Showing 216001 words to 219000 words out of 276165 words
Chapter 73 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
suka ga motar ƴan hisba da ƴan sanda ta zagaye su,a kiɗime Any ta kalli Billy da ta sauke Face mask ɗin ta suka haɗa ido tana wani shu'umin murmushi......................
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 87:
Any ma murmushi tayi sannan ta zare hannun ta daga cikin na Billy ta hau kallon saman titi,zuciyar ta ta gama yin tauri saboda baƙin cikin dake cin ta,lallai da alama Billy bata san irin capacity ɗin da take da shi a ƙasar Nigeria ba baki ɗaya,tana tunanin wannan hukumar hisban da ƙananan ƴan sandan Nigeria'n da ta raina ne za su iya dakushe tasirin ƙungiyar da suka jima da kafawa? Ta kuwa san irin manyan mutanen dake cikin ƙungiyar tasu? Da alama dai reshe ne yake nema ya juye da mujiya,wani murmushin ta sake saki sannan ta hau tapping ƙafar ta ta na buga yatsun ta a jikin cinyar ta, leb'en ta na ƙasa ta taune tare da rintse idanun ta,bata sake buɗe idanun ta ba sai da ta ji motar ta tsaya da tafiya.
Jin an buɗe marfin ɓangaren da take ne ya sanya ta buɗe ido ta kalli ɗan sanda da bai wuce ta wurge shi da dubu daruruwa ba ta sanya shi aiki,murmushi tayi masa tare da duƙar da kanta alamar yi masa godiya,baya ya ja ta fito cike da ƙasaita ta taka har inda taga jami'an ƴan sanda dana hisba sun shiga da Billy,hannun ta zube a aljihun wandon suit ɗin ta dake numfashin kud'in da aka kashe wajen siyan su, takalmin ta fari ƙal ta kalla ta kalli kujerar dake gefen Billy a ofishin kwamandan na hisba,zama tayi sannan ta harɗe ƙafar ta ta zaro wayar ta a aljihu zata fara dannawa,ɗaya daga cikin matan dake ofishin ce ta karɓe ta ajiye mata a gaban ta, sannan cikin sakin fuska da daddaɗan kalami ta ce wa Any,
"Baiwar Allah a yi haƙuri da latsa wayar nan tinda kin shigo wajen Malam,saboda muyi abinda ya tara mu anan a gama da wuri ko?"
Murmushi Any tayi mata sannan ta juya ta haɗe hannayen ta waje daya ta kalli kwamandan da kallon ina jin ka,sallama kwamandan hisba ya fara yi sannan ya yi wa annabi salati tare da wasu addu'o'in da ake gabatarwa yayin fara jawabi.
Kallon Billy ya yi sannan ya ce,
"Daga jin muryar ki da kika yi salmama da yanda kika yi mana bayani zan iya cewa dake muke waya da tattaunawa ko?"
Gyara zama Billy tayi kafin ta ce,
"Eh malam ni ce."
Man ne ya yi sallama ya shiga wajen a dai-dai wannan lokacin sanye da shadda riga da wando farare tas har da hula,cike da kamala ya samu waje ya zauna,Any ce ta kalle shi kallon na san ka farin sani, amma me kake yi anan? Kauda kan shi ya yi sannan ya gaida malam da mutanen dake wajen,Malam ne ya bawa Billy umarnin yin bayanin dik abinda ta sanar da su ta waya bayan Man ya haɗa ta da Hisba committee,nan take Billy ta hau zayyano musu irin muguwar rayuwar da tayi a baya,masu jarida da masu rubutawa hisba rahoto suna kwashewa a takarda tare da naɗar sautin muryar ta,tin Billy na bada labarin cikin ƙwarin guiwa har ta zo dai-dai inda suka yi auren jinsi da Any,daga nan sai kunyar idanun mutanen wajen ya kama ta, nan take ta fara kuka cike da nadama da dana sani,kuka take yi sosai wanda ya sanya ta kasa ƙarasa ci gaba da bada labarin,Man ne ya ci gaba da magana kamar haka,
"A lokacin da suka yi auren jinsi da Any, ni kuma ina nan a gefe saboda sabo da soyayyar da muka yi a baya sai muka kasa rabuwa da juna,soyayyar mu muka ci gaba da gudanarwa cikin kwanciyar hankali kafin daga baya na dena jin ta akai-akai kamar yanda muka saba,ana haka har hisba tayi nasarar kama mu a gidan shan barasa ni da abokai na aka yanke min hukuncin da ya dace akan abinda na aikata, daga nan kuma aka sanya malamai suke yi mana karatun addini saboda an gano har da ƙarancin ilimin addini ke damun mu shi yasa muke aikata zinace-zinace da shaye-shaye yanda muka ga dama a gari,sannan mu jawo wasu mu lalata su,wannan baiwar Allah'n da Alhajin da take yi wa aiki sun jima suna bani wasu ƙananan ayyuka na kai musu ƴan mata kyawawa su sallame ni,ita kanta Billy bata san na san Any ba,dan kuwa ban taɓa nuna mata na san ta ba,wannan kuma dik a cikin takun mu yake na ɓatar da shaidar da zata sa a kama mu dika idan har tsautsayi ya gifta an kama ɗayan mu.
A irin wannan halin da muke ciki ne hisbah na ta aikin Allah ana yi mana nasiha tare da wa'azi mai ratsa zuciya,har Allah yasa ina cikin wanda suka samu nasarar taimakawa aka tsamoni daga fad'awa halaka,daga nan shine akai dace Billy naso ta kub'uta daga wajen su Any, sanda ta sanar dani cutar da take addabar ta sai na sanya ta uzzirawa Any akan a maido ta gida taga iyayen ta,anan ne muka haɗa plan da Billy na sanar da Hisba su kuma suka sanar da hukumar ƴan sanda dan a kama Any,domin idan Any ta shigo hannu kamar Alhaji ya shigo hannu ne,tinda dik dodo ɗaya suke yi wa tsafi,dikkanin su wakilai ne na turawa,wakilai ne na shaid'an da suke ɓata tarbiyyar al'ummar Annabi,sune suke so dolen dole sai mutum ya faɗa tarkon zina ko ta wacce hanya ce."
Man na kawowa nan a bayanan shi Any ta gane wautar da ta tafka na barin Billy da waya da tayi,gashi an haɗa baki da ita ta wayar ana neman a kawo ƙarshen ta,murmushi tayi da ta tina karfin ikon da ƙungiyar su ke dashi a ƙasar,hannayen ta ta harɗe a ƙirji tana kallon kowa a wulaƙance,kwamandan Hisba ne ya fara nasiha tare da jawo ayoyin Alkur'ani da hadisai,dik ayar da ya jawo kafin ya fassara ko ya dire ta Any ta ƙarasa masa ta dire ta ta kuma fassara tare da yin bayani bisa tafarkin tafsirin malamai,hadithi kuwa idan ya kawo sai ta kawo masa wani mai kama da shi sannan ta yi sharhi,tsananin mamaki ne ya sanya mataimakiyar kwamandan Hisbah ta kalle ta ta ce mata,
"Ke yanzu baiwar Allah kina da irin wannan tarin ilimin amma kike wasa da damar da Allah ya baki ta zama mutuniyar kirki?"
"Ina mutanen kirkin suke a lokacin da ƙanin ubana uwa ɗaya uba ɗaya ya yi min fyad'e? Ina mutanen kirkin suke a lokacin da uwata ta mutu saboda baƙin ciki? Kuna nufin mutanen kirki za su bani abinci a table d'ina ne haka kawai ba tare da na biya da wani abu na jiki na ba? Ko za su ci gaba da kula dani kyauta ba tare da na bauta masu da jiki na ba? Ko kuwa kuna ganin mutanen gari da unguwanni suna mutunta yarinyar da aka yi wa fyad'e? Kar ku dinga mantawa fa ba ita ta kai kanta ba, ƙarfi aka sanya mata aka keta alfarmar ta da ke lulluɓe,amma a haka mutane suke zagin ta,ake ɗora mata laifi,sannan su wanke wanda ya aikata koda kuwa sun san shi,sannan babu wanda zai aure ta sai dai a aure ta a wulaƙance,shi kuma idan ya tashi aure a bashi budurwa sabuwa dal ya angwance,to ki faɗa min ya kuke so nayi a wancan lokacin da nake da ƙarancin shekaru aka yada ni aka keta mutuncin marainiya?"
K'walla ce ta zubo a idon Any ba tare da ta shiryawa hakan ba,bata taɓa jin karayar zuciya da dana sanin abinda take aikatawa ba irin yau, cikin sauri ta sa hannu ta yarfe ƙwallar tare da faɗin,
"Shit ! I can't do this,let...let me go please."
Kwamanda hisba da ya kula da alamun samun nasara a tattare da Any sai ya yi murmushi ya ce,
"Yes you can do this,na tabbata you can do more than this,na yi imani da Allah'n da ya sanar dake ƙur'ani da hadisan Annabin rahama ba zai barki ki wulaƙanta a hannun shaiɗanun mutane kamar turawa ba,Allah yana son ki, yana son ki da rahama Anam,shi ne babban dalilin da yasa ya dawo dake ƙasar ki ta haihuwa lafiya bai yi fushi da laifukan da kika dinga aikatawa ba har ya kifar da jirgin ya halaka ku ba,Allah yana son ki da rahama ne shi yasa bai goge maki ilimin dake kan ki ba har ya baki ikon zurfafawa a ilimin addini dan kiyi amfani da shi wajen jawo ra'ayin mutane a saɓa masa,to a wannan karon saboda Allah mai yawan gafara ne, mai yawan afuwa ne sai yake so ya yi amfani dake wajen sauya rayuwar wasu da ilimin da ya baki,ko kin san shiryar ki zata karya lagon maƙiya Annabin rahama da suke yaƙi da abinda ya yi fafutukar kafawa a tsawon rayuwar shi? Anam ko....."
Wani irin kuka Any ta fashe da shi tana ɗaga hannu da girgiza kai alamar roƙo ya barta haka,Billy da Man kansu kuka suke yi saboda yanda wa'azi da nasihar Kwamanda ke ratsa zuciyar su,Billy bata taba zaton Any zata yi laushi da wuri irin haka ba, a zaton ta sai an sha baƙar wahala kafin ta yarda da nasihar da za a mata,wataƙila ma sai dai a hukunta ta mummunan hukunci akan ta saki wannan mummunar ɗabi'ar ta ta,sai gashi a cikin abinda bai di mintina ashirin ba Any na kukan nadama da data sanin abubuwan da ta aikata, hamdala ta dinga yi a ranta sannan ta sanya hannu tana tapping bayan Any da sigar lallashi,cikin kuka Any ta ce,
"Malam ba dan na san Allah mai yawan rahama bane,sannan mai afuwa ne ga bayin shi ya shafe dik abinda suka aikata a rayuwar su mara kyau ya yi masu babbar kyauta ta aljannah, tabbas da na ce maka ni kam ƴar uwa ta."
Nan take wajen ya ɗauka da faɗin,
"Subhanallahi ! Ya salam !"
Kwamanda ne ya ce,
"Yanzu ba lokaci ne na tone-tonen abubuwan da suka gabata bane,lokaci ne na ki gaggauta fara istighfari tare da neman afuwar Allah,laifi da hak'k'in mutane da kika ɗauka kuma ki dinga addu'a Allah ubangiji ya wakilce ki a zuƙatan bayin shi da kika zalunta da su yafe maki,wanda suka mutu ma Allah yasa ko a ranar gobe ƙiyama su yafe maki,domin shi laifi idan ya wuce na tsakanin bawa da ubangijin sa ya haɗa da bawa da bawan Allah, to fa wuyar sha'ani ne da shi, dan kuwa dole sai bawan nan ya yafe maka sannan Allah zai yafe maka."
"Malam sanin hakan ne nake sake jin tsoro,na ɗauki hak'k'in mutane da yawa,na yi sanadiyyar..."
"Ki tuba zuwa ga Allah,da ace baki tuba ba kin yi mana taurin kai, da tabbas mun nuna maki wannan gwamnatin daban take da sauran da suka gabaceta,domin kuwa a baya ana yi mana kutse a ayyukan mu saboda manya dake cikin harkokin baɗala,amma a yanzu komai girman ka,komai muƙamin ka Hisba za ta hukunta ka kuma babu abinda za ka yi akai,amma dik da haka dole zamu miƙa ku zuwa kotu,dik hukuncin laifukan da kuka aikata wanda ya dace a yanke maku hukunci dan rage maku nauyin zunubi za a yi hakan,sannan kafin nan muna so kuyi mana wani babban taimako a wannan hukuma tamu mai albarka."
"Dik wani taimako da goyon baya da ake buƙata a waje na, na yi alƙawari ni Bilkisu Abubakar Mai Dusa zan bayar dashi."
"Haka zalika ni Usaini zan bayar da dik gudummawar da ake nema na bayar."
Murmushi mataimakiyar kwamandan hisba tayi kafin tace,
" Ƴata Anam fa? Ko babu wani taimako da zaki iya yi wa wannan ƙungiyar tamu "
"Ni kuwa nake da taimakon da zan baku,domin kuwa daga Alhaji a ƙungiyar mu sai ni a muƙami,inshaa Allahu dik wata gudummawa da kuke nema zan bada haɗin kai a samar da abinda ake nema a wannan hukuma."
Anan taro ya tashi aka tattara su Any domin gabatar da su wajen kuliya manta sabo.
*************************
Tinda suka koma gida daga police station Mommy take kuka,wayar da suka yi da Abdussaboor kuwa tafi komai ɗaga mata hankali,ina alƙawuran da ya yi mata suke? Bai cika ko ɗaya ba shine zai bi ta da tukuicin saki, sakin ma kuma ta waya?
Cikin fushi ta miƙe ta hau haɗa kayan su ita da Abdul, tana yi tana kuka,Aunty Naja tayi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta ci abinci amma Mommy ta ƙi sam,banda tunanin halin da Abdul yake ciki a asibiti babu abinda take yi,da ta sanin abinda ta aikata ne ya yi mata dirar mikiya a zuciyar ta,cikin kuka ta zauna ta zuge akwatin kayan da ta gama haɗawa sannan ta zauna a ƙasan wajen ta sake fashewa da wani sabon kukan,da ƙarfi ta buɗe murya ta ce,
"Yanzu ya za a yi na koma rayuwar da na bari a baya? Kaico na ni Hadiza na yi kirari na lumawa kai na da kai na wuƙa a maƙoshi,gashi yanzu na saki reshe na kama ganye, Wayyoo Allah na ba zan iya jure wannan ƙuncin ba,ba zan iya rayuwa a ƙauye ba,wa zai dinga bani abubuwan da na saba da su na more rayuwar duniya a yanzu? Da na sani da ban illata Abdul ba ko banza ba zai yi min irin wannan sakin wulaƙancin ba,Aunty Naja dan Allah ki bashi haƙuri gobe idan mun je kotu alƙli ya maida auren mu,na tuba na bi Allah na bi miji na ko mata uku zai aura a rana ɗaya ba zan hana shi ba."
"Ai aikin gama ya gama Hadiza,kin hau dokin zuciya gashi ya yi muguwar sukuwa dake ya kayar dake a cikin yashi mai zafi,da kin sanyawa zuciyar ki salama da cikin ruwan sanyi zamu hana wannan auren kamar yanda muka hana na farkon,yanzu ina budurwar shi ta farko take Hadiza? Amma kika hau dokin zuciya kika yi aikin jahilci da jahilai gashi inda kika kai kan ki."
(Tooo jama'a dama shi zuwa wajen boka aikin masu ilimi ne banda masaniya?)
Kuka Mommy ta dinga yi tana jin kamar ta kashe kan ta ta huta da baƙin cikin da take ji a ran ta,Amir ne ya farka ya fara kuka yana neman mahaifiyar shi,cikin share hawaye Naja ta miƙe ta d'akko jaririn da ko arba'in basu yi ba ta miƙawa Mommy,kamar ba zata karɓe shi ba sai kuma ta miƙa hannu ta karɓe shi ta rungume a ƙirjin ta,kuka ta fashe da shi mai tsanani kafin ta fara shayar da shi.
A haka suka kwana cikin baƙin ciki, Naja ta kasa kiran Innoh ta sanar da ita mugun labarin da ya same su,ta yi yunƙurin kiran ta tana fasawa yafi sau bakwai,ƙarshe dai Kaka ta kira ta sanar da ita dik abinda ke faruwa sannan ta ce mata,
"Da an gama da kotu gobe dik abinda alƙalin ya yanke hukunci akai zan kira ki na sanar dake."
'Ohhh ni ƴasu yanzu abinda Hadiza ta aikata kenan? Ni wannan jarabar kishi nata na bani mamaki tinda ko uwarta ma bata irin wannan zazzafan kishin,to ai sai ta dawo ƙauyen ta zauna ga kutirin ta ga na uwar ta,ɗazun nan ake sanar dani wai an ga Sule ya dawo a wani irin mugun hali,yanzu haka da jimamin abun na kwanta sai kuma ga wannan mugun labarin shima,to Allah ya kyauta.'
"Amin Goggo,zuwa safiya zan kira ki naji ya jikin Sulen Allah ya taƙaita mana wahala."
'Amin kedai ƴannan,se da safe.'
Sallama suka yi kowa ya kwanta zuciya babu daɗi.
Washegari da sassafe suka farka suka hau shirin zuwa kotu,Bilal kamar wanda ya kwana a gidan haka ya iso ya hau buga masu ƙofa a zafafe,Naja ce ta je ta buɗe masa ta gaishe shi,gaba ɗaya haushin matar yake ji dan yana zargin dik iskancin da Mommy ke aikatawa da sa hannun ta a ciki,dan haka a daƙile ya amsa mata sannan ya ce,
"Ku fito na kai ku kotun lokaci na tafiya."
"To bari na leƙa na ga ko ta gama shiri."
Ko wanka Mommy bata yi ba ta shirya ta goya Amir ta bi bayan Naja suka shiga mota,Bilal ne ya karɓe makullin gidan ya rufe sannan ya koma motar ya tuƙa su suka wuce kotun,ko da suka isa sun tarar alƙali bai zo ba,kowa ya hallara shi ƙadai ake jira.
Da misalin sha ɗaya da rabi alƙali ya gama sauraren ƙarar su mommy,ya bata damar kare kan ta ta kasa,dan kuwa da bakin ta ma ta yi wa kotu ƙarin bayanin abinda ta aikata tare da danasanin abinda ta aikata ɗin,tana magana tana kallon Abdul da aka turo a keken marasa lafiya ko zai tausaya mata,bayan kammala sauraron komai alƙali ya gyara gilashin shi ya yi jawabai sannan a ƙarshe ya ce.
"Bayan sauraron dika shari'ar da aka gabatar daga bakin mai ƙara da wanda ake ƙara,wannan kotu mai albarka ta yankewa Hadiza Ɗan liti hukuncin shekara 3 a gidan yari, ko ta biya tarar dubu dari biyar under section 246 of the penal code."
Alƙali na buga gudumar shi kotu ta tashi,kuka Mommy ta fashe dashi tana kuka tare da neman afuwa tana roƙon alƙali ya maida mata da auren ta tana son mijin ta,kallon mara hankali wasu suka dinga yi mata,tinda kowa ya ji sanda ta faɗa da bakin ta Abdul ya kira ta a waya ya sake ta saki uku,sannan Bilal ya bada shaidar faruwar hakan,daɗin daɗawa a gaban kotu Abdul ya sake maimaita sakin daya yi mata,to ta yaya za a maida auren saki uku kenan?..............
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 88:
Sai da mommy ta biya tarar da aka sanya mata sannan suka fito daga cikin kotun suka tsaya a waje,ba kud'in da ta biya ke sanya ta baƙin ciki ba,tinanin wai yau ita ce ta koma bazawara shi ke gigita tunanin ta,kamar Bilal ba zai kula su Mommy ba,darajar goyon dake tare da ita ya sanya shi zuwa inda suke fuska a ɗaure ya ce,
"Ku wuce mu je na ajiye ku a gida sai na maida shi asibiti tinda kin gadar masa da zaman can."
Zubewa Mommy tayi a saman guiwowin ta ta hau roƙon Bilal akan ya taimaka a maida auren su da Abdul,cikin kuka Mommy ta kalli inda Abdul ke zaune a kujerar majinyata ta ce,
"Dan girman Allah Yah Bilal