Showing 3001 words to 6000 words out of 276165 words
Chapter 2 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
aikatau ɗin fa can Kano tun da ka k'i na ci gaba da karatun? Ka na ganin yanda mata ke tafiya suna samo abun arziki ni ina zaune a gida a nad'e ba mashinshini babu sana'a ba kuma aikatau ɗin"
"Shima ba Zaki je ba, ke ni duk ba wannan ne ya dawo dani ba, Balki dai ta dawo daga binni ɗazu, ita ce ma ta ce na faɗa maki dawowar ta har na fita na tuna.....
Sai Ɗan liti ya qanqance idanu ya na kad'a mata yatsa a gaban fuskar ta ya ci gaba da magana.
" .... To ba ta dawo ba bana son wannan shegen yawon naku,ki kama kan ki na faɗa maki, kar ki bari na gan ku Kuna bin titi da kwararo da tafasa da masara kuna shegen ɗauke -d'auken hotunan nan naku da baku gajiya,idan na gan ku ran ki zai yi mummunan ɓaci "
Cike da tura baki ta ce,
"To zan kiyaye, amma ai ka yarda na je na yi mata sannu da dawowa ko?"
D'aga kai ya yi a lokacin da yake tafiya soro dan komawa kasuwa a ci gaba da neman kuɗi kuma.
Ya na fita Mommy ta buga tsallen murna ta shige d'akin su,jakar kayan ta ta janyo ta hau duba kayan da ya dace ta sanya saboda ko ba komai wayar Billy tana da camera mai kyau,za ta ɗauki hotunan sanya wa a status da DP na social network ɗin da take kai.
Wata baƙar doguwar riga ta d'akko wadda ta siye ta a gwanjo da mayafin ta ta d'aga sama, kusan duk hotunan ta da rigar take yi, sai dai bata taɓa yarda a gano wani ado na jikin ta saboda kar ta je ƙawayen ta da ta tara a social media su gane ta,a ce bata da sutura.
Yayyafa wa rigar ruwa ta yi ta mata ninkin 'yan Madina ta zauna akai ta ɗauki wayar ta ta shiga group ɗin su na MU SHANA MATA, buɗe wani sabon video ta yi da aka turo,tashi tsaye tayi da kayanta a hannu ta koma can ƙuryar d'akin ta buɗe video ɗin dika ta na fad'in,
"Da alama dai wannan videon d'azu aka turo shi sanda Baba ya kira ni,bari mu ga sabuwar harkar da aka turo mana"
Ta na nan zaune a d'aki ita ɗaya ta na aikata abinda da ace wani zai shiga d'akin nan ba tare da ta sani ba ya gan ta, tabbas da kunyar duniya ta gama yin ajalin ta, Ameerah ce ta dawo daga tallen alale da Innoh ke ɗora mata ta kai kasuwa, cikin sauri Ameerah ta ce,
"Innoh ki na ina? Bari na je na zaga na zo,yau dawaa ta yi nama"
Gud'a Innoh ta rabka ta na murna tare da yi wa Baaba habaici tana faɗin,
"Ahayyee Allah na gode maka,wai ni za a hana aron nera dubu duk da sana'o'in da mutum yake yi sai ya ce ba shi da taro bashi da sisi,ina kuɗin siyar da ƙosan suke shiga ? Babu, ina kuɗin siyar da goron ? Babu duk an cinye wajen bada sadaka, to a ci gaba da bawa na nesa mu ma na kusa Allah na son mu ba zai hana mu na kahyewa (kashewa) ba,kuma alhamdulillahi dama bahaushe ya ce ka na naka Allah na nashi, sa'a a waje na take yau an Saida komai ga kuɗi na cassss a hannu"
Baabaa ce ta fito riqe da dankwali a hannu ta na nuna Innoh cikin kanne idanun ta guda ɗaya, ta na magana goron da take taunawa ya na tsalle ya na fita tsabar masifar da ta ciyo ta,
"Wai ni Innoh ni ce kishiyar ki ko Yadikon Sule? ki bani amsa"
"Yadikon su ce kishiya ta,amma ita sam bata kishin da ni idan ba 'yan baƙin halin nata ne suka motsa ba, amma ke Yaya ji ki ke yi kamar mu mace ni da 'ya'ya na a gidan nan ki huta tsabar yanda ki ka tsane mu"
Salati Baabaa ta sanya ta na matsar kwalla saboda abinda Innoh ta faɗa game da ita, cikin kuka ta bar wajen ta shige d'akin ta ta na nemo mayafin ta, a can bayan kujerar palourn ta ta same shi,irin ginin da take sha'awa kenan tun ta na amarya sai marigayi mijin ta ya yi mata hakan dan faranta ran ta.
Ta na fitowa ta ja k'ofar ta ta zo zata wuce ta gaban su Innoh cikin sauri kamar wata tsuntsuwa tsabar rashin qiba da tsawo, Innoh da Ameerah ne suka kwashe mata da dariya, k'wafa ta yi ta wuce gidan aminiyar ta dan su yi hira ko zuciyar ta ta yi sanyi akan abinda Innoh ke guma mata a gidan,gashi da ta faɗa wa Baban Gida zai ce zai aiko Munir a maida ta Abuja ita kuma bata son zaman Abuja ta taɓa yin shi bata ji dad'in zama ba a cewar ta kaɗaici ya yi yawa dik da irin soyayyar da matar shi da yaran ke nuna mata,musamman Munir da yake babba mai kinanin shekaru ashirin da bakwai.
Innoh da Ameerah na tsaka da lissafa cinikin da aka yi a ranar Mommy ta fito idanun nan sun kad'a sun yi jawur dasu, babu sannu balle Allah sawaqe ta wuce su ta ɗauki bokiti a bakin rijiya ta zuba ruwan wanka, ta na gama zubawa ta wuce band'aki wanka ta hau yi ta na ta dirzar jikin ta kamar zata cire fatar ta,sai da ta fita sosai sannan ta d'auraye jikin ta ta fito ta na karkad'e ruwan da ke kan ta, tsayawa ta yi a Saman kan Innoh ta ce,
"Inno dan Allah ki bani ɗari biyu idan Shamsu ya zo anjima zan biya ki"
" 'Yannan ai idan ɗari biyar Zaki Karb'a bashi zan baki,tun da bahaushe ya ce ai ka gaida mai gaida ka ko ba zai amsa ba ko?"
Murmushi ta yi ta juya ta koma d'akin su, ta na shiga ta tsane jikin ta tare da sanya kayan ta da har a wannan lokacin basu wani risina ba su na nan a cukuikuyen su,kwalliya ta zabga ta gyara guida yaran kan ta ta yi acuci maza ya yi tush da kyau a bayan kanta,da alama dai Mommy aka buɗe mata saloon ba karamin kuɗi za ta samu ba saboda yanda ta iya tsara kwalliya.
Turaren ta ɗan d'uri ta d'akko ta lakata ta shafa sannan ta d'akko wayar ta ta shuri takalmin ta baƙi ta yi waje,ko da ta fita Yadiko kawai ta tarar a tsakar gidan ta na jiqa garin kwaki za su sha da yaranta,dama duk ranar girkin Innoh da rana bata abinci sai ta ga dama, gata da yara mata ba zata saka su su girka ba ko dan saboda fita hak'k'in mutanen gidan da kuma koyawa yaran ta girki, ah ah sai dai kowa ya nemi abinda zai ci da dare ta tuƙa tuwo da miyar da ta ga dama kowa ya ci, da safe a yi d'umamen tuwon da kunu idan akwai kamu, idan babu tuwon babu kamun ma kowa sai dai ya san yanda zai yi, ita dai za ta ɗora abincin siyarwar ta a fitar mata da shi.
Yadiko na Saida kuka,maggi,gishiri,daddawa,citta, kaninfari da sauran kayan miya na cikin gida da mata kan siyar,sannan ta na wankau da sirfe duk dan a rufa wa kai asiri, shi yasa idan ma ba a bata ba za ta siyi abinda take so su ci da yaran ta,duk randa Ɗan liti be bata na cefane ba zata yi amfani da na wajen ta,bata tambayar shi sai idan taga zai yi rashin adalcin nashi da ya saba na baiwa Innoh kuɗi mai yawa ita ya bata kaɗan duk da cewa ta fi taimaka masa a gidan, to a sannan ne yake ganin asalin kalar ta, zata karta masa rashin mutunci ne har sai ya yi rabon adalci sannan take kyale su dika.
Zaman Yadiko da Innoh kuwa zama ne kadaran kadahan, Innoh bata cika jan Yadiko faɗa ba kamar yanda take jan Baaba faɗa,ba dan komai ba sai dan hakuri irin na Yadiko ko ta ja ta da faɗa shiru take yi bata kula ta har ta ƙarata da faɗa da masifar ta ta gaji ta kyale ta dan dole, dan kuwa bahaushe ya ce k'arfe ɗaya baya amo, a duk sanda kuwa aka yi rashin sa'a Yadiko ta biye mata aka yi faɗa a gidan abun baya yin kyau dan kuwa bata iya faɗa ba sam idan ta tashi,tsoron hakan ke ƙara nesanta Innoh neman faɗa da Yadikon.
Bangaren Mommy kuwa ta na fita soron gidan su ta fito da face mask d'in ta da ke maqale a jikin 'yar kwab'irar wayar ta ta saka ta rufe bakin ta,sannan ta sa kafarta fara tass mai dogayen yatsun qafa da suka sha baƙin dayis suka yi wani irin kyau kai ka ce bata taka ƙasa a waje ta na wani lumshe ido ta na ware su a hankali,in dai kyan ido ne da dogayen gashin ido da Kyakkyawar gira da dogon hanci ne Allah ya ba wa Mommy,in dai ba buɗe wa mutum bakin ta ta yi ba babu mai yarda bata haɗa jini da jinsin buzaye ko Larabawa ba.
Direct gidan su Balki ta nufa wadda tun da ta isa gidan su take ta sharara wa mutanen gidan su k'arya, Balki bata taɓa iya zama ba tare da ta yanka k'arya ba,hankali kwance zuciya zaune za ta yi dabarar da duk zata yi ta kawo labari mai daɗi ta yanda za ta samu gab'ar da take so ta gilla ta ta qaryar ba tare da an gano ta ba, wannan shine babban dalilin da ya sa ta tara masoya a accounts ɗin ta na social media.
Da sallama Mommy ta shiga gidan ta na wata tafiya kamar 'yar wani hanshaƙin,kamar mutuniyar kirki haka ta durƙusa har ƙasa ta na gaishe da Mahaifiyar su Balki, Balki kuwa tunda ta ga ƙawarta ta miqe ta na ta murna,amma sai Mommy ta nuna mata ita a natse ta zo ba da hauragiya ba,wannan sabon halin kuwa ba k'aramin bawa Balki mamaki ya yi ba, sai da suka shiga d'akin Balki ne wanda ta k'awata abinta kamar na 'yar masu kuɗin gaske Mommy ta daka tsalle ta rungume ta suka hau murnar ganin juna.
"Ke banza ina ki ka shiga ki ka manta da mu, yau fa shekarar ki ɗaya da watanni biyu rabon ki da qauyen nan fa? Habaa Billy ai ya kamata ace ki dinga waigo mu ko da a wata biyu ko uku ne"
"Ke dalla bar ni ba zan zo ba ɗin,haka kawai ina can ina cin shinkafa da kaza,ga shayin da ya ji madara da soyayyen kwai duk safiya kawai sai in dawo? To idan na dawo me za ku dinga bani ina ci ko kina nufin tuwon nima zan dinga ci? To sam ba zai yu ba, ki duba fata ta mana ki gani ke kin san ta na shan AC kuma k'wai ya zauna a cikin ta,na faɗa maki a bar batun bakin ki yanda Allah ya yi maki fata mai kyau da tsarin Kyakkyawar surar nan zaki yi kyau da zaman birni,dan haka ki biyo ni mu koma cikin garin Kano Hajiya ta ki samu wani gidan aikin irin nawa ki ga yanda Zaki koma,amma inaa kin bi kin nace kin makale kamar wani abun ki ke samu da ya fi wanda Zaki samu a can birnin,ko ni da ubana ke sayar da dusar awaki da ta kajin gidan gona ya amince min na tafi neman kuɗi balle ke da naki uban ke yin Kabu-kabu,na wa yake samu a rana gaba ɗaya idan ya fita tun safe? Gaskiya ya kamata ki san abin yi akan wannan lamarin ki tashi ki nema ki taimaka wa iyayen ki da ke kan ki da sauran 'yan uwan ki, ki dubi mahaifiyata leshin da ke jikin ta kin taɓa ganin irin shi a jikin matar sarkin ƙauyen nan? Ko kin taɓa ganin wata na yafa mayafin da take yafawa a kaf garin nan? Ki duba motar da Babana yake ja ni na sai masa muka fake da cewa shi ya sai abar shi,yau ko motar ki ka sai wa Baban ki ba sai ya dinga tuƙawa ba ya na jeka ka dawo daga wancan ƙauyen zuwa wancan?"
"Hummmm Billy ba Zaki gane bane,Baba ya hana, ya ce aure zan yi bai yarda da ci gaba da karatu ba, kuma bai yarda da zuwa aikatau ba, yanzu haka fitowar nan da na yi sai da ya yi min warning akan yawon da muke yi dan samun baground mu yi hoto"
"Ai kuwa sai mun fita,ki na ganin wannan wankan naki zai tafi a banza ne? Ai ba zai yu ba inaaa, bari ki ga wayar da Hajiya ta sauya min"
Tashi ta yi ta koma tsakar gida ta d'akko iphone ɗin ta ta kawo ta damqawa Mommy a hannun ta, cikin zaro ido Mommy ta kalli wayar da take jin labari ta na tashe da tsada, cike da mamaki take juya wayar ta na kallo Billy da ke wani kad'a ƙafa ita a dole ta kai wata yar duniyar.
"Billy kin tabbata Hajiya ce ta baki wannan wayar?"
"K'warai kuwa, ke ba fa gidan qananan mutane nake aiki ba,gidan Ambasada nake aiki idan baki sani ba ki sani, kuɗi gare su kamar ya kashe su, ba ni kaɗai ba ma hatta da masu gadin gidan wasu arnan wayoyi ne a hannun su, ya na da gidaje a Nigeria masu tarin yawa har da Abuja,ke ki na tunanin in ba gidan manya ba a ina zan dinga cin daɗin da nake ci na kwanta a AC ?Hajiya ta idan Zaki lallab'a Baba ya barki ki lallab'a shi kema ki shiga gari idanun ki ya buɗe ki ga duniya duniya ta gan ki"
Shiru Mommy ta yi ta na nazari, Billy kuwa ta kafe ta da ido ta na so ta samu nasara akan ta, ta jima ta na son ta tsoma Mommy a harkar da take yi,ta rasa ta inda zata bullowa lamarin,ta ɓangare ɗaya kuma tinda Hajiyar da take tare da ita ta k'yalla ido ta ga wani video na Mommy ta na magana cikin salo da iyayi jikin ta babu suturar arziqi ko ina na jikin ta a bayyane take so a kawo mata ita dan ta sanya ta a irin harkar su, dan ta kula Mommy za ta iya duk abinda suke da buk'ata a ƙungiyar tasu.
Wannan dalilin ne ya sa duk kafiyar Billy akan bata so ta zo ƙauye ta wahala sai da ta matsa mata akan ta na so ta zo ta yaudaro mata Mommy da kuɗi ko za su samu nasara a wannan karon.
"Ke ina zuwa na shirya mu je gidan sarki mu sha hotuna media ta san yau ƙawayen juna sun haɗu, maza tashi ki sauya kaya, na zo maki da wasu sabbin kaya wanda na samo a gidan aiki na, kema ko ba komai a san cewa ke kawar Billy ce a ƙauyen nan,dan ba Zaki dinga bi na da abayar da ta yi shekara da shekaru ana sa mata filter ba"
Jiki ba kwari Mommy ta kalli Balki da ita kaɗai ke kiran ta da Billy,ta ga tana zuge akwati ta na fitar da wasu arnan kaya masu kyau da tsada wanda duk ta samo su ne daga wajen Hajiyar ta a birni,wata pink abaya ta baiwa Mommy mai haɗe da mayafin ta ta ce ta sauya,sai ta bata takalmi da jakar da za su shiga da kayan sannan ta bata turarika ta ƙara nuna mata wasu kayan ta ce nata ne, amma sai sun dawo daga ɗaukan hoto za ta bata ta wuce da su gida.
Har Billy za ta fita dan sake wanke fuska saboda ta ji daɗin shafa powder Mommy ta riqe hannun ta ta ce,
"Ke wai ina Yah Shamsu ne? Yau tunda na zo ban ga koda gilmawar shi ba?"
Qanqance idanu Billy ta yi ta na kallon ƙawarta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ta ce,
"Ban gane ba ! me yasa ki ke son ganin shi? Ko dai ko dai?"
Dariya suka yi a tare sannan suka tafa,Mommy ta ce,
"Ba Zaki gane ba, a wani group mu ka haɗu da shi ya na tura mana kayan lamura kin dai gane,sai yake amfani da Sunan mace ya ce duk mai so ya bi shi Private ya biya kuɗi a tura masa, ni kuma bani da sisi kin dai sani,shine na je na dinga daɗin baki bud'ar bakin sa ya yi min audio note ya ce, 'Mommy kar ki damu ai ana tare ko gida ki ke so na zo na tura maki a waya sai na zo ai'daga nan hankali na ya tashi ta ya aka yi matar ta sanni? Tinda da Maman Fadwa nake amfani a social Media,ke na tak'aita maki labari dai muka haɗa za mu haɗu a gidan mu, ina ta jin tsoro amma da na ga mace ce sai na ce ba komai,kawai sanda ta zo ta kira ni,ko da ta iso na yi na yi ta shigo ta ce na dai je na ga waye tukunna, ina zuwa na ga Yah Shamsu"
"Dan Allah ki bari? Yah Shamsu dama ya san wannan harkar? Kan bala'i kin ga yanda yake faɗa idan ya ganni da waya kuwa sai ya ce su Baba ne suke shagwab'a ni nake abinda nake so ashe shima ɗan hannu ne,"
"Ai ba shi kaɗai ba, a hankali na gane Yah Sule ma ya na wannan harkar kin san yanzu duk yawancin matasa an raja'a neman abinda zai ɗebe kewa, wannan harkar kuma ita ce muke ganin ta fi mana samun nishad'i da ɗebe kewar talaucin da ƙasar ke ciki,"
Sun manta da karanta qur'ani,sun manta da tasbihi ga Allah da salatin Annabi da istighfari wanda shine ya kawo mu duniyar ba neman abun ɗebe kewa ba,sun manta Allah da kan shi ya na cewa bai halicci mutum da aljan ba face sai dan su bauta masa, sai suka juya bautar Allah'n ta koma sab'on Allah, to ta yaya za mu ga dai-dai a wannan yanayin da muke ciki? Billy na gama sauraron Mommy ta gyad'a kai ta ce,
"Ehhh tabbas haka ne,ina zuwa"
Da wannan hirar suka gama shiri tsaf suka fita zuwa