Showing 6001 words to 9000 words out of 276165 words
Chapter 3 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
gidan Sarki dan ɗaukan hotuna da videos domin posting ɗin su zuwa social Media......
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI*
RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)
*PAGE 3:*
Wata iriyar kwalliya suka tsara wadda duk wanda ya kalle su sai ya qara, dan kuwa daga Mommy har Billy suna da kyawun sura sai kuma suka ƙara da wanka ga wayewa da iya gayu.
Tafe suke suna rausaya kamar wasu furanni a lambu, sai latsa waya suke yi suna hotuna a Snapchat, a haka suka isa gidan Sarki bakin su ɗauke da sallama, su na shiga suka yi arba da uwar gidan Sarkin mai suna Innah Laminde wadda ta na ganin su ta washe baki tare da fad'in,
"Ah ah ahhhh kanawan dabo ne yau a gidan namu? Lale maraba da 'ya ta, jiya na gama zancen ki a gidan nan da Umman yara, na ce 'ya ta ta shekara ɗaya da watanni ban sanya ta a idanu na ba,ashe kina nan tafe yau."
"Sai gashi kin yi zancen ƴar halak, 'yar halal ta bayyana a gaban ki, Ina yini Innata? Ya gida ya iyali ya Baba Sarki da fatan ya na nan lafiya bai sake cin daɗi ya taso da ciwon sugar ɗin nashi ba ko? Na zo masa da magani ai daga birni ya zo ya sha ko Allah ya sa a dace"
D'aki Innah Laminde ta wuce su Billy na bin ta a baya, babban parlour ne wajen wawakeke mai ɗauke da kayan more rayuwa kala-kala kamar ba a qauye ba, gefe kuma ga wata qofa nan da za ta Sada ka da asalin bedroom ɗin mamallakiyar d'akin, waje suka samu suka zube a cikin kujerun dake zagaye da tsakar palourn, Billy ta sanya hannu a cikin jakar ta ta d'akko maganin masu ciwon sugar da ta siyo wa Sarki wanda yake mijin yayar mahaifiyar ta ne ta miqa mata, Innah Laminde ce tace,
"Allah dai ya yi miki albarka Billyn Lamindedeee, ki na taya ni kula da ɗan tsohon miji na baki ko gajiya, yanzu dai fata na Allah ya sa ya sha maganin nan, saboda kin ga Abdussaboor ma da ya kawo masa daga can kano qin sha ya yi, wai a bar shi da tafasar shi da cabbage da garahuni yafi gane musu,"
"Ohhh Baba Sarki da gargajiya 5&6 ne ai, Allah ya sa to ya sha wannan ɗin dan ya na da kyau, Hajiyar da nake wa aiki da shi take amfani,kuma ya karɓe ta sosai"
"To Ameen dai, ya qanwata kin ɗauke min hankali ban ko tambaye ta ba, ina fatan dai ta na nan lafiya da sauran 'yan uwan naki?"
"Ahhh alhamdulillahi ta na nan lafiya tace ma a gaishe ki sosai, kowa ma na lafiya qlou,Innah Laminde yaushe Yah Abdul ɗin zai dawo gida zai jima kuwa?"
"Eh toh bana ce ba,dan be jima da komawa ba, kin san babban injiniya a Koda yaushe ana bukatar shi a kusa musamman a irin kamfanin da yake aiki shi yasa ya na zuwa kwanan shi biyu ya koma"
Jiki a sanyaye Billy ta ce,
"Ayyaaa ! ba rabon mu gana ashe wannan karon ma,Allah ya kaimu wani lokacin in da rai ai da rabo,ya kamata dai a bani sabuwar lambar wayar shi dan idan na koma kanon na neme shi mu gaisa."
"Hummmm Allah ya sa ya ɗauki wayar taki kar ki zo ki na min k'orafi irin na wancan karon,"
"Ameen dai, kin san shi ɗin ɗan ra'ayi ne,"
Innah Laminde kallon Mommy da ta yi zukud'iii ta na kalle-kalle ta yi ta ce,
"Ita waccan tunda aka gaisa ta ja baki ta tsuke,gashi ta sha takunkumi kamar jaki mai cizo daga ina take?"
Dariya Billy ta yi sosai sannan ta ce,
"Kaiii Innaah Laminde qawata ce fa Mommy 'yar gidan Ɗan liti,mun sha zuwa gidan nan da ita kuma kullum muka zo sai kin faɗi wannan kalmar da ke bata haushi"
"Aiii haushi na ki ke ji ashe ƴannan? To in kin ji haushi ki dena qunshe baki kamar mahaukaciyar kura a tsakiyar gari,haka kawai ki kama baki ki qumshe shi gummm ya dinga miki azabar wari? Wannan ai duk sanda ki ka cire takunkumin wani na kusa sai ki sumar da shi da warin baki,qudaje kuwa sai dai su dinga zubewa su na mutuwa saboda wari."
Haka Innah Laminde ta dinga yankar Mommy wadda ta qi hasala dan kuwa bata taɓa sanya kayan da ta sa a wannan rana ba,so take ta hasala ta ko hoton aka zo yi idanun ta su fallasa b'acin ran ta,dan haka yaqe ta dinga yi kawai, karshe ma ta ce a sammata ruwa zata sha.
Kwala wa mai aikin gidan kira Innah Lamide ta yi, ta na zuwa ta bada umarnin a kawo wa baqi abin motsa baki bari ta shiga ciki ta qarasa abinda take yi.
Ta na shiga kuwa su Billy suka miqe suka hau yin abinda ya kawo su,dan kuwa ba wai dan gaishe da Innah Laminde kawai suka zo ba, ɗaukan hotuna ne da kuma ganin Abdussaboor ne maƙasudin zuwan Billy.
Bayan sun gama hotunan su ne suka zauna cin kayan flour da shinkafa dafadika da ta ji kifi soyayye sai zob'o mai sanyi da pure water, suna ci suna hira a haka Innah Laminde ta fito ta tarar da su,duk zuwan da suke yi bata taɓa yin arba da bakin Mommy ba sai wannan zuwan,salati ta sanya sannan daga qarshe ta kece da dariya ta ce,
"Ahhh ban ga laifin ki ba yarinya, ina da wani takunkumin ma tun na lokacin kwarona (corona) da wannan yaron ya kawo min ban yi amfani da shi ba zan baki aje a yi ta sanya wa, ke Fure taho ki d'akko min wannan takunkumin na 'yan asibiti, ki d'akko dika kwalin"
Madadin Mommy ta ji haushin kalaman Innar sai ta washe dasorin ta ta na zabga godiya tare da fatan Allah ya sa Innah laminde ta fi qarfin babu a rayuwar ta.
A baqar Leda aka sanya mata face mask d'in ta dinga godiya, bayan sun tafi ne suka tsaya a hanya Mommy ta sai data a wajen wani mai saka caji, suna tafe suna hira Billy na tura wa Mommy hotuna da videos da suka yi ta xender dan kuwa bata da isasshiyar datar da za ta iya buɗe su idan an tura mata ta WhatsApp,ko a kan wannan rashin datar ma sai da Billy ta yi wa Mommy surutu tare da kwad'aita mata tafiya kano ta ga yanda zata wadatu da data har ta sawa wasu ma.
Kamar an ce Mommy ta d'aga kan ta ta kalli tsallaken titin gidan su,ta na d'aga wa suka yi ido biyu da Ɗan liti da ya qura wa inda suke ido ya na so ya tantance shin 'yar shi Mommy yake gani da kaya masu kyau haka ko wata ce daban?
Su na ganin haka Mommy ta juya wa hanya baya ta hau tafiya, basu tsaya a ko ina ba sai a gidan su Billy cikin sauri ta sauya kayan ta zata tafi gida jiki na rawa, Billy ta saki wani wawan tsaki sannan ta ce,
"Gaskiya ki na min abinda bana so, ki na min abinda ke sa na ji kunya, habaa ! Sai kace ba mace mai 'yanci ba? Meye abin jin tsoro haka kamar wadda aka kama ta na aikata masha'a? Dan ya gan ki sai me ? Kashe ki zai yi?"
"Humm ba zaki gane ba, ba wai tsoron faɗan nake yi ba mita ce bana so,"
"Karb'i wannan ki na zuwa ki bashi ki ga idan zai maki faɗa"
Kuɗi Billy ta zaro dubu biyar cass ta ba wa Mommy sannan ta tashi ta sake haɗa mata wasu kayan,bata bar Mommy ba sai da ta tabbata ta gama buga mata kai da kyauta har ta rasa bakin magana, cike da godiya da sanya albarka Billy ta raka Mommy har kwanar gidan su sannan suka rabu.
A kafe ta hango babur ɗin Ɗan liti ya na zaune a saman babur ɗin ana ta kiraye-kirayen sallar magariba amma ya qi tafiya ya na jiran isar ta, fuskar nan ta yi jawur, haqoran nan sai qara suke saboda yanda yake taune su, jira yake ta isa ya ga uban da ya tsaya mata take taake dokar da ya ke saka mata a matsayin sa na uban ta.
Qara damqe kud'in da Billy ta bata dan ta ba wa Ɗan litin ta yi,dan kuwa a ganin ta ko ta bashi sai ya yi mitar nan da ya saba,cikin dabara ta zare dubu uku ta b'oye ,ta bar dubu biyu a hannun ta,ta na isa ta tura baki ta na harare-harare ta tsaya a gaban shi ba tare da ta ce masa komai ba,
"Ke dan Babar ki Innoh wa ya ce ki je ki dad'e haka? Ke wato ga tinkiya uwar tinb'ele ba ki san gida ba sai an nemo ki ko? Tun da na ga wannan me kama da birran uwar tsalle-tsalle ta dawo na san shi kenan yanzu ganin ki zai yi wuya, gidan uban wa ku ka je?"
Bata bashi amsa ba sai ta miqa masa kud'in hannun ta zata yi magana ya riga ta cikin washe baki yace,
"Ah ah, uwar masu gida Hadizatul kubura 'yar albarka,a Ina ki ka samo wannan uban kud'in haka? Ai sai ki yi magana kin bar ni ina ta b'arin zance sai kace wanda aka haifa a tsakiyar kasuwa"
"To Baba ba kai bane,kai komai faɗa ni bana son mita ka sani kuma, amma idan ka fara har sai raina ya ɓaci na yi kuka ka ke daina wa"
Hannu ya sanya a aljihun shi ya d'akko ɗari biyu da hamsin ɗin da ya dawo da su ya miqa mata ya ce,
"Amshi sai kilin ki wanke ran naki da na b'ata miki,mu shiga gida ki bani ruwan alwala na yi alwala na je masallaci na ji ma an kusa sallame sallar"
"To Baba"
Suna shiga ta wuce d'akin su ta ajiye ledar kayan ta ta cire mayafin rigar jikin ta ta koma tsakar gidan, ruwa ta ja musu a rijiya suka yi alwala ya fita masallaci ita kuma ta koma d'aki ta yi sallah cikin rashin natsuwa, dan kuwa hankalin ta gaba ɗaya ya na kan wayar ta, ta matsu ta gama abinda take yi ta je ta fara posting hotunan ta a social network, sannan ta duba sauran kayan da aka bata ta gwada su ta ga yanda za su karɓi jikin ta.
Ta na sallame sallar Ameerah ta shiga ta ce,
"Innoh na Kiran ki uwar gantali"
Ko azkar bata tsaya yi ba ta lailaya wa Ameerah ashar ta ce,
"Sa'ar ki ce ni da ki ke kira na uwar gantali? Idan na kama ki sai ran ki ya yi bala'in ɓaci"
"Oho dai ki je ta na Kiran ki"
Tashi ta yi ta jefar da ɗan siririn gyalen ta da take yin sallah da shi ta maida mayafin kayan ta sannan ta ɗauki ledar da ta shiga da ita ta ce wa Ameerah,
"Ai sai mu je ko? Ko a ka aka ce ki kai ni?"
Waje ta yi ta na qunquni, Mommy ta yi amfani da wannan damar ta soke 1500 ɗin ta a bra ta riqe ɗari bakwai da hamsin sannan ta tafi Kiran da Mahaifiyar su ke yi mata.
Ta na shiga ta gan ta zaune daga ita sai ɗaurin qirji,zanin duk ya zazzage zuwa qugun ta, kitson kan ta kamar wanda ya shekara, ta dasa tuwo da miya a gaba ta na miqawa Yayan su Sule nashi,ta na yin ido biyu da Mommy fushin da take yi da ita ya ragu,karkace kai ta yi gefe ta na zuba wa Mommyn miya a nata tuwon ta ce
"Daga ina ki ke tun d'azu ki ka sa ƙafa ki ka bar gida ko sallama baki min ba balle na san inda ki ka tafi?"
"Innoh daga gidan su Billy nake kin ga ma abubuwan da ta bani,ta dawo da himilin tsaraba sai kin gani kawai ke dai,"
Cike da washe baki Innoh ta ce,
"Kai ki bari dan Manzo? Kawo na gani ko da akwai sayiz d'ina?"
Ba musu Mommy ta miqa mata kayan dan kuwa ta san kaff kayan ba me yi mata duba da cewa ita ɗin irin matan nan ne masu jiki ta qasa sosai ta sama kuma ɗan siriri gata kuma da tsaho, ta na gama d'aga kayan ta ce,
"Kashhh ! Gaba ɗaya ba za su yi min ba, karb'i abun ki,amma ina kuɗi na da ki ka ara d'azu?"
"Kin ga ga ɗari bakwai da hamsin ta bani canjin ruwa da muka siya d'azu,na ce bari na kawo maki kud'in ki da na ara na sai katin waya,"
"Shi yasa da kin tambaya nake baki, amma kin ga wannan me kai kamar gidan ungulun? Be kawo ba, bai bada ajiya ba, ya iya Karb'a ya ce zai biya sai dai na gaji na yafe masa,tun dai akan kuɗi ba zan tsine masa ko na yi masa baki ba"
"Hakane kam, bari na je d'aki na ga ko Shamsu ya kira ni ina kyautata tsammanin zai zo yau"
"To a dawo lafiya"
Fita ta yi daga d'akin ta koma nasu d'akin na 'yan mata, a zaune ta tarar da Saddiqa ta na karatun haddar qur'ani da take yi,kullum idan ta je makaranta ta dawo sai ta je wajen Mahaifiyar ta ta sake koya mata sannan ta dawo d'akin su ta yi ta bita, lokuta da dama hayaniyar Mommy da Ameerah ke sanya ta barin d'akin ta koma wajen Yadiko ta yi karatun ta, ko ta je wajen Baabaa dan can ne ba mai takura mata, matsala ɗaya ke hana ta zuwa wajen Baabaa surutu,amma daga baya ta yi maganin abun da yi wa Baabaa wa'azi dan haka yanzu in ta na karatu Baabaa ko motsin azziqi bata yi dan ta riqe wa'azin da Saddiqa ta yi mata akan ba a surutu idan ana ambaton Allah,amma fa da ta gama karatun ta Baabaa za ta sa ta a gaba da qorafin Innoh ta yi mata kaza da kaza,ko kuma yau a gidan qawar ta an yi faɗa da qawarta da surukar ta,haka zata tsare ta da zance har ta rasa inda zata saka kan ta.
Babu ko sallama Mommy ta shiga d'akin ta wurgar da ledar hannun ta ta buga tsaki,
"Ke wai dole ne ki zauna yin karatu anan? Na ga dai Baba yau a d'akin Innoh yake ki je d'akin ku ki yi karatun naki a can mana,salon kawai ki takura wa mutum ya fasa abinda yake da niyyar yi aikin banza kawai"
Da jin haka sai Saddiqa ta tattara littattafan ta a jakar ta ta miqe ba tare da ta ce mata komai ba ta wuce d'akin su, dan ta san halin Mommy da ta amsa ta zata hau masifa wataqila ma ta dake ta Baban su ya zo qarshe a bata rashin gaskiya tun da su ba su bashi kuɗi kamar su Mommy shi yasa baya wani yi da su sosai a gidan da Mahaifiyar su kamar yanda yake bayyana soyayyar shi ga su Mommy a gaban kowa.
"Allah ya so ki yarinya da kin zauna da na daki banza"
Kayan ta ta cire ta samu waje ta zauna daga ita sai under skirt da bra,tuge acucin kan ta ta yi ta baza gashin qeyar ta tare da furzar da iska,sai ta ji jijiyoyin kanta na sakewa a hankali dan kuwa ba k'aramin matsa ta yi wa kan nata ba.
'Yar kwab'irar wayar ta ta d'akko da ta yi full charge a gidan Sarki dan su sola gare su ta cire password ta kunna data sannan ta shiga social media cike da nishad'i da annashuwar son gabatar da qudirin da ke ran ta.....................
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI*
RUBUTAWA:HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)
*PAGE 4:*
Video d'in ta ta sanya a Instagram, sannan ta sanya wasu a status d'in ta na WhatsApp,murmushi ta yi a dai-dai lokacin da take zaɓar sabon hoton take so ta sauya a DP ɗin ta, nan da nan ta tuna wanda ke kai ya fi shekara bata canja shi ba saboda bata yi sabo ba.
Mutane da dama suna ɗaukan Maman Fadwa(Sunan da take amfani da shi a social media) bata son yawan ɗaukan hoto ne, a cewar ta mijin ta ya hana saboda shi ustaz ne ko na Dp ɗin ta ma ya bari ne dan ta dage ta na so ta saka, shine ya umarce ta da sanya face mask dan baya son a gane masa mata.
Dariya ta yi ta buga cinya sannan ta ce,
"Ina ga fa 'yar mu ta farko ni da Yah Shamsu Fadwa za mu sanya mata dan gaskiya idan Sunan nan be bi ni ba ba daraja a lamarin,"
Dariya ta sake bushewa da ita sannan daga qarshe ta miqe ta hau kwala wa Ameerah kira,cike da bata fuska da rashin kunya Ameerahn ta je ta ce mata,
"Gani maye?,"
"Uwar ki ce ! Na ce uwar ki ce, Ameerah kin raina ni ko? Wato saboda kin ga ina zaune ba makaranta ba sana'a ba kuma mijin aure shi yasa na zama sa'ar wasan ki ko? to jeki na fasa aiken naki tunda ke kin zama 'yar matsala zan je da kai na"
Ameerah na jin aike za ta je wa Mommy sai ta hau murna ta na wage baki kamar wawuya,cikin ɗan yake haqora irin na Ɗan liti ta ce,
"To ai Ke ce ki ke ta kwala min kira kamar na yi laifi baki iya magana cikin lumana ba, me za a siyo? Tsire ko balangu ko doya da k'wai ko shayi da burodi da wainar k'wai?"
"Me shegen kwadayin tsiya,zo ki siyo min kifin Tayiragas,ki ce ya kyauta min ya kuma saka yaji"
"Kin san ki na cin kifi sai an san kin kashe kuɗi a gidan nan ko?"
"To sai me ba nawa bane?"
Da jin haka Ameerah ta sassauta muryarta ta ce,
"Dan Allah nima zan sai na ɗari biyu wadda na zara a kuɗin Innoh kar ki faɗa mata,"
"Ke ni surutun ya ishe ni haka karb'i nan sauran ki dad'e har Baba ya baro majalisa ya rufe gida ba zan buɗe ba"
"Alqur'ani kar ki buɗe na cinye kifin kuma gobe ki ka je zance ki ka dad'e har aka rufe gida ko Zaki shekara kukan akuya ba zan buɗe ba"
Murmushi mommy tayi a lokacin da ta tuna duk lokacin da Shamsu ya zo suka bar qofar gidan su suka tafi wani