Showing 270001 words to 273000 words out of 276165 words
Chapter 91 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
kuwa bashi da wani da ya fi kusanci da shi sama da Alhajin,ba tare da ɓata lokaci ba aka saka rana, Juma'a mai zuwa za a ɗaura auren Hadiza da Abdussabour a sabon masallacin Juma'a na garin Ba Mugu,wanda Abdussaboor ɗin ne ya gina shi da kud'in shi.
Sallama suka yi da juna kowa ya tafi yana farin ciki da sake kulluwar alaƙar auren Mommy da Abdul ɗin.
Tinda suka tafi aka sanar da Abdul yanda abubuwan suka kasance ya kira Mommy dan su sha hirar soyayya,tana ganin kiran shi ta ƙi d'agawa, hankalin Abdul ba ƙaramin tashi ya yi ba,nan da nan ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tunanin abinda ya hana ta daukan wayar shi. Ganin irin halin tashin hankalin da yake ciki ne ya sanya Suhailah tashi daga parlour ta komawar ta ɗakin ta ta kunna TVn dake ɗakin ta ci gaba da kallon ta. Ranta ba karamin sosuwa ya yi ba da irin rawar kan da Abdul ke nunawa akan maida auren shi da Mommy,amma dole ta danne ɓacin ranta dan tin kafin ta aure shi ta san labarin soyayyar su a wajen yayan ta Bilal.
Ta ɓangaren Mommy kuwa taƙi amsawa ne saboda ta san yana gida a dai-dai wannan lokacin,idan ita ce yake kiran wata yana cikin gida ba zata ji daɗi ba,dan haka itama ba zata yiwa Suhailah da ko uhum bata ji ance ta ce ba game da komawar ta gidan mijin ta.
A hankali ta furta,
"Ai dole ma na kirawo ka gobe da kaina idan ka fita aiki,dan kuwa akwai mahimmiyar maganar da nake so na sanar da kai kafin na yarda a ɗaura wannan auren.".........
*Wata sabuwa...*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 109:
Abdul ya jima bai yi bacci ba yana ta duba message ɗin da ya yi wa Mommy amma shiru babu amsa,gajiya ya yi da zaman jiran reply ɗin ta ya kashe data ya kwanta bacci ba dan ya so ba.
Washegari da safe haka ya tashi duk jikin shi babu ƙwari,a hankali yake shiryawa,yana kammalawa ya fita parlour ɗauke da jakar shi da wayoyin shi a hannu,Suhailah ya kalla ya ga fuskar ta babu walwala ko kaɗan,zama ya yi a kujerar dinning suna fuskantar juna,murmushi ya sakar mata a dai-dai lokacin da ta deb'i abinci zata kai bakin ta idanun ta suka sauka akan nashi. Juya idanun ta tayi ta ci abincin ta ba tare da ta mayar masa da murmushin ba,a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce,
"Good morning my love."
"Morning."
Ta furta fuska a haɗe,hannun shi ya miƙa ya kama nata dake zaune a saman dinning ɗin,cikin salo yake murza yatsun hannun nata,a hankali ta zame hannun ta ta miƙe tsaye riƙe da plate ɗin da bata ƙarasa cin abincin ta ba,mayar da abincin cikin wata roba tayi ta saka a fridge dan kuwa ta san babu kyau zubar da abinci. Kanshi ya dafe cikin wata iriyar murya ya ce,
"Ki yi haƙuri dan Allah idan na ɓata maki rai akan abinda nayi jiya,a jiyan ne aka yi min tambayar auren Hadiza,har an saka ranar aure ma nan da Juma'a mai zuwa,shi yasa kika ga ina ta kiran ta sai kuma naga bata ɗauki wayar ba."
Cikin hanzari Suhailah ta katse shi ta ce,
"Ta ya zata ɗauki wayar ka tinda hankali ya shige ta ta gane bata son ta yi min abinda idan wata tayi mata baza ta ji daɗi ba? Sai dai kash kai da ya kamata ka kiyaye hakan bai dame ka ba,damuwar ka shine kawai Hadiza ta ɗauki waya ku sha soyayya koda hakan zai sosa zuciyar Suhailah,ina so ka san wani abu Abdussaboor,idan har baka damu dani ba to nima ba zan damu da kai ba,sannan idan ka tsaya ka nuna min damuwa da soyayya to nima zaka samu sama da haka a waje na,ni ba irin matan nan bane da ke bin namiji koda baya son su ka gane?"
Mamakin kalaman ta ne suka sanya shi kasa furta koda kalma ɗaya ne,a haka ta yi masa sallama ta wucewar ta motar ta ta fita zuwa asibiti. Da ƙyar Abdul ya samu ya tura abincin shi ba dan yana jin daɗin shi ba,nanata kalaman Suhailah ya dinga yi a ran shi,cikin mutuwar jiki ya sauke ajiyar zuciya tare da furta,
"Maganar ki gaskiya ne Suhailah,dole ne na maida hankali na tsaya akan adalci gudun kar na faɗa halaka,ya Allah ka bani ikon kamanta adalci a tsakanin matana,Allah kasa kar na cutar da kowacce a cikin su,Allah ka bamu zaman lafiya."
Tinda ya yi wannan addu'o'in sai ya samu natsuwar zuciya,ƙarasa cin abincin shi ya yi ya fita office,yana zuwa ko zama bai yi ba Mommy ta kira shi,murmushi ya yi ya amsa wayar cikin amsa sallamar da ta yi masa,a shagwab'e Hadiza ta ce,
'Shine baka fito office da wuri ba kooo?'
"Ya akai kika gane yanzu na shigo office?"
'Ya kake amsa min tambaya da tambaya? Sannan ta yaya ba zan san lokacin zuwan ka office da tashin ka ba? Ai a ganina duk macen da bata san lokacin tashin mijin ta aiki da zuwan shi ba ta binciki kanta gaskiya."
"Wannan gaskiya ne,to me yasa jiya kika ƙi ɗaukan waya ta na kira na taya mu murna?"
'Humm Abban Amir kenan,wato so kake yi na shiga lokacin ƙanwata ko? Auu yayata zan ce,dan yanzu na koma nice ƙarama.'
"Har abada kece a gaban kowacce mace a zuciyata Hadiza."
Kalaman shi sun sanyaya mata zuciya sai ta ji kamar ta taka rawa dan murna,murmushi mai sauti ta saki kafin ta ce,
'Uhumm ni fa baka sanar dani inda zan zauna ba bayan auren mu.'
"Duk inda kike son zama anan zaki zauna Baby,abu ɗaya nake son sanar dake dama,kar ki damu da siyan komai ni da kaina zan yi maki duk abinda ya dace."
'To dama ni dai ina son sanar da kai nafi son zama anan bana son sake zama a kano sai idan Allah ne ya nufa kuma.'
Ba ƙaramin daɗi maganarta ta yi masa ba,domin kuwa ya riga da ya san idan aka haɗa mommy da suhailah a gida ɗaya,watarana sai ya zo ya ga sun haɗa masa tashin hankalin da ba zai iya warware shi ba,sai gashi ta sauƙaƙa masa ta kawar masa da tsoron da yake ji. A hankali ya furta,
"To shikenan tinda haka kike so,amma naso ace kina kusa dani a koda yaushe."
"Kar ka damu,idan bana tare da kai a zahiri ai ina tare da kai a zuciya ko? Sannan sai wani abu da nake so kayi min,ina son ka yi zaman ka a kano ka dinga zuwa waje na duk ranar Juma'a da ka tashi daga aiki, sai ka koma ranar lahadi da yamma.'
"Kaiii inaaa ba zai yuwu ba gaskiya,zan dai dinga zuwa duk ranar girkin ki,na yi maki kwanakin ki, sannan itama na yi mata kwanakin ta ranar nata girkin."
'Baby ya za ayi ka dinga yawo a hanya koda yaushe?'
Sunan da ta kira shi dashi ne ya sanya shi murmusawa kafin ya ce,
"Tafiyar ai ba wata mai nisa bane,dan haka kar ki damu."
Da ƙyar Mommy ta shawo kan Abdussaboor ya amince da abinda take so kafin suka yi sallama,suna kashe waya ya tura mata dubu ɗari uku sannan ya yi mata message ya ce gashi nan ta yi hidimar biki dasu,godiya ta yi masa sosai kafin ta tashi ta tafi ɗakin Innoh cike da murna ta sanar da ita yanda suka yi da Abdul ɗin,shiru Innoh ta yi kafin ta ce,
"Wannan magana ai Yayah ya kamata ki sanarwa dan ni ban wani san ya za ai ba."
Dariya Mommy ta yi sannan ta tashi ta je d'akin Baaba,zaune ta gansu ita da Sadeeq wanda ke ta tilawar karatun ƙur'ani,Baaba kuwa sai gyangyaɗi take zabgawa abunta,dira a gefen ta Mommy tayi sannan ta ce,
"Baaba ki farka ki bi ayari kar su wuce su barki."
A gigice Baaba ta buɗe idon ta tana so ta miƙe tsaye,bakin ta sai surutai yake saki wanda ba a gane inda ta dosa,Sadeeq ne ya rufe ƙur'anin shi yake ta sheƙa dariya,Mommy kuwa tsabar dariya har kwantawa ta yi a wajen,sai da Baaba ta dawo hayyacinta ne ta ɗauki maficin dake gefen ta ta kwaɗawa Mommy akai sannan ta ce,
"Kin tsorata uban ki Ɗanli,kafira me ƙaton baki."
"Ah ah fa Baaba, Ah ah fa Baaba, dan na ga ƴan'uwan ki zasu wuce na faɗa maki laifi ne? Meye na zagi na haka?"
"Ki rama in kin so,dama uwar ki ta kwana biyu bata min tijara ba,se ki fanshe ta."
Dariya Mommy tayi kafin ta ce,
"To ni dai ba faɗa bane ya kawo ni wajen ki,dama kuɗi Abdul ya turo yace nayi hidimar biki,shine na kaiwa Innoh tace na same ki na baki,da ke yafi dacewa nayi maganar ba da ita ba."
"Masha Allahu,Innohn Ɗanli ta fara hankali,haka ake so ai idan an girma asan an girma,yanzu abinda nake so dake shine,alewa za a raba da cingam a gari ayi gayya sosai saboda kowa ya shaida wannan aure,abinda ba a yi ba a baya dole ne mu yi shi a wannan karon,yanzu ne nasan Uwar masu gida za tai aure,aro min hanci na zabga guɗa."
Nan take Baaba ta karkace ta sheƙa guɗa,Innoh na ɗaki ta jiyo guɗar Baaba sai ta saki murmushin farin ciki,ashe dama zaman lafiya daɗi ne da shi? Ashe ƙiyayya ciwo ne da ke cinye farin ciki da zaman lafiyar mai yin ta?
Da wannan shawarar Mommy ta kira Aunty Naja ta sanar da ita duk abinda ke faruwa, sannan ta ce ta bata mijin nata ta roƙe shi ya barta tazo bikin dan kuwa ita ce uwar amarya,da ƙyar ya amince zai barta tazo tun ana sauran kwana biyu bikin.
Da rana ta baiwa Sule ATM ɗin ta bayan ya dawo daga makaranta ya ciro kuɗi,ita da Abbe da Shalele suka shiga kasuwa suka fara siyayyar duk da suke da buƙata.
Washegari da safe Ameerah tazo da Fadilah suka hau ɗaura alewa da cingam a leda suna baiwa yaran maƙota suna rabawa gida-gida,cikin ƙanƙanin lokaci gari ya ɗauka mutane suka shaida za a maida auren Hadiza da Abdussabour. A can gidan Sarki ma rabon alewar shagalin bikin Abdul ɗin suke tayi kamar wannan ne auren da ya taɓa yi a duniya.
Sadeeq Mommy ta cikawa leda da alewa har da biscuits ta ce ya kaiwa dangin Yadiko dake ruga,dan kuwa sun ji labarin dawowar su,hakan da Mommy ta yi ya sa Sadeeq ya ji matuƙar daɗi a zuciyar shi. Cike da farin ciki ya karb'i kud'in machine ɗin da ta bashi ya tafi kai saƙon.
Ameerah da mommy ne ke ta faɗa akan kai alewar gayyata gidan Malam,Mommy tace akai,Ameerah tace ba za su gayyaci iyalin boka sabgar su ba,da kyar Baaba ta shiga maganar Ameerah ta bari aka kai wa Tsahare alewar gayyata.
Bayan Abdul ya koma gida da dare ya sanar da Suhailah yanda zaman su zai kasance da Mommy,fatan alkhairi ta yi musu baki ɗaya,dan kuwa ta gama ƙudirtawa a ranta ko nan gidan Mommy tace zata zauna matsawa zata yi ta bata fili,ita ba baƙuwar zafi bace,sai dai tsarin da mommy tazo dashi ya yi matuƙar burge ta itama.
*****************************
Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce rana bata ƙarya,sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, ranar alhamis rana ce da mutanen ƙauyen Ba Mugu suka tashi cike da farin ciki,baƙi ne ko ta ina ke zuwa mutan gari an cika a ƙofar gidan Sarki,gidan Ɗan liti kuwa mata ne kawai ke kai komo a tsakanin su,saboda murnar walimar bikin Hadiza da Abdul.
Da misalin ƙarfe biyu na rana iyalan Alhaji Baban Gida suka iso ƙauyen, Saddiqa na shiga gidan ta yi arba da ƙanwar Yadikon ta,a bakin ƙofar ta saki jakar ta ta isa gare ta da gudu ta rungume ta ta fashe da kukan farin ciki,sun jima a haka kafin su zauna ta fara gaishe da ɗangin mahaifiyar ta da suka cika gidan saboda kara da sukai wa Innoh. Sai da suka gama gaisawa sannan ta ɗauki jakar ta da Munir ya ajiye mata a gefen ta bayan ya gaishe da surukan nashi ya wuce zuwa ɗakin Baaba, direct ɗakin Innoh Saddiqa ta shiga suka gaisa ta yi mata Allah ya sanya alkhairi,da kallo Innoh ke bin jikin Saddiqa da ya gaji da haɗuwa ko ta ina,kama daga kan fatar ta har zuwa suturar dake jikin ta,jakar da take riƙe da ita ma abun kallo ce,nan take abubuwan da ta dinga yi mata na matsantawa da musgunawa suka dinga dawo mata a kan ta,ba tare da jin nauyi ko kunyar mutanen dake ciki ɗakin ba Innoh ta hau tsiyayar da hawaye ta riƙe hannun Saddiqa,kafin ta yi magana Saddiqa ta gane me zata ce,dan haka cikin sauri ta tari numfashin Innoh ta hanyar faɗin,
"Allah ya jiƙan Yadikon Sule,na san kewar ta kike yi,ni kaina ina kewar ta,mu ci gaba da haƙuri sannan mu bita da addu'a,bari naje mu gaisa da Baaba."
Kafin Innoh ta ce komai Saddiqa ta bar ɗakin,cikin zuciyar ta take jinjina karamci da mutunci irin na yarinyar,lallai yau ta tabbatar da ana gadon mugun hali ko kyakkyawan hali a wajen iyaye. Ta kuma tabbata Saddiqa ta yi gadon kyakkyawan hali a wajen mahaifiyar ta,fatan ta Allah ya yafe mata abubuwan da ta yi a baya,sannan ya ƙara haɗa kan iyalin su.
Amarya na can gidan Alhaji Baban Gida da su Aunty Naja Abbe da Shalele da yaran su suna girkin abincin walima,sun share ko ina sun gyara saboda sun san masu gidan na nan tafe dan halartar bikin. Suna tsaka da zuba abinci a take away mai yiwa Mommy kwalliya tazo daga kano,wadda Abdul ne ya ɗauki nauyin hakan,hatta da kayan da zata sanya duk saida ya aiko mata su,banda lefen da aka kawo akwatina biyar kamar ba auren bazawara ba.
Suna tsaka da kwalliya Saddiqa ta isa gidan,rungume juna suka yi da Mommy,ita da Ameerah kuwa sai suka yiwa juna murmushi kawai,tinda Ameerah take a duniya bata taɓa jin kunyar wani mahaluƙi ba sama da yanda take jin kunyar Munir,wannan dalilin ne ma yasa da taga ya shigo ɗakin tayi saurin kauda kai ta na yiwa yaron ta wasa,murmushi Munir ya yi bayan ya gaida Mommy ya cewa Ameerah,
"Damisar gidan Baba Ɗan Liti ba magana?"
Tura baki ta yi ta hau hararar shi tana ƙunshe dariyar ta,dariya kowa ya sanya musamman su Saddiqa da suka san asalin abinda ya sanya shi kiran ta da damisa. Bai wani jima ba ya yiwa Saddiqa alamar yana jin yuwa ta sama masa abinci,ɗakin su ya tafi ya rage kayan jikin shi ya kwanta. Babu jimawa Saddiqa ta shiga ɗakin ɗauke da babban faranti dake ɗauke da abinci da ruwa akai,ajiyewa tayi a saman table sannan ta ce masa,
"Bismillah taho ka ci abinci,kaga yaron ka tinda muka zo be kula ni ba, yana can yana tarawa Ummina gajiya ko tausayin ta baya ji."
Kallon ta Munir ya yi,yaga tana wani ƙyalli,cike da zolaya ya ce,
"Ke zo nan,wai wannan ƙyallin goshin da naga kina yi na meye? Ba makaranta kika ce zaki yi ba?"
"Uhumm makaranta nake yi mana me yasa ka faɗi haka?"
"Ohh baki gane ba ko? To shikenan matso nan na yi maki bayani da kyau."
Nan take ta gane me yake nufi,cikin sauri ta miƙe tsaye tana dariya ta ce,
"Ni bani da komai,ka rufa min asiri dan Allah na kammala karatu na lafiya."
Fita tayi ta barshi yana yi mata dariya,wanka ta shiga tayi a ɗakin baƙin da su Mommy ke zaune suna bidirin su,sai da ta fito sannan ta zauna aka tsara mata kwalliya itama,Ameerah kuwa duk yanda akai da ita ta bari a yi mata kwalliyar zamani ƙi tayi, tace hoda kawai ta ishe ta,bata son wanna kalolin da gashin idon da aka maƙalawa Mommy ta zama dodo,ana tsaka da yi mata kwalliya Billy ta kira wayar Mommy ta yi mata Allah ya sanya alkhairi,dan kuwa har yanzu tana jin nauyi da kunyar shiga cikin taron mutanen garin nasu saboda gudun surutun jama'a akan ta.
Gaba d'ayan su sun shirya cikin kyakkyawar shiga kafin su fara raguwa su tafi gidan Ɗan liti,Mommy kuwa na nan bata fita wajen taron walimar ba sai da Abdul da Bilal suka iso suka ɗauke ta a mota su da Suhailah.
Ba ƙaramin mamaki ne ya kama Mommy ba da ta ga Suhailah taje wajen bikin nata fuska a sake kamar dama can sun saba da juna (wayayyiyar mace kenan) itama sakin ranta tayi ta shiga motar Bilal ya ja yana ta janta da hira suka wuce ƙofar GIDAN ƊAN LITI..........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
*LAST PAGE ALHAMDULILLAH!*
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 110:
Wajen walima ya cika da mata a zazzaune a kujerun roba farare sai washe baki suke yi. Malam liman ne ya yi wa'azi mai ratsa zuciya akan zamantakewar aure,wanda ba iyakar ma'auratan ne suka bada hankalin su wajen sauraran wa'azin ba,hatta da dattijan mata da mazan da suka samu halartar wajen sun ɗauki manyan darussan da basu taɓa sanin akwai su ba a gidan aure. Sai da aka kusan tashi daga taron ne su Aunty Naja da Ameerah suka dinga bi layi-layi suna rabon abincin da suka zuba a take away har da lemon roba da ruwan leda. Ɓangaren maza kuma Sule da Sadeeq ne ke rabon abinci.
Bayan an rufe taron walimar da addu'a ne mutane suka dakawa sauran abincin da ya rage wawa,kowa na kwasar rabon shi,tun Ameerah na zagin su tana kai duka har ta gaji ta sakar masu buhun ta koma gefe tana maida numfashi,Naja ce ta dafa kafad'ar ta ta ce,
"Rabu da su su kwasa,ai hakan ma arziƙi ne,duk wanda ya ci ya saka albarka ai mun gode."
Cikin ɓacin rai Ameerah ta ce,
"Dube su kamar wasu ƴan yunwa,kowa fa an bashi amma dan zalama suke ƙwacen na hannun mutane."
Dariya kawai Naja ta yi ta kama hannun Ameerah suka shige gida,masu kwashe kujeru da rumfuna ne suka fara kwashe abun su suna lodawa a mota. Amarya kuwa na cikin motar Ango ta yi lunƙui a bayan mota suna shan hirar su,duk wanda ya wuce suna kallon shi,amma su ba a ganin su,mommy sai magiya take yiwa Abdul akan ya barta ta shiga gida,ta gaji tana buƙatar hutu,wani lagwaɓe kai Abdul ya yi tare da turo baki kamar yaron goye sannan ya ce,
"Haba baby yanzu kora ta kike yi?"
Murmushi Mommy ta yi mai