Showing 240001 words to 243000 words out of 276165 words

Chapter 81 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

angwance.

Tin da ya fita gaisawa da sauran matan shi da mahaifiyar shi bai dawo ɗakin ba ballantana yaga a halin da ya bar amaryar shi,tana nan zaune tana kuka ya yi sallama ya shiga ɗakin,tsayawa ya yi yana binta da kallo tare da tina garar da ya kwasa a daren ranar,cikin sigar lallashi ya zauna a bakin gadon sannan ya ce,

"Haba amaryata Hadizatuwa menene abun kuka kuma? Kar fa ki manta ko a musulunci dole sai mun kwanta gado ɗaya auratayya ta shiga tsakanin mu sannan zan sake ki,idan ma zan sake kin."

Mommy ji tayi gaban ta ya yi wata iriyar bugawa,cikin sauri ta ɗaga kai ta kalleshi tana zaro ido waje ta ce,

"Malam ban gane idan ma zaka sake ni ba? Kai fa ka fara kawowa Aunty Naja shawarar nan,kace idan ka aure ni cikin sati biyu za ka sake ni sai ka yi mana zazzafan aikon da zai jawo hankalin Abdul ya maida ni ɗaki na."

Cikin wani irin fushi da kishin da Mommy bata taɓa gani ba,Malam ya buge mata baki sai da ta ji galmi-galmin gishirin da jini ke ɗauke da shi a bakin ta,ihu ta fasa mai ƙarfi tana taɓa bakin tana kallon shi,cikin kuka ta ce,

"Wai ni meye nufin ka dani ne? Me na yi maka kake ta jibga ta tun jiya?"

"Idan kina yi min gardama abinda ya fi jibga ma shan shi za kiyi a gidan nan Hadiza,ki duba mata na kafff su ukun,duk wadda ta buɗe maki bayan ta ba za ki samu inda zaki saka yatsa ba saboda tabon bulalai ya rufe bayan kirif,dan haka idan baki son zama kamar su kina so wannan kyakkyawan jikin ya zauna lafiya,to ki kiyaye kiran sunan wani namijin a gida na."

"To idan ban..."

Wani irin mugun kallo ya sakar mata,babu shiri Mommy ta had'iye maganar ta tana zubar da hawaye,tashi tayi dan dole ba dan ta so ba ta hau gyara jikin ta,ruwan zafi ta dora a rishon ta dake ɗakin ta juye a bokiti ta shiga wanka,cike da ƙyanƙyami ta fito daga band'akin tana jin ta kamar za ta yi amai,alwala ta sake ɗaurawa ta koma ɗakin ta tada sallah.

Tana idarwa aka sallama aka kawo mata tuwon masara sabo dal da miyar kuɓewa busasshiya,sai koko a jug,hawaye ne suka fara zarya a kuncin ta,ga yunwa tan ji sosai amma bata jin zata iya karyawa da irin wannan abincin da sassafe,ƙarshe dai haka ta ja tuwon ta fara ci tana yatsina fuska,dik abinda take yi malam na ganin ta yana murmushin mugunta......
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI




RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨

*Masu nema daga farko ku yi hakuri mun yi nisa, ku duba wattpad ko WhatsApp channel zaku samu.*

PAGE 97:


Hawaye take ta zubarwa tana sake kallon tuwon,Malam kuwa sallama ya yi mata bayan ya gama feshe jikin shi da turarukan saman madubin ɗakin nata, wanda dikan su na maza dama ya saka mata a akwati ɗayan da ya yi mata na lefe. Sallama ya yi mata ya ce,

"To ni na fita nema,sai anjima zan dawo,ki ƙoƙarta ki ci tuwon nan ki ƙoshi,saboda kar na dawo na nemi haƙƙi na ki ce min ga zance ga magana."

A rikice Mommy ta ɗaga kai ta kalle shi,cikin kuka ta ce,

"Da ranar Allah'n za ka dawo karɓar haƙƙin naka?"

"Ƙwarai da gaske,ko haramun ne? Kar fa ki manta sati biyu kacal zaki yi a gidan,kuma na baiwa matana hutu a cikin wannan satin biyu,babu ke babu girki sai dai ki ci ki ƙoshi ki sauke haƙƙin auren dake kan ki dare da rana, wataƙila har da safe kafin na fita aiki,sati biyun na cika na sallame ki,idan kika karya min doka nima na karya maki taki dokar,dan ni bana magana biyu."

Wani irin yawun wahala Mommy ta haɗiya tana kallon Malam daga sama har ƙasa, bashi da makusa ta ɓangaren halittar shi,haka ma ɓangaren tsafta bashi da aibu,ita dai tinda Allah ya haɗa ta da Abdul gani take yi duk namijin da ya raɓe ta zunubi ne,sannan babu wani namiji da take kallo a namijin gaske da ya wuce Abdul ɗin ta,cikin share ƙwalla ta ce,

"Ni dai dan Allah ka ɗaga min ƙafa ba zan iya da ɗaukan lalurar ka ba a kullum sau uku ko biyu a rana,ina laifin sau ɗaya ma? Gaskiya ka sauya min da wani abun."

Murmushi ya yi mai ɗauke da ma'anonin da shi kaɗai ya san su,cikin murmushin ya ce mata,

"To ya yi na ji,kin amince duk abinda na sauya maki da shi zaki ɗauka kuma zaki yi?"

Ba tare da dogon nazari ba Mommy ta ce,

"Ƙwarai zan yi,da dai ka dinga wahal dani kullum gwanda ka bani wani aikin."

"Kin tabbata kin amince? A tsari na bana magana biyu,amma akan ki yau zan fara,dan haka duk aikin da na zaɓa maki fa dole ne kiyi kin amince?"

"Na amince daga nan har na bar gidan ka kar wata alaƙar auratayya ta shiga tsakanin mu,in dai zaka sauya min da wani aikin."

"To ai shikenan magana ta ƙare,sai na dawo."

Shiru tayi masa bata ce komai ba,murmushi ya sake yi sannan ya fita,direct ɗakin uwar yaran shi ya nufa wato uwar gida,yana zuwa ya same ta tana rabawa yaran ɗumamen tuwon dawa miyar kuka, abincin baƙi ƙirin dashi sai tashin ƙamshin daddawa  da sabuwar kuka yake yi,sallama ya yi dika yaran suka watse cikin sauri,dan kuwa mugun tsoron shi suke ji saboda zafin shi da saurin kai hannu.Cike da ladabi matar shi Tsahare ta ce,

"Sannu da shigowa ranka ya daɗe Malam,za a fita ne? To Allah ya bada sa'a ya bada kasuwa mai albarka,Allah yasa yau a samo ya fi na kullum."

Ba tare da ya amsa mata ba ya zaro ɗari biyar ya miƙa mata ya ce,

"Gashi nan,anjima a gyara dawa a niƙo a kaiwa amarya, ita zata karɓi girki a hannun Mero,ku kuma zaku huta da girki,amma zan raba maku kwana a tsakanin ku ukun har tsawon sati biyu,daga nan sai ku koma karɓa-karɓa kakar yanda kuka saba a baya."

Zuciyar ta cike take da tambayoyi,amma sai ta kame bakin ta tayi shiru,dan kuwa bata da hurumin tambayar shi komai,dik abinda ya zarta shine dai-dai a gidan,shi ba a tambayar shi kuma ba a yi masa musu,dan haka yana gamawa ya baza rigar shi da sunan karkaɓewa ya bar gidan.

Ta gaban ɗakin Mommy ya wuce,waya take yi da Sule,dan haka duk ta marairaice masa,ta ce ya samo mata abinci na dubu biyu zata biya shi idan ya kawo mata,cikin wata iriyar muryar kamala da ta sanya Mommy mamaki Sule ya ce,

"Ji nan Hadiza,rayuwar nan fa bata da tsawo bata da yawa,ya kamata duk mu natsu mu ɗauki ƙaddara a yanda tazo mana,ke ba sana'a ba shine kike son kashe kud'in hannun ki ki dawo kina hamma ko? Haƙuri zaki yi ki yi adapting da rayuwar gidan watarana zaki saba,yanzu haka ni bana ma gidan ina primary na gama dik wani abu da ya kamata na gabatar wani satin zan kama aiki."

Hawayen ta ne suka ƙaru dan kuwa ta tabbatar da dik abinda Sule ya sanar da ita gaskiya ne,amma to ta ya ya zata saba da rayuwar gidan gandu irin wannan? Cikin sanyin murya ta ce,

"To Yah Sule Allah ya sanya alkhairi ya sa ka fara a sa'a,na gode."

"Yauwa Hadiza,daɗi na dake akwai ki da sauƙin kai,sai mun sake magana watarana ko? A gaida me gidan."

Sallama suka yi tace ya gaishe da iyayen su da Baaba,gaban ta ne ya faɗi sanda ta tina da yaron ta,cikin sauri ta kashe wayar ta baje a gado ta rushe da kuka,tinda aka kawo ta dama maman ta ke ciwo,saboda babu shiri ta zare Amir daga shayarwa,a haka bawan Allah'n nan babu tausayi duk sanarwar da ta dinga yi na ta yi yaye ba jimawa,be hana shi murje ta daren jiyan ba.

A hankali ta tashi tana jin yanda ƙirjin ta ke yi mata nauyi da ciwo,cikin rintse ido da gimtse baki ta ja kwanon tuwon gaban ta ta buɗe bismillah ta yi ta fara ci,hawaye ne kawai ke zuba a dai-dai lokacin da ta tina yanda take cin kaji da kayan daɗi a gidan Abdul,a rana idan taso tana iya girki da kaza ɗaya da rabi,da dare ta yi abinci da naman rago ko na saniya,da safe tana iya yi musu farfesun naman kan rago ko na saniya,ko wani ɓangare daga cikin naman dabbobin nan masu daraja,idan kuma taso takan iya soya dankalin turawa da ƙwai ta yi farfesun kifi kalar wanda take so,ice cream da chocolates da su biscuits kuwa basu yanke mata,sutura wata na jiran wata kafin ta saka haka Abdul ke ajiye mata, kuɗi a account ɗin ta kuwa duk wata sai ya saka mata,dan kuwa ya ce shi dan ita da ɗan su yake nemar wa kuɗi,tinda Allah ya hore wa iyayen shi sai dai ya kyautata musu,soyayya da kulawar da Abdul kuwa ke bata abun har mamaki yake bata,hatta da tausar ƙafafun ta yi mata yake yi,koda kuwa ya dawo daga aiki a gajiye tace masa tana so zai yi mata ba tare da ya musa mata ba,watarana idan tace ba za ta yi girki bama nashi take so haka yake zagewa,daga shi sai gajeran wando ya shiga kitchen ya dafa mata kuma ya bata a baki,to wai ina hankalin ta ya tafi a lokacin da ya ce zai ƙara auren dik bata tuna waɗannan abubuwan alkhairin da ya ke yi mata ba? Iya rashin sanar da ita da ya yi ne matsalar? To ai ko rannan ta ji wani malami daga cikin manyan malamai yana wa'azi ya ce,idan Annabi zai ƙara aure baya sanar da matan shi na gida gudun kar ya tada masu da hankali. (Ku duba wa'azin Shaikh Mansur Yelwa na Bauchi kafin mata masu gari su yi attacking ɗin Hamibrah boyar Allah).

Gashi nan gajen haƙuri ya sa ta rabu da mijin ta dan kar ya yi mata kishiya guda ɗaya jal,ta auri wanda yake da mata har uku itace cikon ta huɗun,gashi ta baro ƙaramin yaron ta ta zo gidan da yake ɗauke da yara kaca-kaca kamar tsaki,anya Malam yana iya ƙayyade yaran shi ma nawa ne kuwa? Mommy na tsaka da wannan tunanin Mero ta shiga ɗakin cike da masifa ta tsaya akan Mommy,tin daga ƙafar ta mai tsananin datti da faso kamar ba a alwala a jikin ƙafar Mommy ta fara kallon ta,zanin ta da ya yi maƙal-maƙal da datti ta kalla an daura shi a shagiɗe,a hankali ta dire a saman wata shimi da ta koɗe ta jeme kalar ja, dik ta cinye ta wuya,ido suka haɗa ta ga kyakkyawar mace,amma ƙazanta ta dafar da ita ta maida ita wata iriyar kala.

Murmushin yaƙe Mommy ta sakar mata kafin ta sanya hannun ta ta goge hawayen ta,cikin sanyin murya ta ce wa Mero,

"Ina kwana?"

Tsaki mai tsawo Mero ta ja kafin ta ce,

"Da ban kwana ba kin ganni? Tsaya ki ji ni ba gaisuwa ce ta kawo ni nan ba,na zo ne na sanar dake saƙon malam tin da wuri,dan ba zaki zo anjima a sanar dake ga abinda zaki yi ba kice ba haka ba mu kuma mu yi zaman yunwa,idan ma tin yanzu zaki fito ko fara ɗora sanwar miyar tuwon ki fara ai goma tayi,ana kawo garin tuwo sai ki tankaɗe ki ɗora  tuwon,idan kika tsallake dokar malam kin ga nan?"

Juya bayan ta tayi ta kwashe rigar ta ta nuna wa Mommy yanda jikin ta ya yi kaca-kaca da shatin bulala har zuwa ƙirjin ta,tana gamawa ta maida rigar ta tace,

"Idan kunne yaji,to fa jiki ya tsira,sannan bahaushe yace gani ya kori ji."

Cikin kukan da Mommy ta fashe dashi ta ce,

"Kina nufin tuwon dika gidan nan zan tuƙa? To ni ai ban iya ba? Na ga fa tukunyar da ake girki da ita babba ce irin ta gidan bikin nan,gaskiya ta yi min girma ba zan iya ba dama shinkafa ce,amma tuwo ba zan iya ba."

Ƙanƙance idanu Mero ta yi ta kalli Mommy,sannan ta buga cinya tana nunata da hannu ta ce,

"Idan kin ga dama ki ce ma baza ki yi ba,mu zamu dafa saboda yaran mu,amma ki jira abinda zai biyo baya, dan kuwa ba a yi wa Malam musu,gwanda ki gwada ki gaza zai iya sassauta maki hukunci koma ya yafe maki,akan ki ƙi yin abinda ya umarce ki dashi gaba ɗaya,ni kinga tafiya ta,da kika samu ma na zauna ina maki bayani shi yasa kika samu damar faɗin abinda kika so."

Tsaki ta ja ta bar ɗakin Mommy dake tsananin jin yunwa,gashi an tarwatsa mata ƴar ragowar kwanciyar hankalin da take tunanin tana da shi,da ƙyar ta iya ɗaukan kunun ta sha,babu laifi ya yi daɗi,dan haka bata aje jug ɗin ba sai da ta shanye shi tass,gyatsa ta yi sannan ta yi hamdala ga Allah ta tashi zaune,kayan da suke da buƙatar gyara ta gyara ta share ɗakin sannan ta sanya doguwar riga da wando a ciki ta d'aura ɗankwalin kayan ta ja ƙofar ta ta fita. Direct ɗakin surukar su taje ta duƙa har ƙasa ta gaishe ta,sai da suka gaisa sannan ta tashi ta shiga dika ɗakunan matan gidan ta gaida su,Uwar gida Tsahare ce ta yi mata nasiha cikin lallashi ta nuna mata ta daure ta bi abinda malam ya ce, zata aiko mata yaran ta da suka tasa su dinga taya ta wasu abubuwan,ta kiyaye malam baya son musu,godiya tayi mata sannan ta tafi ɗakin ta ta kwanta a gado tana jin kamar ta kira Innoh ta sanar da ita abinda ke faruwa,rashin samun wannan shaƙuwar ne ya sanya ta fasa Kiran Innoh ta kirawo Naja,bata jima ba tana ringing Naja ta dauka bakin ta ɗauke da Sallama,Mommy na jin muryar Naja sai ta fashe da matsanancin kuka,cikin mamaki Naja ta ce,

'Hadiza lafiyar ki kike kuka kamar wata budurwa?'

"Aunty Naja mutumin nan jiya so ya yi ya kashe ni kafin wayewar gari,ba dan Allah ya nufa da sauran kwana na a gaba ba, da sai dai ku zo ku ɗauki gawa ta,shine da safe na ce masa ni dai ba zan iya da lalurar shi ba har tsawon sati biyu,ina neman ya sauya min da wani abun,kin san wai mutumin nan me ya ce na fara yi?"

'Ah ah Hadiza sai kin faɗa min.'

"Girkin gidan nan zan dinga yi aunty Naja har na tsawon sati biyu babu fashi,kwana na kuma zai kaiwa matan shi."

'Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ! Girkin wannan gidan da mutane sun fi talatin zaki yi? Yaushe zaki iya? A gaskiya zan zo na same shi ai ba haka muka yi dashi ba.'

Cikin kuka Mommy ta ce,

"Ah ah kar ki zo ! idan kika zo zai hakan iya zama matsala kuma, dan baki ga azabar da yake yiwa matan shi ba, bayan su babu masaka tsinke saboda mugun dukan da yake musu."

'Oh ni Naja na shiga uku,wannan shi ake kira gaba kura baya sayaƙi,ban taɓa zaton haka lamarin zai zama ba da ban bi shawarar shi ba a lokacin da na kawo masa koken matsalar ki.'

"Babu komai Aunty Naja zan jure,sati biyu kamar yau ne ai,Aunty idan kin je gida ki gaida min da Amir ɗina."

Shiru taji Naja tayi har ta zaci kiran ya katse,dan haka sai ta dinga faɗin,

"Hello ! Hello ! Kina ji na kuwa?"

Da jin haka kawai sai Naja ta kashe kiran,sannan ta kashe wayar gaba ɗaya,hawayen ta ta share tana faɗin,

"Hadiza ki yafe min na kai ki gidan halaka,gashi yanzu ɗan ki ma za a maida shi dangin uban sa,wanda nake ganin gwanda a kai shin a can zai fi samun kulawa tinda wankin shi ma kakar shi baza ta yi ba sai ta kira ni naje na yi masa."

Tana gama faɗin haka ta miƙe ta zari mayafin ta ta yiwa Kaka sallama ta wuce gidan Innoh dan yiwa Amir wankin tafiya gidan Innah Laminde.

*********************

Zaune take a ɗaki tana hutawa ta kira Abdul dan su gaisa,sai dai basu jima da fara gaisawa ba ya katse ta ta hanyar bata labarin da ya bata mamaki na rabuwar shi da Huzaimah,wanda bata ji labari ba sai bayan ta sanar da shi zata karb'o Amir a wajen kakar shi,tinda Hadiza ta yi aure. Cike da mamaki ta buɗe baki ta ce...........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨










*A yi haƙuri a dena tambaya daga farko saboda mun yi nisa an kusan gamawa,me so daga farko su duba wattpad ko WhatsApp channel,ko a jira a fara ɗora audio a YouTube inshaa Allah.*





PAGE 98:








"SARAUTA yaushe hakan ta faru baka sanar dani ba? Yanzu da nake shirin karɓo yaro na damƙa shi amana a hannun matar ka da kawai sai na zo na ga bata nan?"

Cikin sauri tare da tsantsar ladabi Abdul ya ce,

"Dan Allah Innar mu ki yi hakuri,ni kaina abun yazo min a bazata ne,da safen nan kawai na wayi gari bata nan ta tafi gidan yayar ta,koda muka je ni da Bilal a wajen yayar ta da ita kanta yarinyar suka tirsasa ni na sake ta saboda lalurar da nake tattare da ita."

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,amma dai wannan yarinya Hadiza an yi..."

"Ki yi haƙuri Innah kar ki zage ta,ammm naji kin ce ta yi aure? Yaushe tayi auren?"

Jimm Innah Laminde ta yi tana sauraron yanda ta jiyo damuwa ƙarara a muryar shi,me hakan yake nufi? Kar dai ace har yanzu Abdul na son Hadiza? Lallai da ya cika mara zuciya kuwa,cikin haɗe fuska sosai kamar yana ganin ta ta ce,

"Me kake nufi da maganar ka Abdussaboor? Kana nufin wai har yanzu kana son yarinyar nan dik da irin abubuwan da ta yi maka a rayuwa?"

"Ba haka bane Innah kawai dai ina tambaya ne."

"To ina son hakan ya tsaya a iya tambayar kawai,domin kuwa ko ku biyu kuka rage mace da namiji a duniya ka gama auren ta,ko bayan raina ban yarda na ji wata matsala ta rabo ta da gidan mijin ta kai kuma ka aure ta ba."

"Allah ma ya kiyaye,Allah yasa ta auru kenan har abada ba fita, ta je ta ƙarata da rayuwar ta nima na ƙarata da tawa,yanzu dai Innah idan an dawo da Amir ɗin ya zauna a wajen ki kawai,ya dinga taya ki hira."

"Ai dole ni zan riƙe abuna,Allah ya raya mana shi da imani kawai."

"Amin Innah a gaida su Azizah,ni fa ban san


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login