Showing 210001 words to 213000 words out of 276165 words
Chapter 71 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
biyu masu zuwa za a ɗaura auren,ganin nisan waje ne ya sanya Kawu Sidi da waziri suka yanke shawarar kawai a saka rana baki ɗaya."
Gud'a Ta Annabi ta sanya sannan ta yi shewa ta ce,
"Alhamdulillahi Allah na gode maka da ka nuna min Sarauta zai ƙara aure,wancan lokacin gaba ɗaya bana cikin natsuwa ta akai hidimar bikin sa, wannan karon kuwa inshaa Allahu dani za a yi komai cikin daɗin rai."
Ameerah uwar son jin gulma kuwa fitowa tayi saɓe da yaro a kafad'a,riga da skirt ne a jikin ta sun zauna cif a jikinta,tinda ta dawo gidan ta jego ya karɓe ta saboda Ta Annabi na matuƙar ƙoƙari wajen kula da ita da jaririn ta,cikin washe baki ta duƙa ta ɗauki chewing gum ta hau ɓarewa ta jefa a baki sannan ta zauna a saman turmin dake tsakar gidan, Fadilah ce cike da tsokana tace,
"Babbar yaya wato kema murna kike za a yi wa Ƴar'uwar ki abokiyar zama ko? Shine har da ɗaukan cingam ki watsa a baki tin kafin a yi maki tayi."
Cikin rashin fahimta Ameerah ta dakata da taunar Chewing gum ta kalli Fadilah,sannan ta maida kallon ta kan Ta Annabi da ta rage fara'a,Azizah ce ta miƙe tsaye ta ce musu,
"Ni bari na koma gida, dama rabon goro nake yi kar a ga na jima."
"To ki gaida Yayah ki ce nace Allah ya sanya alkhairi,ga wannan tukuicin albishir ne,Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya."
Da ƙyar Azizah ta karb'i dubu dayan ta yi musu sallama ta wuce gida,hararar Fadilah Ameerah tayi sannan ta ɗauki biscuit ta fara buɗewa kafin ta ce,
"Ƴar rainin hankali har kin faɗar min da gaba ɗazu,ashe auren Azizah ne ya taso, to Allah ya sanya albarka ya nuna mana lokacin da rai da lafiya,Innah ni dai a raba a bani nawa dan Allah na tafi wajen majinyaci na."
Da jin haka Fadilah ta manta da tsokanar da zata yi ta ce,
"Me ya samu Yayan naji kin kirashi da majinyaci?"
Dariya Ameerah ta fashe da ita kafin tace,
"Ai ke baki sani ba Fadilah, yayan ki amana ta yake ci da wata bazawara,soyayya tayi zafi sosai na ɗaga hankali na na dinga yi masa magiya da rashin mutunci akan ya dena ya ƙi,ashe dai yarinya ƴar hannu ce,ina sabon mai turin nan da ya buɗe shago a kasuwa? To yanzu can take zuwa a tura mata kallon soyayya sannan a yi mata soyayya a zahiri a nan cikin shagon,shine ɗazu wani ya kawowa yayan ki rahoto ya tafi yaje ya gane wa idanun sa har aka ɗan baiwa hammata iska a wajan,da alama malam Shamsu bayan cin amanar shi da bazawarar shi tayi ya sha duka shine yake kwance yana jinya tin ɗazu"
Dariya sosai Ameerah ta fashe da ita a ƙarshen labarin ta, ita kuwa Ta Annabi da ta gane inda zancen ya dosa sai ta tattare tarkacen ta tawuce ɗaki ta bar su Ameerah da Fadila na tattaunawa game da mayaudariyar budurwar shamsu.
****************
A can Australia kuwa Billy ta rasa hanyar da zata kub'utar da kanta daga wajen Any,duk wata dabara da salo da take tunanin zata yi dan kuɓutar da kan ta abun ya gagare ta, kuɗi dai gasu nan dik sati samun su take yi masu tsananin yawa,gefe ɗaya kuma Any har takan tuna mata tace ta tura wa iyayen ta wani abu mana,ta haka ne za su san tana cikin ƙoshin lafiya,ko Billy ta ƙi turawa Any zata tura musu ta kuma yi amfani da wayar Billy ta yi wa Shamsu ko Baban Billyn message tace ta tura masu kuɗi ne dan ayi hidimar gida.
Gaba ɗaya Billy ta rame sosai saboda damuwa,a hankali ta fara wani irin zazzaɓi mai zafi,Any ta danganta hakan da yawan damuwar da ta sanya wa ranta ne da kuma yawan aikin da suke yi kwana biyu a kamfanin su na fina-finan porn,amma dik da haka sai ta yi mata alƙawarin kai ta asibiti dan ta ga likita,kafin satin da Any tayi alƙawarin kai Billy asibiti ya zagayo Billy ta fara yin wasu ƙuraje a bakin ta masu zafi ta ciki da wajen leɓen ta,dan haka cikin sauri Any ta ɗauke ta suka wuce asibiti,ko da suka je aka yi wa Billy gwaje-gwaje sai aka gano ta kamu da ciwon nan da ake ɗauka ta hanyar yin oral sex wato syphilis, hankalin Any ba karamin tashi ya yi ba,Billy kuwa da ta ga tashin hankalin da Any ke ciki sai ya gigita ta ta hau kuka tana faɗin,
"Shikenan na san ma mutuwa zan yi,na shiga uku ni Bilkisu na bi son zuciya na halaka rayuwa ta da kai na,dan Allah k taimake ni ki maida ni Nigeria bana so na mutu ban ga iyaye na ba."
Hawaye Any ta share kafin ta rungume Billy,cikin taushin murya ta kalli likita ta roƙe ta akan ta basu maganin da zai warkar da ciwon cikin sauri.
Har aka gama basu magani da dik abida ya dace Billy bata dena kuka ba,a haka suka koma gida Billy na sanye da face mask,wunin ranar gaba ɗaya a kwance ta yi shi,Any kuwa sai hidimta wa Billy take yi,fatan ta kawai Allah ya sa ta dage da shan Antibiotics ɗin da aka bata ta warke da wuri.
Yanda Any taga Billy ta rame a kwana biyu ga ciwon na ƙara yaɗuwa sai ya firgita Any,dan haka a cikin satin ta hau nema masu visa dan su koma gida Nigeria,idan ta kama ta ci gaba da jinyar Billy har ta warke ne sannan su dawo sai ta yi,idan kuwa taga abun bana ƙare bane sai ta lallaɓa ta barta a Nigeria ta gudu,ko babu komai ta mori Billy fiye da yanda ta mori sauran matan da ta yi tarayya da su.
*************************
Bikin Abdul da Huzaimah na ta matsowa amarya da ango tare da dangi da iyayen su suna ta shiri uwar gida bata san ana yi ba,ranar da za a kai lefe ta zagayo wanda ya yi dai-dai da sauran sati ɗaya ɗaurin auren Abdul da Huzaimah.
Ta Annabi na cikin wanda za su tafi katsina kai lefe,dan haka tin tafiyar saura kwana ɗaya ta fara shirin tafiya katsina,washegari da sassafe motar da Sultan zai kai su Katsina ta tsaya a ƙofar gida ta na danna wa Ta Annabi oda akan ta fito su tafi,a shirye ta fito tsaf cikin shiri sanye da kaya na alfarma,a ƙofar ɗakin Ameerah ta tsaya ta na ƙarasa sanya ɗan kunnen ta na zinare da ta siya babu jimawa cikin irin kuɗaɗen da Billy ke aika masu,Ameerah ce ta fito tana hamma da miƙa tace,
"Innah ina zaki je na gan ki cikin shiri haka da sassafe?"
"Ah ah ! Wai har kin manta alawa da biskit ɗin da Azizah ta kawo na saka ranar auren Abdussaboor? Ai yau zamu je kai lefe ma ni da Yaya Ta Zariya da Goggon shi Marka,ga ruwan wanka nan na mayar maku yau ki ƙoƙarta ki yi wa yaron nan wanka da kan ki,kunun gyaɗar ki na nan na dama a kula da gida sai na dawo "
A sheƙe Ameerah ke bin Ta Annabi da kallo kafin ta ɗura wani hanshaƙin ashar tace,
"Wai kina nufin Yah Abdul ɗin Yah Mommy ne zai ƙara aure shine bamu sani ba saboda baƙin cin amana da rashin mutunci?"
Da jin ashar ɗin da Ameerah ta saki Shamsu ya fito, ita kuwa Ta Annabi gaba tayi dan ta tsammaci abinda ya fi haka ma a wajen zuri'ar gidan Ɗan liti, Shamsi ne yace,
"Ke Ameerah wa kike zabgawa wannan ashar ɗin?"
A hasale tace,
"Da kafatanin zuri'ar maciya amana nake Shamsi idan zuri'ar ku na ciki ban ware ta ba,matsa ka bani waje."
Wani irin tsoron Ameerah ne ya kama Shamsi,dan kuwa sai yaga ta juye ta koma masa wata iriyar kumurcin maciji,cike da ɓacin rai ta hau dube-dube,can jikin soket ta hango wayar ta tana caji,a zabure ta nufi wayar ta ɗauka ta hau latsa lambobin Mommy,dan tsayawa searching a wajen ta ɓata lokaci ne...............
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 85:
Mommy na ɗaukar wayar ta ji muryar Ameerah a sama kamar tana magana da mutanen da ke nesa,zare wayar tayi daga kunnen ta ta sanya ta a handsfree sannan ta riƙe a hannunta ta ce,
"Ameerah ke da wa kike wannan maganganun da bana gane komai a cikin su? Dan Allah ki natsu ki yi min magana ta yanda zan fahimce ki."
'Ni da wannan zuri'ar masu cin amanar nake mana,ki na nan ki kwana da miji ki tashi da shi zai yi aure amma baki sani ba,ahhh baki sani ba mana,tinda na tabbata da kin sani da yanzu hankalin kowa a tashe yake.'
Wani ashar Mommy ta saki sannan ta dangwara Amir a cinyar Aunty Naja ta miƙe tsaye tana bin ta da wani mugun kallo kamar itace Abdussaboor ɗin,cikin wata iriyar murya Mommy ta ce,
"Ki ka ce me? Waye zai yi aure Ameerah? Kar ki sake kiyi min ƙarya saboda gudun aikata aikin dana sani."
'Mijin ki Abdussabour Abdulkarim Yariman Sarkin Garin Ba Mugu shine zai yi maki kishiya Hadiza Ɗan Liti.'
Ameerah ta faɗa tana wata iriyar jijjiga kamar ita za a yi wa kishiyar,Shamsu mamakin halin da Ameerah ta shiga yake yi,su kenan zuri'ar su ba za a yi masu kishiya ta daɗin rai ba sai hankalin kowa ya tashi? Haka fa ta dinga yi masa tijara da rashin mutunci akan budurwar da ya yi,yanzu kuma sai wani jijjiga take yi kamar shi taji zai ƙara aure,hannun ta ya kama yana miƙa mata yaron su dake kuka, wata uwar harara ta zabga masa sannan ta kashe wayarta ta zauna ta karb'i yaron ta wurga masa mama a baki,cikin ƙunar rai tace,
"Amma dai gidan Sarki sun iya harkar ƙaranta,sun zama ƙananan mutane,yo ƙananan mutane mana,wa yake ƙara aure a wannan zamanin ba tare da ta gida ta sani ba? Na yi rantsuwa da....."
"Kar ki rantse sahibata, ni ɗin banza nayi maki kishiya baki sani ba? Ai ko zan ƙara aure da sa hannun ki da amincewar ki zan ƙara shi, ballantana ma ni ke kaɗai kin ishe ni rayuwar duniya dai ba ta ƙiyama ba."
"Kai dallah can rufe min baki ! Wanne daɗin baki ne Abdul be yi wa Mommy ba tin a daren su na farkon aure? Yanzu baga shi can auren su za a yi da wata ba?"
Shiru Shamsu ya yi bai ce komai ba, daga ƙarshe ya zame ya bar gidan,yana fita ya nufi shagon shi dan ya fara aikin shi na turawa mutane sabbin films ɗin da ya d'akko,gani yayi mutane ba su wani zo ba sosai, masu saka caji ne kawai suka fi zuwa,duk an tattare an koma wajen me sabon turin da ke bakin kasuwa, ƙwafa ya yi yana ayyana yanda zai sabauta sana'ar sabon mai turin,dan kuwa ba ƙaramin samu yake yi ba a sana'ar dik da yanzu ba da ita ya dogara ba, kuɗaɗen da Billy ke turo masa suna da yawa har ya fara tunanin sayan fili ya fara gini.
A can garin Kano kuwa Abdul yana ɗakin shi riƙe da waya yana magana da Huzaimah sai shagwab'a take yi masa tana faɗa masa kunya take ji,idan masu kawo kaya sun zo ba lallai su ganta ba,ta tafi gidan wata yayar su,dariya yake yi mata saboda yanda take Shagwab'ar abun na ratsa shi sosai, wani irin shauƙi yake ji na musamman tare da fatan Allah ya gabato da ranar auren su da gaggawa ya samu yanda yake so a wajen ta.
Babu zato babu tsammani ya ji an fizge wayar hannun shi an yi wurgi da ita jikin gini ta tarwarse,kaca-kaca screen ɗin wayar ya yi kafin ta yi wani haske ta ɗauke gaba ɗaya, iPhone ce ƴar yayi mai tsadar gaske,cikin sanyin jiki ya kalli Mommy da idanun ta suka kaɗa suka yi wani irin jaa kamar ba ita ba,farar fuskar ta ta sauya ta koma jawur kamar tumatur,hannu biyu ya d'aga sama kamar wanda ƴan sanda suka zo kamawa,cikin dakewa ya buɗe baki zai yi magana muryar shi ta kasa fita,da hannu ya hau nuna mata gefen gado yana yi mata alamun ta zauna ya yi mata bayani,wasu hawaye Mommy ta ji sun fara zuba a kuncin ta masu tsananin zafi,kallon shi ta yi sannan ta nuna kanta cikin kuka tace,
"Abdussaboor me kake so na yi maka kafin ka gane bana son kishiya ina so in rayu da kai daga ni sai kai sai ƴaƴan mu? Raina ka ke so in siyar ko jiki da ruhi na? Me kake so nayi maka kafin KA FAHIMCI NA TSANI KISHIYA ZAN IYA KASHE KA AKAN KAYI MIN KISHIYA !"
Ta ƙarasa maganar ta cikin ɗaga murya da ƙarar da ta kiɗima Abdussaboor,cikin gigicewa Mommy ta juya ta d'akko wata kwalbar turaren wutar ta dake saman madubin ɗakin,kwalba ce babba mai kauri da nauyi, tana ɗauka ta saita gaban shi da ke sanye da zallan gajeran wando ko vest babu a jikin shi ta wurga masa,wata iriyar gigitacciyar ƙara Abdussaboor ya saki ya fara layi,nan take kwalbar ta faɗi ƙasa ta tarwatse,ta kan kwalaben Mommy ta bi ta ƙara saka hannun ta ta naushe shi a gaban shi, nan take ya baje a saman gado a sume,ƙarfin ta ta saka tana kuka tana ci gaba da dukan shi a wajen tare da faɗin,
"Sai na illata ka Abdussaboor sai dai mu zauna da ni da kai bamu amfana da wajen ba, dan na tabbata babu yarinyar da zata zauna da kai baka da kayan aiki."
Naja ce ta shiga a guje ta ɗaga Mommy daga saman Abdul da ya suma,Bilal da ya jima zaune a parlour yana jiran hayaniyar da ake ta lafa kafin Aunty Naja ta kira masa Abdul ne ya gaza haƙuri ya jira saboda ƙarar da abokin shi ya saki,direct shima ɗakin ya nufa ya kutsa kai babu neman izini kamar yanda ya saba,ganin ash colour ɗin wandon Abdussaboor na ɗigar da jini ne ya sanya shi ƙarasa shiga ɗakin a guje,yana isa gaban Mommy dake ci gaba da kai wa Abdussabour duka ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari ya yi wurgi da ita ƙasa,cikin kwalaben da suka tarwatse a ƙasa ta faɗa,ko jin azabar yankan da ta samu a hannun ta da cinyar ta bata yi ba ta miƙe ta cakumo wuyan Bilal tana ɗura masa ashar,cikin kuka ta ce,
"Matsiyaci tsinanne wanda ba zai sadu da rahamar Allah ba kawai,ai kai ne babban munafukin dake taya shi rufe min maganar auren,Abdul baya aikata komai sai da shawarwarin ka, da ka faɗa masa ya sanar dani ko ya ma fasa auren da fasawa zai yi,amma dake kai ɗan zina ne baka ƙaunar Allah sai ka goya masa baya ya ci amana ta,Allah ya isa ba zan taɓa yafe maku ba,sai Allah ya saka min."
"Sakar min wuyan riga balama ! Shashasha mara hankali daƙiƙiya kawai,bari ki ji na faɗa maki Hadiza,zan kai aboki na asibiti, idan wani abu ya samu lafiyar shi sai kin ƙare rayuwar ki a gidan yari,ko zan yi yawo tsirara sai na wulaƙanta ki."
Yarfe hannayen ta ya yi daga jikin shi ya sungumi Abdussaboor a kafad'ar shi ya nufi hanyar waje, Aunty Naja ce cikin kuka ta ɗauki jallabiyya ta bi bayan Bilal ta miƙa masa sannan tace,
"Maza ka kai shi asibiti Allah ya bashi lafiya, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri,kuyi hakuri da dik abinda Hadiza ta aikata."
Ko kallo Naja bata ishi Bilal ba ya fizge jallabiyya ya sakawa Abdul da ya kwantar a saman kujera a parlour,yana kammala saka masa ya ɗauki ruwa a glass cup ɗin wajen ya sheƙa masa,ko gezau Abdul bai yi ba balle ya farka,ganin haka ne ya sake ɗaga hankalin Naja da Bilal, da sauri ya ɗauki Abdul a kafad'a ya fita waje dashi,da motar Abdul ɗin ya yi amfani wajen kai shi asibiti.
Ko da yaje asibiti ya yi wa likita bayanin me ke faruwa cikin sauri suka kai shi emergency room aka fara bashi taimakon gaggawa,jinin dake zuba ne yafi ɗagawa Bilal hankali,likita ya jima yana duba Abdul kafin ya fito,zare gilashin idanun sa ya yi ya kalli Bilal yace,
"Biyo ni zuwa office d'ina."
Cikin sauri Bilal ya bi bayan shi suka shiga office suka zauna,a hankali likita ya fara magana Bilal na sauraren shi,
"Wato da farko dai ina so in sanar da kai cewar kar ka damu jinin nan da ka ga yana zuba ba daga al'aurar ɗan uwan ka bane,ta gefen cinyar shi ne ya yanke da abinda aka dake shi dashi ko aka yanke shi da shi, mun ɗinke masa inshaa Allahu zai warke ba tare da wata matsala ba,sai abu na gaba kuma shine,zamu ɗan yi masa wasu gwaje-gwaje da zarar ya farfaɗo saboda mu gani ko ya samu matsala a gaban nashi,wanda muna fatan Allah ya taƙaita ya sa kar a samu wata matsala."
Ajiyar zuciya Bilal ya sauke sannan ya ce,
"Na gode likita,dan Allah a kula min da shi sosai,ko nawa ne na yi alƙawarin zan kashe akan ya samu lafiya,fata na kawai a tabbata bai samu matsala a wajen nan ba dan girman Allah."
Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo wa Bilal, tsantsar tsana da ƙiyayyar Mommy da ya binne a zuciyar shi ya tono har ya samu damar zuba masu taki suka yi yaɗo suka mamaye ko ina na jiki da ruhin shi,cikin zafin nama ya miƙe ya yi wa likita sallama ya bar asibitin, direct police station ya wuce ya yi ƙarar Mommy akan tana son ta illata mijin ta dan zai ƙara aure,nan take kuwa aka shigar da ƙarar shi,aka haɗa shi da ƴan sanda biyu, mace ɗaya namiji ɗaya suka shiga mota suka nufi gidan Abdul,zaune suka tarar da Mommy Naja na gyara mata inda ta yanke tana yi mata faɗa akan abinda ta aikata, ita kuwa jin zuciyar ta take a bushe a ƙeƙashe,idanun ta sun soye ta ƙure waje ɗaya da kallo sai jijjiga jiki take yi, ganin ƴan sandan nan bai karya guiwa ko zuciyar ta ba,hasali ma miƙewa tayi ta nufi ɗakin ta ta d'akko mayafi da zanin goyo ta goya jaririn ta,hannun ta riƙe da handbag dinta da wayar ta kamar mai shirin zuwa biki ko suna.
A shirye take ta je kotun ƙoli akan Abdul yayi mata kishiya,dik laifukan ta da ƴar