Showing 162001 words to 165000 words out of 276165 words
Chapter 55 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
yi,"
Murmushi tayi tana sunne kanta tare da satar kallon shi, a haka ta wanke abinda suka ɓata ta hau kallon kitchen ɗin da yanda aka shirya mata kayan da bata san wanda yayi mata su ba, sai dai tafi bada zargin Abbah ne yayi mata komai da taimakon Ummi,a can gefe ta hango yanda aka jera mata wanda dangin mahaifiyar ta suka yi mata cikin tsari gwanin burgewa, har da su ƙwarya mai zane da fai-fai.
Hamdala ta dinga yi a ranta suka koma ɗaki ta sake gyara ko ina ta kunna turaren wutar HUMKAM da ta gani a ɗakin da burner,nan da nan ƙamshin turaren wutar ya dinga saukar musu da wani yanayi na natsuwa da annashuwa na musamman.
Parlour suka dawo Saddiqa ta ninke rigar shi ta ajiye a kujera suka samu waje suka zauna ya kunna masu kallo, manne suke da juna kamar su shige jikin junan su saboda so da kulawa, gani nayi ana kallo Munir gaba ɗaya hankalin shi baya kan TV ya koma kan amaryar shi yana bata kulawa ta musamman, tin ina iya kallon su har abun ya girmi tunanin yara sai na basu waje na koma ƙauyen Ba mugu.
***********************
Su Abbe sun koma gida cike da arziqi da kayan arziqi kala-kala a washegarin ranar da aka kai Saddiqa d'akin ta, dan kuwa ko sallama basu koma sun yi mata ba Ummi tace ayi hakuri abar ango da amarya su huta duba da cewa kowa yaje yaga gidan bata ga dalilin yi musu sintiri ba da safe,dan haka a gidan Baabaa suka kwana za su koma gidajen su da safe, Baabaa kuwa bata ji ƙyashi ko haushin ɗebar wa su Innoh komai ba, hatta da robobi da aka raba a wajen bikin sai da Baabaa ta ɗebar musu har Ameerah da Mommy,ƙullin Sule kuwa daban ne da na kowa,nan da nan Innoh ta sakko daga dokin rashin kunyar da take zubawa Baabaa ta hau yashe baki.
Cikin yada habaici Abbe tace,
"Haka dai aka iya, ƙuda wajen ƙwadayi aka mace ai."
Ko kula ta Innoh bata yi ba ta kawwame kan kayan ta ta wuce d'akin ta,sai da ta shiga ta ajiye komai sannan ta leƙo da kan ta ta labule tace,
"Kan ki ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya yace wanka na nake yi, idan baki san wani abu ba yau ki sani, shi raba arne da makami ibada ne, kuma kayan nan da kuka bamu ai ya zama dole ku bayar ne tinda uban ta ya kashe kud'in shi akan ta,nima kuma dole a bani kaso na na ladan riƙo a matsayi na na matar uban ta."
Wani kallo shalele da bata magana ta yiwa Innoh na takaici,cikin saurin maganar da take dashi tace,
"Ke mara mutunci ! Ke har kina da abun cewa a bangaren riƙon Saddiqa? Ke wacece a cikin dangin mu kaff? Ki jira ki sha mamakin abinda zai biyo baya akan iskancin nan da kike yi wa mutane, ki rubuta ki ajiye sai mun baki mamaki, koni nan Autar Baabaa na girme ki amma haka kike rufe ido ki dinga zagin uwar mu ko mu kammu,an faɗa maki tsoron ki muke ji? Ki kiyayi zuwa rafi da tulu Innoh saboda ina matuƙar jiye maki fashewar shi baki shirya wa hakan ba."
"Kullum ai cikin shan mamakin ku dama nake ni ai? To hali ne aka tsotso kala-kala kunga kuwa dole....."
Wata mahangurɓa Shalele ta sakarwa Innoh a baki,ta bi ta a guje d'akin nata tana ihu, Innoh ma kwasa tayi da gudu tana ihu ta na ci gaba da zagin Baabaa,dika yaran Baabaa basu da jiki kamar ta, Alhaji Baban Gida ne kawai yake da ƴar ƙiba irin ta hutu da jin daɗi.
Wani irin yare Shalele take yi bakin ta na kumfa tana dukan Innoh a ka,banda salatin Innoh baka jin komai a ɗakin,Abbe na bakin ƙofa tana tiƙar dariya, dama babban burin ta a rayuwa watarana Innoh ta fusata Shalelen Baabaa mara magana da son hayaniya,ta tabbata dik sanda haka ta faru ba da ita za a yi faɗan ba da babarbariyar aljanar ta za a kacame,idan kuwa haka ta faru ko bafulatanar Baabaa bata isa raba wannan faɗan ba sai ta gaji da kanta ta sauka take bari.
Baabaa ce ta fito sanye da hijabi hannun ta riƙe da carbi,sallar walaha/dhuha take yi dama sanda suka fito kawowa Innoh kayan, sai kuma taji ana faɗa,Abbe ta kalla dake dariya tana riƙe Sule tare da faɗin,
"Kana shiga zata haɗa ku ku dika ta yi ta duka."
"Eh ni ki barni na shiga, kina ji ana dukan uwa ta amma kike dariya kin ƙi ki raba su faɗan,wannan wanne irin abu ne dan Allah?"
"Shiga Sule, ai shi mai rabon shan duka sai ya sha, maza jeka ka ceci uwar ka hannun barebarin aljanu."
Baabaa ce ta kama baki tace,
"Wooo me kuma wannan mara kunyar tayi wa Shalelena har barebarin ta suka zo?"
"Daga abun arziƙi ne tsiya ta biyo baya har tana haɗawa da zagin ki, kin kuwa san kowanne ɗan halak aka zagi iyayen shi sai ya ɗauki mataki, to fa matakin Shalele ke ɗauka."
Sule ne ya fito daga ɗakin a guje bakin shi riqe da hannayen shi bibbiyu, ihu ya kurma saboda ganin jini a hannun shi haƙorin shi ya taɓa ta gaba yaji rabin guda ɗayan ya yanke, a guje ya shiga ɗakin shi ya ɗakko madubi ya kalli bakin shi yaga yanda yayi window, shi ba hushirya ba kuma haƙorin bai gama fita ba yanke wa yayi,kuka ya fashe dashi yana faɗin,
"Shikenan na shiga uku na lalace,yanzu ta ya zan kalli baby na da wannan wawulon? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na shiga uku ni sulemanu."
Dariya Abbe ta dinga kwasa, Baabaa kuwa d'akin ta shiga taga Shalelen ta kwance a gefen Innoh da ta suma dan wuya,ita kuwa shalele sai jera atishawa take yi bakin ta zuwa rigar ta duk kumfa ne jiki,da kyar Baabaa ta d'aga ta ta k'wala wa Abbe kira tace ta kai mata ruwa,koda Abbe ta shiga ɗakin sai ta tarar da Innoh yashe a ƙasa babu zani rigar ta ta yage, kanta yayi malulu ko ta ina saboda dukan da ta sha da murfin kwanon langa,bakin ta kuwa sai jini yake fitarwa damatsan ta duk shatin haƙoran Shalele,tausayi Innoh ta dawo tana bata,ruwa suka zuba mata ta farfaɗo,ta jima bata gane a inda take ba kafin ta buɗe ido da kyau ta zuba su akan Baabaa, Abbee da Shalele suna tsaye sun zuba mata na mujiya, nan take kuwa ta koma luuuuuu ta sake sumewa........
*Innoh kika ce ba kya ji?*😂
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA:HAERMEEBRAEH ✍️✨
*SANARWA !*
*Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....*
*MAZAUNA GIDA 300*
*ƳAN ABUJA 300*
*A GARIN MU 300*
*KAI NE JARUMI 300*
*KUN MAKARO 300*
*TAUBASHI 300*
*KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻*
*IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.*
*KAR KU MANTA AKWAI KAYAN GYARAN JIKI A KANO, KADUNA DA KEBBI STATE.*
*FACE OIL*
*SKIN OIL*
*BODY SCRUB*
*HAIR OIL*
*HAIR CREAM*
*HAIR MASK*
*GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423*
PAGE 64:
Ruwa Baabaa ta sake shafa wa Innoh a ƙafafun ta ta farka tana lumshe idanu,idanun ta na sake sauka akan Shalele sai ta fashe da kuka mai tsanani har da majina,cikin lasar busasshen leb'en ta dake fitar da wata iriyar azabar zafi saboda fashewar da yayi tace,
"Ki yiwa Allah ki yafe min ba zan sake faɗar wata muguwar magana akan yaya ba, dan Allah ki yi hakuri Shalelen sarkin aljanu."
Hararar ta Shalele tayi sannan ta miƙe ta bar d'akin ba tare da ta ce komai ba, tana komawa sashen Baabaa sai ta kwanta a gado ta hau bacci abunta kamar babu abinda ya faru. Baabaa da Abbe ne suka yi wa Innoh faɗa akan abubuwan da take yi, hakuri ta basu sannan suka koma d'akin Baabaa a tare, bacci suka tarar da Shalele nayi, Abbe tace,
"To ni Baabaa zan wuce gida,gwanda ita bata da nisa da gidan nan ni kuwa kinga tafiya ta da nisa, Allah ya sake sada mu da alkhairi, Allah ya sa wannan aure mutuwa ce zata raba shi, idan Shalele ta farka ayi mata sannu, yau dai aljanun da ake faman su rabu da ita shekara da shekaru sun yi rana."
"Ke ina wata rana a wajen aljani kedai Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani kawai, Allah kuma yayi muku albarka ya saka da alkhairi, Allah ya baku ladan sada zumunci."
"Ameen Baabaa bari nazo na wuce,nasan mutanen ki anan can ana zuba ido aga ta ina zan ɓullo."
Har bakin ƙofar gida Baabaa ta raka Abbe kafin ta koma ɗakin ta, Shalele na can na ci gaba da bacci Baabaa ta haɗa mata nata kayan da alƙawarin tana tashi zata sata a gaba itama ta koma nata gidan.
Innoh kuwa da kanta ta haɗa wuta Sule na taya ta suka tafasa ruwan zafi ta gasa jikin ta musamman kanta da yayi ƙololo saboda dukan da ta sha da murfin langar tuwo.
Tinda abun nan ya faru har yamma Sule yaƙi buɗe baki balle yayi magana da kowa,ya rasa hanyar da zai bi dan haƙorin shi ya dawo dai-dai,dik wata dabara da yake ganin zata fitar dashi ya gwada haƙorin shi na nan a ɓalgace, d'aki ya shiga ya zabga tagumi hawaye na bin kuncin shi, kiran Babyn shi kuwa yana ji yana gani haka ya dinga shiga yana katsewa amma bai ɗauka ba.
Da dare abokan shashancin sa sun ji shi shiru bai hau online ba sai suka dinga kira, Sule na cikin damuwa da tashin hankali, ta yaya zai yi live aga haƙorin shi a haka? Ko dai Facebook zai koma tinda can dama rubutu yake yi a page ɗin shi tare da tallata kanshi zuwa ga matan banzan dake neman wanda zasu lalace da shi ta waya su biya shi? Yana gama ayyana hakan a ran shi ya buɗe data ya shiga Facebook dan ɗebe kewar damuwar da yake ciki.
*****************************
Watanni uku kenan da auren Mommy da Abdussaboor,soyayya ake zubawa kamar su lashe junan su,a haka hutun da Abdul ya ɗauka ya ƙare, Bilal da kan shi ya kira shi yana yi masa tuni da komawa aiki zuwa wani satin,Abdul yaso kwarai ya bar Mommy a nan yaje ya ƙara gyara musu gidan nasu amma ta kafe tace ba zai yuwu ba sai dai su wuce tare a haka, ta gaji da zaman ƙauye akwai abubuwa da dama da take son ci ko sha babu a ƙauyen, dai-dai da suturar da take sakawa dik ta raina tana so ya kai ta ta sayi wasu kamar yanda yayi mata alƙawarin haɗa lefe idan sun koma kano.
Shirye-shiryen komawa Kano ya kankama babu kama hannun yaro, gaba ɗaya Mommy tayi busy ba zama, dan haka da kyar ta samu damar ware ranar da zata kai ziyara gidan sarki tayi musu sallama, washegari kuma ta je gidan su da gidan Ameerah tayi musu nasu sallamar.
Sanye take cikin doguwar rigar da ta zama shigar ta a koda yaushe ta yafa mayafin rigar sai zuba ƙamshi take yi, yanda Mommy ta ƙara cika tayi famm a cikin rigar ne ya ƙara fito da mazaunan ta da qirjin ta, ita da kanta idan tana kallon irin shape ɗin da Allah yayi mata irin wanda mata ke kashe miliyoyin kuɗi dan su mallake shi sai ta godewa Allah.
Abdul ne ya ajiye ta a gidan nasu ya wuce fada wajen mahaifin shi ita kuma ta shiga cikin gidan bakin ta ɗauke da sallama,zaune ta tarar da su Aziza da abokan zaman Innah Laminde a tsakar gida suna hira,tabarmar da Azizah ke kai ta hau ta dafa cinyar ta suka yi wa juna murmushi,cike da sakewa mommy ta gaishe da matan sannan ta kalli Azizah tace,
"Ina Innahr mu?"
"Tana ɗaki karatu take yi."
"Allah sarki, bari na huta na shiga na gaida ta, sallama fa nazo yi muku Hajiya inshaa Allahu jibi zamu wuce kano."
Murna suka dinga taya ta da fatan alkhairi ita kuwa tana amsawa cike da jin daɗi,suna nan zaune mai aikin gidan dake daka kayan ƙamshi ta kwashe ta shiga madafi ta zuba kayan ƙamshin da ya haɗa da tafarnuwa da citta da masoro a miya ta juya, ƙamshin miyar ne ya taso ya cika tsakar gidan kamar ba miyar ƙauye ba, nan take kuwa ya daki hancin Mommy dake ta ƙoƙarin maida aman da take jin yana taso mata,dik ƙoƙarin ta na ganin ta danne aman nan da take ji ya gagara dan haka a guje ta miƙe ta nufi bakin tap ɗin tsakar gidan tana ta kwarara amai.
Guda ɗaya daga cikin mata masu kula da ɗakin Innah Laminde ce ta zabga guɗa tare da faɗin,
"Allah yayi dare gari ya waye,magajin yariman Sarkin garin Ba mugu ya bayyana da dikkan alamu,Allah ya sanya alkhairi ya raba lafiya, ayyiiiiiriiiiii."
Dik budirin da ake yi a saman kan Mommy ba wani ganewa take yi ba saboda jirin dake ɗibar ta, a hankali ta miƙe tsaye bayan ta wanke fuskar ta da bakin ta sannan ta goge fuskar da zanin da Azizah ta bata tana murmushi,jiri ne ya ɗebe ta a dai-dai lokacin da ta miƙe tsaye, cikin sauri Azizah ta kama ta suka wuce parlourn Innah Laminde dake zaune tana jin dik abubuwan da ake faɗi,ji tayi zuciyar ta tayi sanyi daga ƙin da take yi wa Mommy, murmushi tayi a lokacin da idanun ta suka sauka akan Mommy da halittar ta dik ta sauya, jinjina kai Innah Laminde tayi a ranta ta ayyana,
'Lallai babu shakka yarinyar nan da alama ciki ne da ita, Allah ya inganta mana ya bada rayayye mai albarka.'
A zahiri kuwa tashi tayi ta isa gaban Mommyn tana yi mata sannu kamar bata gane meke faruwa ba tace mata,
"Sannu Hadiza ya jikin naki?"
A hankali Mommy tace,
"Da sauƙi, lafiya ta ƙalau fa babu inda ke yi min ciwo,dama na kwana biyu ina jin irin wannan yanayin a duk sanda miya ko ruwan jellop ya tafaso,sai in yi ta amai ina jin jiri, banda haka lafiya ta ƙalau bana jin ciwon komai a a jiki na."
"Allah sarki Allah ya baki lafiya, idan kun tafi can kanon ya kai ki kiga likita."
"Haka yace dama shima."
"To Allah yasa ku koma a sa'a,Allah ya kiyaye dikkan abun ƙi, idan kun tafi dai Hadiza ki kula, ki kiyaye dikkan dokokin Allah da suka rataya akan ki, tsaida sallah, kare mutuncin auren ki da kula da mijin ki,kar ki kuskura ki sake kulla abota da duk wani wanda kika yi rayuwa dashi a baya a wannan garin gudun fad'awa cikin halaka koda kuwa Bilkisu ce tinda taƙi dawowa gaban mu,Allah yayi muku albarka."
Cike da jin kunyar abubuwan da ta aikata a baya ta amsa da,
"Ameen Innah in Allah ya yarda zan kiyaye."
Daga nan bacci mai daɗi ya ɗauki Mommy hirar da ta ci burin idan ta je su yi da Azizah bata samu ba, Sultan ma da ya shiga gidan ya tarar da ita tana bacci Innah Laminde korar shi tayi tace ya je dakin shi ba zai zauna yana kallon ta ba tana bacci,fita yayi yana mamakin yanda Innah ke nesanta tsakanin shi da Hadizan.
Tinda Mommy ta fara bacci bata farka ba sai bayan azahar, tana tashi tayi sallah a gaggauce ta hau neman abinci, har za a zubo mata shinkafa da miyar kajin da aka yi tace bata son da miya a saka mata manja da yaji taci.
Nan take Innah Laminde ta sake gasgata zargin ta na samuwar ciki a a tattare da Mommyn, nan da nan kuwa ta sa aka soya mata manja da albasa sosai aka daka mata sabon yaji mai daɗi aka zuba mata shinkafar, soyayyan nama da dambun nama Innah ta bayar aka kai mata sai zob'o mai sanyi,Mommy kuwa mamakin hidimar da Innah Laminde ke yi mata ce ta kama ta, dan kuwa idan bata manta ba tsakanin su daga gaisuwa sai tambayar iyayen ta da mai gidan shikenan, Innah Laminde bata sakar mata fuska balle har ta yi hidima da ita irin haka, rasa gane dalilin samun sauyin da take gani ne ya sanya ta ɗauke hankalin ta da tunanin ta akan nemo dalilin ta mori kayan daɗin dake gaban ta, dan kuwa bata tashi ba sai da ta ci ta ƙoshi ta gyatse sannan ta zabga hamma ta yi miƙa, lalubo wayar ta tayi ta kira Abdul tace masa idan ya gama abinda yake yaje su tafi.
Abincin Innah Laminde tasa aka sake ɗebar musu da nama sannan ta kwashe mata gorinan zob'on da suka rage tace su je da shi tinda tana so, godiya Mommy ta dinga yi tana mamakin wannan sauyi da ta samu na soyayya da kulawa daga wajen surukar ta.
Sai da aka yi sallar la'asar Abdul ya iso ya ɗauke ta bayan ya gaida iyayen nashi mata suka wuce gida. Tin a hanya Mommy ke bashi labarin sabon sauyin da ta gani a wajen surukar tata da kuma murnar da matan gidan keyi akan aman da tayi tare da hasashen su akai,murmushi yayi yace,
"To ai ke sai dai na taya ki murna tinda ko babu komai an samu daidaito a tsakanin ki da surukar ki ko? Sannan kuma ni kaina na jima ina hasashen nan duba da cewa yanzu kusan watannin ki biyu baki ga al'adar ki ba, ko kin manta ke da kanki kike yi min complain akan hakan?"
Shiru tayi tana nazari,a hankali ta kalle shi tace,
"Yanzu Baby kana ganin ciki gare ni kaima?"
"K'warai da gaske i am 99% positive,ki bari mu je kano dai na kai ki a duba min ke da kyau a tabbatar zaki ce na faɗa maki."
Ranta ne taji gaba ɗaya ya baci, hankalin ta ya tashi,cikin wani irin yanayi ta furta........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 65:
"Kai ni gidan mu zan karb'i abu wajen Innoh."
Time ya kalla a jikin motar tashi sannan ya juya ya kalle ta, ganin tayi bala'in b'ata rai alamar bata nufin wasa sai kawai ya juya kan motar tashi zuwa gidan su,sun isa gidan