Showing 123001 words to 126000 words out of 276165 words

Chapter 42 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

raina take ganin idan ta ɗauka bana ganewa,"

Cike da borin kunya Innoh tazo zata fice ta bar ɗakin, Saddiqa tayi saurin bata hanya, hannun ta data jimqe kud'in Baabaa tayi wuff ta damqe ta matse da ƙarfi sannan tace,

"Sake su tinda ba gadon da Delu ta bar maki bane kan ta tafi ƙiyama,"

Nan take abu ya zama rikici tsakanin Innoh da Baabaa, Munir na gani yaƙi rabawa, Saddiqa kuwa sai kuka take yi tana roƙon shi da ya raba, ya na jin ta yayi wucewar shi ɗakin Yadikon ya hau duba inda kayan ta suke dan ya taya ta kwashewa, ta na ganin haka ta shiga ɗakin a guje ta danne sif ɗin da kayan ta ke ciki tana zaro idanu waje kamar mara gaskiya.

Baabaa ce ta shiga d'akin tana haki tace,

"Mahaukaciyar banza da wofi kawai,ta na nan tana satar kud'in da ba nata ba yaran ta na ƙofar gida suna faɗa da mijin da Allah ya zab'awa ƴar ta ta taƙi karɓar ƙaddara, ah ah ku kuma menene haka kuke yi?"

Kallon Saddiqa da Munir tayi taga suna kici-kicin buɗewa da rufe sif, cikin Sauri Saddiqa tace,

"Baabaa ki ce masa ya bar min kaya na na ɗauka da kai naaaa"

"Taya ta fa zan yi,"

"Kai ni ba zan iya da jarabar ku ba ku cinye kan ku in kun so, na yi ɗakina na ɗauki abinda zan buƙata nima, ai na godewa Allah da Allah yasa na biyo bayan ku, da ku kaɗai ne da waccan baƙar dagar ta ƙulla muku wani sharrin,"

Baabaa na gama maganar ta ta wuce d'akin ta ta hau tattara abubuwan da zata buƙata kafin nan kafin Saddiqa ta gama jarabawa ta dawo, dan ba a can zata ci gaba da zama ba.

Innoh kuwa tinda ta samu ta samfe daga faɗan borin kunya sai ta shige ɗaki tana fatan Allah yasa suyi su tafi kar wani yasan abinda ya faru.

Munir kuwa yayi nasarar janye Saddiqa daga jikin sif ɗin ta na kaya ya hau taya ta kwashe kayan nata a cikin akwatin da ya gani a jingine a ɗakin, wanda dama nata ne Yadiko ta sai mata na musamman saboda tafiye-tafiye zuwa garin kakannin ta fulani.

Yana cikin kwaso kayan ne ya ɗakko da bra ɗin ta da panties ko a jikin shi kuwa ya zuba su a akwatin ya ci gaba da kwashe sauran, matsananciyar kunya ce ta hana Saddiqa tsayuwa a ɗakin sai ta yi waje kawai ta bar shi yana kwasar kaya kamar ya gama sanin wanne ne nata wanne ne ba nata ba, domin kuwa hatta da littattafan ta na islamiyya da boko sai da ya kwashe, yana gamawa ya janyo akwatin nata da na Mommy dake ajiye a gefe ya yo waje da su, ya sake komawa ya ɗakko katifar Mommy da kayan ta da ta baza a saman katifar yayi waje da su dika Innoh na ɗaki bata san ana yi ba.

Yana gama fitarwa Saddiqa tace,

"Me yasa ka fitar mata da kayan ta waje?"

"Saboda ba ɗakin gyatumar ta bane,wannan ɗakin rufe shi zamu yi dik sanda kike da sha'awar zuwa zaki zo gidan ku nan zaki sauka kin gane?"

D'aga masa kai tayi tana kure shi da ido tare da cije leb'en ta na qasa tana murmushi, kallon ta shima yayi sannan yace,

"Ki dena yi min irin kallon nan ko kuma....."

"Ni babu wani kallo da nake yi maka na musamman haka kallo na yake,Yah Munir to ka mayar musu da kayan su d'akin su mana bai kamata a bar mata a waje ba gaskiya,"

"Ni ba bawan gidan su bane,"

Bata sake kula shi ba dan ta san ba yi zai yi ba tinda ya nuna bayi zai yi ba ɗin, dan haka da kan ta ta kwashe kayan Mommy dika ta mayar d'akin su na 'yammata ta ja ƙofar, suna nan tsaye suna hira sama-sama Ɗan liti ya dawo, tin daga waje suka jiyo ƙarar adaidaita sahun shi wanda ya sanya gaban Saddiqa faɗuwa sosai, Baabaa ce ta fito daga ɗakin ta ɗauke da jakar kayan ta a hannu ta tsaya tana rufe ɗakin tare da tambayar Munir ya saka kwaɗo a ƙofar Yadikon ko?

"Eh na saka na rufe ga makullin ma nan,"

"To da kyau mu je ko akwai abinda baku gama ba kuma?"

"Ah ah mun gama komai ke muke jira,"

Baabaa na ganin Ɗan liti amma tayi banza dashi zata wuce shi, cikin sauri ya tsaida ita yana bata hakuri, kallon shi tayi a sheƙe sannan tace,

"Ɗanli ai haƙuri kai ya gani kuma kai ya kama, tinda dai kai ka zama shanyayye to mu munyi nan,Allah ya sada mu da alkhairi, uhumm dangane da maganar Sadeequ kuma zai bi su Baban Gida can Habuja idan za su tafi gobe, amma dai nace dole a sanar dakai dan kai ne uban sa, idan ka amince tom,in baka amince ba shikenan ya bar maka ɗan ka a ƙarasa lalata rayuwar shi da rashin zuwa makaranta,"

Cikin zuciyar Ɗan liti zai so ace ya bar ɗan nashi an tafi dashi dan inganta rayuwar shi, amma bai san me ya ja ra'ayin shi har yace,

"Ah ah babu inda Sadeeq zai je, a bar min shi anan ina ganin shi ina jin daɗi, ni dai ina sake bada haƙuri akan..."

"Ai magana kuma ta ƙare kuma Ɗanli, Sadeequ zai zauna anan garin, amma ba zai dawo gidan nan ba sai sanda na dawo nima,Allah ya ganar da kai, gaskiya"

Yana kallon sanda Baabaa da Munir suka bar gidan ɗauke da kaya a hannun su,Saddiqa kuma na tsaye ta kasa gaba ta kasa baya kamar mai neman izinin shi, cike da zubar hawaye ta durqusa a gaban shi tace,

"Baba ka yafe min dik abinda nayi maka da wanda nake yi maka yake ɓata maka rai har ka daina nuna kulawar ka a kai na ni da Sadeeq, Baba bamu da kowa yanzu sai kai Yadiko ta rasu, me yasa kake jin haushin mu a koda yaushe kake kyarar mu?"

Shiru Ɗanliti yayi dan bai san amsar da zai bata ba, kallon ta kawai yake yi idanun shi sun kad'a sun yi jawur kamar gauta,shirun da ta ji yayi yawa ne ya sanya ta cewa,

"Baba ka sanya min albarka, sannan kayi min addu'a zan zama jarabawa ta ta qarshe kwanan nan,"

Kallon ta yayi ya d'aga hannu kamar zai dafa kan ta, wani irin zafi yaji kamar zai manna hannun shi a wuta,dan haka cikin sauri ya janye hannun shi yace mata,

"Allah ya sanya wa rayuwar ku albarka ya bada sakamako mai kyau,"

Yana gama faɗin haka ya shige d'akin Innoh dake lab'e a jikin window tana ganin duk abinda ke faruwa a tsakar gidan nasu.

Da kuka Saddiqa ta isa mota ta buɗe gefen da Munir ke zaune yana jiran ta ta zauna, Baabaa bata ce komai ba dan kuwa ita kanta zuciyar ta na ƙuna akan halin da yaran ke ciki a gidan uban su, sai dai ta sani dik daren dad'ewa asirin Innoh sai ya tonu,wannan rayuwar da yaran ke ciki ba zata dore ba.


************************

A can kasuwa kuwa a gaban idon Shamsu aka gama gyara wa Ameerah da Mommy kai har aka fara yi musu ƙunshi ja da baƙi, wani shago ya tafi da sauri ya siyo lemo mai sanyi da pure water ya kawo wa Ameerah ya buɗe ya miƙa mata yana faɗin,

"Karɓi ki sha gimbiyar mata na san ana zafi,"

Cike da jin takaicin Shamsu ta Karb'a tace,

"To ɗan anace na Karb'a ai sai ka koma waje ko?"

Dariya mommy tayi da ta tina sanda suka fito daga gida ya tare su yace sai ya raka su, sun sha artabu sosai kafin Ameerah ta kyale shi ta bar shi ya biyo su, cikin dariya Mommy tace,

"Amma dai Shamsu baka da kirki babu kuma amana, Ameerah ce kaɗai anan da zaka siyo wa matar ka lemo ni ka barni cikin ƙishi? Babu komai ke zo nan karb'i wannan ki siyo wa dik wanda ke cikin shagon nan lemo ɗaya da ruwa da cincin,"

Yarinyar shagon ce ta isa gaban Mommy tana washe baki ta karb'i kuɗin hannun Mommy ta tafi siyo lemo, shamsu kuwa ko kula ta bai yi ba yana gefen Ameerah yana zuba mata surutun yanda aka gyara sashen da zata zauna, wato tsohon ɗakin shi da tin asali yake a killace da langa-langa a cikin gidan nasu, wani irin haushin shi ne ya kama ta taji kamar ta shaqe shi wataqila ta huta da baƙin cikin shi.

Haka su Mommy suka zauna har bayan magariba sannan aka gama yi musu dik wani gyara da suke da buƙata, ana gamawa ta ɗauki hoton ƙunshin ta turawa Abdussabour dake ta zabga mata waya, yana gani kuwa hankalin shi ya kwanta, dan kuwa da har ya sanar da Bilal su shirya ya raka shi wajen Mommy, Bilal yace ba zai je ba, cikin ɓacin rai Abdul yace shi zashi ganin matar shi kar ya raka shi ɗin,ya kula kamar adawa yake yi da auren shi ma.

Bayan Mommy da Ameerah sun koma gida ne suka tarar da Naja da wasu 'yan uwan Innoh suna zaune ana hira ana cin shinkafa dafa dika, suna ganin su Mommy suka b'arke da gud'a da shewa tare da faɗin,

"Ga amare ! Ga amaren nan sun dawo,"

Naja ce ta ja su d'akin su na 'yammata ta ɗakko wani tsumi na kayan mata tace wa Mommy,

"Ga wannan,na musamman na karb'o shi gidan boka, idan kuka sha wannan mallaka ce ta har abada, mazan ku babu su babu maganar ƙarin aure,"

Cike da murna Mommy ta rungume Naja tace,

"Kaiii Aunty Naja Allah ya biya ki, kin ga bamu dawo ba tinda aka gama yi mana qunshi sai da na biya na siyo maganin nan na mata, ashe kina nan kina yi mana tanadi na musamman,Allah Allah ka sa maganin nan yaci,bana son kishiya, bana ƙaunar kishiya, Allah ka nesanta ni da ita har abada,"

Ameerah kuwa taɓe baki tayi ta wuce su ta kwanta a katifa dan ta huta,kallon ta Naja tayi tace,

"Ke baza ki tashi ki sha bane? Maganin mallaka ne fa,"

Cike da fushi fa masifa Ameerah ta hayyaqo wa Naja tace,

"Nabi mallakar da gudu babu wando, yau na ji maganar banza, ai kun san wanda nake son na mallake amma baku yi hakan ba, sai yanzu dan na auri lusarin miji kamar wannan shine zaku dame ni da wani maganin mallaka?"

Juyawa tayi ta kwanta tana matse k'wallar baqin ciki,Mommy kuwa zama tayi ta kwankwad'e maganin nan duka, ta haɗa da wanda ta siyo dika ta shanye,sai da ta gama ne ta kula da an dawo mata da akwatin ta da katifar ta d'akin su na 'yammata, taso tayi Maganar ta basar dan kuwa ta sani yau ba a gidan zata kwana ba,to menene na damuwa? Wanka ta fita yi domin ta shirya kanta da kanta dan bata ga alamar 'yan gayun da za su yi mata kwalliyar arziqi ba a wajen ballantana a yi mata shiri mai kyau.

***************************

Gidan sarki ya cika maqil ana ta hidimar biki da ware masu ɗakko amarya, dik da cewa a qurarren lokaci bikin yazo hakan bai hana mutane zuwa taya babban ɗan sarkin murna ba,gidan amarya an gyara shi ya haɗu ya gaji da haɗuwa dan kuwa a kaff ƙauyen ba lallai a samu kamar shi ba, Abdussabour ya yi wanka cikin wata babbar shadda fara k'wal ta sha aiki daga sama har qasa, an yi masa rawani mai bala'in kyau da ash colour rawani kalar aikin jikin kayan shi, wani ash colour ɗin takalmi ne a ƙafar shi irin na sarakai an yi masa ado da farin zare,banda tashin qamshi babu abinda Abdussabour ke yi, dik inda ya gilma kuwa sai taya shi murna ake yi shi kuwa yana wage baki yana amsawa cikin farin ciki .

A cikin gida kuwa Innah Laminde sai yaqe take yi dan kuwa rashin ganin qanwar ta ta a bikin Abdussaboor ba qaramin damun ta yayi ba,ita kanta ba wani son auren nan take yi ba dan dai ya zamana bata da yanda zata yi ne, da baza ta bari Abdul ya auri Mommy ba, amsa sallamar cousin ɗin ta tayi sannan ta bata izinin shiga ɗakin nata, kallon ta 'yar uwar ta ta tayi tace,

"Laminde hakuri zaki yi ki fito cikin mutane a yi shagalin nan a gama, abinda dare ma yayi yanzu zamu je ɗakko amaryar? To me ya rage kuma? Ita dai Ta Annabi dole ta sanya wa zuciyar ta salama ta gane komai muƙaddari ne daga Allah,matar mutum kuma kabarin shi ce ko ba haka ba?"

Wani abu Innah Laminde ta had'iya mai ɗaci sannan tace,

"Hakane,gani nan fitowa, amma da kin barni a ɗakin tinda ko na fita ba dani za a je ɗakko yarinyar nan ba ko?"

"Ah ah, gwanda kowa yaga idanun uwar ango, ba dan mun raina ƙoƙarin abokan zaman ki ba,"

Murmushi Innah Laminde tayi suka fita a tare cikin jama'a, nan waje ya b'arke da gud'a da kirari daga wajen maroƙa, babu b'ata lokaci kuwa Innah Laminde ta dinga kyautar kudi da turamen atampa dan nuna farin cikin ta.

Da misalin qarfe goma dai-dai mata daga gidan sarki suka shirya dan tafiya ɗakko amarya Mommy a dangana ta da gidan mijin ta Abdussabour..........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI











RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨












PAGE 48:













Motoci uku ne zasu tafi ɗaukan Mommy dan su kai ta gidan ta dake cikin ƙauyen Ba Mugu, dik yanda Bilal ya dinga zillewa dan kar ya zama drivern motar Abdul da Mommy hakan bai samu ba, dan kuwa har ɗaki Abdul ya kira Bilal ɗin suka zauna ya roqe shi alfarmar ya tuƙa shi zuwa ɗaukan amaryar shi,cikin ɓata fuska Bilal yace,

"Malam ba dan ka ji na amince ka aure ta ba zai sa ka zaci wai ina son tane, bana jin akwai ranar da zan so yarinyar nan fa, gaba ɗaya aljanun kammu maƙiyan juna ne, wataƙila a duniyar su ma sun taɓa gwabza yaƙi,na amince zan tuƙa ku sannan jibi zan koma Kano na sa a gyara maku can gidan zan baku waje a ci soyayya lafiya Allah sanya alkhairi,"

"No babu inda zaka je,bayan akwai d'akuna har uku a gidan akwai parlour biyu kawai sai na barka ka kama haya? Ai wannan idan sarki yaji ma sai ka jawo min faɗa a wajen shi,"

Galala Bilal yayi yana kallon Abdul yana tinanin anya yana lissafi kuwa? Gani yayi dare nayi dan haka bai sake kula shi ba kawai ya miƙe yayi gaba, direct wajen motar Abdul ya nufa ya buɗe ya shiga yana fad'in,

"Idan kai baka da hankali ni ina da shi, har yanzu zargin yarinyar nan nake yi,ba zan iya zama gida ɗaya da ita ba inaaa,kai da ka ji ka gani Allah ya bada sa'a,"

Abdul na shiga Bilal ya tashi mota suna hira har suka isa ƙofar gidan su Mommy, anan suka tarar da motocin su Sultan da wani cousin ɗin su Abdul ɗin sun ajiye matan da suka je ɗaukan amarya.

Bayan fitar Motar su Bilal da minti 3 ne Ta Annabi mahaifiyar Billy ta faɗa gidan sarki a gigice numfashin ta na fita da kyar, direct parlourn Innah Laminde ta shiga ta zube a ƙasan carpet ta rushe da wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi.

Innah Laminde na tare da 'yan tsirarun dangin su da basu tafi ba sai ta miƙe cikin azama ta kama Ta Annabi suka bar ɗakin gaba ɗaya suka nufi na Abdul ta sa sakata ta kulle su ta ciki,zaunar da ƙanwar ta ta tayi a bakin gadon Abdul da har a wannan lokacin d'akin na fitar da ƙamshin turaren da ya fesa, cikin murya mai taushi Innah Laminde ta fara baiwa ƙanwar ta ta hakuri akan abubuwan da suka faru, cikin kuka da fyace majina Ta Annabi tace,

"A gaskiya Yaya idan nace maki abinda ya faru bai yi min ciwo ba nayi ƙarya, akan wannan baƙin cikin muke ta shirin gyara wa Shamsu inda tashi amaryar zata tare, yaro yabi ya firgice ya gigice ji yake yi kamar aje a ɗakko masa ita su yi rayuwa a wannan akurkin ɗakin nashi,ganin halin da ake ciki sai Bilkisu ta amince zata kwashe kayan ta dika ta mayar d'akin shamsu shi kuma ya gyara nata saboda amaryar shi,idan dangin ta sun yi mata jere su suka sani, idan basu yi ba su zauna a haka a tsohuwar katifar shi ai su suka san shige da ficen da suka yi aka ƙulla auren.

Mun gama magana rimi-rimi da yarinyar nan kamar ta haƙura da maganar auren da Abdul yayi kawai ɗazu da almuru naji tana waya da wani tana sanar dashi zata zo su je dik inda yake so amma wannan karon zai biya ta kuɗi masu yawa sannan zai saya mata gida da mota, ba zata sake komawa ta jingina da kowa ba, wannan karon so take yi ta zama....so take ta zama...ka...karuwa...mai lasisiiiiii yayahhhh,"

Cikin kuka mai tsanani Ta Annabi ta ƙarashe maganar ta, da sauri Innah Laminde ta dafe ƙirjin ta ta zauna tana salatin da bata san iya adadin da tayi ba kafin ta sake maimaita kalmar ƙarshe da ƙanwar ta ta faɗa,cikin jimanta lamarin Innah Laminde ta dafa kafad'ar Ta Annabi tace,

"Yanzu ina ita Bilkin take?"

"Shine tashin hankalin da nake ciki Yayah, daga jin kalaman ta a waya na shiga ɗakin na daki kayan banza da icce sannan nace kar ta sake ta saka ƙafa ko da ƙofar gida ne sai da izini na, a take ta fashe da kuka tace,

'Ba zan taɓa zama talauci da babu su kashe ni ba,idan ke kin ji kin gani zaki ci gaba da rayuwar ƙauye ni ba zan iya ba, kala ta da ƙira ta ba ta zaman ƙauye bane,na gama yawon duniya na san maza kala-kala sai na dawo ku aura min wa kenan? Ina ji ina gani kun hana ni auren Yah Abdul saboda baku ƙauna ta daga ke har munafukar yayar ki dake nuna min son ƙarya, ita kanta Hadizan wanne irin tarko ne ban ɗana mata ba akan na kusance ta......amma yarinyar nan tana tsallakewa, ina son ta, ina tsananin son kasancewa da ita, amma kun aura mata Yah Abdul, ku aura min shi mana na shiga rayuwar su dikan su tinda ina son su? Idan kika yi alƙawarin aura min shi zan zauna babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login