Showing 246001 words to 249000 words out of 276165 words

Chapter 83 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

wuce hisbah, acan aka kira su dika aka dinga yi musu nasiha da nuna masu illar guje maki da za su yi,sannan nima na zauna na tonawa kaina asiri a gaban su,Aunty na ta Abuja har suma tayi da ta ji abubuwan da nake aikatawa a baya, saboda su a cewar su kullum a mutumin kirki suke ɗauka ta,anan ne ake nuna masu da mace da namiji idan suka aikata zunubi iri ɗaya,matsawar sun balaga,hukuncin su ɗaya,mu mutane ne ke ware laifin namiji a koda yaushe,a ce dik abinda ya yi ado ne,ita kuma mace ita ce mai laifi koda kuwa sau ɗaya ta aikata zunubin,bayan doguwar nasiha suka yanke jibi za su je ƙauyen ku a nema min auren ki wataƙila ma idan muka samu yanda muke so a ranar za a ɗaura mana aure."

Tsallen murna Any da Billy suka saka,daga baya kuma Billy sai ta fashe da kukan farin ciki,Any lallashin ta ta hau yi tana yi mata video tana faɗin,

"Yau ranar farin ciki ce dole na ajiye video nan dan tarihi,Allah ya sanya alkhairi ya sa albarka,Allah ya nuna mana ranar auren ku da rai da lafiya."

"Amin Anam,Allah kema ya dube ki da idanun rahamar shi ya kawo maki miji na gari."

"Amin ya Allah.

Da haka suka zauna suka dinga hira,ƙarfe goma na yi Man ya yi musu sallama suka rufe shago suka tafi gida cike da farin ciki.

Bayan kwana biyu iyayen Man suka shirya cikin shiga ta alfarma kasancewar shi cikin zuri'ar manya masu hannu da shuni,motoci biyar ne masu tsada suka tafi nemawa Man auren Billy,motar Man ce ke gaba kasancewar shi yasan waje,dan haka sai suka sanya shi ya zamo musu ɗan jagora.

Tin kafin su isa Billy ta sanar da iyayen ta,har ta ce zata tura kud'in da za a tarbe su da kyau, faɗa sosai Ta Annabi ta yi mata akan hakan, sannan ta ce a baya ma son zuciya ne da mutuwar zuciya ya sanya su karɓa abun hannun ta,dan haka kar ta sake yi musu irin haka. Haƙuri Billy ta bata ta kashe waya jikin ta na ta mazari tsabar murna,sai kaiwa da komowa take yi tana tinanin ya abubuwa ke wakana a can,Any kuwa sai dariya take yi mata kafin daga ƙarshe Man ya kira Billy yana murna ya sanar da ita iyayen ta sun bashi ita, su kuwa sun bayar da kuɗin sadaki Mahaifin Billy ya kirawo ƙannen shi da yayun shi biyu aka daura auren. Sakin wayar Billy tayi a gado ta yi sujjada tana yi wa Allah godiya, ko da ta ɗago ma bata bi ta kan wayar ba,hannayen ta kawai ta daka tana ta zabgawa Allah kirari da godiya,bata sauke hannayen ta ba har sai da ta ji babu wasu kalamai da suka rage a bakin ta sannan ta zauna jiki a sanyaye,Any kuwa dik abinnan da Billy ke yi ashe tana tsaye tana yi mata video,sai da ta gama ɗaukan ta sannan ta ajiye wayar ta tafi da gudu suka rungume juna suna murna,hamdala suka dinga yi tare da fatan samun zaman lafiya.

*****************************


Kwanan mommy goma sha ɗaya a gidan Malam gaba ɗaya ta sauya,ta rame ta yi duhu sosai saboda wahala,idanun ta sun yi ciki sosai haƙoran ta sun bayyana a waje fiye da da,nan da nan Sweet H ta koma Hadizan Ɗan Liti ta ƙauyen Ba Mugu,banda hips ɗin ta na da cika sosai tabbas da babu abinda zai hana su zubewa.

Tsugunne take gaban Malam tana hawaye,cikin dakewa ya ce,

"Ki fa daina roƙo na dan ba amince maki zan yi ki je gidan tsofaffin surukan ki ki ga ɗan ki ba,idan su suna da hankali ai sun san inda uwar ɗan take ko? Me zai hana su kawo maki shi? Sai ke ce zaki ce zaki wani je gidan su? Hadiza kina neman ki dinga karya min dokokin da na gindaya a gida na,bana so,ina faɗa maki bana so."

"Dan Allah Baban Bukari ka bari na je,na yi maka alƙawarin ko awa ɗaya ba zan cika ba zan dawo,kewar ɗana zata yi ajali na,ka tausaya min ka duba ka ga yanda na koma a gidan ka,na yi zaton tausayi na ne ya sa ka kawo shawarar nan ashe kai muradin ka akai na daban?"

"Ke dallah rufe min baki ya ishe ki haka ! Kin san asarar da na tafka kuwa tinda na aure ki? Idan ba ma tsananin tausaya makin da na yi ba ai da ba zan aure ki ba ina ji ina gani babu tauraron arziƙi ko ɗaya a tsakanin mu,ke ba haihuwa zan dake ba,ke ba kuɗi zan samu ta dalilin aure na da ke ba, gaba ɗaya babu wani haske sai duhu da asara shine zaki zo kina faɗa min maganar banza anan,tashi ki ɓace min da gani kafin na wulaƙanta ki."

Cikin kuka Mommy ta mike zata fita, da kallo ya bita yana jan tsaki,dole ma ya gaggauta rabuwa da ita dan kuwa babu wani arziƙi a cikin auren su da zai sa ya ci gaba da riƙon ta,jikin nata da yake kwad'ayi ya duba ƙasa ya gano idan ya ci gaba da mu'amala da ita zai ci gaba da tabka asara kala-kala a dukiyar shi,dan haka tinda ya kusance ta sau ɗaya yana ji yana gani tana gilmawa ta gaban shi bashi da halin bin ta.

Ko da ta koma ɗakin ta gado ta faɗa ta hau rusa kuka iya ƙarfin ta,nadama da data sani babu wanda bata yi shi ba a wannan lokacin,ji take yi kamar ta fito da zuciyar ta ta manna mata ƙanƙara ko zata dena zafin da take yi mata,rashin hankali da rashin sanin ciwon kai ya ja ta yakice yaro ta yaye shi a lokacin da yake da buƙatar ta,gashi yanzu soyayyar shi da tausayin shi na neman illata ta,tinda ta ji Innah Laminde ta karɓe shi kuwa nutsuwa ta ƙaura daga gare ta,tabbas idan har suka ƙarbe shi ta san ba za a sake bata riƙon shi ba,dan kuwa ta san a yanda Innah Laminde ta tsane ta ba zata so jikan ta ya zauna a hannun ta ba balle ya yi agolanci a wani gidan.

Tana tsaka da kukan ta Mero ta shiga da garin masara a wata shirgegiyar ƙwarya tana wani taunar chewing gum kamar irin karuwan lagos ɗin nan,dire ƙwaryar ta yi a tsakar ɗakin Mommy ta na yatsina ta ce,

"To akoke sai a fito a ɗora sanwa tinda ba a kan ki aka fara haihuwa ba,yo ɗa ɗaya ma wata tsiyar ce har da zaki cika mana gida da ihu se kace kin haifi taron idi?"

Kafin ta juya ta bar ɗakin Mommy ta yi sufa ta dira akan ƙwaryar garin ta hau tsalle,gari na ta tashi sama yana zubewa a ƙasa,daga ƙarshe ta duƙa ta ɗauki ƙwaryar ta yi wurgi da ita a tsakar gidan ta rarumi Mero ta damfara ta da kasa ta haye ruwan cikin ta,Malam na sanya takalmin shi daga ƙofar ɗakin Meron ya ga an wurgo ƙwaryar gari waje ta zube,ihun Mommy kuwa shi ne ya sanya shi fitowa daga ɗakin tin farko,dan haka bai tsaya ƙarasa sanya takalmin ba ya bazamo d'akin Mommy dake ta dukan Mero har da cire mata kitson ta guda ɗaya da ya tsufa ya ci duniya,kuka Mero take yi tana kiran Allah ya isar mata a je a taimake ta,amma babu mai karfin guiwar isa ɗakin mommy,Tsahare ce ta riga Malam isa ɗakin ta yi kan Mommy ta na faɗin,

"Subhanallahi Amarya me yake faruwa haka? Yi hakuri ba halin ki bane wannan,idan kika daka ta rashin kunyar Mero kullum sai kun yi hayaniya a gidan nan,shi yasa basu ga maciji da Asabe."

Cikin haki Mommy ta ce,

"Ni illata ta zan yi idan tace zata shiga gona ta,yanzu ma ba zan barta ba sai na shata mata billen da Malam be taɓa yi mata ba dik dake-daken shi."

Juyi Mommy ta yi ta warto wuƙar dake hannun Tsahare,dik warin albasa ke tashi a jikin wuƙar,albasa take yankawa za ta yi wa Malam farfesu ta ji ana rikitiɓar faɗan ta shiga,a guje Malam ya karasa ya amshe wuƙar ya wurgar a waje sannan ya fizge Mero da ta sha shaƙa a hannun Mommy,banda tari da numfashi babu abinda Mero ke yi,Mommy kuwa sake kai mata duka take yi amma Malam na tarewa,ganin faɗan ya ƙi rabuwa ne ya sanya shi hantsila Mero waje ya riƙe Mommy ya wurga ta saman gadon ta,kuka ta fashe da shi tana so ta yi masa bayanin abinda ya faru,cikin fushi da ɓacin rai ya ce,

"Bana son na ji komai,haka kawai ina tare da Mero taurarin mu sun haɗu ina samun arziƙi ta dalilin ta kizo ki nakasa min ita, bayan ke ba tauraruwar arziƙi na bace,Hadiza ki tattara naki ya naki na sake ki saki biyu,ba zan iya ci gaba da zama da ƴar ta'adda me faɗa da wuƙa ba,dama haka kike? Haka kike haukacewa idan ana faɗa dake? Haka kawai ina zaune watarana na ɓata maki rai nima ki hallaka ni irin yanda kika yi wa tsohon mijin ki? To ba zai yiwu ba,maza ki tattara ki bar min gida kin yi iddar a ɗakin tsohuwar ki."

Mommy rasa me zata yi ta yi,shin murna zata yi an sake ta ko baƙin ciki zata yi,tinda ta riga da ta sanyawa ranta zata yi haƙuri ta zauna tayi zaman aure a gidan Malam tsakanin ta da Allah,yanzu ina ta nufa da ya sake ta?........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI











RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨








PAGE 100:






Kwashe kayan ta take yi cike da sanyin jiki,Tsahare na tsaye tana salati dan kuwa ba ƙaramin mamaki sakin da aka yi wa Mommy ya bata ba. Nan take ta hau tina yanda ya dinga yanka masu gargaɗi akan auren Mommy har hakan ya sa Mero yin yaji ta bar gidan,da ƙyar ya je ya yi bikon ta ta dawo,lallai lamarin soyayyar Malam da Mero sai a bar ta kawai,jinjina kai ta yi sannan ta ƙarasa gaban Mommy ta ce,

"Ki yi haƙuri Hadiza,haka rayuwar aure ta gada dama,dik daren daɗewa in dai an ɗaura shi to za a wayi gari ya mutu,ko saki ya shiga tsakanin ka da miji,ko miji ya mutu,ko matar ta mutu,ko miji ya ɓace a neme shi a rasa ko kuma mace ta ɓace a neme ta a rasa,dan haka ki godewa Allah a dik halin da kika tsinci kanki,Allah ya baki wanda ya fi malam alkhairi."

A dai-dai wannan gaɓar ne kuka ya ƙwacewa Mommy,cikin kuka ta ƙarasa zuba kayan ta a akwati ta kulle,sannan ta ja mayafin ta dake saman kujera ta yafa,kallon Tsahare dake matsar ƙwalla ta yi ta ce,

"Na gode da soyayyar da kika nuna min Iya,Allah ya raba su Binta da auren mai mata,idan yana cikin ƙaddarar su Allah ya sa su fiki nuna halin dattako,Allah ya sake sada mu da alkhairi."

Kuka sosai Tsahare ta fashe dashi,Hadiza ma kukan take yi har suka fita bakin ƙofar ɗakin Hadiza ta sa makulli ta kulle ɗakin ta kafin azo kwashe mata kaya,Asabe ce ta shiga gidan afujajan ƙafafun ta duk sun yi ƙura kamar wadda ta yi gudu cikin tulin ƙasa,zufa kawai take yankawa fuska ta yi mata maiƙo kamar ta shafa man gyad'a,gishirin hancin dake saman hancin ta da zufar duk sun haɗe waje ɗaya,cikin maida numfashi da fitar dashi ta ce,

"Wanne irin mummunan labari nake ji haka Hadiza? Ina can gidan Ƴarraƙai Hanza ya je ya ce min Baba ya saki amarya,dan Allah ku ce min ba gaskiya bane."

Ganin Mommy na tsaye tana kuka Tsahare na yi,ga kuma garnaƙeƙen akwati cike da kaya a gaban Mommy sai zargin ta ya tabbata,zaman ƴan bori ta yi a wajen ta ɗora hannu a ka ta kurma ihu,nan take aljanun ta suka tashi ta hau fizge-fizge tana sambatu,ganin haka ne ya sanya Mero buga shewa ta daki cinya ta ce,

"Lallai ma matan gidan nan an yi munafukai,nan nan nake tare da ku shekara da shekaru baku taɓa nuna damuwar ku ba akan sakin da Malam ya taɓa yi min saboda na karya dokar shi cikin laluri,sai dan an saki wannan yarinyar da ko wata ɗaya bata cikashe ba a gidan shine kuke wannan haukan,to dan Allah ku ɗau aniya ku ma ku bar gidan mana shine ƙarshen kauna."

A fusace Asabe ta yi kan Mero tana ci gaba da ihu da fizge-fizge,Tsahare ce ta cewa Mommy,

"Yi sauri ki bar gidan nan,dan kuwa wannan aljanun ba yanzu za su kwanta ba se malam ya zo an musu yankan jan zakara,in kuma be ga dama ba ba zai yanka mata ba haka zata kwana tana abu ɗaya."

Cike da tausayawa Mommy ta kalli Asabe da ke jijjiga ƙofar Mero da ta arce zuwa ɗakin ta,haka ta ja akwatin ta tana jinjina yanda matan suke ƙaunar ta,ashe Asabe dake yawan harar ta ko ta dinga gyara mata abu idan tayi ba dai-dai ba cikin faɗa duk so ne hakan,ashe da ta ci gaba da zaman aure a gidan ba zata wahala ba yanda ta yi zato. Da wannan tunanin mommy ta samu ɗan acaɓa ya kai ta gida. Innoh na zaune ta na lissafa cinikin alale da almajirin ta ya yo mata ta ga Mommy da akwati ta shiga gidan,a gigice ta miƙe tsaye tana nuna Mommy baki na rawa ta ce,

"Mommy me me...me kika dawo yi a...a..a gidan nan kuma? Dan Allah ki ce min ba sakin ki ya yi ba ! "

Cikin share hawaye Mommy ta samu bakin rijiya ta zauna ta jingine akwatin ta jikin turmi ta sanya hannu tana yaye mayafin ta ta ce,

"Saki na ya yi Innoh har saki biyu."

Baaba dake zaune a tabarmar ta tana kankare goro ta buga salati ta ce,

"Ke kuwa ƴannan me kika yi masa haka da zai sake ki har saki biyu?"

Sallamar Naja da Ameerah ce ta katse musu jajen da suke yi,Mommy na ganin Naja ta ce,

"Aunty Naja ta tabbata dai yau Malam ya sake ni har saki biyu,ba dan kewar su Tsahare ba da sai in ce a yanzu kam na samu natsuwa burin mu ya cika."

Ƙyaftawa Mommy ido Naja ta dinga yi amma bata yi shiru ba,kasa gane inda maganar su ta dosa Innoh ta yi,cike da ruɗani ta ce,

"Me kike nufi da cikar burin ku a saki Hadiza? Da alama baki koyi darasi a zaman zawarcin da kika yi a baya ba ko?"

Ameerah ce ta kwantar da yaron ta a tabarmar da Baaba ke zaune sannan ta juya ta kalli Innoh ta ce,

"Kar dai ki ce min baki san auren kisan wuta Mommy ta yi da Malam ba Innoh?"

Butar dake hannun Ɗan Liti ce ta faɗi a dai-dai lokacin da ya fito daga band'aki, Innoh kuwa kafin su isa gare ta ta yanke jiki ta faɗi saboda shiga tashin hankalin da ta yi,ihu Ameerah ta sanya ta yi kanta tana kiran sunan ta,cikin sauri Ɗan Liti ya tsugunna ya ɗauki butar da ya yar ya nufi wajen Innoh. Tafe yake ƴar sharar rigar shi na kad'awa a iska kamar wanda zai tashi sama,ruwa ya yayyafa mata sannan ya tsugunna yana gwale idanun ta tare da kiran sunan ta,a cikin wani mawuyacin hali Innoh ta farfaɗo tana bin kowa da idanu,magana ta buɗe baki zata yi amma ta kasa,hawaye ne kawai ke zuba a kuncin ta tana kallon Naja sannan ta koma ta kalli Mommy.

Cike da masifa Ameerah ta ce,

"Wai dama kuna nufin baku sanar da Innoh da Baba auren kisan wuta kika je yi a gidan Malam ba? Sannan mommy ina shawarar da na baki? Ashe ba za ki iya fawwalawa Allah lamarin ki ba ki haƙura ki zauna a ɗakin ki tinda dai-dai misali gidan Malam kowa ya shaida babu yunwa babu takura."

"In ji uban waye ya ce babu takura? Ke kin san yanda yake jibgar matan shi kuwa? Ni kaina Allah ne ya tseratar dani wataƙila da idan ya yi min wani duka ba za ku gane ni ba,sannan a zaton ki idan na sanar da Innoh auren kisan wuta zan je nayi zata bari ne? A kullum ita bata da burin da ya wuce na mu matsa a gaban ta ta samu sarari ta yi yanda take so,dan haka kar ki ƙara yi min tsawa aka idan ba haka ba..."

"Me zaki yi idan na ƙara yi miki tsawar? Ke fa bari ki ji ni bana tsoron ki."

Ɗan Liti ne ya miƙe a gaban Innoh yana sharar ƙwalla ya ce

"Tabbas biri ya yi kama da mutum,ni dai na jima ina mamakin dalilin da zai sa Uwata auren boka,ashe-ashe wata ƙulalliyar kuka ƙulla,Naja kin ci amanar zumunci,kin cuce ni kin cuci ƴar'uwar ki da ta baki amana da yarda."

Cikin kuka Naja ta ce,

"Tabbas na yi kuskure ba ƙadan ba,ina jin kunyar ɗaga kai na kalle ku dika,a zato na da kuma guntun tinani na na zaci haka shine gatan da zan yi wa Hadiza,bani da burin da ya wuce naga na yi mata abinda zai faranta mata rai,sai dai kashh ga abinda na jawo mata nan."

Kuka Naja ta fashe da shi,Mommy kuwa ita bata ga abin tashin hankali a nan ba har Innoh ke wani suma,Baaba kuwa tsananin mamakin halin yaran zamani ne ya hana ta cewa komai. Shigar Sule da Saddiq gidan ne ya dawo da ita hayyacin ta ta ce,

"Sule da Saddiqu ku kama Innoh ku kai ta ɗaki maza."

Sai a lokacin Sule ya kula da Innoh dake yashe a ƙasa tana hawaye,cikin sauri ya wurgar da jakar shi dake rataye a kafaɗar shi ya nufi Innoh,Sadeeq ma a gaban ta ya tsugunna yana faɗin,

"Me ya same ki Innoh? Me ya sa ta kuka?"

"Ku taimaka min mu kai ta ɗaki ta kasa tashi da kanta." In ji Ɗan liti da ya duƙa zak ɗaga ta.

Da ƙyar su Sule da Sadeeq da Ɗan Liti suka yi tara-tara suka kai Innoh ɗakin ta suka ajiye ta a ƙasan ɗakin,Sule ne ya miƙe tsaye ƙofofin hancin shi na buɗewa da rufewa ya ce,

"Wai meke faruwa ne a gidan yau? Ke Mommy me kike yi a gida da akwati haka?"

Kamar Ameerah aka tambaya,cikin sauri ta ce,

"Yo auren kisan wuta ya ƙare ina kake tsammanin ganin ta idan ba gidan ubale ba?"

Rintse ido Innoh ta yi tana hawaye,kalmar auren kisan wutar nan na rura mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login