Showing 66001 words to 69000 words out of 276165 words
Chapter 23 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
kuɗi ya siya wa Saddeqa abinci da lemo da ruwa ya haɗa mata da dubu biyu ya bata, taso taqi Karb'a sai kuma ta ga bata da dalilin qin Karb'a tinda ba da wata manufa ya bayar ba, godiya ta yi sosai ta Karb'a,ta fita daga ajin ta je bakin ajin su Sadeeq ta jira shi har saida ya dawo daga gida, tana kallon idanun shi ta gane yau ma ya yi kuka, murmushin takaici tayi tace,
"Na faɗa maka ka dena komawa cin abinci indai ka ga ban je ba, ta riga ta yi rantsuwa indai ban dafa ba baza ta bamu ba, ni kuma ba zan ajiye karatuna da na fara ba saboda na zauna na yi bautar da ina yi ana zagin uwata dake qasa ba,ka d'inga hakuri da girkin safen da nake yi mu ci wasu ma basu samun na safen,watarana sai labari,"
Cike da qunar rai take yi masa bayanin nan, shi kuwa kuka kawai yake yi saboda yunwa da baqin cikin abinda ke faruwa da su, gashi yau da yaje gida har baban su ya gani amma da ya gaishe shi ma tambayar shi ya yi wai waye? Yace Sadeeq ne, yace wanne Sadeeq ɗin? Kukan da ya ci qarfin sa ne ya hana shi amsa masa ganin haka Ɗan liti ya hau mamakin meye abun kuka daga tambaya ya shige gida ya bar Sadeeq na kuka a qofar gida.
Rungume shi Saddeqa ta yi tana bashi hakuri itama idanun ta fal hawaye, nuna masa abincin da aka bata tayi ta ce masa,
"Mu je mu ci abinci yunwa nake ji nima,"
Murna ce ta kama shi dan kuwa yana jin alamun ulcer ta kama shi saboda yawan zama da yunwa da yake yi, wanda Saddeqa ta jima da kamuwa da muguwar ulcer.
Waje suka samu suka ci abincin su sosai har da nama a ciki suka raba lemon suka sha ta bar masa ruwan gorar yana ta murna kafin ta ɗauki ɗari biyar ta bashi tace,
"Yau dai kaima ka samu ka ci wani abun da kake so da dare a kashe kwad'ayi,wani bawan Allah ne ya bani, sun zo duba ginin makarantar muka gaisa ya ce a kawo min,"
"Allah ya yi masa albarka ya sa ya fi haka mun gode sosai,"
Da fara'a sosai a fuskar Sadeeq suka rabu da yayar tashi dake ta zubawa bawan Allah'n da ko sunan shi bata sani ba addu'a akan sanya su farin ciki da ya yi, a haka ta koma ajin su ta tarar da d'alibai sun zazzo suna ta bitar haddar su kafin azo Karb'a.
************************
Har suka isa gida da qanin nashi be sake cewa komai ba, direct pampon gidan nasu ya nufa ya wanke hannayen shi da qafafun shi sannan ya wuce d'akin Innah Laminde, a saman kujera mai ɗaukan mutum biyu ya zauna ya miqe qafafun sa da kyau ya saki wata ajiyar zuciya,lumshe idanun shi yayi yana hango Kyakkyawan gashin idanun ta da ya kwanta samb'al ga girar ta mai cika da tsaho,yana hango lokacin da ta buɗe idanun ta a fuskar shi sai ya buɗe idon shi da sauri ya miqe zaune da kyau yana sauke ajiyar zuciya.
Innah Laminde ce ta shiga parlourn sanye da hijabi hannun ta riqe da carbi tace,
"Abdul har kun dawo kenan, da alama aikin ba yawa ko? Ai mai martaba ya shigo yana tambayar ina kake nace kaje duba makaranta ne amma kana nan dawowa yanzu, dan haka ya kamata kaje ka same shi yanzu yana can turakar shi,"
Miqewa yayi ba tare da yace komai ba yayi waje dan zuwa jin me yasa mahaifin shi ke neman shi bayan sun gaisa kafin ya fita, murmushi Innah Laminde tayi dan ta san har yanzu fushi yake yi da ita akan maganar da ta kawo masa daren jiya.
Sallama ya tsaya ya yi a bakin kofar shiga turakar mahaifin nashi, saida aka amsa aka yi masa izinin shiga sannan ya shiga bakin shi ɗauke da wata Sallamar, cikin sakin fuska mahaifin nasa da suke tsananin kamanni ya amsa sannan ya yi masa nuni da carpet ɗin dake gefen shi mai ɗauke da wani tuntu mai laushi irin na gidan sarautar nan, zama Abdul yayi ya tankwashe qafar shi ya sake gaishe da mahaifin shi kafin yace,
"Abbu barka da war haka,na dawo daga makarantar yaran can ne Ummah tace kana nema na shine nace bari na zo da wuri kar na sa ku jira,"
"Abdussaboor mahaifiyar ka ta yi gaskiya ina neman ka, ba komai ne yasa nake neman ka ba face ina so na ji ina muka tsaya akan maganar da muka yi da kai last week game da fitar da matar aure? Mahaifiyar ka ta kawo shawara akan had'in auren da take so ayi maku kai da Bilkisu amma na dakatar da maganar, nace kar ta yi maka maganar ma saboda bana son irin wannan auren had'in, nafi so ka zaɓi matar ka da kan ka saboda samun kwanciyar hankalin kan ka da d'orewar zaman lafiya a gidan auren ku,"
Sosa qeya ya ɗan yi kafin daga baya ya sake duqar da kan shi yace,
"Abbu na gode da bani wannan dama da ka yi,kuma alhamdulillahi an yi sara akan gab'a dan kuwa a yau na ga wata yarinya da na ji hankali na ya kwanta da ita a can makarantar da na kai ziyara sai dai ban yi mata magana ba,"
"Asshaa ! To in banda abinka Babana me yasa baka sanar da ita muradin ka ba nan take? Ai a bari ya huce shi ke kawo rabon wani ko? Kuma barin kashi a ciki ai baya maganin yunwa,"
Murmushi Abdussaboor yayi ya sake duqar da kan shi sannan yace,
"Maganar ka gaskiya ne ranka ya dad'e, zan yi wa Sultan magana ya bincika min a wanne gida take, dan kuwa na bashi aike ya kai mata na san ba zai rasa sanin ta ba tinda shi mazaunin gari ne,"
"Da kyau Babana, haka nake son mutum idan zai yi abun alkhairi to ya gaggauta yin shi kar a jinkirta, Allah ya sanya muku albarka da kai da sauran 'yan uwan ka,zaka iya tafiya,"
"Ameeen Abbu na gode, ammm Abbu,"
Cike da kulawa Sarki Ilyas ya d'aga kai ya kalli ɗan nashi yace,
"Na'am Babana akwai wata maganar ne?"
Sosa kai ya yi sannan yace,
"Eh toh ! Dama dan Allah ina neman alfarma wajen ka ne, ka sanar da Ummah na samu mata ta janye maganar yarinyar can bana son ta gaskiya, dan Allah Abbu ka goyi bayana, sannan ina so gobe na koma zamu yi wata tafiya ta gaggawa,zan bar maganar gyaran da za a yi a hannun Sultan,"
"Kar ka ji komai Babana fatan mu dai Allah ya zab'a maka abokiyar zama tagari kamar mahaifiyar ka, koma in ce wadda tafi ta,Allah ya yi maka albarka ya bada ladan abinda ake yi na d'awainiya,Allah ya sa afi haka,"
"Ameeen Abbuna na gode,"
Yana komawa d'akin Innah Laminde ta gan shi ya washe ya dena fushin da yake yi da ita, nan fa ta matsa sai ta ji me yake faruwa yaqi sanar da ita komai,cikin murmushi tace,
"Anya Uban masu gida ba wata qulalliyar kuka qulla ba kai da mahaifin ka tinda kun saba ware ni? Yanzu 'yar 'yar uwar tawa ce baka so? Yarinya me hankali wayayyiya tana son ka, kullum tazo se ta neme ka har lambar wayar ka ta Karb'a dan ta dinga gaishe ka fa,"
"Ta kira ni sau biyu na ga sunan ta ta true caller na qi ɗauka,tin daga nan bata sake kira na ba, kinga alamu sun nuna itama ba so na take yi ba kece dai kike ganin kamar sona take yi, kuma kike son ki haɗa ta aure da gudan jinin ki dan ki faranta musu, to farin ciki na fa Ummah?"
"Kai ma ina son farin cikin ka Baba, na dai so a yi tuwo na mai na ne,amma shikenan dik abinda yake alkhairi Allah ya nufa ya tabbatar,"
"Ameeen, kar ki ma damu ni nayi matar aure ma, idan na sake dawowa zan gabatar da kaina a wajen ta, yanzu tafiyar gaggawa ce ta taso mana saboda zamu shigo da wasu kaya da ake da buqata dan haka ina ga ba zan fi sati biyu zuwa uku ba zan dawo sai na gabatar da kaina wajen ta, kafin nan zan saka Sultan ya binciko min ko 'yar waye a garin nan,"
"Ikon Allah ! To Allah ya sanya albarka, shine kawai abinda zan iya cewa yanzu, amma fa a gaskiyar magana in har yarinyar nan Bilkisu ta nuna tana son ka dole zaka aure ta dan kuwa gida bata qoshi ba wa zai je yana kaiwa dawa?"
"Humm Allah ya zab'a mana abinda ya fi alkhairi, na kula dai kin fi son wannan yarinyar me ruwan fitsararru akaina,"
"A kul na kuma jin kana aibata min 'ya,"
Haka hirar Abdussaboor ta ci gaba da wakana tsakanin sa da mahaifiyar sa cike da shaquwa da kulawa.
Ko da dare yayi yaje kwanciya bacci ma haka ya dinga tunanin Saddeqa yana yi yana maimaita sunan ta a labb'an shi yana murmushi, a haka har bacci b'arawo ya sace shi.
Da sassafe kuwa ya yi shiri ya yi wa iyayen sa sallama ya shige motar shi mai bala'in kyau da tsada ya tafi ya bar Innah Laminde da kewa.
A ranar bayan tafiyar shi aka fara kawo qasa ana jibgewa da katak'waye da langa-langa da qusoshi, duk wani kayan aiki da za a buqata an kawo, an saka ranar laraba ta zama rabar da za a fara aiki, lokacin yaran suna gida ana hutun mako.
*************************
Tinda su Mommy suka tafi da Alhajin ta Billy ke jin matsanancin kishi da quncin rabuwa da Mommyn musamman yanda ta ga an yi mata gyaran jiki kyawun fatar ta ya sake fitowa, cikin dabara ta bar parlourn qasa ta haye sama ta sauya kayan ta ta ɗauki wayoyin ta ta sauka qasa,ba ta tarar da kowa ba dan haka sai ta zari makullin mota ta kira Sallau ta bashi saqo ya sanar da hajiya ta tafi club.
Cikin sanyin dake kad'awa na magaribar take tuqi a cikin unguwar tasu ta masu hannu da shuni ta sanya waqar su Brick&Lace ta Love is wicked, a hankali take bin baitin kamar wata k'wararriya tana yarfa hannu tana gyad'a kai,ana zuwa dai-dai inda suke cewa....
'Running around i can't get through my day...'
(You feel me?)
'Thoughs of you just keep consuming me...'
(Inna me head, Inna me head, okey)
'And i though i could do it but now i see that you are not mine....'
'And i was wrong to think you'd change, Yeah....'
'I wish you could stay with me another day (ay)....'
'I wish i could change your mind and make you stay (stay).....'
'Cause I, I'd give anything to hear you say (say).....'
'I'll be loving you eternally (love you eternally)'
Your love is wicked.......
Wayar tace ta fara ringing hakan yayi sanadiyyar tsayawar waqar da take sha tana rawa cike da kewar Mommy, kallon sunan me kiran tayi ta sanya hannu cikin sanyin jiki ta amsa.......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
*Masu tambaya daga farko ku yi hakuri ku jira a gama a haɗa document ko kuma ku duba channel d'ina ta nan Whatsapp,ko page d'ina na Facebook mai suna Haermeebraerh's Novels,ko wattpad Haermeebraerh9900 Idan kuka yi following kuna liking zaku fi ganin new update da zarar an dora, ina yi wa masu neman Audio na novels d'ina albishir da cewa inshaa Allahu a cikin shekarar nan ko me zuwa za su fara samun audio ɗin a YouTube Channel d'ina.*
PAGE 25:
"Ina wuni Ummah?"
"Lafiya qlou ke ina kika shiga kwana biyu ba waya ba aike shiru,kin san kuwa yanzu haka danake miki magana ina gidan ƊAN LITI yarinyar nan Hadiza ta sai wa Uwar ta ingin markad'e ta sai wa Uban ta sabon adaidaita sahu gadagal da ledar shi da komai? Kin ga yanda Sulemanu ke kashe nera yana watayawa a qauyen nan kuwa? Anya yarinyar nan aikatau take yi ko dai ta kauce hanya ne Bilkisu?"
Cikin sauri Billy tace,
"Haba Ummah,kin ga dalilin da yasa bana sakewa na kashe muku kuɗi sosai ko, to ke da kan ki kin fara zargin samun kuɗin Mommy da muke tare muke wahala da jikin mu mu samo ina ga sauran mutane? Ba fa qananan mutane muke yi wa aiki ba, mutane ne da ke riqe da madafan ikon qasar nan, mu yi wanke-wanke mu yi shara mu goge inda suke takawa, mu gama mu ɗora girki,mu wanke band'akin da suke zuba qazantar su,to yanzu haka aike na aka yi ko sallah ban yi ba, kin ga kuwa dole suma su zage bakin aljihu su biya mu da tsoka tinda ba me yi musu idan ba mu ba, kuma su ma baza su iya yi wa kan su wannan wahalar ba,"
Mahaifiyar Mommy ce ke nuna wa sauran matan wayar hannun Ummahn Billy tana gyad'a kai tana farin ciki da jin kalaman Billy, caraf ta cafe maganar tace,
"Allah dai ya yi muku albarka kin ji Bilkisu? Gwanda da Allah yasa ke aka kirawo kike yin wannan bayanin da Mommy aka kirawo se ace dan 'yata ce, to gashi nan dai kowa ya ji da kunnen sa duk d'an baqin ciki se dai ya mutu,"
Da sauri Mahaifiyar Billy tace,
"To Bilkisu za mu yi waya idan na koma gida, Yayan ki ma yazo yau kwanan shi huɗu amma gobe zai koma saboda wai tafiyar gaggawa ta taso masa,"
Lumshe ido Billy tayi kafin tace,
"Allah sarki a gaishe shi to, sai anjima zan kira ki idan na gama ayyuka na,bari na yi sauri kar a yi ta jira na,"
Kashe wayar suka yi Billy ta kashe motar gaba ɗaya ta dafe kanta, cikin wata iriyar murya tace,
"Wai meke damuna ne? Wace iriyar zuciya gare ni ne ni da bana gane inda na dosa? A gaskiya bana jin son Mommy nake yi sai dai tsananin sha'awar kasancewa da ita dan biyan buqata ta, Yah Abdul shi ne wanda zuciyata ke so da aure,na tabbata a duk sanda na gama more rayuwa ta na koma gida zai aure ni,Allah ka nuna min lokacin da zan yakice bariki a rayuwa ta na koma gida,"
Cikin sanyin jiki ta tada motarta ta bata wuta sosai ta nufi club ɗin nasu da ya tara manyan yaran masu hannu da shuni da madafan iko,banda bushe-bushen kayan maye da shaye-shayen kwayoyi da giya ba abinda ake yi a wajen, mata ne kaca-kaca kusan tsirara wasu na zuba soyayya da samarin su a bainar nasi wasu kuma suna rawa, wasu kuma sun shawu sun bugu ba su iya sarrafa kawunan su.
Haka Billy ta samu ta kutsa ta zauna a saman kujerar dake gaban bar ɗin wajen ta yi bayanin irin had'in kaurin da za a yi mata dan kuwa tana buqatar caji sosai, bata jin daɗin zuciyar ta sam, ta rasa ina zata tsaida tunanin ta da soyayyar ta tana cikin rud'ani, ga kewar Mommy da ta kasa barin ruhin ta ya huta, ana gama yi mata had'in nata bar tender ɗin ya miqa mata qaramin cup ɗin ta d'aga kai ta kwankwad'e abinda ke cikin shi tana yamutsa fuska tare da kakari tana damqe wuyan ta, cikin abinda be fi mintuna biyu ba ta dawo normal ta sake cewa a yi mata irin wannan had'in, kallon ta mutumin ya yi yaga ba wasa a fuskar ta, sai ya Karb'a ya yi mata, ta kuwa d'aga baki ta shanye kamar yanda ta yi wa na farkon,tana gamawa ta tashi da kyar tana layi ta shiga filin rawa ta dinga cashewa, a nan ta haɗu da wani kyakkyawan saurayi ya yi mata tayin kwana da shi ta amince ba domin kud'in ba ma sai domin kyawun fuskar da taga yana da shi.
A can gidan Ɗan liti kuwa bayan Billy ta kashe waya sai shewar mata ta tashi suka dinga taya Innoh murnar samun ingin markad'e nan take tace musu,
"Ai ba markad'e ba kawai har niqa zan dinga yi tinda kun dai san garin nan an fi cin tuwo da kunu ba safai ake yin markad'en kayan miya ba,"
Ummahn Billy ce tace,
"Kin kuwa yi dabara Allah ya taimaka ya tsare mana yaran mu a dik inda suke,"
"Ameeen"
Shine abinda qawayen Innoh da 'yan uwan ta irin su Naja suka dinga faɗa kafin daga baya su fara watsewa kowa ta tafi gidan ta, Baabaa kuwa na gefe tana kallon su bata ce komai ba, cikin ranta tunanin su Saddeqa take ta yi, tana son yau dai ta basu abincin dare ko ta halin qaqa ne sai dai ayi bala'in da za a yi a shirye take amma ta dena barin yaran suna kwana da yunwa,ita ba azzaluma bace.
Qarshe dai kafin kowa ya gama watse sai da suka sakar wa da Baabaa baqar magana akan tana baqin ciki da samun Innoh, ko kula su bata yi ba suka gama rashin kunyar su wadda Innoh ce ta basu lasisin yi mata hakan suka tafi.
Da yamma liss su Saddeqa suka dawo daga makaranta basu tarar da kowa a tsakar gida ba, dan haka d'akin su ta wuce direct ta fara cire kayan jikin ta ta d'aga katifar Yadiko ta saka kud'in hannun ta a inda take ajiye kud'ad'en ta sannan ta sauya kaya ta fita tsakar gida dan zuwa ta gaishe da mutanen gidan kafin a yi magariba.
D'akin Innoh ta nufa ta yi sallama, Naja ce ta amsa mata sannan cikin dakewa tace,
"Ki shigo ni bana son munafurci dalla,"
Jiki a sanyaye Saddeqa ta d'aga labulen d'akin ta leqa tare da durqusawa ta gaishe da Najar sannan ta gaida Innoh dake ta cika tana batsewa ita a dole ga uwar mai kuɗi, cikin muryar rashin mutunci tace,
"Sannu tinkiya uwar tinb'ele baki san gida ba se an nemo ki,kin ga dama kin dawo? To maza ki je madafi ki qarasa tuqe tuwon nan tasss ki raba kuma ki jiqa tukunyar idan kin gama,"
"To Innoh, amma ba za a yi qanzo ba za a jiqa tukunyar?"
Shewa tayi sannan tace,
"Kin taɓa ganin na yi qanzo ni? Wannan ai se uwar ki da ke qas ita ce ke yin qanzo saboda tsoron babu,ni kuwa kin san tin da can Allah ya rufa min asiri ballantana yanzu da 'yata ke aiko min da damman kuɗi,wuce ki je ni kiyi min abinda na saka ki"
Cike da zubar