Showing 183001 words to 186000 words out of 276165 words
Chapter 62 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
Junan su Khaleesat da Saddiqa suka yi cike da alamar tambaya a fuskokin su..........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️ ✨
PAGE 74:
Drivern da ya tuƙo dalleliyar motar ne ya miƙawa Munir makulli sannan yayi musu sallama shi da mai gadi ya wuce,cike da murna Munir ya ƙarasa shiga cikin gidan, a hanya yayi karo da Saddiqa dake ta washe baki ita da khaleesat, kallon su yayi da alamar tambaya a saman fuskar shi, murmushi suka yi masa Saddiqa tace,
"Rouh wannan motar sabuwa fa?"
Goshi ya kama tare da lumshe idanun shi yana murmushi yace,
"Kashhh ! Ba haka naso lamarin ya kasance ba,amma tinda kin gani maza jeki ki sako hijabin ki ki zo nan."
Da sauri ta bar parlourn ta wuce zuwa d'aki ta sanyo ƙaton hijabin ta har ƙasa, a waje ta tarar da su suna buɗe motar shi da Khaleesat, tana ƙarasawa inda suke Munir ya miƙa mata makullin motar yace,
"Congratulations maman ƴan biyu, ga gift ɗin ki da na so baki tun kina amarya ban samu dama ba saboda kuɗi na basu cika ba a wancan lokacin."
Hawayen farin ciki ne suka fara zarya a kuncin Saddiqa, cikin sauri ta maƙale shi tana sumbatar kuncin shi tare da yi masa godiya da addu'o'i masu matuƙar daɗi da faranta ran wanda ake yiwa,amsawa Munir da Khaleesat suka yi kafin Khaleesat ta karb'i makullin motar tace,
"To yanzu a madadin ki bari na fara tuƙa motar kafin kema ki iya,Allah ya sanya alkhairi ya sanya albarka, Allah ya tsare ya kare dikkan abun ƙi."
Cikin tsananin farin ciki Saddiqa ta miƙawa Khaleesat makullin motar ta zauna a gefen mai zaman banza, mai gadi ne ya wangale masu gate suka fita suna d'agawa Munir hannu dake tsaye yana yi masu video,sai da suka zaga gari cike da murna da farin ciki sannan suka ɗauki hanyar zuwa gidan Ummi,Saddiqa kuwa na ta ɗaukan su video tana murna,kamar wadda aka bugawa kuduma a kai haka ta tuna da bata baiwa Munir abinci ba, cikin fargaba tace,
"Keee maza mu koma gida ban baiwa Rouhee na abinci ba saboda tsabar zumud'i da zirgilli."
"Yau ɗaya dai ya ɗiba da kan shi mana tinda an gama komai, ba zan tsaya a ko ina ba yau sai a gidan Ummi."
"Wayyo Allah na kunya ta Khalee dan Allah mu koma, ni kunyar Ummi nake ji."
"Ai ita ta jima da mantawa da abinda kuka yi, shi yasa ma kika ga da kika dena zuwa ita take zuwa ta gan ki, ko zaki tabbata ne ba zaki je gidan ba?"
"Allah na san da na shiga zan tuna da abinda ya faru."
"Ni fa in ba ke ba, ban taɓa jin suruka mai kunya irin taki ba musamman a wannan zamanin da muke ciki, yo dan kin bi mijin ki daga ku dai-daita tsakanin ku meye a ciki? Wata ma gidan iyayen ta mijin zai je daga a dai-daita tsakani sai dai iyayen ta su fito suga bata nan ta bi shi."
"Exactly my point ! Ni fa gidan surukai ne, kin ga kuwa dole na ji kunya."
"Ke kika sani, mun ma iso sai ki dira ta window ki koma wajen Rouh ɗin naki."
"Innalillahi na shiga uku Khaleesat."
Cike da dariyar shaƙiyanci Khaleesat ta samu waje tayi parking ɗin motar ta buɗe ta fita tana tsallen murna kamar wata ƙaramar yarinya, akan dole Saddiqa ta buɗe itama ta fita tana ƙoƙarin b'oye kunya da nauyin Ummi dake addabar ta, kafin ta isa Anisah ta fito tana ihun murna,koda ta waiga sai taga Ummi na biye da ita, cikin dai-daita kanta ta nufe su itama tana murnar,nan dai suka dinga taya ta murna da fatan alkhairi, Anisah da Ummi saida suka hau motar suka tuƙa suma suna ta santin motar,a haka Abbah ya dawo ya tarar da su shima ya sanya albarka tare da yi mata fatan Allah ya sauke ta lafiya sannan ya haye sama.
Sai bayan magariba Anisah da Khaleesat suka maida Saddiqa gida,ita kuwa sai hamdala take yi da babu wanda ya sake d'aga maganar abinda ya wuce a tsakanin ta da Munir,suna isa gida suka tarar da Munir kwance a doguwar kujera yana kallo,yaci abinci dik ya b'ata wajen kamar wani ƙaramin yaro,kallon su yayi yana murmushi yace,
"Sai yanzu kuka ga damar dawo min da matata?"
Cikin shagwab'e fuska Khaleesat tace,
"Habaa Yah Munir ji yanda ka ɓata wajen nan dan Allah."
"Na b'ata ɗin,wani yace ku tafi min da mata bata bani abinci ba?"
"Humm gata nan to mun dawo maka da ita ai,sarakan soyayya,mu zamu koma dare yana yi."
"Ta yaya zaku koma to bayan babu mota a hannun ku?"
"Akwai mota a waje ,Yah Neesah ta bari ne a wajen bamu shigo da ita ba saboda ba jimawa zamu yi ba."
Anisah ce ta kalli Saddiqa dake ta bin Munir da kallon so da ƙauna tare da godiya tace,
"To Lailah mu zamu wuce a baiwa Majnun kulawa da kyau, Allah ya sanya alkhairi ya tsare."
Rufe fuska tayi da hannayen ta dika biyu tana dariya, har suka fice daga gidan bata ce komai ba,Munir ne ya raka su ya dawo ya kulle ko ina sannan ya zauna kallo,zama tayi a gefen shi tana sake yi masa godiya,cikin murmushi yace,
"Wai godiyar nan bata isa bane haka?"
"Ai dole na yaba maka kuma na gode maka Rouh."
Kallon ta yayi yana murmushi tare da kashe idanu yace,
"Idan godiya kike so kiyi min muje d'aki ni bana gane me kike faɗa anan."
Babu musu kuwa Saddiqa ta miƙe suka shige d'akin su suna dariya,zama nayi dan in ƙarasa kallon film ɗin da ba dani aka fara ba.
Da misalin sha biyu na dare suna kwance a saman gadon su manne da junan su Munir sai shafa cikin Saddiqa yake yana hamdala,cikin sake shigewa jikin Munir Saddiqa tace,
"Yah Munir ba zan gaji da yi maka godiya ba har abada, saboda ka yi min kyaututtukan da ban taɓa koda mafarkin zan samu irin su ba a duniya,Allah ya saka da alkhairi ya raba ka da iyayen ka da duniya lafiya,Ina so in roƙi wata alfarma a wajen ka, sai dai dan Allah bana so ka ɗauki hakan ta wata fuskar ta daban, ina so ka yi min Kyakkyawar fahimta."
Ɗan haɗe girar shi yayi waje guda sannan yace,
"Uhumm ina jin ki,Allah ya bani ikon yi maki wannan alfarma da kike nema a waje na."
"Yah Munir kaga ni ban iya tuƙa mota ba,amma Babana ya iya,kuma shi ƙaramin direba ne da yake jan adaidaita sahu,ina neman alfarma ka bani dama na mallaka masa motar nan saboda ya sanya min albarka, shi kaɗai nake da shi yanzu Yadiko ta rasu,dan Allah kar ka...."
"Babu komai Saddiqa, ai mota yanzu mallakin ki ce,dan haka sai abinda kike so kiyi da ita zaki yi,ki dena neman alfarma,inshaa Allahu idan na samu kuɗi zan sake saya maki wata saboda ina sha'awar naga kina da taki motar ta kan ki."
Da sauri ta tashi zaune ta hau murna tana sake yi masa godiya,Allah-Allah take yi washegari tayi ta kirawo Baban nata da baya wani sake mata a duk sanda za su gaisa.
Washegari kuwa tun da asuba suka yi wanka suka shirya, Munir ya wuce masallaci ita kuma ta yi sallar ta a ɗakin ta,bayan ta idar ne tayi azkar da karatun ƙur'ani kamar yanda ta saba, sannan ta tashi ta hau aikace-aikacen da ta saba yi dik safiya.
Kallon agogon jikin wayar ta ta dinga yi tana kumawa,a yau sai taga kamar lokacin baya gudu,abincin karin su ta ɗauka ta ajiye a dinning table ta koma parlour ta zauna, wayar Baabaa ta kirawo suka gaisa sannan tace dan Allah a baiwa Sadeeq ya kaiwa Baban nasu,babu musu kuwa Hajiya Baabaa ta bada waya aka kaiwa Ɗan liti tana mamakin me yasa ba a kira shi da wayar shi ba.
Koda aka kai masa wayar aka ce masa Saddiqa ce ta kirawo, yaji daɗi a ƙasan ran shi, amma a zahiri sai yace,
"Ni bani da waya ne da ba za a kira ni ta waya ta ba sai an kira da ta wasu?"
Shiru Sadeeq yayi bai ce komai ba,bai kuma dena miƙa masa wayar ba, a hasale ya karb'i wayar ya hau banbamin faɗa, Saddiqa kuwa hawaye ta hau sharewa tana bashi hakuri,Ɗan liti na matuƙar jin zafin abinda yake yi musu amma ya kasa dena musgunawa yaran nashi da yake tsananin so.
Innoh ce ta fito ta tarar da abinda ke faruwa sai ta karɓe wayar da salon makirci ta saka a handsfree ta ce,
"Yo ke ƴannan banda abinki me yasa zaki kira shi da wayar makiya? Ko bashi da waya ai akwai ta yayan ku Sule ko? Inda Mommy ta fi ku wayo kenan,ko bata same shi ba bata kiran shi a wayar kowa sai ta yayan ku."
'Ku yi hakuri Baba,dama na kirawo ne aka ce min kashe take sai nayi zaton babu caji ne, kuma Yah Sule a wannan lokacin na san barci yake shi yasa ban kirawo a tashin ba.'
"To ya isa haka yanzu dai meye dalilin rangad'a masa wannan sammakon?"
Ɗan liti ne ya ƙure wayar da ido kamar zai hango Saddiqa a cikin ta, cikin muryar kuka Saddiqa tace,
'Baba kana ji na? Dama mota ce Yah Munir ya saya min jiya, shine naga ni bai dace na mallaki mota ba kai baka da ita, shine nace bari na aiko maka da ita sai ka dinga jigila da ita.'
Wata iriyar guɗa Innoh ta saki ta miƙawa Ɗan liti wayar tana rawa da manyan mazaunan ta,ganin Innoh na murna sai shima ya saki ran shi ya hau murna yana saka albarka, jin farin ciki a muryar mahaifin ta ne ya sanya saddiqa share hawayen ta tana godewa Allah.
"To yanzu yaushe za a kawo motar kenan?"
'Inshaa Allahu cikin satin nan za a kawo ta Baba.'
"Allah ya yarda a gaida Mannirun a yi mana godiya."
'Zai ji inshaa Allahu.'
Suna kashe wayar Innoh ta dinga murna tana faɗin,
"Alhamdulillahi muma mun yi mota Ramman Malam Jibo sai a dena yi min gori,Malam dan Allah da motar nan ta iso ka kaini kasuwa a cikin ta ko ba zan sai komai ba a dai ganni a ciki,har ƙofar gidan Ramma nake so ka kai ni mu gaisa ka dawo dani."
Cikin washe baki Ɗan liti yace,
"Kar ki ji komai Uwar gidan Ɗan liti,abinda kike so shi za a yi."
Lokacin da labarin siyan motar ya riski Baabaa ta sanyawa Saddiqa albarka sosai, amma taso ace ta riƙe motar ta, dan kuwa tana jiyewa Ɗan liti haukan Innoh,fatan alkhairi ta leƙa tayi musu kafin ace baƙin ciki ya hana ta zuwa,ile kuwa tana zuwa ta tarar da Innoh har ta fara yada habaicin baƙin ciki ya hana mutanen gida su zo su taya su murnar samun motar da suka yi, cikin hasala Baabaa tace,
"Yo Allah na tuba abinda yayi Baban Gida ai shi Yayi Manniru,da ban haifi uban manniru ba da babu Manniru balle ya auri Saddiqa har ya saya mata motar da zata baiwa ubanta har wasu suce za su yi min gori akai, ni kaina da ina zuwa wani wajen da mota za a ajiye min kamar yanda ake ajiye min duk wani abun buƙata ta na yau da gobe a wadace,gori ai ke za a yi wa mara zuciya, kina ƙin uwar yara da yara amma kina son abun hannun su."
Ganin babu ribar da Innoh zata diba a wannan faɗan ne ya sanya ta cewa,
"Kin ga dai ban kula ki ba,ni ba dake nake ba ki dena zagi na da faɗa min baƙaƙen maganganu,tammm."
"Nima ban kama sunan ki ba ai,ko tsarguwa kika yi?"
Innoh bata sake cewa komai ba ta wuce ɗakin Sule ta hau buga masa ƙofa dan ta sanar dashi labari mai dad'in da ya same su da sassafe.
********
Bayan kwana uku da maganar siyan mota aka kawo motar har garin Ba Mugu,yara da manya da tsofaffi ne suka yanyane motar ana ta yabawa tare da fatan alkhairi, cikin farin ciki Ɗan Liti ke washe baki yana amsawa tare da godiya.
Malam Jibo babban abokin Ɗan liti ne ya matsa kusa dashi yace,
"A gaskiya ya kamata kaima ka fara jigila daga ƙauyen nan namu zuwa wasu ƙauyukan da kuma birane, kai shaida ne akan irin manyan kud'in da nake kamawa a duk tafiya ɗaya da nayi, dan haka idan ka shirya kayi min magana na ɗora ka a hanya kaima a fafata da kai."
"Ai kuwa na ji daɗi da wannan shawarar taka, inshaa Allahu ranar Juma'a zan zo mu tattauna akan hakan."
A haka Ɗan Liti da malam jubo suka tsaida magana zuwa ranar Juma'a za su haɗu a tattauna, ɗan liti yayi register da tashar su sannan yayi duk abinda ya dace.
Haka kuwa aka yi,ranar Juma'a da hantsi Ɗan Liti ya isa tasha ya tarar da Malam Jibo suka gudanar da dik abinda ya dace, cikin sa'a kuwa akwai mutane a ƙasa da yawa babu motoci nan da nan aka fara yi wa Ɗan liti lodin tafiya birni,wanda cikin ranshi ya zaci lodin kauyuka za a yi masa ya fara kafin ya ƙware ya fara zuwa birnin,kafin rana ta take an gama lodi Ɗan liti ya sallami mutanen tasha ya saka kai ya nausa saman titi cike da farin ciki.
Wata iriyar hanya ce suke bi mara kyau, dik kwaltar ta farfashe,titi yayi ramuka babu daɗin tafiya,rashin sabo da irin wannan tafiyar da tuƙin kanshi ne ya janyo samuwar hatsarin da motar Ɗan liti ta kusan samu a hanyar, nan take kuwa ta tsaya cakkk mutane suka hau yi masa masifa tare da faɗin ya sauke su su nemi wata motar su hau basu shirya mutuwa ba,cikin damuwa Ɗan liti ya sauka daga motar yana basu hakuri yace,
"Ku yi min aikin gafara ƴan uwa,kun dai ga ba laifi na bane yanayin hanyar ce da bata da kyau, ku zo ku taimaka min a gyara abinda ya sanya ta tsayawa sai mu ci gaba da tafiya tsayuwa a irin dajin nan hatsari ne saboda yanda rayuwa ta lalace."
Wani abokin Malam Jibo da tinda suka hawo motar yake taya abokin shi Malam Jibo kishi akan motar da ɗan liti yake da ita ne yace,
"Mu taya ka ka gyara me? Da kai baka san kan motar ba ka fara shiga dawa da ita? Babu abinda za mu taya ka, kai matsa sa mana hannu a motar nan me zuwa mu hau mu ware ka ji da shi kai kaɗai,ba dai junan ku gasa da kishi ba? Daga ganin aboki na nada mota yana samun kuɗi kaima ka sayi mota,to gaka ga hanyar ai sai ka gyara kayar ka da kan ka."
Kamar waɗanda aka yi wa baki ko dama suna jin haushin Ɗan litin gaba ɗayan su sai suka sanya wa motar dake tafe hannu,suka shige suka bar Ɗan liti shi kaɗai a dajin ilahi.
Zufa yake sharewa da hannayen shi bibbiyu saboda ranar da ta ƙwalle a saman kan shi,kallon dajin da yake ciki ya sake yi cikin wani irin yanayin da yake ji kamar ya tsala ihu,ko yayi ta zabga kuka babu ƙaƙƙautawa,ya rasa da wanne suna zai kira wannan yanayin da yake ciki,wannan shi ake kira gaba kura baya sayaƙi,kallon matacciyar hanyar da ya biyo ya sake yi sai yaji kukan da yake ta sha'awar yi ya kufce masa,zama yayi ya jingina da motar shi ya ɗage bakin shi sama ya buɗe dika haƙoran shi ya hau tsaga kuka, cikin kukan da yake yi ya hau faɗin,
"Kaico na ! Kaico na ! Yau ina zan saka kai na a wannan dajin na ubangiji? Malam Jibo ya cuce ni ya ci amanata daya bani gurguwar shawarar biyo wannan dajin na ubangiji,nidai na tabbata dai sabuwar mota irin wannan ba za a samu wani gyara a tattare da ita ba,sai dai idan yanayin hanyar ne da bata da kyau da kuma rashin sanin ina zan taɓa ta tashi ne ya jawo min shiga wannan tashin hankalin."
Majina ya sharce ya sake shiga cikin motar a karo na biyu tin bayan tafiyar fasinjojin shi da suka gudu, taɓe-taɓe ya fara yi cikin ikon Allah da rashin sanin abinda ya taɓo mota ta tashi,da azama Ɗan liti ya fita ya rufe kowacce ƙofa da aka bar masa a buɗe ya koma ya shige cikin motar shi ya ci gaba da tafiya, nan take ya ƙudirta idan ma mugunta ce ta sanya Malam Jibo bashi shawarar ya shiga birni shi kuwa zai bashi mamaki, ba zai dawo ba har sai ya samo alkhairi daga birnin.........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 75:
Da misalin takwas da rabi Aunty Naja da Mommy suka kammala dik wani shiri da za su yi,sannan suka rufe gidan suka fito harabar gida suka tsaya, Naja ce ta kalli Mommy cike da tantama da tsoro ta ce,
"Anya Hadiza kina ganin satar fita daga wani gari zuwa wani garin zai haifar mana da ɗa mai ido kuwa? Ko dai ki kira mijin naki mu yi wata ƙaryar ya san da fitar tamu?"
Mayafi Mommy ta sake gyarawa a saman kafad'un ta sannan taɗora jakar ta a kan mayafin ta kalli Naja ta ce,
"Aunty dan Allah mu tafi kafin ƙarfe biyu mun dawo, ba sani zai yi ba in dai ba ke kika sanar da shi ba."
Bakin gate suka nufa suna tattaunawa, Mommy ce ta sanya makulli ta kulle gidan sannan suka fara takawa a ƙafa suna kallon hanya ko Allah zai sa su samu abun hawan da zai kai su tasha. Babu jimawa kuwa wani mai adaidaita sahu ya tsaya a gaban su yana tambayar su ko tafiya za su yi, cikin sauri Naja ta bashi amsa da,
"Tafiya zamu yi bawan Allah, tasha zaka kai mu ta rijiyar zaki nawa ne?"
"Aunty mu hau dan Allah ko nawa ne zan bashi bana son ɓata lokaci."
Murmushi mai adaidaitan yayi da ya ji furucin mommy, ya tabbata yau ranar sa'ar shi ce,dan haka har da kiɗa ya saka musu bayan sun shiga, a guje yake tafiya bisa umarnin Mommy har suka isa tashar, dubu biyu ta bashi suka sauka suka nausa cikin tasha, sai godiya mai adaidaitan yake yi musu tare da fatan Allah ya kaisu dik inda za su je lafiya ya maida su gida lafiya.
Tinda suka shiga tashar Mommy ke baza ido tana neman mota mai ƙwari da kyau da zata ɗauka shata ta kaisu garin