Showing 54001 words to 57000 words out of 276165 words
Chapter 19 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
tayi, Munir da 'Yan uwan Ɗan liti kaff sai da suka bata hakuri taqi, Yaran Baabaa su Abbe da Alhaji Baban gida da ya zo ta'aziyya duk sun sanya baki amma bafulatanar nan ta kafe tace tinda ba qaunar 'yar uwar ta ake yi ba dama dole zata tafi da yaran ta, su kaɗai suka rage mata yanzu sauran 'yan uwan su sun tafi kudu kiwo basu ma san da rasuwar ba,dan haka ba zata bar su a wulaqanta su ba.
Ganin yanda ta kafe ta nace ne ya sanya Ɗan liti zama a bakin qofar d'akin Yadiko ya dinga kuka kamar qaramin yaro, dan kuwa shi kan shi ba ya jin zai iya rabuwa da yaran shi,ganin yanda Ɗan liti ke kuka ne ya sa jikin ta yin sanyi, itama ta zauna a saman turmi cikin hausar ta gurɓatacciya tace,
"To shikenan na hakura su zauna a gaban ku, Yaya am ka dena kukan haka ya isa,gasu nan zan bar su amana a hannun ku, duk wanda ya shi amanar marayu amanar Allah hye ta ci shi aradun Allah, ni zan tafi rigar mu sai watarana, dan Allah yaran nan a dinga barin su suna kawo min ziyara ko zan ji daɗi a raina nima, kuma duk sanda na samu wayar kawunan ki zan sanar da su rasuwar 'yar uwata za su zo duba ku"
Cikin kuka Saddeqa tace,
"Inshaa Allahu Inna Jumare zamu dinga zuwa, zan so nima na biki can rugar taku, to amma Innah ina zuwa makaranta anan Sadeeq ma haka, burin Yadiko ne in zama cikakkiyar likita, dan haka zamu dinga kawo muku ziyara a duk sanda muka samu hutu,ki gaishe min da kawu da 'yan uwa na"
Ɗan liti ma godiya ya dinga yi mata, dik da ya san ko ana muzuru ana shawo ba zai bata yaran nan ba, dan kuwa ko shari'a ta bashi damar riqe su amma ba zai so ya rabu da 'yar uwar Yadiko cikin faɗa ba, har bakin tasha ya kai ta a machine ɗin shi da kan shi ya bata na mota ta qi Karb'a,duk yanda ya buga ta Karb'a qi tayi,se driver ya bawa da kan shi, sallama suka yi ya dawo gida ya shige d'akin Yadiko ya kwanta a saman gadon ta yana tsiyayar da hawayen kewar ta.
Innoh kuwa tinda aka yi kwana biyar maganar mutuwar ta sake ta ta koma sanya wa Ɗan liti ido akan ya dena zuwa d'akin ta balle ya kwana, abinci kuwa in dai ita ta dafa to fa ba zai ci ba,bayan ta ya yi sauqi sosai dan kuwa yanzu ita ke hidimar gidan da komai, 'yan gaisuwa na zuwa su yi gaisuwa su tafi.
Ganin yanda ya dawo fuska ba walwala ya shige d'akin Yadiko ne ya sanya Innoh yin k'wafa ta shige nata d'akin ta kirawo Ameerah, Ameerah na shiga tace,
"Maza ki je ki kirawo min Naja ki ce ta zo zan aike ta, dan kuwa ban ga ta zama ba miji ya juya min baya yana gaba da ni a cikin gida,ki yi sauri kar ki tsaya shiririta,"
(Naja qanwar Innoh ce uwa ɗaya uba ɗaya,ita Innoh 'yar asalin qauyen Ba mugu ce)
Cikin sauri Ameerah ta sanya hijabi ta bar gidan, tana fita Innoh tace,
"Haka kawai se ka zauna ka dinga ci min magani kamar ni na sa pillow ko wuqa na kashe maka mata? Wanda ya mutu ai ya riga ya mutu, lamarin duniya da mai rai ake yi, ba zan ɗauki iya shege ba ah toh, dole ne na yi maganin ka.................."
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA:HAERMEEBRAERH
*SANARWA MAI MAHIMMANCI*
*INDA ZA A SAMU GIDAN ƊAN LITI DA ZARAR AN ƊORA*
*WATTPAD HAERMEEBRAERH9900*
*FACEBOOK PAGE HAERMEEBRAEH'S NOVELS*
*WHATSAPP...GIDAN ƊAN LITI NOVEL GROUP...HANWA FANS GROUP*
*DANNA LINKS ƊIN DA ZAN YI SHARING KAWAI ZAKU YI KU SHIGA KO KU YI FOLLOWING, BA SIYA ZA A YI BA BALLE ACE TUNUBIYYA TA HANA.🤭*
PAGE 20:
Ameerah ba su shigo gidan Ɗan liti ba sai daf da magariba, sun dawo sun tarar da Munir da Saddeqa a tsakar gida zaune su na magana ga leda nan baqa a gaban Saddeqar sai share hawaye take yi shi kuma ya na bata hakuri, cikin sassanyar murya mai daddad'an sauti Munir yace,
"Ki yi hakuri na san ban kyauta ba da ban yi maki ta'aziyya ba, amma na yi wa Yadiko addu'a fiye da tunanin ki,na kasa fuskantar ki ne a tsawon wannan lokacin saboda tausayin ki dake narkar da zuciya ta,yanzu ki share hawayen naki ki ci gaba da yi mata addu'a dan ita take buqata daga wajen yara nagari kamar ku,duk lokacin da kika ji zaki iya komawa makaranta sai ki yi amfani da wannan sabon uniform ɗin anjima idan kin shirya sai mu je a sai takalmi, Allah ya jiqan Yadiko,"
"Ameeen Yah Munir na gode Allah ya saka da alkhairi, ba ina kuka bane saboda baka zo ka yi min ta'aziyya ba, ina kuka ne saboda kawai ganin ka ya sa na ji a jiki na zan iya yin kuka ka lallashe ni ka faɗa min kalaman da nake so naji daga bakin wani makusanci na dan zuciya ta tayi sanyi, kuma gashi alhamdulillahi ka faɗa min kalamai masu kwantar da hankali,na gode da kular min da Sadeeq da ka ke yi har ya rage damuwa,"
Suna nan zaune suna hira sama-sama su kuma su Ameerah na tsaye suna mamakin lamarin,Naja ce ta taɓa Ameerah murya qasa-qasa tace,
"Wannan ne yaron da kike faɗa min?"
"Eh Innah shine,ki duba ki ga tsabar karuwanci daga mutuwar uwar ta har ta manta ta fara hira da saurayi a qofar d'akin uwar tata,"
Ta qarasa maganar cikin d'aga murya yanda Saddeqa da Munir za su ji,Munir ne ya juya dan ya ci wa Ameerah mutunci Saddeqa ta yi saurin cewa,
"Yah Munir ka je ka kwanta ka huta dan na san baka saba da tuqi a irin hanyar garin nan namu ba akwai gajiya,"
Nan take ya ji haushin da yake ji ya kau, sai ya juya fuskar shi ɗauke da fara'a yace,
"Ahh dama kin taba barin qauyen nan ne?"
"Eh ina zuwa rugar su Yadiko wajen iyayen ta kafin su tashi, daga baya kuma na je gidan Innah Jumare sau ɗaya tun bayan da iyayen Yadiko suka bar rugar,"
"Lallai kin san hanyar taku, hanya se kace a daji? Ai bada ban su Daddy bane da ba zan sake fita daga garin nan ba har sai sanda zan tafi, da na kai su airport ɗin na so na kwana ko a hotel ne na huta kafin na dawo,sai kawai na tuna da ɗinkin ki shine na ce ya kamata na dawo na karb'o akan lokaci,kar naje tela be saɓa alqawari ba ni na saɓa,sannan ina na ga ta kwanciya ba a sai takalmin makaranta ba?"
Hira suka ci gaba da yi har basu san sanda su Ameerah suka shige d'akin Innoh ba, Ameerah na shiga ta fashe da kuka tace,
"Innoh kina ganin waccan yarinyar a tsakar gida suna soyayya da mijina baki hana ta ba?"
"Waye mijin naki kuma banda labarin d'aurin auren naku?"
Cikin tura qaton bakin ta gaba tace,
"Yaya Manniru mana, ni Allah hyi nake so kuma hyi zan aura, wai ke Innoh baki ga irin kayan da ke jikin uwar shi da uban bane? Ke da gani kin san kuɗi sun zauna a jikin su,kuma idan ban aure hyi ba wa kika ajiye min da zan aura me kuɗi irin haka? Ke bama kya fatan 'yarki ta auri me kuɗi ki huta da saida alale?"
"Ni ko nake so ku auri me kuɗi ke da Mommy, amma bazan taɓa haɗa zuri'a da Baabaa ba,"
"Ohh ke dai yaya ana gabar ki na yamma, yo se me dan kin haɗa jini da ita? Matar da gata nan tsabar tsufa ido ɗaya ya kanne duk ta yamushe daga qashi sai fata a Jikin ta? Ki amince kawai a yi wannan auren ki sha mamaki, dukiyar ahalin kafff hannun Ameerah zata dawo sai yanda tayi da su, dan haka tun wuri ma ki ajiye wannan aqidar da zata cutar da ke kiyi danasani anan gaba, idan aike na zaki yi wajen boka me shiqa to ki haɗa da wannan aure a buqatun ki, to kin ji na faɗa miki gaskiya bana qarya ke kin sani,"
Shiru Innoh tayi tana nazarin maganar tasu baki ɗaya kafin daga baya tace,
"Kuma fa maganar ku na kan hanya, yanzu yanda uwar ta ta mutu kowa zai ɗauki tausayin duniya ya ɗora akan su ita da ɗan uwan, a ɗauketa da qanin nata su koma Habuja se sun ci su jefo mana, idan ma sun tuna da mu kenan, to na amince a miqa buqatu na wajen Mai shiqa,wannan bawan Allah'n ma naga kan shi ya fara rawa a taro min shi a tsaida shi waje guda ba zan ɗauki lalata da iskanci da wulaqanci ba a wajen namiji, ah toh,"
"Kar ki ji komai, kedai bada sulalla ki ga aiki daga nan zuwa jibi na je na dawo,"
Tashi Innoh tayi ta deb'o kuɗi a cikin wanda take tarawa na ribar alale da sauran na zakkar da aka basu da ta adana ta qirga dubu talatin bata ci ba bata sha ba ta bayar a kaiwa boka.
Ameerah jikin ta har rawa yake yi dan su fito tare da Innoh ta zage mata Saddeqa, sai dai suna fitowa suka ga wayam,dafe qirji Ameerah tayi tace,
"Innoh na ga ba haske a d'akin Yadiko fa kar dai yarinyar nan ciki ta ja shi,"
A rikice kuwa Innoh ta shiga d'akin Yadiko ta d'age labule, duhu ne ya yi mata sallama,cikin duhun take magana ta na faɗin,
"Ke Saddeqa wato ciki kika ja shi ko? Kaiiii jama'a ni wannan yarinya na ga jarababbiya, ko dake ban ga laifin ki ba gado k...."
Kafin ta qarasa Maganar bakin ta taji wani siririn hannu mai kama da rodi d'auri guda ya sauke mata mari a kuncin ta, ji tayi wata wuta ta yi taratsatsi ta gilma a idanun ta, a gigice ta fito da kan ta daga cikin d'akin tana rarumar waje kamar makauniya, muryar ta gaba ɗaya ta kasa fitowa,sai da ta yi nasarar fita tsakar gidan ne da kyau ta kurma wani uban ihu tace,
"Wayooo Allah na hyiga uku na lalace na rasa idanu na, idona ya fita Naja'atu nemo min shi ki manna min abuna,"
Cikin hargowa Ameerah ta isa d'akin tana faɗin,
"Qarya aka yi miki ba gadon iskanci kika yi ba wajen uwar ki shine za....."
Da wani irin gigitaccen duka aka rufe ta a cikin duhun, nishin Ɗan liti ne ya ankarar da ita wanda ke yi musu wannan kisan mummuqen a cikin duhu, ihu take ta zundumawa tana faɗin,
" Wayyoo Allah na Innoh ki cece ni,"
Naja na ganin abinda ya faru sai ta damqe kud'in hannunta da kyau ta juya ta bar gidan a guje, dan kuwa ba karen hauka bane ya cije ta da zata shiga inda aka yanka wa yayar ta tafi, kuma tana ji tana gani Ameerah ke ihu ana dirmar ta a ciki,tinda ta sa kai arewa tana tiqar gudu bata tsaya ba se da ta isa gidan su.
Ɗan liti kuwa be kyale Ameerah ba sai da ya ji ta dena ihu dan kan ta, sannan ya bayyana a tsakar gidan, Baabaa na jin su ta qi zuwa ceto dan kuwa ita kan ta da tana da iko abinda zata yi musu kenan, dan ma Allah yasa Munir ya nemi izinin Ɗan liti da ya shiga gidan ba jimawa sun tafi zaɓen takalmin makaranta da duk wannan rashin mutuncin a kunnen yarinyar da qanin ta za a yi shi.
Cikin haki ya kalli Innoh yana nuna ta da yatsa yace,
"Daga yau se yau, idan na sake jin sunan Yadikon Sule a bakin ki se na zubar miki da haure,ke ko alheri ban yarda ki ambace ta da shi ba ki faɗa a ran ki in yazama dole se kin faɗa ɗin,idan kuma kika qi ji ba kin qi gani ba alqur'an, wawuya kawai wadda bata san waye Allah ba"
Cike da tsoro da rashin kunya Innoh ta ja baya zata gudu ta na tafe tana faɗin,
"Alqur'an baka daki banza ba, se ka yi daka sanin wannan dukan da ka yi min ni da 'ya ta,se ka shiga tashin hankalin da ba zaka iya fitar da kan ka ba balle wannan tsinanniyar yarinyar taka,"
Zabura Ɗan Liti ya yi zai bita d'akin ya jibge ta da kyau, ta zabura itama ta zuba da gudu ta shige d'akinta ta rufe ta saka sakata ta ci gaba da zagin shi shima yana zagin ta, ganin abinda suke yi babu mutunci kar su Saddeqa su dawo su tarar da abinda ke faruwa ne ya sanya Baabaa fita ta yafici Ɗan liti zuwa d'akin ta, yana shiga ya zauna ya dafe kan shi se hawaye suka hau zuba a idanun shi.
"Haƙuri za ka yi, wannan halin nata na rashin kan gado na daga cikin babban dalilin da ya sa ka qara aure tun farkon rayuwar ku, to yanzu gashi matar da ke faranta maka ta zam babu, dan haka hakuri zaka yi har Allah ya baka ikon cinye wannan jarabawar, karb'i wannan ci ka sha ruwa, dankali ne na soyawa wancan yaron da k'wai na ɗebar maka da su Saddeqa kuma ku taɓa,Allah ya jiqan Yadikon Sule, Allah ya bamu haƙurin rasa ta da muka yi,"
"Ameeen Baabaa, anya ni zan iya sa wani abu a cikin nan nawa,zuciya ta zafi take yi Baabaa, ashe haka kika ji sanda Yaya ya rasu? Tabbas na ji mutuwar yaya, amma zafin da nake ji a yanzu babu haɗi,dama ni ban san iyaye na ba ku na sani a matsayin iyaye, duk yanda Yaya yake tunamin su kafin ya rasu sam na kasa tuna komai game da su,"
"Wayyoo Ɗanli ai mutuwar miji ko mata zafin su daban ne ba zaka haɗa su da ta yayan ka ba,duk da dai na sani kowanne rai muka rasa abin kokawa ne, amma mutuwar miji ko mata daban ne a wajen me rai, Allah dai ya jiqan magabatan mu, maza dauki ka cusa ba dan daɗi ba sai dan gujewa wahala,"
Haka kuwa Ɗan liti ya dage ya tura dankalin nan ba dan yana jin dad'in sa ba har ya gama ci, suna zaune suna jajanta rayuwa sai ga su Saddeqa sun dawo, bayan takalmin makaranta harda jaka da sababbin littattafai ya siya musu, da abun shan ruwa da food flask, sai biscuits da alawa yace su b'oye sun dinga ɗauka a boye suna ci dan haka tun suna shiga gidan Saddeqa ta kai d'akin Yadiko ta boye, sannan suka nufi d'akin Baabaa inda suka jiyo hirar Baban nasu da Baabaa.
Godiya sosai Ɗan liti ya yi wa Munir sannan yace,
"Ai hidimar ta yi yawa kai kuwa Manniru, to Allah ya yi maka albarka ya sa kafi haka,"
"Ameeen Baba babu abinda ya yi yawa anan, mu a ta can idan yara zasu koma makaranta ai sai ka kashe maqudan kuɗi kafin ka gama sai masu komai da suke da buqata,"
"Nima dai Baba sai da na ce masa sun yi yawa amma yaqi ya dena kashe kud'in, ni da ma na kusan gama makarantar SS3 zan shiga fa,"
"Duk da haka da sauran ki, Allah dai ya bada ilman nafi'an," munir ya faɗa yana wani kashe mata idanu, a kunyace tace,
"Ameen ya Allah,"
"Amma nace Baba idan ta gama secondary ɗin ya za a yi da maganar ci gaba da karatun nata?"
Shiru Ɗan liti yayi kafin ya nisa yace,
"A gaskiyar magana saboda yanayin rayuwa zan so na aurar da ita,idan mijin ta ya amince suje can ta ci gaba, idan be amince ba shikenan ta yi bautar ubangiji,to sai dai matsalar ma Saddeqa bata da saurayi, duk masu nuna suna qaunar ta ban yarda da su ba,yara ne da basu isa aure ba, wanda suka isa auren masu mata ne da kuma marasa sana'a,ni kuma ba zan so Saddeqa ta qare da auren shashashu ba, aure be jima ba a sako min ita ta dawo zawarci wannan gidan,"
Cikin kuka Saddeqa tace,
"Dan Allah Baba ka barni na yi karatu,burin Yadikona kenan na zama likita, nima kuma burina kenan, dan Allah Baba yanda ka bar Yah Mommy ta tafi aikatau birni nima ka amince min idan na gama secondary na tafi kano na yi Jamb in lokaci yayi idan na samu jami'a sai na koma hostel da zama na yi karatun,"
"Ni zan ɗauki nauyin karatun ki na yi alqawari Saddeqa"
Munir ya faɗa a lokacin daya kafe Saddeqa da kallo,ita kuwa kuka kawai take yi ko zata samu Ɗan liti ya tausaya mata ya amince, Baabaa ce ta share hawayen ta tace,
"Manniru kai da baka da aiki? Ka bari ni zan biya mata kud'in komai na makarantar, yo me zan yi da kud'in da uban ka ke bani in ba yaran nan da ke auren faqiran maza suke cin kud'in? Dan haka ni zan ɗauki nauyin komai har ta gama,"
Dariya Munir yayi sosai, dan kuwa da alama basu san ya karatun likita yake bane, babbar consultant tace masa tana so ta zama,dan haka zai gaggauta komawa gida ya kama aiki dan ya taimaka wa Saddeqa, duk da ya sani ko baya aiki mahaifin shi zai taimaka mata ta cika burin ta, amma zai so shi ya taimaka mata da kan shi, cikin dariyar da yake yi yace,
"Baabaa kar ki damu kin manta aiki na na can na jira na? Da izinin Allah zan biya mata har ta kammala,"
"To Allah ya kaimu da rai da lafiya,"
Nan da nan Saddeqa ta hau washe baki,ta rungume Sadeeq dake gefen ta tana faɗin,
"Na gode Allah ya qara arziqi,Allah ya biya da babban rabo,"
Haka suka zauna suna ta hira kafin daga baya Munir yayi musu sallama shi da Sadeeq su wuce gidan su su kwana.
Saddeqa kuwa a d'akin Yadiko ta kwana shi yasa bata haɗu da Ameerah da Ɗan liti ya yi wa walmukalifatu ba,rufe qofar tayi bayan ta yi alwala ta yi sallah ta samu waje ta kwanta,dan kuwa a d'akin Baabaa ta ci nata dankalin ita da Sadeeq, da kyar bacci ya ɗauke ta kamar kullum saboda yawan tunani, na farko dai tunanin Yadiko ya addabi zuciyar ta, sannan na biyu tunanin irin kallon da Munir ke yawan yi mata da jirwaye me kamar wankan da yake mata na sanya