Showing 249001 words to 252000 words out of 276165 words

Chapter 84 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

wutar azaba da tashin hankali a zuciyar ta,ta tabbata hawan jinin ta ne ya tashi har ta faɗi,likita ya sha yi mata gargaɗi akan hakan,yanzu shikenan kuma ba zata sake takawa ba a duniya ko kuma idan ta taka ma zata rasa wani sashe na jikin ta.

Hayaniyar Ameerah da Mommy ne ya sanya Sule daka musu tsawa,Ɗan Liti kuwa tini ya fita waje ya bar musu gidan,dama cikin shi ne ya murd'a ya dawo gida dan rage shi,ran shi a matuƙar ɓace yake akan abinda ya faru da Hadiza. Cikin faɗa Sule ya ce,

"Ke yanzu da hankalin ki da komai kika yi auren kisan wuta? To gidan uban ki kike son komawa da aure da ya ki har kika kaso auren ki?"

"Yah Sule tsaya ka ji,tabbas da fari auren kisan wuta nayi,amma tin ranar da Ameerah ta je har gida ta min nasiha na watsar da komai na ci gaba da rayuwa ta,babu irin neman gafarar Allah da ban yi ba a lokacin da na gane kuskuren da na tafka,har na cire rai akan auren kisan wutar zan zauna da shi malam cikin aminci sai kewar Amir ta dame ni,daga zuwa na roƙi arziƙin ya bari naje na gano ɗana ya ƙi amincewa,haka na yi kuka na haƙura na bar ɗakin,ina komawa ɗaki Mero ta biyo ni tana gasa min maganganu son ran ta wannan ne ya hasala ni muka yi ɓatacciya har ya sake ni."

Ameerah ce ta yi shiru kamar ruwa ya ci ta, Sule kuwa gaba ya yi yana faɗin,

"Allah ya kyauta."

Sadeeq ne ya duƙa ya ɗauki akwatin Mommy ya kai ɗakin su na da ya ajiye mata,yana fitowa ya ce,

"Yah Mommy bari na cire uniform d'ina na zo na share maki ɗaki."

"To Sadeeq na gode."

Ameerah bata jima ba ta goye yaron ta ta bar gidan, dama daga barka suke ita da Naja wata ƴar'uwar su Innoh ta haihu,shine suka je barka suka biyo ta gidan,har zata fita ta juya ta ce wa Mommy,

"To Allah ya kyauta ya sa hakan shine ya fi alheri."

A daƙile Mommy ta amsa da,

"Amin."

Mommy da Naja ne suka shiga ɗakin a tare, suna shiga wani wari ya ziyarci hancin su,a guje Mommy ta fita tana kelaya amai,Naja kuwa tsayawa ta yi tana son tantance me ke wari haka a ɗakin,gani tayi ƙudaje na bin jikin Innoh dake ta zubar da hawaye a kwance a wajen,ganin ruwa me kala-kala na gangarowa daga ƙasan Innoh ne ya baiwa Naja tabbacin abinda take zargi a ran ta,cikin toshe hanci ta isa gaban Innoh ta duba ta da kyau,tabbas bahaya ta yi a kwance,nan take ta furta kalmar,

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una"

Cike da damuwa Naja ke kallon Innoh,shin me ke shirin faruwa da Innoh ne? Da ƙyar Naja ta iya zama ta gyara Innoh,tana gamawa ta ɗage labulen dan ɗakin ya sha iska,Mommy kuwa tinda ta fita waje tana amai bata koma ɗakin ba har sai da ta ga Naja ta gama komai na gyara jikin Innoh.

Sadeeq kuwa abinci ya ci ya ƙoshi sannan ya shiga ɗakin Mommy ya gyara mata shi tasss sannan ya leƙa ya yi wa Innoh sannu,godiya mommy ta yi masa ya fita yana jimanta abinda ya faru a ran shi,yanzu dai dole ya kirawo Saddiqa ya sanar da ita wannan mummunan labarin. Naja kuwa na nan a gidan har isha'i ta na kula da Innoh,da zata tafi kuwa sai da ta damƙa amanar kula da ita wajen Sule da Mommy,a ƙyanƙyame mommy ta tsartar da yau gefe ta ce,

"Kina nufin wai idan ta kuma yin bahaya kamar wanda ta yi ɗazu nice zan wanke mata? No way ba zan iya ba gaskiya sai dai Yah Sule."

"Ji shashasha,kina mace baki iya ba sai ni da nake namiji ne zan iya?"

Sa insa suka fara yi a tsakanin su,nan take Naja ta fashe da kuka ta ce,

"Yanzu akan kula da mahaifiyar ku kuke wannan maganganun?"

"A gaskiya Aunty Naj ba zan iya ba,akwai sauran kuɗi a hannu na mu dai tafi a kai ta asibiti a fara duba ta,a bata magani da sauran su wataƙila ta miƙe,aikin kashin yaro ma ya na ƙare da shi balle na babba kamar Innoh."

"Hadiza ! Hadiza ! Innoh fa mahaifiyar ki ce."

Kauda kai tayi gefe tana ƙunƙuni,Sule kuwa shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi,dan kuwa shima baya jin zai tsaya jinyar kashi da fitsari,sulalewa ya yi ya bar ɗakin ya koma nashi. A haka Ɗan Liti ya dawo daga aikin shi,Naja ce ta yi masa bayanin dik abinda ke faruwa da Innoh,cikin jimanta lamarin ya ce,

"Inshaa Allahu gobe zan sata a mota na kai ta Kano taga likita,fitar nan da na yi alhamdulillah an samu ciniki sosai."

"To Allah ya kaimu, zan wuce gida goben da sassafe zan zo mu je tare."

"To Allah ya kaimu."

Ko sallama bata yi wa Mommy ba ta wuce ta bar gidan, itama Mommyn bata tsammaci haka daga wajen Najar ba,dan haka sai kawai ta fara takawa zata wuce ɗakin ta,Ɗan Liti ne ya tsaida ita ya na kallon ta daga sama har zuwa ƙasa,tabbas ta rame,ta yi baƙi,amma a ganin shi ko ya gidan miji yake yafi gidan uba,dan haka cikin wani irin yanayi ya ce mata,

"Uwata kin kaso auren ki kin dawo gida ko? Zama da mu ne bai ishe ki ba a wannan shekarun naki? To ai shikenan Allah ya sa hakan ne ya fi zama alkhairi,ga waje nan ki zauna har sanda kika so,amma ina mai tabbatar maki da cewa idan ma kin kaso auren ki ne dan Abdul ya aure ki a karo na biyu,to Abdul ba zai taɓa maida aure dake ba ko da kuwa ku kaɗai ne kuka rage a duniya."

Wata iriyar faɗuwar gaba ce ta riski Mommy,cike da tashin hankali ta ke kallon Ɗan Liti da ke gyarawa Innoh kwanciya.............[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨











PAGE 101:







Zubewa ta yi a gaban Ɗan Liti tana zare ido cike da tashin hankali ta ce,

"Dan Allah Baba kar ka yi min mugun baki,ka barni haka na ji da masifun dake hawa kai na kudu da arewa gabas da yamma."

Ko kallon ta Ɗan liti bai sake yi ba ya samu waje ya kishingiɗa kafin ya ce mata,

"Idan kin fita ki ja min ƙyauren ƙofar."

Jiki babu ƙwari Mommy ta miƙe ta fita daga ɗakin tana matsar ƙwalla,dan kuwa ta tabbata Baban nasu ya gama magana kenan tinda ya bata umarnin ja masa ƙofa,anya zata iya ci gaba da rayuwa mai kyau kuwa idan bata sake auren Abdul ba?

Da wannan tunanin ta shiga ɗakin ta ta kwanta ta rintse idanu hawaye na zubar mata. Ranar da ta fara haɗuwa da su Abdul da Bilal ne ta gifa a idanun ta,bata samu yin bacci ba har sai da ta dire tinanin ta gidan Malam da faɗan su da Mero har zuwa sakin da akai mata a gidan,hamma ta yi mai tsawo ta sake yin juyi a karo na babu adadi sannan ta rintse idanun ta,a hankali ta furta,

"Ya Allah ka sa Innah Laminde ta bani yaro na tinda na dawo gida."

Washegari da sassafe Mommy ta tashi ta hau sharar gida,Baaba kuwa dake share bakin murhun suyar kosan ta ce ta kalle ta da mamaki, gaisuwar da Mommy ta yi mata ta amsa, sannan ta ce,

"Sannu da aiki uwar masu gida,Allah ya yi miki albarka,amma a gani na da kin fara zuwa kin duba ya Innoh ta kwana idan da taimakon da zaki yi mata sai kiyi mata ko?"

Ɗan yatsina fuska Mommy tayi kafin ta ce,

"Baaba ina son hakan nima a cikin zuciya ta, amma a gaskiya ba zan iya aikin najasa ba,a dai bari har Aunty Naja tazo sai na jawo mata ruwa a rijiya ta kula da wannan sashen."

Shiru Baaba tayi bata matsa mata ba,dan kuwa ta san a hakan ma an samu ci gaba ai tinda gata tana yi musu sharar tsakar gidan,sannan ta hura wuta ta ɗora abun karyawa,wanda da ko ɗakin da take kwance ze ruɓe ba za ta share ba,sai dai ta sanya Sadeeq sharewa. Bata jima tana sharar ba ta kammala,ta koma kitchen ta ƙarasa dafa abun karyawa,tana saukewa Naja ta buga sallama,cikin murmushi Mommy ta ce,

"Ni na san Aunty Naja ƴar alƙawari ce ai,dan kuwa ta yo gadon cika alƙawari wajen Kaka,bismillah Innoh na jiran ki."

"Uhumm Hadiza kenan baki da dama,kun tashi lafiya? Ya jikin Innoh?"

"Sai kin shiga kin sanar dani yanzu,dan tinda na tashi ban leƙa ba,amma bari na ja maki ruwa a rijiya na tara maki dan na san zaki buƙace shi."

Wani irin kallo Naja ke bin Mommy da shi,sannan ta waiga bayan ta ta kalli Sule da ke fitowa daga ɗakin shi yana hamma riƙe da brush ɗin shi da ƙaramar buta,sake maida kallon ta tayi akan fuskar Mommy da bata wani damu da abinda ta ce ba,itan ma bata sake magana ba kawai sai ta nufi ɗakin Innoh,sallama ta yi a bakin ƙofar shiga ɗakin ta ji shessheƙar kukan innoh na tashi,cikin sauri ta afka ɗakin ta hau duba Innoh dake kwance a gefe ɗaya,wanda da alama tin daren jiya take a haka,da sauri ta juya ta tana nishi da kyar,hawaye Innoh ta ci gaba da zubar wa tana kallon saman gadon ta,wajen da take kallo Naja ta bi da nata idanuwa,nan take suka sauka a kan Ɗan Liti da ya maida kan shi can ƙuryar gado sannan ya ɗora pillow a saman kan shi yana ta bacci.

Salati Naja ta yi sannan ta ce,

"Au dama Baban Sule na ɗakin nan shine kike ta kuka babu mai taimaka maki?"

Ji ta yi kamar ta ɗakawa Ɗan Liti duka,amma bata da wannan ikon,a zuciye ta fita tsakar gida ta tarar da Mommy har ta kusan cika baho da ruwa,Sule kuwa ya fito daga wanka zai koma ɗaki riƙe da ƙaramar butar shi da brush a hannu,cikin tsananin ɓacin rai Naja ta ce,

"Amma dai kun yi asara,Allah ya wadaran naka ya lalace,uwar taku? Uwar taku za ku wofantar haka? Idan uban ku ya kyale ta ta ji da kanta ku ya kamata ace kun yi haka? Kai Sule ina hankalin ka yake? Anya kuna son ku gama da duniya lafiya kuwa? To bari ku ji na faɗa maku,daga yau se yau idan na sake zuwa na tarar da Innoh a wulaƙance se na ci mutuncin ku ta inda baku taɓa zato ba,ƴan iska marasa mutunci kawai."

Shiru tsakar gidan ta ɗauka dan kuwa ko Baaba bata taɓa ganin wannan ɓangaren na Naja ba,a ƙufule ta je ta sungumi wata robar da zani,sannan ta ce Mommy ta kawo mata ruwan d'aki,ƙarar shiga da tarkace ne ya tada Ɗan liti yana magagin bacci,ga kuma yawun bacci kwance a gefen kumatun shi,tsaki Naja ta ja mai ƙarfi sannan ta dangwara robar a ƙasa,tana sane take yin komai da ƙarfi dan ya tashi.

Mommy na tsaye a ƙyanƙyame Naja ta gama gyara Innoh,ruwan kunu ta dinga bata,da ƙyar take iya had'iyar shi,a haka suka samu suka cika mata ciki da kunu,Ɗan liti kuwa tinda ya farka ya ga Naja baza ta bari ya koma bacci ba sai ya miƙe ya sungumi buta ya faɗa banɗaki,sai da ya gama lalurar shi sannan ya fito ya yi alwala ya dungura sallah a gaggauce ya fita.

Kasuwa ya je ya bi layi ya ɗan yi kaiwa da kawowa hudu ya tara dubu uku da zai ƙara mai sannan ya dawo gida,ko da ya dawo ya tarar Naja da Mommy sun gama shirya Innoh shi kawai ake jira,Ameerah ce ta gaida shi tana sharar hawaye,dan kuwa bata yi baccin kirki ba a daren saboda tinanin halin da Innoh ke ciki,taliyar da ta dafowa Innoh ta kasa ci ya ja ya tsugunna yana afkawa a bakin shi,sai da ya ci ya ƙoshi sannan ya leƙa Baaba suka gaisa ya mata sallama.

Da ƙyar suka kama Innoh shi da sule suka sanya ta a mota,Mommy da Naja ne suka shiga mota suka kama hanya sai kano. Sule kuwa makarantar da yake koyarwa ya wuce suka bar Ameerah na gyara d'akin Innoh.

Sun isa kano ana azahar. Suna isa Ɗan liti ya fita ya shiga cikin asibitin ya yi bayanin rashin lafiyar Innoh,nan da nan ma'aikatan wajen suka gungura gado aka ɗakko Innoh,sun jima ana yawo da su daga nan zuwa can dan a yi mata wasu gwaje-gwajen kafin daga karshe su tsaya a ɗaki ɗaya,likita ne ya ce su bashi waje zai duba ta da kyau.

Suna fita Mommy ta fita waje dan ta ciro kuɗi saboda hidimar asibitin,sai da ta ciro dubu ɗari cif sannan ta kamo hanya dan ta dawo,a hanyarta ta dawowa ne ta yi kaciɓus da wani mutum ya sha purple ɗin shadda yana ta karairaya,kallon juna suka yi a lokaci ɗaya,Mommy ce ta hau tinanin shin a ina ta san wannan fuskar,shi kuwa mutumin babu wani ɓata lokaci ya ce,

"Hadiza Sweet H? Ashe rai kan ga rai baiwar Allah? Lallai rayuwar nan abun tsoro ce,ke ce kika koma haka?"

Nan take Mommy ta gane mai maganar,cike da mamaki ta ce,

"Hajiya K'waisan alheri! To ai kai ne za a ce wa kai ne ka dawo haka,tinda nake da kai na taɓa ganin ka da shadda ne? Kai ni na ma taɓa ganin ka da suturar rijalu kuwa?"

"Ke point of correction ! Ki kira ni da suna na yanka kar ki sake kira na da wani Hajiya K'waisa,tini na tsinewa wannan sunan kamar yanda Allah ya tsine masa,na jima ina neman ki dan in baki haƙuri ke da Billy akan dikkan abubuwan da suka faru a baya,saboda darasin da na gani a rayuwa ba kaɗan bane Hadiza."

Cikin sanyin jiki Mommy ta koma ƙasan wata bishiyar mangwaro dake cikin asibitin ta jingina ta ce,

"Humm ai ni ce zan faɗa maka na ga rayuwa,bana fatan maƙiyi na ya shiga halin da na shiga a rayuwa ta."

Haɓa ya kama ya buɗe baki ya ce,

"Anya kin ga jarabawar da na gani kuwa Hadiza? Ke ni fa tsabar azabar rayuwa da na shiga se da na rasa ko asin da zan ci gero dashi dan maganin yunwar ciki na,kowa ya guje ni saboda wari da tsutsotsin da nake fitarwa a baya na,ke ban taɓa tinanin wannan wajen zai ƙara fitar da kashin arziƙi ba tsutsa ba,Sallau shine kaɗai be guje ni ba,dashi muka dinga gwagwarmaya har ya sa gidana a kasuwa aka siyar aka yi min aiki a baya na,yanzu haka haya nake yi a wani shago da nake soya doya da ƙwai a bakin titin singa dik yammar duniya,abu ɗaya da na godewa Allah Hadiza shine tuban da Allah ya nufe ni na yi,da na mutu a harkar daudu ana amfani da ni kamar tsohuwar karuwa Hadiza ai na shiga uku."

"Ai dubu ma zaka shiga ba uku ba,yanzu ina Sallau ɗin yake,sannan me ya kawo ka asibiti?"

"Humm magani nazo karɓa, kin san dake na haɗu da jahilar wato ciwon sida (HIV)shi yasa bana zama sai da magani,Sallau kuwa ya yi aure yau sati uku da kwanaki huɗu kenan,yana can da matar shi ni kuma ina nan ina suyar doya ta,to ita kaɗai na iya Hadiza, kin ga ko dole ita zan yi,tinda babu wanda ze bani sisi yanzu ba tare da ya nemi wani abu a waje na ba,banni da uwa banni da uba ban san dangi na ba balle naje na raɓe su na ji sanyi a rai na."

"Allah sarki rayuwa,babu komai watarana sai labari,mu godewa Allah ma da rayuwar tamu ta tsaya a haka,wasu suna can sun wulaƙanta fiye da tunanin mai tunani,Allah ya ƙara kare mu daga afkawa ruɗin shaiɗan."

"Amin ya Allah,ni yanzu matsala ta ɗaya yanda mutane ke tsangwama ta,bani da ikon yin abu sai zagi da tsinuwa da la'anta,babu wanda ya san gwagwarmayar da na yi a rayuwa ta har Allah ya tsamo ni daga halaka,amma mutane ba za su barni na shaƙi iskar ƴanci ba,sannan da dare haka zaki ga masu zagin nawa sun zagayo suna son su sake fafake min bayan da na wahala har na fitar da rai da rayuwa akan shi."

"Humm ai halin mutane kenan,sai su zauna su dinga zagin ka akan zunubin da suma suna aikata irin shi koma mafiyin shi a ɓoye,amma kuma da sun samu dama sai zagin wani su yi ta aibata shi koda kuwa shi ya tuba ya bari tsakanin shi da Allah."

"Ai zamu je lahira ne za su yi bayani matsiyata."

Dariya Mommy ta ɗan yi kafin ta ce,

"Ina babyn ka Sam kuwa da Alhaji? Tin ɗazu ban ji ka ambace su ba."

"Humm yana can wajen dangin shi a Onicha,dake uban sa nada nera har waje aka kai shi aka masa jinya,amma fa har yanzu allura baya iya d'agawa balle ya tsinanawa kanshi komai,Alhaji kuwa ana can gidan maza ana fama."

"Ohh Allah kenan,Allah ka yafe mana mun tuba Allah ba dan halin mu ba."

Hawaye ne suka zubo daga idanun Mommy,wani irin tsoron Allah ne mai girma ya mamaye zuciyar ta,nan take ta gane cewa Allah yana da hanyoyi da dama da zai yi maganin duk wani mai saɓa masa,amma sai yake kauda kai saboda shi ɗin Al-halim ne,sannan shi ne Al-wadud,kuma shi ne Al-Afuwwu sannan Al-ghafuru, yana yin gafara ne a lokacin da yaso zuwa ga bayin shi,sannan shiriya a hannun shi take. Mommy da K'waisa basu rabu ba sai da suka yi musayar lambar waya,yaso yaje ya gaishe da Innoh da Mommy ta sanar da shi tana kwance babu lafiya,sai Mommy ta doje,dan kuwa ta tabbata iyayen nata baza su so ganin ta da ɗandaudu ba,sallama sukai wa juna tace ya gaishe da Sallau idan sun haɗu.

Koda ta koma an gama yiwa Innoh duk abinda ya dace,sai bill ɗin da ke hannun Ɗan Liti yana ta jujjuyawa, kud'in da aka rubuta masa sun shallake ɗan ƙaramin budget ɗin shi,dika dika dubu goma sha shida ne da shi,wanda a baya yake tunanin za su ishe shi ya kai Innoh asibitin,ganin irin tashin hankalin da Ɗan Liti ya shiga ne ya sanya Mommy karɓar takardar ta ce,

"Dan Allah Baba kar ka tada hankalin ka,zan ji da komai inshaa Allahu,yanzu da zai yuwu ina so ku koma gida kai da Aunty Naja,a je a kwaso kaya na na gidan Malam a sa a kasuwa, kud'in da aka samu dik a tattara a kawo mu ci gaba da jinyar Innoh


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login