Showing 72001 words to 75000 words out of 276165 words
Chapter 25 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
kawai take yi hawaye na zuba a idanun ta alamar ta ji me suke magana akai kuma zata kiyaye .
Ba dan ta so ba haka Alhaji ya bata wata riga ta ɗora a saman kayan jikin ta saboda sanyin da ake zubawa, ya bata wani mayafi ta rufe wuyan ta da shi sannan ya saka mata baqin tabarau suka fita.
A haka suka fita suka tarar da sauran mutanen da duka yi tafiya tare tin daga Kano har Uganda, gani tayi basu da wata alamar damuwa a tattare da su, nan take ta kama kan ta itama dan gujewa fad'awa tashin hankalin da yafi wannan da take ciki.
Cikin abinda be fi mintuna ashirin ba suka kammala fita daga jirgin ruwan suka haye wasu baqaqen motoci, motocin kuwa suka hau sharara gudu suka bar filin jirgin ruwan ɗauke da su Mommy wadda lokaci zuwa lokaci take share hawayen ta.
Sun jima suna tafiya kafin ta ji motar ta tsaya a wani makeken waje mai bala'in kyau,fita suka dinga yi a motocin kafin daga baya su haɗu da wasu turawa farare tass kamar mutum ya taɓa su jini ya zubo, sai masu gadin lafiyar su dake barbaje a wajen kamar sojoji riqe da bindigogi, tafe suke suna dudduba su Mommy kamar yanda ake duba ragon layya akasuwa.
Kusan fiye da rabin turawan nan Mommy ce ta yi musu dan haka sun jima suna musayar yawu a tsakanin su kafin wani matashin bature ya yanko wasu arnan kuɗi masu yawa ya ce ya siyi mommyn a haka, sai ya tsaya yana jiran idan da wanda zai qara nashi akai kuma to yana saurare.
Kusan mintuna biyar suka ɗauka a haka kafin a tabbatar da cewa shine wanda yayi nasarar siyan mommy a kan wannan farashi mai matuqar tsada.
Ɗaya daga cikin yaran shi ne ya buɗe mota ya d'akko maqudan kuɗi a akwati ya bawa Alhaji, Alhaji kuwa kamar zai kwanta a qasa saboda murna ya Karb'a ya tsaya aka ci gaba da cinikin sauran matan wanda sai a lokacin ne suka san meke faruwa, kuka suka dinga yi a tsorace sakamakon bakin bindiga da suka ga ana nuna musu.
Mommy na ji tana gani aka tankad'a qeyar ta zuwa cikin mota Alhaji ko haɗa ido yaqi yarda su sake yi da ita, bata tashi sanin ta shiga uku ba sai da mota ta fara tafiya, a gigice ta dinga ihu tana dukan glass ɗin tare da miqawa Alhaji hannu ta gilashin motar ko da zai taimake ta ya cece ta amma inaa ko kallon inda take be sake yi ba har motar tabar farfajiyar wajen da ta tabbata anan ake kulla duk wata harqallar rashin gaskiya ba tare da hukumar qasar ta sani ba.
Tsananin kukan da mommy tayi ne ya saukar mata da zazzafan zazzaɓi da matsanancin ciwon kai wanda ya sanya ta komawa ta takure a waje ɗaya kamar wata kaza, babu wanda ya kula ta a motar balle ya sanya ta yin shirun dole har suka isa wani qaton mansion ɗin da bata taɓa ganin gida irin shi ba.
Cikin sauri aka buɗe wa mamallakin motar qofa ya fita kafin a buɗe qofar da mommy ke zaune a takure, a hannu wanda ya buɗe mata motar ya ɗauke ta yabi bayan baturen, bai ajiye ta a ko ina ba sai da ya haura da ita saman bene hawa na uku a wani d'aki na alfarma, d'akin da ko a fina-finan turawan da suka saba gani a waya bata taɓa ganin me kyau da tsaruwar irin shi ba.
Yana fita ta sauka daga gadon ta takure jikin ta a waje ɗaya tana kukan danasanin rayuwar da ta jefa kan ta,gaba ɗaya halin da ta shiga be sa ta tuna da addu'a ba ko sau ɗaya, fatan ta kawai ta samu hanyar da zata gudu daga gidan take yi wanda ta san hakan zai yi mata matuqar wahala.
Kwanan mommy huɗu a gidan tana jinyar zazzaɓin da take yi, kuma a iya kwanakin nan bata sake ganin wannan baturen da suka zo tare ba, wata mata ce farar fata budurwa sharrr ke kawo mata abinci da magani, ita ke haɗa mata ruwan wanka ta sanya ta a gaba dole sai ta yi wankan ta shirya sannan take fita ta bar ta.
Yau ne mommy ta cika kwana biyar ciff a gidan baturen da bata san sunan shi ba, bata san sunan qasar da aka kawo ta ba, zaune take taci kuka ta godewa Allah idanun ta sun kumbura sun yi jajawur, hancin ta da leb'unan ta kuwa sun koma pink ta ji takun tafiya ana nufato d'akin da take, daga jin takun nan ta gane ba wanda ta saba ji bane kullum idan za a kawo mata abinci, gaban ta taji ya yi wata iriyar muguwar fad'uwa,hannun qofar aka kama aka murd'a a hankali, cikin wasu baqaqen kaya irin na turawa ta ga kyakkyawan baturen ya shiga d'akin nata yana sakar mata murmushi...................
*Su mommy ai tinda abinda ya fito dake kenan banga dalilin kukan ki ba, kowa akan sana'ar sa ai ci gaba yake nema ko ya kuka ce my fiful?*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH
PAGE 27:
Banda rawa babu abinda jikin Mommy yake yi, hakan ne ya yi sanadiyyar jijjigar kowacce gab'a ta jikin ta, leben ta take ji kamar ba a jikin ta yake ba saboda yanda yake karkarwa, ido ta fitar waje tana kallon yanda bawan Allah'n nan ya samu saman gado ya rashe kamar ya shiga d'akin matar shi, cikin harshen turanci ya fara tambayar ta sunan ta, nan take kan mommy ya shiga rud'ani da jin kalmar da ya furta, shin what is your name da ta saba ji ya ambata ko kuma su ta nan kalmar na da tata ma'anar ne?
Cikin ɗan haɗe fuska ya tashi zaune da kyau ya sake maimaita tambayar da ya yi wa Mommyn, bakin ta na rawa ta kalle shi ta furta,
"My name is Hadiza Ɗan liti ko kace Mommy,"
Haɗe girar shi ya yi cikin harshen turanci ya sake cewa,
"Me kike nufi da Hediz Dant? Mommy ? Me kike nufi bana gane me kike faɗa,"
Hannu mommy ta fara yarfawa saboda yanda taga yana kusantar inda take a rakub'e yana miqa mata hannu dan ta je inda yake,da dane babu abinda zai hana ta yin farin ciki da kwana da bature har ma ta ɗauka a waya ta ajiye dan kafa tarihi, amma a yanzu da take cikin tashin hankali da damuwa tare da tsoro ji take yi har abada ma ta dena karuwanci,in har tana zaune za a sato ta daga qasar ta,sannan a wuce da ita ta qasashe mabanbanta ta jirgin sama da na ruwa a kawo ta qasar turawa a siyar a gaban idanun ta to fa karuwanci be yi mata rana ba, ta tsinewa ranar da ta baro garin Ba Mugu zuwa cikin garin Kano da sunan aikatau ta sauya layi zuwa karuwanci.
Tana tsaka da tunani ta ji ta a saman cinyar baturen nan yana shafa jikin ta ya na sunsunar ta kamar wata mage, da sauri ta zabura ta sauka daga jikin shi ta yi bakin qofa zata gudu, murmushi ta ga yana yi mata, cikin sauri ta juya ta hau qoqarin buɗe qofar amma ta ji ta a rufe an saka mata makulli,ihu ta ware baki tana yi tana faɗin,
"Jama'a dan Allah ku zo ku cece ni wajen wannan nunar ranar, na shiga uku ni Hadiza an kawo ni mahallaka,"
Cikin abinda be fi minti biyar ba bawan Allah'n nan ya kama mommy ya cire mata kayan jikin ta, cikin rashin imani yake sarrafa ta ta yanda tinanin ta da hankalin ta be taɓa kawo mata wani ɗan Adam zai nemi mace cikin mugunta haka ba.
Wuyanta ne a hannun shi yana shaqewa kamar zai kashe ta, fuskar ta tayi jajawur saboda mari da dukan da ta sha a qoqarin ta nayi masa musu da take yi, be kyale ta ba sai da ya ɗauki awanni yana wahal da ita da sunan biyan buqatar shi,a dai-dai wannan lokacin kuwa Mommy ta sha wahala ta yanda ko hannun ta bata iya d'aga wa, jin ta take yi kamar ba a duniya take ba, tinanin ta ya gama bata ta mutu bata da rai shi yasa bata jin gab'ob'in jikin ta na motsawa.
Qarar rufewar qofar d'akin ne ya sanya ta lumshe idanun ta a hankali ta sanya harshen ta dan ta lashi labb'an ta da ta ji sun qara girma akan girman da suke da shi, da sauri ta maida harshen ta saboda yanda ta ji ta laso wani abu me kama da jini haɗe da majina a jikin shi.
Sake buɗe qofar d'akin nata aka yi, a sannan ne taji wani kuka ya zo mata saboda ta gane takun wadda ke zuwa kullum ta taya ta wanka da shiryawa ne,ita kanta baturiyar da ta shiga taga b'arnar da uban gidan ta ya yi wa Mommy sai da ta saki wata ajiyar zuciya tare da toshe bakin ta, da gudu ta qarasa wajen mommy ta ja abun rufa ta rufe mata jikin ta sannan ta d'ago ta ta manna ta da qirjin ta.
Kuka kawai Mommy take yi tana furtawa baturiyar nan,
"Help me dan Allah, ki maida ni garin mu ko zaman kanon ma ni na fasa gida zan koma,"
Banda kalmar Help me baturiya bata gane komai ba, sai kawai ta tashi a hankali ta kama mommy ta kai ta band'aki,ruwa mai d'umi ta haɗa ta sanya mommy a ciki, ihu mommy ta dinga zubawa tana qoqarin fita daga ruwan saboda yanda take jin azaba a dikkan sassan jikin ta.
Da kyar baturiyar nan ta samu Mommy ta natsu ta zauna a ruwan ta na jin dad'in yanda ruwan ke ratsa ciwukan jikin ta, ruwan na hucewa ta sake haɗa wa mommyn wani, bata barta ba sai da ta yi dressing ciwukan da ta samu har na gaban ta, sannan ta fito da ita ta bata magunguna ta bata madara mai d'umi ta sha ta kwanta a saman gadon da ta sauya wa zanin gado.
Cike da tausayawa ta fita ta bar Mommy dake tunanin rayuwar da ta faɗa, amma me yasa a fina-finan turawan da take gani bata taɓa cin karo da wadda aka azabtar irin ta ba? Ko dan ita ta yi masa gardama ne yasa ta daku haka? Ashe dariyar da bature ke yi a waya dik qarya ne mugunta ce fal cikin shi?
Da ire-iren tunanin nan mommy ta rintse idanu bacci mai nauyi ya sace ta wanda ko minti uku bata yi da fara baccin ba ta farka da ihu tana faɗin,
"Wayyoo Allah na Innohta wayyoo Babana ku zo ku ɗauke ni daga nan ze kashe ni, Allah na tuba ba zan sake yawon iskanci ba daga nan qauyen mu zan koma na yi alqawari, Allah ka taimake ni kar mutumin nan ya kashe ni,"
Ihun ta ne ya janyo hankali masu aikin gidan har suka kirawo mai kula da mommy wadda ake kira da Miranda,da gudu kuwa ta shiga d'akin ta kama Mommy da ke fizge-fizge da shure-shure,cikin kuka mommy ta hau yi wa baturiya magana ta sigar da take ganin zata fahimce ta,
"Please my sister help me, ni 'yar uwar ki ce Female, dan girman Allah female help female run, i want to go to my house,help me no kill me please,"
Wani irin matsanancin kuka Mommy ta fashe da shi kamar ranta zai bar gangar jikin ta, yanda jikin ta ke rawar sanyi kuwa shi yafi tsorata Miranda ta tashi cikin sauri ta shiga bathroom ta buɗe wata locker ta kwaso magungunan zazzaɓi da kashe rad'ad'in ciwo har da masu sanya bacci ta dawo ta ɗauki ruwan dake cikin wani babban glass cup ta bawa mommy dan ta sha, qin Karb'a Mommy tayi ta ci gaba da kuka tana roqon ta da ta taimake ta, hawaye Miranda ta yi saurin sharewa saboda tsananin tausayin Mommy, ba tin yau ubangidan nata ya fara cin zarafin mata irin haka ba, sai dai wannan karon abun yayi yawa, bata taɓa ganin ya jiwa mace ciwo irin wanda ya jiwa mommy ba, lallab'a mommy tayi tana yi mata alqawarin zata taimake ta idan ta yarda ta sha maganin, da kyar Mommy ta yarda ta sha maganin ta koma ta kwanta saboda qarfin da suka yi mata nan da nan bacci ya ɗauke ta.
Cikin sauri Miranda ta kwashe magungunan ta mayar bayan gida ta jawa Mommy qofa ta bar d'akin cike da jimamin abinda ya sami mommy.
A can dakin Alex kuwa kwance yake cikin farin ciki yana busa qatuwar tabar da ya kunna me kama da itace, hayaqi ya busar ya jawo wayar shi dake ringing ya amsa kiran ya kanga a kunnen shi, nan take ya hau hira da abokin shi da suka siyi mata a rana ɗaya, anan abokin shi ke sanar da shi yarinyar da ya siya ta bashi haushi kuma bai same ta yanda yake so ba ya kashe ta har an b'atar da gawar ta,yana so yanzu ya sake haɗa shi da mutumin da suka siyi 'yan matan dan ya sake siyan wata,(Alhaji yake nufi mai safarar yaran mutane yana siyarwa turawan da kuɗi yayi musu yawa basu san me za su yi dashi ba)
Cikin lumshe idanu Alex ya hau tuna yanda ya samu mommy har hakan yayi sanadiyyar kasa hakuri da ita da yayi ya yi mata fata-fata,nan take ya hau baiwa abokin shi labarin haɗuwar mommy har ma ya yi masa tayi idan yana da buqata shima zai iya zuwa ya bashi aron ta.
Babu b'ata lokaci suka yanke shawarar cewa abokin nashi zai zo nan da sati ɗaya shima ya ji abinda Alex ɗin ya ji wajen mommy, bayan sun kammala wayar ne ya tashi ya fita daga d'akin shi ya sauka zuwa benen da aka ajiye masa mommyn, ko da ya shiga d'akin sai ya tarar da ita tana bacci, irin wahalallen baccin nan mara daɗi mai cike da rad'ad'in ciwo da gajiya,juyi ta sake yi ta na sambatu shi kuwa sai ya samu gefen gadon ya kwanta ya rungume ta a jikin shi yana ci gaba da busa tabar shi.
************************
Dare ne sosai dan kuwa agogon hannun Abdul ya nuna masa qarfe ɗaya tayi da mintuna ashirin da uku, tafe suke a cikin garin na New York wanda ya ɗauki sanyi sosai duba da yanda ake ruwan qanqara ko ina yayi fari tas saboda qanqarar,dan haka dole mutum ya samu manyan kayan sanyi ya sanya dan rufe jikin shi gudun kada sanyin yayi masa illa.
Abdussaboor ne sanye cikin manyan kayan sanyi baqaqe da baqin takalmi shi da abokin aikin shi da suka je qasar domin gudanar da wani aiki na musamman da kamfanin su ya tura su, coffee suke tafe suke sha suna hira har suka isa hotel ɗin da suka sauka, direct d'akin da suka kama suka shiga suka hau cire rigar sanyin dake saman kayan su suka kunna room heather dan su d'umama jikin su.
Abdussaboor ne yace,
"Ni fa ina ga duk waɗannan abubuwan da muke son siya mu kai qasar mu dik zamu iya qirqirar su a Nigeria tinda muke da ma'adanan kuma mu muke siyar musu ma'adanan namu,amma na rasa me yasa ba za mu yi hakan ba sai dai mu siyar masu da ma'adanan da ake sarrafawa a yi abubuwan da muke kashe maqudan kuɗi akai, kuma mu sake kashe wasu maqudan kud'in jirgi, hotel, abinci, kayan sakawan da zai yi dai-dai da yanayin da suke ciki mu siya mu sake mayarwa qasar mu, wannan toshewar basira na da yawa Bilal,me yasa dik aka bar kamfanoni masu mahimmanci suka mace a Nigeria? Me yasa ba za a qirqiri wasu ba dan samun ci gaban mu? Me yasa ba za a bawa matasa aikin yi ba ta hanyar buɗe sabbin kampanoni da inganta wanda muke da su? Kai babban abun takaicin fa shine nan nan noman kayan miya da su doya da dankali wai dole sai damina tayi sannan za a same su ib large quantity,da damina ta wuce sai dai ka samu a farashi mai mugun tsada sabodaba kowa ke noman rani ba kuma masu kud'in mu da shugabannin mu sun qi su yi investing kud'ad'en su wajen gina manyan kamfanunuwan da za a kula da noman ranin,kaii Allah ya sawaqe ya kawo mana mafita mafi alkhairi a qasar mu Nigeria,"
"Hummm Ameen dai SARAUTA, ai duk wannan bayanin da kake yi aboki na gwamnati ta san da shi, a sanya hakan a aikace ne ba za a yi ba,banda kashe manyan kuɗi wajen biyan mutanen da sai sun ga dama suje Office da waɗanda ke aiki a cikin AC babu abinda aka sani, qananan ma'aikata musamman malaman makaranta da likitoci da manoma kuwa sai dai babu da yunwa ta kashe su, su fa da alama shugabannin namu sun riga sun shirya ɗaukar nauyin zunubin dake cikin yin mulki na rashin adalci shi yasa kaga suke cin kud'in talaka yanda suke so,"
"Tabbas sun shirya mutumi na, to in ko haka ne a bar musu kayan su su ɗauka haqqin su ne,"
Dariya suka kwashe da shi sannan suka tafa, bathroom Abdul ya shiga ya bar Bilal zaune yana danna wayar shi, ko da ya fito gadon shi ya haye ya ɗauki wayar shi ya kira Innah Laminde suka gaisa, daga nan ya kirawo Sarki suka gaisa suka ɗan taɓa hira game da aikin makarantar da ya bayar ake yi wanda har an kusa gamawa fenti kawai ya rage, daga qarshe sarki ya dinga sanya wa ɗan nashi albarka tare da yi masa fatan Allah yasa arziqin shi ya fi haka.
***************************
Kwanan mommy uku tana jinyar jikin ta,babu laifi ta fara samun sauqi saboda yanda Miranda ke kula da ita ta fannin cin abincin ta da bata magunguna tare da gasa mata jikin ta.
Duk wani inda jini ya kwanta a jikin ta saboda marukan da ta sha ya fara warewa fatar ta ta fara dawowa normal saboda ointment ɗin da ake shafa mata na kawar da ciwuka a jikin ɗan adam.
Miranda ce tsaye a gaban Mommy tana yi mata magana akan ta fito ta sauka qasa ta je lambun gidan ta ɗan yawata ta shaqi iskar ilahi ko zata ji sauqin