Showing 36001 words to 39000 words out of 276165 words

Chapter 13 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

daudu ne Hajiyar taki? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na shiga uku ni Hadiza ina na kawo kai na?"

Cakk Hajiya K'waisa ta tsaya daga hawa benen da take yi, ta juya cikin fari tace,

"Rasss ! Ragasss namiji ne ni a da, amma yanzu ni macece kuma kin ji suna na K'waisan alheri, kar ki kuskura ko da gigin wasa na sake jin kalmar Kai ko namiji a bakin ki kin kuma danganta ni da ita,idan haka ta kasance ki tabbata kin kori kan ki daga gidan nan da kan ki, idan kuma kina ganin bazaki zauna ki ci azziqin dan hamsin ba ga hanya nan a buɗe take ba wanda ya riqe ki,abu ɗaya nake nema a wajen ki, wannan abun kuwa baya wuce loyalty, na tsani cin amana ko yaɗa sirri na a waje,bana son cin amana na faɗa maki na sake maimaita maki,kin ganni nan mutanen da na salwantar wa da rayuwa sakamakon cin amana ta da suka yi suna da yawa, ki bincika da kyau zaki sha labari, domin shi labarin duniya baya b'uya,"

Hajiya K'waisa na kai wa nan a maganganun ta ta haye sama cikin takun isa da qasaita, ta na shiga d'aki direct wanka ta wuce.

Mommy kuwa na nan zufa na karyo mata saboda abun ya zo mata a bazata, bata taɓa tsammani ko zaton matar da ta gani da qirji irin na mata da mazaunai na mata sak ba wai namiji ce,nan take ta juya ta kama hannayen Billy tace,

"To shi maman da ke qirjin ta da mazaunan da nake ganin ta a manne a fatar ta kamar nata ina suke?"

Dariya sosai Billy tayi kafin tace,

"Siddabaru ne abun ba zaki gane ba, ke dai ki yi kawai abinda ta umarce ki da shi, abinda be shafe ki ba kar ki tsoma kan ki a cikin shi,ki ci arziqi ki bar arziqi a mazaunin sa,sannan kema ki zage ki nemi arziqi da abinda Allah ya hore miki, ni yanzu da ki ka ganni gobe tafiya zan yi zuwa South Africa ni da wani Alhaji da aka haɗa ni da shi jiya a live ɗin mu na TikTok, zan tafi zan barki da su Sallau duk abinda kike so ki yi musu magana kafin na dawo,idan kuma ba abinda ya shafe su bane ki sami Hajiyata ki yi mata magana, kamar yanda ta faɗa maki, kar ganganci ko sub'ul da baka ya sa ki kira ta da sunan namiji, idan ki ka yi haka sai dai mu haɗu a garin BA MUGU A GIDAN ƊAN LITI,"

Wani yawu mommy ta had'iya mai d'umi sannan tace,

"Inshaa Allahu zan kiyaye,amma.."

"Babu amma a cikin wannan maganar,idan kin ji jin ya amfane ki,indan kika saɓa zaki ga ba daidaiba kema"

Wunin ranar haka Mommy ta yi shi sukuku, dan a zaton ta zata kasance cikin farin ciki da murna a duk ranar da ta mallaki sabuwar waya mai kyau da tsada kamar ta hannun ta, sannan ta gan ta cikin kowanne account na social media tsundum, sai gashi a yau an buɗe mata kowanne account da sabon sunan da take jin anya bata jefa kan ta cikin tsaka mai wuya ba, anya ba zata juya ba tun kafin rayuwar ta ta sauya? Tagumin da ta zabga Billy ta janye mata tace,

"Wai ni tunanin me kike yi ne haka ina ta yi miki magana baki jin me nake faɗa? Nace sunan ya yi miki?"

Sake leqa wayar tayi ta ga an rubuta Sweet H, sai ta yi yaqe tace,

"Eh ya yi, amma Maman Fadwa da nake amfani da shi fa?"

"B'ace wa zata yi a neme ta a rasa, yanzu ke ba qaramar yarinya bace da zaki na b'uya a bayan sunan tsofaffi kin gane, wannan sunan shi zai jawo maki masoya a irin duniyar mu, duk rintsi duk wuya kar ki sanar da kowa sunan ki na asali kar ki manta a bariki ba a yarda da kowa, idan aka matsa da tambayar ki me H ke nufi kice musu Heart ne"

Gyad'a kai mommy tayi sannan, Billy tace,

"Ki shirya da dare za a zo a yi maki hotunan da zaki fara sakawa a social media accounts ɗin ki da short videos haka"

"Gidan hoto zamu je?"

"Ah ah, mu muna da komai a gidan nan da muke da buk'ata,idan lokacin ya yi zan zo na kai ki da kai na"

Daga nan Billy ta tafi d'akin ta ta bar Mommy cikin zullumi da fargaba, duk wannan abubuwan basu ta zata zata tarar ba a birni, da fari ta yi farin ciki da maganar samun kuɗin da zata yi ko da kuwa ta hanyar karuwanci ne ba zata damu ba in dai zata yi kuɗi,amma ganin Hajiya K'waisa a matsayin namijin da ya juye ya koma mace kuma yake da saurayi namiji sai ya kashe mata jiki, tabbas ta sani zina haramun ce, amma ace tana huld'a da mutumin da ta tabbatar da maza 'yan uwan shi na amfani da shi ya kashe mata jiki, anya za ta iya ci gaba da wannan rayuwar kuwa?



**********************


Baabaa ce zaune ta na hira da Baban gida ta waya yana sanar mata da cewar Munir ya samu nasarar kammala karatun shi ya yi bautar qasar shi ya gama lafiya,a yanzu bashi da burin da ya wuce na ya zo garin Ba mugu ya ga dangin mahaifin shi su ganshi suma kafin ya kammala hutun shi ya koma Abujan ya kama aikin gwamnati, cikin jin daɗi Baabaa ta hau murna tana faɗin,

"Allah ya kawo shi lafiya, zan kuwa sa yara su buɗe gidan ku a share shi tsaff a gyara saboda kar ya zo ya tadda waje da datti,"

'Ah ah Baabaa shi kaɗai zai zo bana so a bar shi a gida shi kaɗai ba wani babba, Munir baya jin magana Baabaa sai dai a yi masa addu'a kawai, ya zauna a nan d'akin samarin gidan kawai idan ya zo,'

"Su waye samarin? Jikana ba zai takura ba ka ji na faɗa maka, uban sa na da muhallin da zai zauna a ciki ba zai je ana kara shi ana yi masa wulakanci ba, "

Murmushi mai sauti Baban gida ya yi da alama har yanzu Baabaa da Innoh suna buga 'yar tsama kenan a tsakanin su,

'To Baabaa duk yanda ki ka ce haka za a yi'

Suna kammala waya kuwa ta fita tsakar gida ta k'wala wa jikokin ta kira ta basu makullin gidan Alhaji Baban gida ta ce suje su share gidan tasss su gyara shi, Innoh dake tsakar gida ta na zaune ta na wanki ne ta ji abinda Baabaa tace, nan da nan ta miqe ta na shewa tace,

"Ahayyyee Allah na gode maka, wai dan tsabar fariya da qifad'i dan za a yi baqo sai an fito ana hura hanci ana bada umarnin sharar gida a gaban mutane, kaiii Allah ya nuna mana ranar da zamu fara ruwan nera a gidan nan muma mu huce takaicin gori, namu arziqin sai ya sha banban da na su oo, oon da ba a kama suna,"

Baabaa na jin ta ta yi banza da ita bata kula ta ba, Innoh kuwa ganin babu wanda ya kula tane ya sanya ta komawa ta zauna ta na sake baza kunnen ta dan ta ji shin Baban gidan ne zai zo da iyalan sa ko kuma waye zai zo? Shiru-shiru bata sake jin komai ba daga wajen Baabaa sai kawai ta qarasa wankin ta ta shanya ta zari mayafin ta ta nufi gidan qawar ta Ramma, dan ta san Yadiko ba biye mata za ta yi ba su yi gulmar Baabaa.

A hanyar ta ta zuwa gidan Ramma ne ta ga Saddiqa na dawowa daga makarantar boko,tsaki ta ja mai tsaho sannan tace,

"Iska na wahal da mai kayan kara, a yi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, ke kenan kina nan tafe cikin rana da zufa, ruwa da sanyi da Sunan kin tafi makaranta, haka zaki ƙare a gama cin wahalar a yi aure ba a mori karatun ba, ga yaran arziqi can sun bazama nema wa iyayen su na kai ke kina nan kina fama da takarda,"

Sai da ta gama ciwa Saddiqa mutunci tass a hanya, yarinyar ta duqa ta gaishe ta, ko amsa mata bata yi ba ta buga tsaki ta wuce inda zata je,cikin sanyin jiki Saddiqa ta wuce gida ranta babu daɗi game da maganganun da Innoh ta faɗa mata, ko da ta isa gida ta tarar da Yadiko na matsar quli duk sai ta ji maganganun Innoh na dawo mata akan ta, anya kuwa ba da gaske asarar lokacin ta take yi ba ba lallai a barta ta cika burin ta na zama likita ba za a yi mata aure? Ga mahaifiyar ta na ta wahala akan nema masu kuɗi ita tana can ta na bin rana da sunan neman ilimi.

Yadiko ce ta kalli Saddiqa ta ga yanda tun shigar ta gidan jikin ta yake a mace kuma a sake, dan haka da hikima da dabara irin ta iyaye masu dabara ta ja yarinyar a jiki har sai da ta sanar da ita abinda ya faru, ran ta ya ɓaci sosai amma sai ta danne, dan kuwa faɗan nasu ne ita da Innoh ba na Saddiqa ba, albarka ta sanya mata sosai sannan tace,

"Kar ki damu da dik abinda kowa zai ce game da neman ilimin da kike yi, watarana hakan zai zame maki tarihi mai daɗi,domin kuwa da izinin Allah zaki mori ilimin da kike nema wasu ma zasu amfana dake a rayuwa,musamman waɗanda suke ganin ba zaki yi nasara ba a rayuwar ki, sannan shi aure ana tsaka da karatu ba aibu bane a wajen kowacce mace, ana iya ci gaba da karatu kuma ana da aure har ma da yara,babban abinda ake buqata ya zamana mutum na da kyakkyawar niyya da kuma son abinda yake yi,ta haka ne ake samun cin nasara,"

Murmushi Saddiqa ta yi sannan ta jingina da mahaifiyar ta suna ci gaba da hirar su cikin jin daɗi da nishad'i.

Innoh bata tashi dawowa ba sai yamma, ta na shiga gidan ko mayafi bata cire ba Yadiko ta tare ta cike da masifa tace,

"Keee Innoh ki saurare ni da kyau ki ji ! Daga yau sai yau kar ki kuskura ki ƙara tarar yarinyata a hanya ko a cikin gidan nan ki ce zaki na gaya mata ya goben ta zata kasance,babu wanda ya yi wa naki yaran wannan mugun fatan dan haka kar ki sake yi wa nawa yaran ya ishe ki haka"

Baki sake Innoh ke kallon Yadiko wadda ke jijjiga ta na jin zata iya aikata komai saboda kare martabar yaran ta, shewa Innoh ta yi sannan tace,

"Sannu kaza me 'ya'ya, ina abun yake wai faso a ido?  Dan kin samu ma na bawa 'yar taki shawara ta dena wahal da kan ta akan karatun da ba morar shi zata yi ba shine har zaki tare ni da zancen banza? To ta sa himma ta yi ta karatun shirmen da ta ɗauka a wata tsiyar ta ga me zai tsinana mata a rayuwa"

"Alhamdulillahi yarana karatu suke yi ba yawon tazubar ba,"

Cikin qanqance ido Innoh tace,

"Yaran wa ke yawon ta zubar ɗin?,"

"Yaran wanda ya tsargu"

Kafin Yadiko ta rufe bakin ta Innoh ta sab'e ta sama ta doka da qasa ta bi ta ta taushe, nan da nan dambe ya kacame a tsakanin su, Saddiqa kuwa ganin Yadiko a qasa an danne ta ana kilar ta ne ya sanya ta rusa kuka tana kiran sunan mahaifiyarta tare da roqon Innoh ta d'aga ta,Innoh na ji ta yi banza da roqon da Saddiqa ke yi mata ta ci gaba da jibgar Yadiko da ke ta qoqarin kare kan ta.

Baabaa ce ta rugo a guje da wata mulmulalliya kuma doguwar tab'arya irin ta masu dakan hatsin nan, cikin ihu da kururuwa take faɗin,

"Allaaaahuuuu Akbarrrr Allah ka bani ikon yin jahadi, ko na kashe ko a kashe ni."

Kamar an ce Innoh ta waiga kuwa ta na juyawa ta ga Baabaa ta yo kan ta da tab'aryar casar hatsi a guje,da ssuri ta d'aga Yadiko zanin ta na k'wance wa ta kwasa a guje zata shiga d'akin ta tana ihu, shigowar Ɗan liti gidan ya yi dai-dai da samun nasarar da Baabaa ta yi na shemawa Innoh tab'arya a gadon baya, Yadiko ce ta yi saurin zuwa zata karb'i tab'aryar saboda kar Baabaa ta yi kisan kai, cikin kumfar baki Baabaa ta ce,

"Barni Yadikon Sule wannan fad'an ba naki bane, ba ke na shigarwa ba, dama nima da tamu a qasa, kin zata a banza ɗazu na yi miki shiru da kina cin zarafi na?"

Ihun Innoh ne ya karad'e gidan, dan kuwa ba kaɗan ba Baabaa ta sami gadon bayanta da tab'aryar nan, cikin kuka take faɗin,

"Malam kana tsaye ka na ganin wannan mahaukaciyar matar za ta illata ni? Saboda an ga 'ya'yana ba sa nan shi yasa za ku kashe ni ko?"

Duk wani qarfi Yadiko ta saka dan k'watar tab'arya a hannun Baabaa ta kasa, sai da suka haɗu su uku har Ɗan liti da Saddiqa sannan aka samu nasarar karɓe tab'aryar daga hannun siriryar tsohuwar, banda maida numfashi babu abinda Ɗan liti yake yi, cikin wata iriyar muryar mai ban tausayi yace,

"Anya mutane na tara a gidan nan kuwa? Anya ba ku zaku yi ajali na ba? Ace na fita tun safe ina fama da qarfen nasara mara tabbas a wajen masu gyara a gama gyarawa na saka fetur na yawata mai ya qone na dawo ban samo ko taro ba na zo na iske irin wannan tashin hankalin?"

Saddiqa ce ta zube a gaban Ɗan liti tana kuka ta ce,

"Dan Allah Baba ka yi hakuri wannan abun da ya faru duk laifi na ne, da ban sanar da Umman mu abinda Innoh tace ba da duk haka bata faru ba"

Ba tare da Ɗan liti ya sake cewa kowa komai ba ya wuce d'akin Yadiko dan kuwa ita ke da girki a ranar, waje ya samu ya kwanta ya na jinyar zuciyar shi a bisa ɓacin ran da iyalan nashi suka sanya shi a ciki.

***************

A can gidan Hajiya K'waisa kuwa Mommy ce a wani d'aki wanda za a iya kiran shi da photo studio, dan kuwa babu abinda babu na ɗaukan hotuna da kuma kayan k'walliya da na sakawa, Mommy ce zaune a wata kujera ta alfarma ta ci ado da tufafin da za a iya kiran su da da babu gwanda ba daɗi, Hajiya K'waisa ce sanye cikin wani tsadadden leshi da ya sha ado da wata uwar sarqar zinare gashin nan yana tab'o mazaunan ta sai nuna wa Mommy kala-kalar zama da kwanciyar da zata yi duk dan daukan hoto............


*Toooo muna nan muna zuba ido muga inda wannan rayuwar zata kai ki Mommy, ko in ce Sweet H*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI






RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH











PAGE 14:










Hotuna aka ɗauki mommy na ɗaukar magana, domin kuwa ba wanda zai kalli hotunan nan bai sake kallo ba,duk mai hankalin da ya kalla abinda zai fara tunani shine,shin wannan musulma ce kuwa?Wanda kuma duniyar ke yi musu daɗin zama kuwa za su ce ta yi kyau, dan kuwa kaff hotunan babu na yarwa, wasu ta banqaro qirji an buɗe wani sashen na qirjin nata, wasu cinyoyin ta gaba ɗaya ta kwaye waje,wasu kuma kafad'ar ta ta buɗe ta juya baya hips ɗin ta suka bayyana da kyau yanda kowa zai ga shape ɗin da take da shi, ita kan ta da ta gan su rikicewa ta yi da murna ta tafi da gudu ta rungume Hajiya K'waisa ta na godiya, cikin wata 'yar qara kamar an matse mage yace,

"Washhh Allah na qashin kafad'a ta, ke sake ni ni kar ki jirkicen qashin allon kafad'a ya kalli yamma na dena sallah, na samu ina gaida ubangiji ina neman tuba ki yi min sanadin tsiya,"

Dariya Mommy tayi sosai sannan tace,

"A gaskiya dole na gode mak...maki Hajiya,Allah ya sa ki fi haka ki yi ta taimakon mu,"

"Ameeen, amma ban taɓa jin wani ya yi min irin addu'ar nan ba,kowa so yake ya zama kamar ni ko ya fi ni,ke me yasa baki da burin ki fini sai ma ki ke fatan na fi haka na yi ta taimakon ki?"

"Ai shi nagaba idan yayi gaba baka fatan ya yi baya, sai dai ka yi masa addu'ar samun ɗaukaka kai kuma taka zata same ka a duk inda ka ke,"

"Kema kin ce wani abu, ahhh ai dole ki samu abin faɗa 'yannan Allah ya hore maki shafataini har na mutum uku gine a fuskar ki? Ba wannan bama, a gaskiya na yaba da qoqarin ki na ganin yanda kika yi hakuri da sanya facemask sannan ki ke gyara labb'an ki, amma fa dole ki qara yin aiki akan hakan har yanzu be isa ba, ita waccan gobe da sassafe zasu yi tafiya, ba za a sanya ta a lissafi ba yanzu zan tura maki wasu videos ki kalla dan ki ga yanda ake sarrafa irin wannan leb'unan naki domin kuwa kadara ce,ko baki da labarin har allurai muke zuwa a yi mana dan su yi girma irin naki? Ai yanzu su ake yayi a wajen irin mu, bari ki ga dai a gama uploading hotunan ki a social media handles ɗin ki sai mu yi waccan maganar"

Mamaki ne sosai ya kama mommy, nan take ta gane komai Allah ya halitta a jikin ɗan adam yana da mahimmanci da amfani a jikin shi, ta yaya za a ce mutum ya kai kan shi da kan shi a yi masa allura a qara masa girman leb'e ya yi suntumtum kamar an ɗora maka su?

Har aka gama ɗora hotunan a duk inda ya dace Mommy bata sani ba ma saboda tana can ta faɗa duniyar tunani a dik daqiqa ɗaya da take qarawa tare da mutanen nan sabon abu take ji da gani a rayuwar ta da take ganin ta waye, ashe ma dai bata san komai ba har yanzu,shin ɗazu da ta yi wa Hajiya K'waisa fatan ci gaba a irin hakar nan dama ya kamata a yi ta ci gaba a sab'on Allah babu neman yafiyar Allah da fatan a dena aikata zunubai idan an kai wani limit?

"Ke lafiyar ki kika b'ata shiru ana ta harkokin arziqi?"

Murmushi ta yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login