Showing 99001 words to 102000 words out of 276165 words
Chapter 34 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
zai aura,ganin yanda Abdussabour ke kallon Saddiqa ne a kyautar da zai bata ta qarshe ne ya motsa kishin Munir har ya haɗe fuska kamar be taɓa dariya ba.
Abdussabour kuwa wani irin kallo yake yi mata na alfahari da kuma tausayin kanshi da yayi asarar mace nagartacciya kamar ta, murmushi yayi mata sannan ya sanya hannu a aljihun shi ya zaro wani box qarami ya ɗora mata a saman kyautar da ya bata, hotuna aka yi musu sosai,kasa jurewa Munir yayi ya miqe ya isa wajen ya karb'i kyautar tare da sakar wa Saddiqa murmushi mai hoton da ya d'akko ya dinga yi musu hotuna kamar dama jiran hakan yake ta faru,har suka isa wajen zaman su mai hoton nan be daina daukan su hoto ba, Munir ne ya riqe mata dika kyaututtukan ta wanda yaji kamar yayi wurgi da jan box ɗin dake saman kyaututtukan nata amma ya daure, bayan an kammala dik wani abu da za a gabatar a wajen aka hau rabon take away su kuma ɗalibai masu sauka suka hau rufe taro da addu'o'i cikin waqe, a haka taro ya tashi kowa na cike da farin ciki, banda Abdul da ya rasa ina zai saka ran shi, zuciyar shi cike take da tsananin son Mommy wanda a kwanakin nan yake jin kamar ana hura masa wuta akan son nata, ya kasa sanar da kowa saboda ya gama yanke shawara ba zai auri kowa a cikin Mommy da Billy ba, ya yarda soyayyar ta tayi ajalin sa akan ya aure ta tinda ba ita ce Saddiqa ba, motar shi ya nufa dan tafiya gida ,fadawan dake a masarautar su na take masa baya, cikin wani irin taku Mommy ta yi saurin riga shi isa wajen motar tasu, ana buɗe masa inda zai zauna tayi wuf ta buɗe ɗayan bangaren ta afka itama, Abdul na zama ta cire gilashin idanun ta idon su ya sarqe a na juna, nan take masifar da ya d'akko zai yi mata ta maqale, rasa me zai ce mata yayi sai kawai ya kafe ta da kallo, hawaye ne ya fara zuba a idanun mommy idon ta yayi jawur saboda tsananin yanda take jin zafin yanda yake nuna qin ta a zahiri bayan ta san yana son ta a cikin zuciyar shi, buɗe baki tayi baki na rawa ta fara gabatar da abinda Innoh ta koya mata, cikin rawar murya tace,
"Yah Abdul dan Allah gobe ka sa a aiko gidan mu neman aure na, ka sani ina son ka kaima kuma kana so na, mu manta da komai ka manta da laifin da na aikata maka ka aure ni, idan baka aure ni ba zan iya rasa raina, Yah Abdul ina son ka, ina yi maka son da ban taɓa yi wa wani mahaluqi ba, dan Allah ka qarasa ladan ka ka aure ni,"
Tana gama fad'in haka bata jira amsar shi ba ta fita daga motar ta maida baqin gilashin ta ta hau goge hancin ta da fuskar ta da hannun rigar ta, cikin sauri take barin harabar wajen, saidai tana zuwa inda taga Munir ya ajiye motar shi taga wayam ba motar ba kuma 'yan gidan su dika, tsaki tayi ta kama tafiya da qafa zata tafi gida, har tayi nisa tana tafiya taji mota ta tsaya a gefen ta, tana d'aga kai sai taga motar Abdul ce, nan take murmushi ya sub'uce mata, lallai maganin bokan nan yana aiki, har ya faɗa tarkon ta da wuri haka? Hamdala tayi a ranta ta buɗe motar ta shiga, babu wanda yace wa kowa komai har suka isa qofar gidan ƊAN LITI, a qofar gida suka tarar da motar Munir suna zaune da shi da Saddiqa suna hira cike da nishad'i tana nuna masa murnar ganin shi da tayi dan kuwa bata zata zai zo ba duba da yanayin aikin shi.
Mommy taji daɗin yanda Abdul ya ɗauke kan shi daga kallon su kamar be san su ba, kallon Mommy yayi yace mata,
"Sai mun yi waya ko?"
Cike da fara'a da jin daɗi tace,
"Da yaushe kenan?"
"Ina isa gida zan kirawo ki dan ban gaji da jin muryar ki ba,"
Mommy ji tayi kamar ta rungume shi dan tsananin farin ciki, a guje ta fita daga motar ta yi cikin gida tana ihun murna kamar zata tashi sama, a guje Innoh dake jiran shigar ta gidan ta fito daga d'aki ta damqe wa Mommy baki suka afka d'akin ta dan kar taje tayi b'aram-b'arama a tsakar gida.
A can waje kuwa Mommy na fita Abdul yaji kamar ya bi bayan ta, wata iriyar wutar son ta ce ta dinga ruruwa a zuciyar shi, ji yake yi idan bai aure ta ba zai iya rasa ran shi, cikin gaggawa ya bawa driver umarnin ya kai shi gida, Munir kuwa yana nan yana jiran ko ta kwana dan ya ga yanda Abdul ɗin ya dinga kallon masa mata kyale shi kawai yayi dan a cikin taro ne, yanzu kuwa ya shirya karta masa rashin mutunci ba ruwan shi da rawanin sa,sai dai ganin yanda yake yi wa Mommy abun ya d'aure musu kai daga shi har Saddiqan, sai dai babu wanda yace komai a cikin su suka ci gaba da hirar su.
A can d'akin Innoh kuwa Mommy ta gama labarta mata komai cike da murna, Ameerah kuwa kuka ta fashe da shi ta hau surutai tana fad'in,
"Ai dama ba tun yau nasan baki qauna ta ba Innoh,ni me yasa baki yi min abinda kika yi wa Mommyn ba har Abdul ya fara son ta gashi har yana fad'in zai kira ta, wato ni saboda bana baki kuɗi ko? Ga masoyina can da waccan shegiyar yarinyar a waje ni ina nan zaune kamar mara gata, Innoh kin san yanda nake ji a zuciya ta kuwa? Ji nake yi kamar zan mutu zafi qirji na yake yi min ki taimaka min nima,"
Cike da tausayawa Innoh tace,
"Ameerah dik abinda kika faɗa ba haka bane, yaron nan an kai sunan shi an yi anyi asiri ya ci shi shida matsiyaciyar tsohuwar nan abun ya faskara, shi kanshi Bokan yayi mamaki matuqa, dik da cewa ita kakar tashi an gano k'wank'waman kanta jigajigai ne baza ta tab'u ba, idan muka dage sai an yi mata asirin da zata yarda ya aure ki komai zai iya lalacewa,Ameerah ki yi amfani da jikin ki ki jawo ra'ayin shi idan ba haka ba babu wata hanya da zan iya taimaka maki da ita,"
"Nima a bani k'walin na gwada mana, idan baiyi ba sai na sake wani salon amma ba wai ki bawa 'yar so ba ni ki hana ni,"
Cike da fushi Innoh ta karb'i kwallin a hannun mommy ta wurgawa Ameerah tace,
"Gashi nan Ameerah Allah ya bada sa'a ki samo zuciyar Manniru kema ya tsani Saddiqa shikenan?"
Baabaa da ta doso d'akin hannun ta ɗauke da babban kwano da ta zubo wa Innoh da iyalan ta abinci da soyayyun naman kaji ce taji maganar da Innoh tayi ta qarshe.................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 38:
Jikin Baabaa ne ya hau wata iriyar jijjiga kamar irin ta qaurayen da ake kad'awa gangi a filin daga, ba tare da ta san sanda ta ajiye abincin ba ta nufi robar dakakken barkonon Innoh na alale ta buɗe ta damqi yaji ta sanya hannun ta a bayan ta ta nufi d'akin Innoh, Sallama tayi ta ce,
"Ameerah ke ! zo nan ki ɗauki abincin ku,"
Duk wanda ya san muryar Baabaa to tabbas ya san an samu sauyi a cikin ta, amma bahaushe yace, mai rabon shan duka sai ya sha, dan haka ba tare da tinanin komai ba Ameerah da ta gama gwagud'a kwallin sihiri ta buɗe labulen d'akin Innoh ta sako kai waje da niyyar karb'ar abinci, suna haɗa ido da Baabaa taji hankalin ta yayi mugun tashi saboda yanda taga jikin Baabaa na tsuma idanun ta sun yi jawur kamar jan yadi,juyawa ta so yi dan guduwa cikin d'aki amma kafin ta ajiye qafarta da ta d'aga Baabaa ta damqo wuyan ta ta matse ta a hammatar ta ta bankawa fuskar ta yajin nan wanda ya shiga har bakin ta da hanci da idanun ta, wani azababben ihu Ameeerah ta saki kafin daga baya jikin ta ya saki ta faɗi yaraf a wajen, Innoh ce ta fito da gudu cike da tashin hankali dan ganin abinda ke faruwa, ido huɗu suka yi da Baabaa dake tsuma tana wata iriyar zufa, katar katar Innoh ta juya da manyan duwaiwaka zata koma d'aki Baabaa ta daka tsalle ta dira a wuyan ta ta shaqe ta ta baɗe fuskar ta da barkono, Mommy da ta ga dik abinda ya faru kuwa tini ta dannawa d'akin sakata ta rufe har window jikin ta na b'ari da fidda zufar tashin hankali.
Yare Baabaa ta farayi tana nuna wa Munir da ya shigo shi da Saddiqa Innoh da Ameerah,gaba ɗaya sun kasa gane yaren da take yi dan haka sai suka hau yi mata addu'a dan aljanun nata su lafa, dik yanda Munir yaso d'aga Baabaa ya maida ta d'akin ta kasawa yayi har abun yaso bashi tsoro, Saddiqa kuwa ta duqufa wajen yi wa Baabaa addu'a taji Baabaa ta dawo yin hausa,cikin wata iriyar muryar bafulatanar da bata jin hausa Baabaa tace,
"Barni da su....ki barni da su nashe na nuna masu qarfin ikon da god'iyar mu ke dashi,"
"Ku yi hakuri Allah yana tare da masu hakuri," in ji cewar Saddiqa da ke shafewa Baabaa zufa,cikin kumfar baki da masifa Baabaa tace,
"Allah kuma baya tare da azzalumai ba, mu za a yi wa asiri? Ke kin san ko ni washeshe?"
"Allah ya baku hakuri, ku yi hakuri dan Allah,"
Ruwa Munir ya ɗebo a cup ya yi addu'a a ciki ya kafawa Baabaa a baki ta sha sannan ya shafa mata a fuska, atishawa ta dinga jerowa tana kumawa har sai da tayi sama da biyar kafin ta miqe tsaye kamar wata tsuntsuwa, waiqe waige ta farayi tana neman madoki, Saddiqa da Munir ne suka ja ta d'akin ta suna ta bata hakuri, Innoh da Ameerah kuwa na nan sun gigice sun rasa ina za su nufa su sami ruwan wanke idanun su.
Cikin kuka Innoh tace,
"Yaya kiwa Allah kiyi hakuri kar ki mamaye ni zuciya ta zata buga saboda tsoro ban san ta ina kike ba, ke kuma dan uban ki ba zaki samo min ruwa na wanke ido na ba?"
Ta juya inda take jiyo muryar Saddiqa ta faɗa haɗe da daka mata tsawa, a guje Baabaa ta kwace daga riqon da Munir yayi mata ta yi bakin rijiya ta ɗauke guga ta yi d'akin ta ta boye, fitowa tayi hannun ta riqe da wayar ta yau ko wanda zai kira mata Alhaji Baban gidan nata bata nema ba da kanta ta danna wayar, jikokin ta dake tsaye suna kallon ikon Allah sai qunshe dariyar ganin dirircewar Innoh da Ameerah suke yi,dik cikin su babu wanda yayi yunqurin taimaka musu da ruwa.
Wayar bata jima tana ringing ba Alhaji Baban gida ya ɗauka cike da fara'a yana taya Baabaa murna akan saukar da Saddiqa tayi, katse shi tayi da faɗin,
"Baban gida wace ta haife ka?"
Ji yayi gaban shi ya yanke ya faɗi, a tsorace ya furta,
"Kece mana Baabaa me ya faru?"
"To idan dai ka tabbatar da ni ce uwar da na ɗauki cikin ka watanni tara da kwanaki, na haife ka, sannan na rene ka na shayar da kai mamana to ka tabbata gobe kana cikin qauyen Ba mugu da kud'in auren Manniru da Saddiqa,sannan ka faɗa wa uwar Manniru ta haɗa gagarumin shagalin bikin tarbar surukar ta nan ba da jimawa ba,"
Baabaa na gama faɗar abinda zata faɗa ta kashe wayar ta ta koma d'akin ta ta zauna ta buga tagumi sai hawaye suka fara zuba a idanun ta na tsananin tausayin Saddiqa da kewar Yadikon Sule,cikin kuka tace,
"Inshaa Allahu in dai ina raye 'yar ki ba zata wulaqanta ba, zan tsaya tsayin daka dan na inganta rayuwar ta tinda ubanta bashi da amfani an shanye shi,"
Saddiqa da ta gama jin maganganun Baabaa sai ta duqa a gaban Baabaa ta kwantar da kan ta a 'yar siririyar cinyar Baabaa tana share hawaye tace,
"Baabaa na gode da soyayyar da kike nuna min, yanda kike kula da ni da qanina Allah ya kula da zuri'ar ki kar su yi mummunan qarshe,na gode Baabaa,"
Munir ne ya shiga yana murmushi yace,
"Ah ah, wai me bayin Allahn nan ke yi ne aka ware Munir bawan Allah ? Baabaa yunwa muke ji a zuba mana abinci kwano ɗaya da gimbiya ta mu ci,"
Share hawaye Baabaa tayi tana murmushi tace,
"Anqi zuba maka abinci kwano ɗaya da itan mara kunya kawai,"
"Ai kuwa gwanda ma ki haɗa mana dan ko baki haɗa ba mu zamu haɗe abun mu ko ya kika ce MANSEEQ ɗina ?"
Wani iri Saddiqa taji a jikin ta saboda yanda ya furta sunan da ta tabbata yayi amfani da sunayen su ne ya haɗe su waje ɗaya ya fad'e su, cikin sauri ta miqe ta bar d'akin tana murmushi, tana fita tsakar gida fara'ar ta ta ɗauke dan ganin Ɗan liti a tsakar gida yana zubawa Innoh ruwa ita da Ameerah suna wanke fuskar su suna kuka,suna haɗa ido hantar cikin ta ta kad'a domin kuwa idanun Ɗan liti har wani ja suke yi saboda ɓacin rai, sum-sum-sum ta bi gefen rumfar d'akunan nasu ta shige d'akin Yadikon ta, yana gama zuba musu ruwan Innoh ta d'ebi gishiri ta lasa ta baiwa Ameerah wai ko yajin zai musu sauqi,majina kuwa haka suka dinga tararar da ita kamar an buɗe pampo,cike da b'acin rai Ɗan liti yace,
"Me ya faru a gidan yau kuma? Tinda ku dai kun riqe qur'ani kun yi rantsuwa ba za a zauna lafiya a gidan nan ba, ina can bakin sana'a ta Baban Gida ya kira ni yace na zo gida babu lafiya,"
Kuka Innoh ta fashe da shi zata hau bayani Baabaa ta riga ta,
"Dole gida ya kasance cikin rashin zaman lafiya tinda ka gaza a matsayin ka na miji, ka gaza a matsayin ka na uba, kuma ka gaza a matsayin ka na qanin miji na da na ɗora ran koda bani da 'ya'ya Ɗanli zaka kula da ni har bayan raina ba zaka gajiya ba, sai gashi kana ta nuna min banda mahimmanci a rayuwar ka,ko da yake me zai b'ata raina bayan wanda suka zama wajibin ka ma baka kula da su ba, idan da asiri har da halin ka ma Ɗanli,yau fa yarinyar nan ke saukar alqur'ani amma baka je ba, kowa uban ta yaje uwar ta taje, wadda duk ka ga waɗannan biyun basu je musu ba to fa ɗaya ya mutu a cikin su, amma saboda mace ta bada ruhin ka ma rauhanai sun fitsare shi, shine ka qi zuwa bayan kasan uwar ta ta rasu, da babu ni shikenan sai ya zamo babu wanda zai je taya ta farin cikin wannan ranar kenan?"
Jikin Ɗan liti yayi mugun sanyi, shi kan shi yana jin babu daɗi akan yanda yake yi wa su Saddiqa, amma a zahiri ko sunan su baya so a faɗa a gaban shi tsabar tsanar su da yake ji na d'awainiya da shi,Innoh ce ta buɗe baki zata yi magana Baabaa tace,
"Wa ya halicce ki Innoh?"
Cikin sauri Innoh tace,
"Allah,"
"To idan kin raina mahaliccin ki yau ki yi wata maganar banza anan ki sha mamaki,idan kin saba da shirka da raina mijin ki ni ba zan ɗauka ba ko babu aljanu qarshen ki zan gani cikin salama, kai kuma Ɗanli na kirawo Baban Gida nace yazo gobe, ina so ka shaida a goben za a d'aura wa Manniru da Saddiqa aure idan kuma zaka nuna wa matar ka ni ba kowa bace a wajen ka ban isa da kai ba balle abinda ka haifa bismillah,"
"Dama wake son haɗa zuri'a dake? In banda Ameerah ma data nace ai kema kin san qarya ne ni da kaina na haɗa zuri'a da dangin aljanu dangin bala'i da masifa,"
Zabura Baabaa tayi zata yi kan Innoh, Innoh ta bi bayan Ɗan liti ta tsaya tana haki, gaba ɗaya sai ya zama wani ɗan tsurut a gaban ta, kusan ita ta b'oye shi dan kuwa ba shi ya b'oye ta ba.
Munir ne ya kama hannun Baabaa yace,
"Dan Allah Baabaa ya isa haka, ku wai baku gajiya ne? Ku dinga haƙuri da junan ku please rayuwar nan dika nawa take ne?"
"Dubu take dan uwar ka Saliha, nace dubu take sake ni kafin na bige ka kai ma,"
Dariya yayi ya sake riqe ta suka shiga d'aki tana ta sababi da cin alwashi kala-kala akan Innoh da zuri'ar ta idan basu fita a hanyar ta da Saddiqa ba.
Duk wannan tashin hankalin da ake yi Mommy ta gaji da zama a d'akin a waje ɗaya sai ta kwanta a gadon Innoh dan ta huta daga firgici da tsoron da ta shiga a haka bacci ya ɗauke ta cike da mafarkai na tashin hankali da ban tsoro, wayar ta na ta ringing bata san tana yi ba balle ta amsa.
***************************
Abdussaboor ne riqe da wayar shi a hannu yana ta kaiwa da komowa a d'akin shi hankali tashe saboda qin amsa wayar shi da Mommy tayi ba, nan take zuciyar shi ta bashi wataqila taqi amsawa ne saboda abubuwan da ya yi mata a baya ya nuna baya son ta ba kuma ya qaunar ta zamo matar auren shi,cikin sauri ya ajiye wayar ya sanya rigar shi da ya cire ya zira takalmin shi ya nufi d'akin Innah Laminde.
Zaune take a qasa Billy na tsefe mata kai tana so tayi mata kitso a cewar ta kan ya tsufa tana buqatar a wanke mata shi a gyara,cike da jin daɗi Innah Laminde ta amince dan kuwa bata da 'ya mace dika yaran ta maza ne sai yaran kishiyoyin ta mata guda uku.
A hargitse ya shiga d'akin cikin damuwa ya furta,
"Innah kin ga ina ta kiran wayar ta taqi ɗauka ko? Dan Allah Innah kiyi wa mai martaba magana a aura min ita idan ba haka ba zan iya rasa raina, ina son ta, na amince ina ina qaunar ta Innah,"
Cike da jin daɗi Innah Laminde ta d'aure kanta da d'ankwalin atampar dake jikin ta