Showing 132001 words to 135000 words out of 276165 words

Chapter 45 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

inda take zaune, cikin murmushi ta kalle shi saboda ƙamshin da yake zubawa kaɗai ya isa ya isar mata da saƙon wankan da yayi, kallon shi ta tsaya tana yi daga sama har ƙasa cikin lumshe idanu da cije leb'en ƙasa tana wani abu kamar mai son wani abu daga gare shi,shigar farar shaddar da yayi da hula ash colour ba qaramin kyau tayi masa ba, tana son taga namiji ya saka manyan kaya ya ɗaura agogo da zoben azurfa,kallo shi take cike da alfahari da tsantsar so da ƙauna..
Ta ɓangaren Abdul kuwa kallon da take yi masa ba ƙaramin tasiri yayi a jikin shi ba, domin kuwa sai yaji shi kamar wani had'ad'd'en saurayin da babu kamar shi a birni da ƙauye,kallon nata yasa yaji cewar shima wani namiji ne mai mahimmancin da mace zata yi alfaharin samun shi har ta dinga yi masa irin kallon so da ƙauna da bukatuwar kasancewa da shi, yana nan yana murmushi yaji ta ɗora hannun ta saman gemun shi da sajen shi tana shafawa a hankali, lumshe idanu yayi sannan ya sauke su akan fuskarta,cikin wata iriyar murya mai ɗauke hankalin mai sauraro Mommy tace wa Abdul,

"Baby ka ga yanda kayi kyau kuwa? An taɓa sanar dakai idan ka sanya manyan kaya ko ƙananan kaya kana yin kyau? Ko dake dama kai mai kyau ne,kaya su suke yi wa jikin ka biyayya ba kai ke yi musu ba,Baby Allah ya tsara halittakar ka da kyau da kamala, dan kuwa a duk samarin duniyar nan ban taɓa ganin namiji kyakkyawa sama da kai ba,ina son ka miji na, Allah ya bar mu tare har abada,"

Wani irin farin ciki ne ya lullub'e Abdul har bai san sanda ya ɗauki Mommy daga kan kujerar da take zaune ba ya ɗora ta a saman cinyar shi ya rungume ta kamar zai mayar da ita cikin shi.

Ba namiji bane kawai zai zauna yayi ta yaba ki kina jin daɗi da alfaharin kin cika mace, shima yana son a yabe shi a yabi jarumtar shi sai hakan ya ƙara masa son ki da ƙaunar ki da kuma jin cewa shi wani ne a cikin taron maza tinda ya na da babban matsayi a zuciyar matar shi, mommy kuwa tayi bariki ta san kan yanda zata sace zuciyar namiji shi yasa take gigita Abdul da kalaman ta a koda yaushe,idan akwai asiri a jikin shi to tabbas ayyukan ta na ƙara masa ƙaunar ta.

Wasanni suka fara yi a tsakanin su daga ƙarshe Mommy ta sauka daga jikin Abdul ta turo baki irin na shagwab'ar nan tace,

"Baby yunwa nake ji, dan Allah ka sama min abinda zan ci ko ta can gida ne idan ka je,"

Murmushi yayi mata yace,

"An gama gimbiyar garin ba mugu,bari naje kar Sarki ya fita fada ban gaishe shi ba, yanzu ki fara haɗa tea ki sha da bread ɗin da na kawo jiya kafin na dawo,ki kular min da kan ki, sai na dawo, ina son ki,"

"Ina son ka gwarzo a cikin mazaje,namijin dake mantar dani suna na da kai na baki ɗaya ,namijin da yafi kowanne namiji iya tattali da kulawa da matar shi,ka dawo lafiya Allah ya tsare min kai,"

"Anya zaki barni na fita kuwa Hadizatou na? A duk sanda kika yi min irin kirarin nan ina ji na a cikin mazaje masu sa'a a duniya,"

"Ai kai sa'ar ka har lahira zata bika domin kuwa yanda kake kyautata min kawai zai iya sanya Allah ya tsindima min kai a aljannar data fi kowacce aljannah daɗi,"

Abdul kan shi ya kama yana wani irin farin ciki da juyi, a haka ya fita ya bar gidan yana zabga murmushi, dik wanda ya kalle shi tabbas zai tabbatar da cewa yana cikin yanayi na nishad'i da farin ciki tare da annashuwa.

A haka ya isa gidan su ya parker motar shi a gefen fadar mahaifin shi, gani yayi Mahaifin shi bai fito daga gida ba, dan haka cikin sauri ya isa ciki ya wuce turakar shi ya miƙa gaisuwar shi sannan ya fita d'akin abokan zaman Innar shi ya gaishe su, kafin ya wuce d'akin Innah Laminde,gaba ɗaya matan baban shi saida suka tsokane shi akan yanda suka ga ya sauya a cikin kwana uku da auren su.

Koda ya shiga d'akin Innah ya same ta zaune a saman abun sallah tana jan carbi, dan kuwa ba jimawa ta idar da sallar dhuha/walaha, Abdul na zaune yana ta doka murmushi tare da kallon hotunan Mommy da ya ɗauke ta da kan shi, babu abinda yafi tafiya dashi sama da faɗin qugun ta da cikar ƙirjin ta, Mommy mace ce da ta kai mace,ko ina na jikin ta a cike yake ta bangarorin da ya kamata, idan ta hannu da ƙafarta zaka gane tana da shape to fa sai dai ka sanya ta a layin siraran mata, gashin kanta dake samun kulawa a yanzu yayi tsawo sosai gashi da yauqi, labb'an ta da ake tsonana a da yanzu da ta iya sarrafa su da gyara su sai suka zamo abun so kuma ado a wajen ta da idanun masu kallon ta,shi dai Mommy tayi masa Bilal ma dake zagin bakin ta dan bai san darajar shi bane, murmushi ya sake saki da ya tina dramar da suka kwasa shi da Mommy a daren da zai koma Kano,Innah ce tace,

"Ah ah Babana wannan murmushin fa? Ko dai an samu wani ƙarin girman ne a wajen aiki?"

Cikin murmushi da farin ciki yace,

"Alhamdulillah Innah ai dole nayi murmushi da farin ciki na ajiye 'yar aljannah a gida,"

Gyad'a kai kawai Innah Laminde tayi fuskar ta babu yabo babu fallasa, dan kuwa yanda take matsanancin jin haushin Mommy sai taji ya ragu,tinda ko babu komai a duniya farin cikin Abdussabour na ɗaya daga cikin burikan ta.

"To da kyau Allah ya dawwamar da ku a cikin farin ciki,"

"Ameeen Innah,bari naje na sama mata abinda zata ci na baro ta tana jin yunwa,"

Ɗan haɗe gira Innah Laminde tayi kafin tace,

"Yau fa kwana uku da auren ku amma har yanzu ko ruwan dafa shayi ban taɓa jin kace ta dafa maka ba, haka za a zauna ba za a dafa abinci ba sai dai mu idan mun dafa a zo a kwashe a tafi dashi a cinye?"

Murmushi Abdul yayi sannan yace,

"Habaa Innah wasu ma shigowa gidan nan suke yi su ci su sha su qoshi, ballantana mu ƴaƴan ki? Dan Allah ki ce a zuba min a manyan food flask a kai min mota, da yamma ba sai an kai ba an bamu na safe,"

"Inyeee mune ma zamu dinga ciyar da ku kenan?"

"Innah kafin nan kafin mu koma aiki ne fa kawai,"

"Anyaaa Abdussaboor wannan lamarin zai tafi a haka kuwa? Anyaaa? Hummm Allah ya kyauta ya jiyar damu alkhairi a koda yaushe"

"Ameeen Innah, inshaa Allahu alkhairi zaku yi ta ji, da izinin Allah addu'ar ku baza ta faɗi ƙasa banza ba akan mu,"

"To Allah ya sa Baban masu gida, in kaje ka gaishe ta, kuma ya ake ciki maganar Bilkisu ne wai?"

"Hummm Hajiya Bilkisu fa tafi ƙarfin iyayen ta balle ke da ta ke yiwa wani irin kallo a yanzu, ki bita da addu'a kawai, jiya jiyan nan da na shiga social media ko ina ya ɗauka da hotunan ta da videos ɗin ta akan wani ya sai mata gida da mota da latest wayar da ake yayi,wayar da zata kai miliyoyin nerori,Innah idan kika ji abubuwan da Hadiza ta sanar dani akan Bikisu zaki sha mamaki,"

"To ai itama Hadizan zani ce ta tadda muje mu,ko kana nufin ƙarya videon ta da Bilkisun ta nuna min suke yi? Tinda dai gashi nan ƙuru-ƙuru itace a jiki,"

"Innah tabbas itace, amma ita Bilkisu ita ta shammace ta tayi mata wannan videos ɗin a gidan gyaran jiki saboda ta wulaƙanta ta tozarta ta, waye yake lab'ewa yayi wa wasu video ko hotuna basu sani ba Innah? Ai sai maƙiyin da ba ka sani ba, mai shiga rigar abota dan ya cutar da wanda yake tare da shi ko?"

Shiru Innah Laminde tayi tana nazari akan maganganun shi, tabbas maganar shi akwai ƙamshin gaskiya a ciki,numfashi ta sauke da ƙarfi tace,

"To Allah ya shirya mana zuri'a,Allah ya karkato da hankalin ta ta dawo gida,"

"Ameeen bari na wuce Innah,"

Tsakar gida ya fita ya tambayi Aziza abinda aka dafa, cikin muryar ta mai sanyi tace,

"Yah Abdul kumun tsamiya ne da ƙosai har yanzu Baba kande na can na suya,an yi wa su Innah farfesun kayan ciki sai aka soyawa Baba doya da k'wai,"

Murmushi yayi cikin zolaya yace,

"Inyeee gidan 'yan gayu, to taimaka min ki samu babban mazubi ki ɗebar wa Yayar ki abinci ki kawo min mota,"

Itan ma murmushi ta sakar masa sannan ta wuce dan cika umarnin shi.

Yana nan zaune cikin mota ya kira Mommy, ɗauka tayi tana hamma tare da kashe murya irin ta shagwab'ar nan, cikin salon sace zuciyar Abdul tayi wani nishi alamar miqa take yi sannan tace,

"Baby ka dawo ne banji ƙarar buɗe gate ba ko in zo in buɗe maka ne?"

Miƙa ta sake yi tare da yin wani nishi mai tafiya da zuciyar mai saurare, nan take kuwa saƙon da take son isarwa ya kai ƙwaƙwalwa da zuciyar wanda tayi domin shi, cikin sauke murya da gwauron numfashi Abdul yace,

"Baby gani nan dawowa yanzun nan ki tanadar min abu mai daɗi yunwa nake ji,"

"Nayi maka?"

"Kin yi min masoyiya,sai na dawo, ganin nan ma bisa hanya,"

Kashe wayar yayi ya karb'i food flask ɗin da Azizah ta miƙa masa yana murmushi, godiya yayi mata ya sanya hannu a aljihu ya ciro dubu biyu ya bata yace,

"To 'Yan mata a sai data thanks"

"Ni ke da godiya ai yaya byee a gaida Yah Mommy,"

"Zata ji,"

Cikin sauri ya ja motar shi ya wuce gida fuskar shi cike da annuri da farin cikin son ganin babyn shi, sai dai yana shiga gidan yayi gamo da abun takaicin da ya sanya shi jin kamar ya koma inda ya fito........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI












RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨








*PAID BOOKS*



*MAHREEN 1K*

*MAIDA TSOHUWA YARINYA*


*KYAKKYAWAR FAHIMTA*








PAGE 52:














Zaune take daga ita sai rigar baccin da ya fita ya barta da ita wadda ke nuna dikkan wata sura dake jikin ta ba tare da ta b'oye komai ba,gefen ta Sule ne ke ta yi mata lissafin kud'in da ya kashe a wajen saya wa Ameerah kayan d'akin da ta bayar da kuɗi a siya mata,abokin Sule kuwa na zaune a kujerar da ke saitin ta Mommy ya kafe ta da idanu kamar wani baƙin maye yana kallon ƙirjin ta da ke cike suna sheƙi ta saman riga,wani yawu ya had'iya ya sake gyara zama, cike da ɓacin rai Abdussabour ya ƙarasa shiga parlourn ya ajiye abincin a dinning room ya koma ya sake d'akko sauran food flask d'in ba tare da ya ce komai ba, yana gama ajiyewa Mommy ta yi yunƙurin tashi dan ta isa wajen shi tayi masa barka da dawowa,lura da abinda take shirin yi ne ya sanya shi tafiya da sauri wajen ta yana fad'in,

"Samu waje ki zauna ! Ina zaki je a haka a gaban wannan sokon baƙauyen? Kai tashi ka fita ka jira shi a waje,ka zauna ka kafe ta da shegun idanun ka kamar wani baƙin maye,wuce mana nace ! Kar kuma na sake ganin ka a gidan nan kaji na faɗa maka, kai kuma ji nan mana,idan zaka zo dan Allah na roƙe ka ka dinga zuwa kai ɗaya dan ban isa na hana ka zumunci da ƙanwar ka ba,"

Abdussabour na gama fad'in haka ya wuce ya rufe ƙofar da abokin Sule ya bari a ɓuɗe kafin ya fita, yanda ƙofar tayi ƙara ne ya sanya Sule miƙewa tsaye yana damƙawa Mommy ATM card ɗin ta tare da yi mata sallama,shi kuwa Abdussabour ɗakin baccin su ya wuce ya hau sintiri daga ƙarshe ya zauna a bakin gado ya dafe kan shi yana jin wani irin ɓacin rai yana taso masa,ta yaya zata dinga barin jikin ta kowa na gani haka kamar bata ɗauki hakan komai ba?

Sule kuwa kafin ya fita sai ya tsaya yace,

"Dan samu leda ki ƙullo min abinda mijin ki ya kawo miki kan na wuce, kin ganni nan ko abinci ban ci ba,wani arnen baƙi suka tuƙa a gidan jiya shi akai dumamen shi da safen nan, kin san ni ko farin ma ba ci nake ba sai ta tuƙe min balle baƙi,"

"Tuwon dawar Innoh kuwa ai da daɗi Sule, kai dai kawai kace zaka ci abincin gidan amarya ina zuwa jira ni to,"

Babu ɓata lokaci Mommy ta shiga kitchen ta samo mazubi ta zuba masa abincin ta bashi tace ya kai gida su ci da su Innoh kar ya cinye shi kaɗai, godiya yayi mata sannan ya tafi ita kuma ta samu waje a kujera ta zauna ta zuba abinin ta taci ta yi gyatsa ta tashi tana sakace haƙora da toothpick ta koma parlour ta zauna.

Cikin halin ko in kula ta ɗauki remote control ta na sauya tasha daga waccan ta koma waccan ba tare da ta bi Abdul dake fushi da abinda ta aikata ɗaki ta bashi hakuri ba,shirun da yaji da ƙarar TV ne ya bashi tabbacin su Sule sun wuce, to amma me ya hana Mommy zuwa ta bashi hakuri akan ɓacin ran da taga yana ciki? Gajiya yayi da zaman ya fita dan kuwa yunwa yake ji.

Zaune ya tarar da ita tana ta latsar waya ga TV a kunne ana wani action film mai kyau,kaɗa kai yayi ya wuce shima ya zauna dan yaci abinci, yana buɗewa yaga sauran ɗan kaɗan ba lallai ya ishe shi ba, kallon ta yayi kamar zai yi magana kawai sai ya ƙyale ta ya zuba dika ya hau ci,yana kammalawa ya haɗa shayi ya ci da bread ya miƙe ya koma parlour ya zauna yana kallon yanda Mommy ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ganin fuskar ta a haka ne ya sanya shi sauka daga fushin da yayi da ita ya isa gaban ta ya kwantar da kan shi a cinyar ta yana goga fuskar shi a ƙirjin ta, cike da ƙwarewa da bariki ta hau juya jikin ta a fuskar tashi, nan take salon zaman kuramen nasu ya sauya.

Bayan sun dawo natsuwar su ne Abdul ya kalli Mommy cikin kwantar da murya yace,

"Baby dan Allah na roƙe ki daga yau kar ki dinga zama a gaban mazan da ba muharraman ki ba babu kyakkyawar shiga a jikin ki,kin san har yanzu zuciya ta bata gama warkewa daga tunanin wasu sun gama kalle min jikin ki ba, sannan kawai daga fita ta sai in dawo in tarar da wani baƙauyen yaron ya zauna yana kallon ki kamar ya je gidan kallo?"

Tura baki tayi leb'en ta ya sake tudu, cike da shagwab'a tace,

"To shine zaka yi min faɗa a gaban su? Ni fa ina zaune kawai suka shigo ai da kunya na tashi naje d'akko hijabi ko riga a gaban su ko? Sai su ga kamar nayi musu wulaƙanci ne."

"Ba su zaki duba ba ai, haramcin zama babu sutura a gaban wanda ba muharramin ki ba zaki duba,sannan ki duba martabar aure na dake kan ki,dan Allah ki dena zama babu mayafi a gaban wasu bana so, inshaa Allahu da mun je kano zamu je mu sayi sabbin kaya da hijabbai dan ni ba safai nake son matata ta sanya mayafi ba."

Murmushi Mommy tayi ta sumbaci Abdul sannan tace,

"Ohhh babyna akwai ka da kishi gaskiya,"

Cikin kashe murya da ɓoye fuskar shi a jikin ta yace

"To idan banyi kishin iyali na ba kishin wa zan yi uhumm?"

Cikin jin daɗi da farin ciki tace,

"Babu kam,"

Zuciyar tace ta tafi tunanin lokacin da Alhajinta ke haɗa ta da wasu mazan dake son ta bayan ya gama morar ta,ya sha sanar da ita yana son ta amma bai taɓa damuwa da shigar ta ba, ko wani abu makamancin haka ƙarshe dai har sayar da ita yayi wajen Alex,hamdala tayi a zuciyar ta daya bata miji kamar Abdul.


***************************


Saddiqa nata shirye-shiryen zana jaraba, Munir kuma ya samu yana ta nuna mata dik abinda take ganin ya shige mata duhu, Abbah da Ummi kuwa sun wuce Abuja da saka ran bayan kwana biyu Munir zai bi bayan su saboda nashi aikin, da zarar ta kammala jarabawar ta sai ya dawo ya ɗauki matar shi. Ba haka Munir yaso ba, dan kuwa yaso Abbah ya bar shi kamar yanda suka tsara da fari ya zauna a wajen ta,ya rasa me yasa suka sauya tsarin, amma dole haka zai hakura ya bi umarnin iyayen shi.

Ranar da Saddiqa ta fara zuwa makaranta dan zana jarabawa Munir ne ya kai ta yayi zaman sa a mota yana jiran ta gama ya maida ita gida.


Dik yanda Saddiqa tayi masa bayanin zata jima ya koma gida ƙi yayi ya samu waje ƙasan inuwa ya ajiye motar shi ya kunna karatun ƙur'ani a hankali yana saurara.

**********************


Kwana biyu da kafa tijarar Ameerah sai an yi mata lefe kafin ta tare, shamsu ya sallama mata da safe, kamar baza ta fita ba sai ta samu kan ta da zuwa aiken shi,da k'yar ya samu ta gaishe shi tana wani cin magani, kallon ta yayi yana jin yanda son ta ke fizgar shi yace,

"Sarauniyar mata barka da fitowa, takawar ki lafiya mai mulkin birnin zuciya ta,ina fatan dai kina cikin ƙoshin lafiya?"

Harara ta sakar masa tare da tsaki sannan tace,

"Kai dakata min malam ! Me ya kawo ka gidan mu? Ina lefen da nace ka had'o min suke? Na fa sanar da kai idan babu lefe babu zaman aure dan haka zaɓi yana wajen ka."

Wani yawun tashin hankali Shamsu ya had'iya,shi kanshi yana mamakin yanda lokaci ɗaya Ameerah ta gigita masa lissafi, tin bayan rabuwar su da Mommy bai sake yin budurwa ba, wayar shi ce abokiyar rayuwar shi, ya kalli film ɗin da yake so na batsa ya biya wa kan shi buƙata, ko kuma ya nemi novel ɗin da aka baza batsa a ciki ya karanta ya samawa kan shi natsuwa, amma yanzu gashi a gaban Ameerah da bai taɓa koda yi mata kallon arziƙi ba tana juya shi yanda taga dama, cikin sanyin murya yace,

"Kar ki damu ina nan ina haɗa kuɗin lefen ne, inshaa Allahu yau da na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login