuba masa nasa akan shinkafa da waken da ta dafa musu, naman ta hau ci tana lumshe ido, cikin santi ta labarta wa Ɗan liti abinda ya faru zuwan shamsu, cikin takaici Ɗan liti yace,

"Amma dai Innoh kin ji kunya alqur'an,yanzu Ameerah kika koma yiwa lab'e tinda Yadikon Sule ta rasu? Lallai tin yanzu zan fara yi wa Sule addu'ar kar Allah ya sa ya zauna a gidan nan idan yayi aure, Allah ya hore masa yayi gini a wani wajen ya zauna,"

Cike da ɓacin rai ya ture kwanon abincin ya fita tsakar gida ya wanke hannu da bakin shi, ɗakin Yadikon sule ya kalla yaji wata k'walla na shirin gangarowa daga idanun shi, ba kaɗan ba yayi kewar matar shi da yaran shi, ya rasa me ke danne masa zuciya da tunanin shi a dik sanda yayi nufin zuwa wajen yaran shi ya gan su,tsayuwa ya gama da tunane-tunane ya koma ɗakin ya haye gado ya kwanta zuciyar shi sam babu daɗi.

***********************

Washegari da safe masu siyan gado suka sallama gidan Mai Dusa dan kwashe kayan gadon da Sule ya siyar musu.

Tin daren jiya da Sule ya koma gida ya yanka ƙarya akan yayi waya da Billy ita tace ya ɗauki kayan ɗakin ta ya siyar ya haɗa lefe ita bata da kud'in da zata bashi da ya wuce dubu goma.

Mahaifiyar ta tayi baƙin ciki sosai kuma ta fusata k'warai saboda ta san dik abinda zai sa Billy ta saida kayan ɗakin da kullum take zuzuta tsada da kyan su to ba dawowa zata yi ba kenan,cikin fushi a daren ta furta,

'Au haka tace? Allah ya bata sa'a,'

Tana faɗin haka ta shige d'akin ta ta kwanta tana zubar da hawayen baƙin ciki da nadamar rashin baiwa Bilkisun ta tarbiyyar arziƙi da bata yi ba.

Masu siyan gado kuwa sun ji daɗin siyan kayan gadon Billy domin kuwa tabbas masu kyau ne da tsada kamar yanda take yawan faɗa, sai dai shamsu ya caka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login