Showing 264001 words to 267000 words out of 276165 words
Chapter 89 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
suka kashe maganar saboda baya so ya fara kaiwa Bilal ƙorafi akan ƙanwar tashi,ya riga da ya ƙudirta a ranshi duk abinda Suhailah za ta yi masa zai haƙura ya zauna da ita a haka,saboda halaccin Bilal a gare shi,sannan ita rayuwar aure dik yanda kake samun kwanciyar hankali to dole sai ka samu abu ɗaya ko sama da ɗaya da zai dinga ɓata maka rai dama,dan haka jiki babu ƙwari ya isa gida ya tarar da bata dawo ba,abincin da take yi musu ne duk weekend ta zuba a fridge ya ɗauka ya dumama a microwave ya zauna yana ci yana latsa wayar shi.
Yauma kamar kullum dp ɗin Hadiza ya shiga yana kallon hoton fuskar ta da ke jiki tana murmushi,murmushi shima ya tsinci kanshi da yi,a hankali ya koma Status ɗin ta yana kallo,hotunan tane ita da Amir a jiki tare da video guda ɗaya nata da wani mutum da ta toshe fuskar shi da heart,nan take ya ƙware ya fara wani irin tari kamar wanda ya shaƙe da dambu ,idanun shine suka firfito ya buɗe ruwan dake gaban shi ya kafa kai ya kwankwaɗa,idanun shi sai zubar da ruwan masifa suke yi, majinar dake tsiyaya a hancin shi ya ja tissue paper ya goge sannan ya sake duba status ɗin,rubutun da tayi a ƙasan status ɗin ne ya firgita shi,a kausashe ya maimaita kalmar,
"My heart beat? Lallai Hadiza baki da hankali,duk irin alamomin da nake ta nuna maki tsawon wannan lokacin ace baki gane me nake nufi ba? Se ki auri heart beat ɗin naki na gani, mtswww aikin banza kawai."
Ko tattara wajen da ya ɓata be yi ba ya shige ɗaki ya shige wanka, ya jima yana watsawa jikin shi ruwa kafin ya fito,ƙananan kaya ya sanya a jikin shi kafin ya faɗa gado ya kwanta hannun shi rike da wayar shi,hotunan shi ya shiga ya nemo wasu zafafa guda biyar ya zuba a status sannan ya dinga duba views ɗin shi ya ga su waye suka kalla,cikin sa'a kuwa ya hango Mommy a cikin masu kallon hotunan, hamdala ya yi ya sake gyara kwanciyar shi yana duba sauran hotunan har da ƙirga seconds ɗin da ta ɗauka kafin ta buɗe na gaba,murmushi ya dinga zabgawa dan kuwa ya san dole ne ma ta faɗa cikin tarkon da ya ɗana mata. Cikin abinda bai fi minti biyar ba itama ta sake zuba wasu hotunan ta guda biyu masu kyau,sannan a ƙasa ta rubuta.
"Matar mai rabo,mai rabon ma wanda yake tafe da sa'a."
Ƙwafa Abdul ya yi sannan ya rubuta mata.
Abdussabour: Hummm Mai rabo da Sa'a ko?
Mommy : Eh inshaa Allahu.
Abdussabour: To Allah ya kawo shi da alkhairi.
Mommy : Amin Yariman Sarkin Garin Ba Mugu ina godiya. Amma zan iya cewa Allah ya kawo shi ma,lokaci kawai ake jira.
Abdussabour: Humm koh?
Bata sake bashi amsa ba ta sauka online zuciyar ta fess kamar an wanke mata ita da omo,ɗakin Innoh ta shiga ta ga tana d'aura farin maggin da take siyarwa da maggi irin na ɗaurin nan,zama tayi tana taya ta kafin ta ce,
"Innoh tinda Allah ya baki lafiya kin ji sauƙi ina so a cikin satin nan na tafi Abuja dan na samu halartar bikin yaran nan su Anisa, kin ga Baaba bata da lafiya ga tsufa yanzu baza ta iya wannan doguwar tafiyar ba indai ba a jirgi ba...."
Baaba ce ta shiga ɗakin rike da farantin silver ta ɗebo soyayyar gyad'a mai gishiri ta miƙawa Mommy sannan ta ce,
"Ballantana ma ba zan je ba,tinda idan naje tarko ake haɗa min dan a raba ni da ɗakin miji na,gwanda ke ki je ina nan zan sa musu albarka."
Dariya Mommy tayi sannan ta ce,
"To shikenan Baaba inshaa Allahu jibi zan shirya in tafi tinda ranar Juma'a za a fara gudanar da shagalin auren."
Haka suka dinga hira har Ɗan Liti ya dawo Mommy ta sanar dashi abinda suka yanke da su Baaba, nan take ya ce, shima zai je dan kuwa Alhaji Baban Gida da kanshi ya yi masa waya ya ce ya je,murna Mommy ta dinga yi dan ko babu komai ba zata je gidan ita kaɗai ba tinda ba wani sabawa tayi da su ba.
Kamar yanda suka tsara kuwa haka tafiyar ta kasance har da ƙarin ƴan rakiya,wato Sadeeq da Sule,a cikin motar Ɗan Liti dik suka shirya suka tafi,a hanya Sule na tuƙa motar Mommy ta riƙe masa hannu ta kwantar da jikin ta zuwa nashi ta yi musu video,tana gamawa ta shiga ta yi editing video da kyau sannan ta saka a status tare da rubuta.
"Alhamdulillah hanyar Abuja ni da masoyi"
Wunin ranar Abdul bai hau online ba sai da dare ya dawo gida yana hutawa shi da Suhailah,a hankali yake duba status din mutane daga ƙarshe ya dire a na mommy,cike da tashin hankali ya miƙe zaune yana salati yana faɗin,
"Wai da gaske yarinyar nan take ! Anya tana da hankali kuwa?"
Ba tare da yasan da ƙarfi ya yi magana ba sai ji ya yi Suhailah ta ce,
"Da wa kake ne Hubby? Wacece take yi da gaske? Me ya faru ka rikice haka?"
Cikin zuciyar shi ya ce,
'Dama da karfi na yi magana?'
A zahiri kuwa sai ya fara kame-kame yana sosa kan shi ya ce,
"Ina zuwa baby bari na je na amsa wannan wayar na dawo,wani aiki ne na bayar a office ake nema a yi min shirme akai,bari dai na dawo za mu yi wata magana da ke."
Kafin ta bashi amsa Abdul ya isa bakin ƙofar fita daga parlourn gidan,takalmi ya shura ya saka a ƙafafun shi ya buɗe ƙofa ya fita farfajiyar gidan,gani ya yi idan ya yi magana a wajen Suhailah za ta iya jin shi,dan haka waje ya fita ya tsaya a bakin gate ɗin gidan shi yana kiran layin Hadiza hankali a matuƙar tashe. Mommy kuwa na can ta shiga dangi ta haɗu da Sadeeqa sai hira suke yi,tana kallon kiran shi take ƙin ɗauka,kamar ba zai sake kiran ta ba,ya daure ya sake kira,sai da ta kusan katsewa sannan Mommy ta ɗauka tare da faɗin,
"Baby ina zuwa na amsa wannan wayar dan Allah." (Da yaron Saddiqa take da ya maƙale mata tinda ta je)
Zuciyar Abdul ce ta yi wani irin tarwatsewa kamar ƙankarar da aka saki akan dutse,cike da sanyin jiki ya ce,
"Baby ? Waye babyn? Wannan ƙaton dake yawo dake gari-gari? Look Hadiza ba zan lamunci kina a matsayin uwar yarona ba ki dinga yawo da ƙatti anyhow,ya kike yin abu kamar wata mara kamun kai ne?"
Wani irin malolon baƙin ciki ne ya tokare wuyan Mommy,a hasale tace,
"Ban gane me kake nufi ba? Kana nufin dan kai baka fito ka bayyana abinda ke ranka game dani ba kana ta dukan taiki sai wasu su ƙi nuna min soyayya kenan ko me? Ina so ka sa a ranka nan da sati uku za a ɗaura min aure,ba zan zauna ina da masoya ba na ƙi aure saboda ina so na zauna na riƙe ɗana a gidan ubansa,ka kwantar da hankalin ka kuma babu me kiran uwar yaron ka mara kamun kai."
Tana gama maganar ta ta kashe wayar ta samu gefe ta rakuɓe tana zubar da hawayen baƙin ciki,me Abdul ke nufi da ita ne? Dan tana bazawara yana nufin maza take bi ko me da har yake kiran ta da mara kamun kai? Wannan karon da gaske take yi,idan har bai fito ya furta mata kalmar da ya kasa ba, to tabbas zata baiwa ɗaya daga cikin maneman auren ta dama ya aure ta kawai,ba zai yu ta yi ta jiran shi ba tana yi masa uziri yana cutar da zuciyar ta tsawon shekarun nan.
Ta jima a bakin ƙofar shiga parlourn tana kuka kafin ta faki idon mutane ta buɗe ƙofa ta wuce ɗakin da aka sauke ta,wato ɗakin Hajiya Baaba,kwanciya tayi a saman gado tana kuka mai tsuma zuciya,cikin kuka ta ce,
"Abdul na gaji ! Na gaji da jiran ka,na haƙura da kai, haƙuri na har abada,da alama babu ƙaddarar da ta rage mana na sake zama a inuwa ɗaya ni da kai,Allah ka zaɓa min miji mai albarka."
Wayar tace ta yi ƙara alamar saƙo ya shiga,kamar ba zata duba ba,sai kuma ta samu kanta da jawo wayar ta buɗe saƙon,abinda ta gani ne ya sanya ta miƙewa zaune tare da dafe ƙirjin ta hawaye masu matuƙar zafi suka hau sintiri a kuncin ta.......
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 107:
_Tsoron ƙin amincewar sake aure na a karo na biyu ne maƙasudin kasa tinkarar ki da ƙoƙon barar zamowar ki uwar ƴaƴana a karo na biyu,ki taimaki wannan bawan Allah'n ya sake zarga maki igiyar auren shi guda uku akan ki.Ina son ki Hadiza ke kaɗai ce macen da nake yiwa so na gaskiya._
Hawayen ta da ke ƙona fuskarta ta share sannan ta ziro ƙafafun ta ƙasan gadon,maimaita karanta saƙon take tayi kamar ta samu wani abu mafi mabimmancin da take son haddacewa. Ba tare da ta san iya adadin da ta karanta ba sai ta samu hannun ta da mayar masa da saƙon shi kamar haka.
_Ka yi sake wani ya riga ka sace zuciyar Hadiza har ta bashi dama ya tura magabatan shi wajen iyayen ta kamar yanda ake yiwa kowacce mace idan an tashi auren ta,sannan bata son a ja dogon lokaci kafin ta kasance da shi,wannan bawan Allah'n ba kowa bane face Abdussabour SARAUTA. Ina son ka sani soyayyar ka ita ce zata yi ajalina idan baka gaggauta aure na ba._
Lokacin da Abdussaboor ya fara karanta message ɗin har ya fara zufa zuciyar shi ta matse waje ɗaya,wani irin tashin hankali da damuwa tare da ɗimuwa ne suka fara rikita ƙwaƙwalwa da zuciyar shi,sai dai yana kaiwa ƙarshen saƙon ya durƙusa ya buga sujjadar godiya ga Allah,wani irin farin ciki ne mabayyani ya bayyana a fuskar shi,yana ɗagowa daga sujjadar ya ga wayar shi a hannun Suhailah idanun ta na zubar da hawaye.
Tinda ya fita waje dan ya yi waya da mommy jikin ta ya bata ba maganar aiki bane kamar yanda yace,dan haka sai ta wuce ɗaki ta zauna tana jiran dawowar shi,sai kuma daga baya ta ji ya dawo amma be shigo ɗaki ba,shine dalilin da ya sanya ta fitowa waje dan ta ga meke faruwa,tana zuwa ta ganshi yana murna ya duƙa yana sujjada,a hankali ta tako ta ɗauki wayar shi ta ga saƙonnin da suka yi musaya shi da Mommy.
Nan take ta ji kamar an dunƙule hannu an buga mata naushi a ƙirjin ta,cikin hawaye ta kafe shi da ido. Abdul kuwa sosa kanshi ya fara yi kafin ya karɓi wayar tashi daga hannun ta,hannun shi ya miƙa dan ya zaunar da ita amma sai ta ƙwace ta harɗe su a ƙirjin ta tana jiran ƙarin bayani daga gare shi,fuskar shi ɗauke da murmushin farin cikin da yake yi ya samu waje a saman kujera ya zauna sannan ya ce,
"Suhailah ki yi haƙuri da kika samu wannan labari ta haka,amma har ga Allah na so na yi maki maganar nan tinda jimawa,ganin babu abinda kika rage ni da shi ne ya sanya ban bijiro maki da maganar ba,ke macece da ta amsa sunan ta mace wadda in dai naƙasu na sanya namiji ƙara aure to ba zan maki kishiya ba saboda......"
Cikin hanzari Suhailah ta katse shi da cewa,
"To me yasa yanzu kake so ka yi min kishiyar? Kishiyar ma da macen da kake ikirarin ita ka ke yiwa so na gaskiya? Kenan zaman haƙuri ka ke yi dani,zaman biyan buƙata ko?"
"No ba haka bane Suhailah ki fahimce ni please,kina da ilimin ki da wayewa dan Allah kar kishi ya sanya ki...."
"...na yi maka illa kamar yanda jahilar matar ka ta yi maka a baya?"
Cikin tsawa da ɗaga murya Abdul ya ce,
"Suhailah Kul ! Kar ki sake ki zagar min mata,da jahilcin nata ta amince zata haihu dani,ke kuma fa? Anya kina so na ma kuwa Suhailah? Dan kuwa me son ka ba zai ƙi haɗa zuri'a da kai ba da gangan."
"Ta nan ka ɓullo kenan ko Abdul? Wato kar na zagar maka mata,a ina ta zama matar taka? To bari ka ji in faɗa maka ban shirya haihuwa ba yanzu,ko zan haihu nan gaba be fi na haifi biyu ba mace da namiji sai na rufe haihuwar."
"Tinda ke kike bada haihuwar da har zaki tsara abinda kike so ba?Suhailah koda baki haihu dani ba na roƙe ki zan dawo da Amir nan gidan kika buga ƙasa kika ce baki yarda ba,to ya kike so na yi?"
"Ka dawo da matar ka Abdul,banda matsala da hakan,matsalata bai wuce kalaman da ka yi amfani dasu ba wajen bayyana mata soyayyar da kake yi mata,wanda na yarda na amince daga zuciyar ka suka fito ba daga bakin ka ba,Abdul ni wacece a wajen ka? Ka taɓa so na ma kuwa?"
Kuka Suhailah take yi sosai saboda kalaman shi sun daki zuciyar ta ƙwarai,cike da tausayawa Abdul ya rungume ta ya yi shiru da bakin shi,ba dan komai ba sai dan gudun kada ya yi karya,da gaske yake yi babu macen da yake yiwa so na gaskiya sama da Mommy,yana son dik wani abu nata,shirmen ta,kwaɗayin ta da abinci,yanda take nuna masa so yana yi masa daɗi a zuciyar shi,yanda take kwalliya ta dage ta koyi abubuwa da dama saboda farin cikin shi,yanda ta zage ta dinga addu'a Allah ya bata haihuwa da shi saboda ta reni ɗan shi ko ƴar shi a cikin ta,bata tsaya ba har sai da burin ta ya cika,yana son komai na Hadiza saboda ta nuna masa soyayya maƙura,abu ɗaya ne baya so yanda ta zafafa a kishin shi,da ace zata rage kishin da take yi akan shi da soyayyar su zata zama bata da mahaɗi a wannan duniyar.
Suhailah da ta kula gaba ɗaya rungume yake da ita kawai amma hankalin shi ya yi wani wajen,sai ta zame jikin ta a nashi ta bar masa parlourn,babu abinda ya mata zafi da ƙarin auren shi,amma fa tabbas yanzu ta san cewa ba zata taɓa wuce Mommy ba a zuciyar shi,dan haka zata maida hankalin ta wajen aikin ta da neman kud'in ta dake bata farin ciki.
Kunya ce ta kasa maida Abdul ɗakin,sai kawai ya shige ɗayan ɗakin ya kwanta,ya so ya sake kiran Hadiza su yi hira amma sai ya ga kamar zai takura mata,message ya tura mata yana tambayar ta yaushe zata koma ƙauyen Ba Mugu? Dan yafi son ko za a je tambayar ya zamana tana gida komai zai faru. Bayan ta sanar da shi ne ya kunna data ya rubuta.
"Alhamdulillah yau ina cikin farin ciki,Allah ka tabbatar mana da alkhairi"
Murmushi Mommy ta dinga yi sanda ta ga status ɗin shi,taso itama ta rubuta wani abu,amma sai ta bari saboda bata son ya ga zaƙewar ta.
Da sassafe Abdul ya tashi ya shirya kamar yanda suka saba, a tare suka karya cikin sauri saboda gudun makara,fuskar Suhailah Abdul ke ta leƙawa yana kallo ko zai ga damuwa da ɓacin rai a tattare da ita amma bai ga komai ba,hasalima tinda ta gaishe shi ta zuba musu abun karyawa wayar ta take ta dannawa,a haka suka gama karyawa ta ɗauki makullin motar ta ta bar gidan bayan ta yi masa sallama kamar yanda suka saba.
Hamdala ya yi a ran shi da Suhailah bata ɗauki abun da zafi ba,alƙawari ya yiwa kanshi dole ya koyi boye yawan rawar kai da nuna tsannanin soyayyar Mommy a fili da yake yi gudun ɓacin ran Suhailah. Da wannan tinanin ya tattara plate ɗin shi ya saka a sink ya wanke sannan ya saka a kitchen wire ya bar gidan.
Koda ya isa office ya tarar da Bilal zaune a bakin gate suna hira da masu gadi,hannu suka baiwa juna suka gaisa,sannan Abdul ya gaisa da masu gadin wajen kafin su dunguma cikin kamfanin nasu,sai da suka kusan rabuwa kowa zai shiga office ɗin shi Abdul ya yi gyaran murya ya ce,
"Amm Bilal ina da magana da kai dan Allah,in zo wajen ka ne ko zaka shigo nan mu yi?"
"Bari na zo nan ɗin,Allah yasa ta samu ne."
Sosa kai Abdul ya yi yana wani sunkuyar da kai ƙasa,murmushi Bilal ya yi dan kuwa tin daren jiya Suhailah ta sanar dashi komai,shi ne ma ya sake kwantar mata da hankali har hakan ya yi sanadiyyar cirewar damuwar ta. Bayan sun shiga office ɗin Abdul sun zauna ne,Abdul ya bijiro masa da maganar maida auren shi da Mommy,hannu Bilal ya miƙawa Abdul tare da faɗin,
"Congratulations man,Allah ya sanya albarka,Allah yasa wannan karon tazo da hankali domin kuwa nauyin dake kaina ya ƙaru,idan da kai ɗaya ne zata taɓa na dugunzuma mata lissafi to yanzu akwai ƙanwa ta,idan wani abu ya sake samun ku zan nuna mata dawanau ce akai na tsabar hauka. Allah ya sa kuma abinda ya faru a baya ya zame mana darasi baki d'ayan mu."
Cike da murmushi Abdul ya tashi daga inda yake ya rungume Bilal,sun jima a haka kafin Bilal ya zare jikin shi daga na Abdul ya na gogewa ya ce,
"Kai sake ni dalla sai wani shige min kake yi meye haka? Ko an faɗa maka nima Hadizar ne?"
Dariya suka fashe da ita a tare sannan suka tafa,a hankali fuskar Abdul ta sauya daga fara'a zuwa damuwa,Bilal ne ya ce,
"Kar ka damu, da kaina zan je wajen mai martaba yau ɗin nan na roƙar mana alfarma,daga nan zan shiga wajen Innah na lallaso mana ita,inshaa Allahu ba za su ƙi amincewa ba."
"Bilal a gaskiya bani da aboki,amini,kuma ɗan uwan da ya zarta ka,Allah ya biya maka buƙatun ka na alkhairi,Allah kuma ya ƙara haɗa kammu da iyalan mu."
"Amin ya Allah,bari na koma Office na kama aiki na dan na gama da wuri."
"To na gode Allah ya nuna min nima na yi maka abinda ranka zai yi fari Bilal."
"Ka riƙe min Suhailah da kyau da amana,idan ka yi min haka ka gama faranta min Abdul."
"Inshaa Allahu zaka same ni mai riƙon amana akan Suhailah,Allah ya bani ikon tsaida adalci a tsakanin su."
"Amin ya Allah."
Wunin ranar Abdul ya yi shine cikin farin ciki,ga chatting da suke yi da Mommy akai-akai wanda tin asali basu yin hakan da Suhailah,ko sallama ya yi mata a WhatsApp tana online sai ta ƙi amsawa har sai ta koma