Showing 12001 words to 15000 words out of 276165 words
Chapter 5 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
yara ana ta zuwa ana neman qosai na ga suna ta tafiya da kwano ba komai a ciki,Ameerah ma haka ta k'araci jarabar nacin na bata kuɗi ta siyo a gidan Meri babban kifi na hana na ce ta jira gobe idan kin yi ta ci, ince dai lafiya ki ke yau ɗin? Ba wannan ba ma dai ina ta zuba kamar kanya ga wannan, Allah ya ƙara bamu haƙurin zama, Allah kuma ya jiqan Yaaya,"
Sai ta sa bakin zaninta ta na sharar hawayen da babu su,jikin Baabaa ne ya yi sanyi kalau,ita kanta bata jin dad'in yanda suka maida gidan kamar filin yaqi yau idan ba su saida hali ba gobe za su Saida,dan haka sai ta ja kwanon alalen gaban ta ta buɗe dik da ta san ita dai ta yi suyar ƙosan ta,qamshin manja da ganin yanda aka baɗe alalen da yaji ga tumatur da albasa na kallon ta sai ya sanya yawun ta yankowa, cikin azama ta sanya 'yar wuqar da take cire dattin jikin goro ta yanki alalen ta kai bakin ta, wani yawu ne ya yi tsartuwa ya yi waje,murmushi Innoh ta yi ta tabbata tarkon ta ya kama kurciya, Baabaa na son wake sosai, shi yasa duk abinda ake yi da wake take son shi,'ya'yan ta sunyi-sunyi su hana ta soya qosai amma ta qi bari,babban ɗan ta Baban gida da ke zaune a Abuja har ya yi mata alqawarin ninka mata ribar da take samu amma ta qi ta ce ba zata bar sana'ar ta ba dan da ita aka san ta tun mahaifin shi na raye,haka suka gaji suka kyale ta ba dan sun so ba.
Innoh na nan zaune ta na ta taya Baabaa hira dan kuwa ta ci alwashin zama ta karɓi kuɗin yaran ta da na Ɗan liti a ciki ita ta san yanda za ta yi ta rage abinda zata rage ta ba wa kowa abinda ta yi niyya.
Mommy kuwa sai da ta jira Billy ta yi gayu,itama ta ɗan gyara jikin ta sannan suka fesa turarukan Billy ba ko sallama da mutanen gidan suka fita dan zuwa tasha. Tafe suke suna ta hira wadda rabin ta akan labaran da suke karantawa ne a online da shauqin da suke samu tare da kushe duk wani marubucin da ba ya saka masu abinda suke so,a haka suka isa ATM machine ɗin, Mommy ce ta zaro ATM card a bayan wayar ta ta saka ta hau bin qa'idojin da ake bi kafin a samu kud'in su fito,a cikin jakar Billy ta dinga zuba kud'in har ta gama cirewa tass. Har za su tafi Billy ta ce su tsaya su duba balance su ga nawa Baabaa ke da shi a account ɗin ta,Mommy ce ta yatsuna fuska ta ce,
"Ke rabu da ita ina ruwan wani da nawa take da shi? Ni fa da ki ka ganni ba abinda ya dame ni da kud'in ta,shi yasa ma ta yarda da ni,yanzu ni babbar damuwa ta bai wuce ki bani shawarar yanda zan lallab'a Baba ya barni na biki birni ba"
Cikin jin haushin Mommy ta qi tsayawa su duba balance ɗin kud'in Baabaa Billy ta yi gaba,can kuma da ta ji abinda Mommyn ta ce daga qarshe sai ta saki ran ta ta juyo suna fuskantar juna ta ce wa Mommy;
"Ga shawara qawata, wai me zai hana ku haɗa baki ke da Innoh sai ku sa shi a gaba da lallami har sai ya amince? Dan ta ni yau ya amince maki gobe mu tafi yo me nake yi? Ina zaune ana tuqa tuwo da miyar kuka ana bani da safe da rana da dare,in ina so na ci abu mai daɗi sai dai na aika da kuɗi na,watarana idan aka siyo min naman haushi ke sawa na ji bana son ci dan babu daɗi kamar gashin birni,ni fa bana son rayuwar wahala ko kaɗan,kina dai gani yanda nake ɗora hotuna ko videos a social media kin ga yanda nake cin daɗi na kwanta a waje mai kyau,to ki faɗa min idan na ci gaba da zama anan na koma ai sai su ce bani bace sauya ni aka yi"
"Gaskiya kin kawo shawara haka zan yi bari na koma na kora mata jawabi da ya dawo ta san ya zata yi ta sa shi ya bar ni na biki"
A haka suka isa gidan su Mommy direct d'akin Baabaa ta je ta ciro kud'in a jakar Billy ta damqa wa Baaban sannan ta sa kai za ta fita,
"Ina kuma zaki je ba Zaki tsaya ki karb'i naki kason ba?"
"To kin ce min akwai kaso na a ciki ne tun farko?"
"To uwar ra'ayi tsaya ki karb'i kason ki shike nan ?"
Tsayawa ta yi ta na sauke facemask ɗin ta, sai a kokacin ta kula da Innoh da ta yi k'ifi-k'ifi da idanu ta na jiran ta ga yanda za a yi kasafin komai, ta na tsaka da murnar za a bata riqon kud'in Sule, Ameerah, da Ɗan liti kamar abun had'in baki sai gasu sun dawo gidan a tare,wani tuquqin baqin ciki ne ya kama ta ta ja dogon tsakin da ya ja hankalin kowa a wajen,kunya ce ta kama ta ta hau soshe-soshe ta miqe ta na fad'in,
"To Yaya bari na tafi, Allah ya yafe mu baki ɗaya a kuma ci gaba da haƙuri da mu,dan bahaushe ya ce babba juji"
"To Allah ya bamu hakuri baki ɗaya,ki tsaya ki tafi da naki kud'in mana yaron nan ne ya aiko da zakkar kuɗi,ta abinci ma na tafe kamar yanda aka saba duk shekara, ke Mommy kira sauran mutanen gidan kowa a kasafta a bashi nashi babu cuta ba cutarwa,"
K'wafa Innoh ta yi ta na jiran a bata nata yanda za ta ji daɗin zazzaga wa Baabaa rashin mutunci,Baabaa na lale dubu ashirin ta ba wa Innoh sai ta sa hannu a yatsine ta Karb'a sannan ta ce,
"Ba dan babu kyau maida hannun kyauta baya ba ai da na ce me zan da su? Ni Zaki kalla yanzu ki yi wa baqar magana wai babu cuta ba cutarwa, to wane macucin? Kin ga Baabaa ki kiyaye ni hawainiyar ki ta kiyayi rama ta tommm"
"Ahaff 'yar kunama kenan ga zaqi ga harbi, ni dai na san ba a banza ki ka zo neman gafara ba akwai wani abu a qasa, to ki je dan kan ki Allah ya raba tsakani na da ke kin ishe ni Innoh,kin isheni fa, ki na shigar min hanci a kannad'e kar ki bari na fyato ki ta qarfin tsiya ba Zaki ji da daɗi ba,"
Shewa Innoh ta yi sannan ta buga cinyar ta ta ce,
"Ahayyyeee nanaye in ji 'yan gad'a, Baabaa ban ga laifin ki ba,ganin arhar gabas ne ya sanya karuwa yin sallar nafila,da baki ganni na zo d'akin ki neman sulhu ba kin isa ki faɗa min baqar magana? Wai wani ba cuta ba cutarwa,"
A gigice Baaba ta ke kallon Innoh da ta saki karin maganar da ya gigita tsohuwar, tuni jikin Baaba ya fara rawa ta fara hawaye, kud'in ta tattara daga cinyar ta ta tura su qasan gadon ta sannan ta miqe tsaye jikin ta sai kyarma yake irin na 'yan borin nan da aka kad'awa garaya,Baaba bata dubi ɗan qaramin jikin ta ba da kuma girman jiki irin na Innoh ba haka ta yi wani ihuuu kamar wata qaura a filin daga ta daka tsalle ta d'ale Inno ta dai-daici Muqamuqin ta ta yaga mata cizo bata saki ba sai da ta bar shatin haƙoran ta a muqamuqin Innoh,wani yare ta fara yi wanda yake kama da buzanci,can ta saki ta kama fullanci wato asalin yaren ta,daga baya ta koma wani yaren da ba wanda yake gane me take faɗa banda Kalmar Innoh.
Ba Innoh da wannan bala'i ya saukarwa ba hatta da Ɗan liti da ya isa wajen dan jin hayaniyar Baaban ya tsorata ya kasa qarasawa d'akin, tsakar gida ya koma ya na k'wala wa Sule kira wanda ya wuce d'akin shi tun shigar shi gidan,cikin haɗe rai ya fito ya na fad'in,
"Baba gani maye? "
"Kai ɗan jakar uba ana can ana bori a d'akin Baaba aljanun ta sun tashi ta kafta wa Innoh cizo a muqamuqi maza jeka ka ceci uwar ka"
"Tabbb ! Ban gane na je na cece ta ba kai ba matar ka bace? Inace shekara bakwai da suka wuce da ta tada aljanu irin haka sai da ta bi kowa ta masa tabo saboda tsabar bala'in qarfi irin na tsohuwar nan"
"Ba qarfin ta bane qarfin sarkin aljanu ne wannan duk yanda aka yi,yo Allah na tuba nawa Baabaan take da zata gagare mu muna maza? Taso mu je mu ga me ke faruwa na ji yaren ya lafa"
Kamar marasa gaskiya haka su Ɗan liti da Sule suka lallab'a suka isa wajen Baaba a qofar d'akin suka tsaya su na leqe, karatun qur'ani suka ji ya na tashi daga bakin Yadiko ta na yi ta na tofe Baaban da ayoyin Allah, can gefe kuma Innoh ce kwance a qasa warwas ta suma saboda tsabar shiga tashin hankali aljanun Baaba ka saka ta,sun shammace ta bata taɓa zaton har yanzu suna nan ba duba da jimawa da ta yi bata tada su ba,duk wannan bala'i da masifar da ya sa ta suma bata saki kud'in hannun ta sun faɗi ba suna nan qammm a hannun ta kamar an sa masu gum an manne su.
Ameerah ce ta shiga wajen a guje ta na fad'in,
"Ku matsa! Ku matasa !!......"
A guje su Ɗan liti suka afka d'akin har suna take su Baaba da Innoh saboda neman mafaka a zaton su Ameerah ta yi gamo da aljanun Baabaa ne,sai da suka natsu ne sannan suka jiyo qarshen maganar ta,
"......Ku matsa !!! Na ga me ke faruwa, na dawo ciki na fall da kashi shine na tafi band'aki na jiyo ihun Baaba da Innoh, to me ya faru?"
Tsaki kowa ya ja sannan Ɗan liti ya ce,
"Dallah malama matsa bani waje na tafi neman halali na kin bi kin firgita ni na zaci ma gamo ki ka yi, to ba abinda ya faru da ya wuce tsohuwar gabar da aljanun Baaba ke yi da Innoh ce yau ta motsa ake fitar da raini a tsakanin su."
Baaba na farfad'o wa ta dawo hayyacin ta sai ta kalli Ɗan liti ta fashe da kuka sannan ta ce,
"Yau ko da bani ce Hadiza ba uwar da ta haife ka na ci darajar riqon da na yi maka Ɗanli,yau ni matar ka ke kira da karuwa a cikin gidan nan,kaiii duniya ! Mutuwa me tonon asirin bawa,da malam na raye ke kin isa ki kira ni da karuwa? "
Nan take ran Ɗan liti ya yi mugun ɓaci,lallai wannan karon Innoh ta taka jelar damisa dole ta fuskanci hukunci,maganar Baaba gaskiya ce, ko da ba ita ta haife shi ba dole ta ci darajar yi masa kyakkyawan riqo tun lokacin bai fi Saddiq ba Yayan shi ya auro ta, a lokacin da shi da yayan nashi suna cikin ganiyar maraicin rashin iyaye haka ta kula da su ta dinga sana'a ta na taimakawa gidan kafin Allah ya hore wa yayan nashi arziqin da ya ci gaba da d'awainiya da su,cike da fushi Ɗan liti ya kalli Innoh da ta farfaɗo,yaran ta na kewaye da ita har da Billy da komai ya faru a kan idanun ta ya ce.
"Ke mara mutunci ! Baaban ki ke kira da karuwa a cikin gidan nan da mijin ta ne ya gina shi da kan shi ya bamu matsuguni?"
Cikin sauke nunfashi sama-sama Innoh ta ce,
"Haram Ɗanli ! Ni ban kira ta da karuwa ba, Baabaa bata ƙarya dan haka na amince ta maimaita me na faɗa da kan ta sai kowa ya yanke min hukuncin da ya ga dama."
Kallo ne ya koma kan Baabaa da ke ta sharb'ar kuka ta na faɗin,
"Daga abin arziki tsiya ta kira ni,da na sani ban karb'i kud'in zakkar nan ba yaron nan ya zo ya bawa kowa da hannun shi,na gaji da tashin hankalin gidan nan,zan masa waya ya zo ya ɗauke ni kafin a kashe masa uwa ya yi maraicin gaske"
A hankali Ɗan liti ya sassauta murya ya ce,
"Baaba ya aka yi Innoh ta kira ki da karuwa? Ko za ku iya maimaita mana me ta ce?"
"Tun da baku yarda ta kira ni da wannan Sunan fasiqan ba ba shikenan ba? Ni gidan ma zan bar muku ku yi ta zama har yauma ta nad'e,cikin gatsali da tsiwa fa ta ce min wai ganin arhar gabar ke sa karuwa nafila,ni ce karuwar kenan ko wa? Dama tun da ta shigo da kwanon alale na san ta qullo wani sharrin amma da yake zuciya ta ba ta nufin kowa da sharri na kawar da wannan tunanin ashe asheee ita abinda ya kawo ta daban"
A nan kowa ya gane karin maganar Innoh ne ya jawo mata bala'i dan kuwa ga muqamuqin ta nan har ya haure ya kumbura,cike da qunshe dariya Ameerah ta ce,
"Innoh ina hana ki karin magana a gaban Baaba baki ji kullum ke sai kuna magana ki yanko Hausa a gaban bafulata ki gitta sai kace 'yar sarkin hausawa, to ga irin ta nan an fara da haka Allah ya kiyaye na gaba"
Sule ma dariyar ya yi sannan ya ce,
"Ba yau Baaba ta fara sakarwa Innoh jinnu ba tun ki na qarama Fulanin kan Baabaa ke tashi akan Innoh, matsawar za ta b'ata wa Baabaa rai to fa 'yar garin shanono zata bayyana"
Daga jaje sai waje ya koma na dariya, ƙarshe har da Ɗan liti aka zauna ana bada labaran abubuwan da suka faru a baya sakamakon yawan karin magana mara daɗi da Innoh ke yi wa Baabaa,tun Baaba na b'ata rai ƙarshe sai ta sake ta sanya baki ta dinga basu labarai kala-kala game da yanda aljanun ta ke wahal da Innoh idan ta fusata ta.
Ba wanda ya kula da sanda Innoh ta bar d'akin sai da Baabaa ta d'akko kuɗi ta na rabawa sannan kowa ya kula da babu Innoh ba kayan ta, Ɗan liti na karb'ar nashi kaso ya miqe ya ce ya na zuwa,Yadiko da yaran ta ne kawai suka yi godiya tare da addu'a mai kyau sannan suka tattara suna dariyar farin ciki da kuma ta hirar aljanun Baabaa da aka sha suka wuce d'akin su.
Duk wannan abun da aka yi Billy na nan itama Baabaa ta tsakura mata wani abu a cikin kuɗin ladan ganin ido,wanda ta karb'a ta na nuna ta fi qarfin su,gefe ta ja Mommy ta na waige-waige sannan ta ce,
"Ke wai a haka zaki ci gaba da rayuwa da waɗannan mutanen kamar masu wasan comedy? Ki gaggauta ɗaukan matakin tafiya tare da ni idan ba haka ba haka zaki yi ta zama ke baki kawo zakka gida a raba wa dangi ba ki yi ta karɓar wadda aka kawo,"
"To yaya zan yi Billy? Ki na fa ganin me ya faru yanzu ta ina zan fara samun Innoh da wannan maganar?"
Zo ki ji yanda zaki yi musu daga ita har Baban naku, kama kan Mommy ta yi ta na yi mata rad'a a kunne, cike da jin daɗi Mommy ta washe dasorin ta ta miqawa Billy hannu suka tafa sannan ta ce,
"Kin kawo shawara mai kyau qawata Allah ya bar min ke !"
Dariya suka yi sannan suka yi sallama Billy ta tafi gidan su ita kuma Mommy ta nufi d'akin Innoh.........
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)
PAGE :6
D'akin Innoh Mommy ta nufa cike da k'warin guiwa, ta na shiga ta gan ta jingine da allon gado gefen fuska ya kumbura sai hawaye ke tarara daga idanun ta, cike da qunshe dariya Mommy ta ƙarasa gabanta ta zauna ta ce,
"Sannu Innohta Allah ya baki lafiya,a gaskiya ban ji daɗin abinda Baaba ta yi miki ba, wannan da da tsautsayi haqorin ta ya huda fatar ki ai da yanzu wani labarin ake yi kuma ba wannan ba"
Cikin jimanta lamarin Innoh ta ce,
"Duba min hanya 'Yannan wai makaho ya so gulma"
Mommy kasa riqe dariyarta ta yi ta d'aga haqoran ta sama dasashi a waje ta dinga keta dariya, cikin dariya ta ce,
"Innoh baki daddara ba ko? Garin yawan karin maganarki ki ke jawa kan ki bala'i wajen aljanun Baaba, kin san dai su ba qabilar Hausa bane ki kiyayi yin karin magana a gaban Baaba"
Karkata kai Innoh ta yi sannan ta ce,
"Koh? Habaa mana,ko da na ji ashe ba Hausawa bane ,haka kawai daga ka yi yaren ka sai abu ya zama masifa ita ta yi nata yaren mana wani ya hana ta? "
"Ba wannan ba ma Innoh,kin san duk fa dan ta ga ɗan ta yana da azziqi ne shi yasa take abinda take so a gidan nan Baba na bin bayan ta,da ace Zaki lallab'a Baba ya bar ni na bi Billy birni da ba k'aramin kuɗi zan samu ba kin ga yanda take wadaqa da nera kuwa? Ni yanzu ma ga wannan dubu biyar ɗin ki qara da naki dan kuwa nima daga yanzu na yi alqawarin duk abinda na samu naku ne ke da Baba da 'yan uwa na"
Cikin washe baki Innoh ta ce,
"Alhamdulillahi haihuwa mai rana,Allah ya yi miki albarka Momiyataaa zuwa aikatau birni kamar an yi an gama ne bari Baban naku ya dawo"
"To ! Toh !! In dawo a yi uwar me kuma? Uwar sababi da baki gajiya? Ina can na tafi nema maki maganin da zai saukar da haushin da muqamuqin ki ya yi ki na nan ki na a bari na dawo,to gani kwad'o na za a yi a ci ko me?"
"Kai dai ba ka cin ribar zance Malam,abun arziki na Kiran ka sai ka dinga ja wa kan ka tsiya,duba nan"
Kud'in hannun ta zata bashi Mommy ta yi saurin katse ta ta hanyar miqa masa sauran dubu biyar ɗin hannun ta ta ce,
"Ah ah ba sai kin bashi naki ba, ga nashi yo ni me zan yi da kuɗi iyayena na da buqatar su? Ai ba abinda zan yi da su ni,yanzu ni a rayuwata bani da burin da ya wuce na samo kuɗi na kashe maku su"
"To ka ji da kunnen ka ko? Yarinya mai tausayi irin wannan