Showing 201001 words to 204000 words out of 276165 words

Chapter 68 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

mu gaisa na kasa,Yah Shamsu dan Allah ku taya ni da addu'a ina cikin masifa,ina cikin hatsarin rayuwa,ban sani ba ko zan dawo gare ku a raye ko kuma gawata za a kawo muku,wataƙila ma ko gawar tawa ba za ku gani ba,Yah Shamsu kwaɗayi da dogon buri yasa na kai kaina ga halaka.'

Kuka ne ya ƙwace mata,nan ta hau yin shi babu ƙaƙƙautawa,shamsu kuwa jikin shi ne ya hau rawa saboda jin kalaman ta, buɗe baki yayi domin ya mata magana yaji ana faɗin,

'Da wa kike magana?'

Kafin Billy tayi magana an kashe wayar,cikin sauri ya hau bin layin da ta kirawo shi dashi da kira,cikin rashin sa'a ta fara ringing ya ji ta katse,sake kira yayi ya ji wayar a kashe,hankali tashe ya miƙe tsaye ya yi hanyar fita tsakar gida,tinda ya fita daga ɗakin shi bai tsaya a ko ina ba sai a ƙofar ɗakin iyayen shi,sallama ya dinga yi musu tare da ƙwanƙwasa ƙofar,cikin magagin bacci mahaifin shi ya tashi,wayar shi ya ɗauka ya duba lokaci,gani yayi ƙarfe ɗaya da minti biyar na dare,cike da tsoro ya durƙusa ƙasan gado ya ɗauki barandami da gora,Ta Annabi na ganin haka jikin ta ya hau makyarkyata cikin yin ƙasa da murya tace

"Malam me yake faruwa ne?"

"Nima ban sani ba,muryar shamsu nake ji yana sallama cikin damuwa, ban sani ba ko miyagun da suka shiga gidan Alhaji Tanimu ne suka hauro mana tinda sun ga kwana biyu muna cikin alheri."

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una."

Wani bugun ƙofar tare da sallamar shamsu ne suka sake firgita su Mai Dusa, a kiɗime Ta Annabi ta zagaya gefen gadon ta tayi goho ta b'oye kanta, shi kuwa Mai Dusa cike da tattaro dika jarumtar shi ya nufi ƙofar ɗakin nashi yana rage murya yace,

"Shamsu kai da su waye?"

"Baba dan Allah kuyi sauri ku buɗe mana ni ne fa."

Da jin haka sai Mai Dusa ya zuba makaman shi a bayan ƙofa ya buɗe a hankali ya fita, ganin shamsu shi kaɗai ne ya kwantar masa da hankali yace,

"Ah ah ɗan Baba kai kaɗai ne?"

Cike da mamaki Shamsu yace,

"To da ni da su wa zamu zo? Baba ba wannan ba dai,Bilkisu ce ta kirawo ni tana kuka yanzu,da alama tana ciki tashin hankali da damuwa."

Murmushi Mai Dusa yayi sannan yace,

"Kai babu wata damuwa da take ciki,ko jiya mun gaisa da ita ni da mahaifiyar ku,har ma ta turo kud'in da ka ga an siyo abinci an raba wa mutane."

"Baba baka ji me nake faɗa maka bane? Ita da kanta ta kirawo ni yanzu tace mu taya ta a addu'a rayuwar ta tana cikin hatsari,har tana maganar kisa da mutuwa,dan Allah Baba a kai maganar nan wajen Sarkin malamai a hau yi mata addu'a Allah ya dawo da ita gida lafiya."

Ta Annabi ce ta fito ta tsaya tana dariya tace,

"Yo malam ka barni can gefen gado nayi goho ina boye kamar kaza."

"Ke ba ɓarayi bane,wai kin ji Bilkisu ce take cikin matsala ana mata barazana da rayuwar ta,shine ta kirawo yayan ta take cewa a taya ta da addu'a."

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,Allah ka kare min ƴata a duk inda take daga dikkan sharrin mai sharri."

"Amin ya Allah, kuma maganar ka shamsu gaskiya ne, Allah ya kaimu gobe zan je wajen sarkin malamai a sa abun a addu'a,Allah ya kare mana ita a duk inda take."

"Amin Baba,sai da safen ku."

Bayan sun yi sallama sai kowa ya koma ɗaki,amma gaba ɗayan su bacci ya ƙaurace wa idanun su,banda tinani da addu'o'i babu abinda suke yi,su ba masu dogon ilimin addini bane balle su yi alwala su yi nafila har su roƙi Allah mafita, amma a hakan ma da suke zaune bakin su bai dena neman taimako daga wajen Allah ba.


****************************

Da sassafe motar Ɗan liti da ta kwashi Baaba da Sadeeq da Abbe zuwa Abuja ta tashi, Innoh taji baƙin ciki sosai kamar ta kurma ihu,amma haka suka wuce babu wanda ya bi ta kan ta,Ameerah kuwa ba tare da ta sanar da kowa ba ta gama haɗa kaff kayan ta tana zaune zaman jiran Shamsu yazo su wuce gida.


*********************

Sule ne ke ƙarasa sanya wasu riga da wando masu kyau da suka karb'i kalar fatar shi da hutun kusan wata guda ya sanya shi murmurewa,dik wata muguwar ramar nan da ƙobarewar da sule ke da shi a baya ta miƙe,farin shi ya fito fess saboda a rana Hajiya kan saka shi yayi wanka sama da biyu.

Da ƙyar yanzu ma ta yarda zata barshi ya tafi Abuja saboda sunan Saddiqa da ya nuna mata sanarwar da ya gani a Facebook Munir ya saka,gefe ɗaya kuwa ya fake da sunan ne yana son ya je wajen wasu abokan shi da suka kwaɗaita masa harka da manyan matan Abuja.

Shi yanzu Hajiyar shi ta buɗe masa ido ya gane daɗin harka da manyan mata,ririta shi take kamar ƙwai,tattalin shi take yi kamar wani jinjiri,dan haka yanzu ya gane komai munin mace, komai kyawun ta in dai irin su Hajiyar shi ne zai bi su dan ya samu nerori, tinda yake account ɗin shi bai taɓa ɗaukan dukiyar da yake da ita ba a yanzu,dan haka shi kam wannan harka ta karɓe shi bai ga ranar bari ba,a ciki yake so yayi gida da mota ya kama sana'a,wataƙila ma har yayi aure.

Sai da ya gama shiri tsaff ta riƙo masa ɗan ƙaramin akwatin shi wanda suka siyo a shopping ɗin da suka fita a daren jiya,sai wani Shagwab'a take yi tana yi masa mitar kar ya jima idan ya tafi,cikin nuna mata kulawa yace,

"Haba Baby Nice d'ina ni kaɗaiiii, idan na je na jima in samu natsuwa a ina? Ai ana gama suna zan dawo, kin ga ita ƙanwata da na zo suna wajen ta jego take, d'ayar mai suna Ameerah itama jegon take ba za su samu damar zuwa ba, to wannan uban mu ɗaya idan ban je ba za su ga na yi wariya a tsakanin su,dan haka idan naje ana gama suna zan dawo."

"To Allah ya kiyaye Habibina,Allah ya dawo min da kai lafiya I love you."

Yaƙe haƙori Sule yayi ya kasa mayar da martanin I love you ɗin da aka faɗa masa,akwatin shi ya karɓa ya manna mata kiss sannan ya bar parlourn ya tafi yana ɗaga mata hannu,ya na buɗe ƙofar gidan zai fita ya ci karo da wani mutum baƙi kan shi sol babu gashi sai sheƙi yake yi,a tsorace Sule ya duba bayan mutumin yaga wasu ƙattin maza biyu na take masa baya ɗaya da jaka a hannun shi riƙe wadda da alama ta wannan bawan Allah'n dake gaban shi ne tsaye, wani irin yawu Sule ya had'iya ya fara ja da baya yana komawa cikin gidan....
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI









RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨











PAGE 82:










Ganin yanda jikin Sule ya hau makyarkyata ne ya baiwa Hajiya dariya,da kanta ta ƙarasa gaban Sule ta sake buɗe masa ƙofar ta ce,

"Sai mun yi waya ko? Allah ya kiyaye hanya."

Cike da tsananin mamaki ya kalli wajen da Alhajin yake sai ya ga wayam babu kowa,murmushi Hajiya tayi masa sannan ta ce,

"Kar ka wani samu damuwa,babu abinda zai ce dan ya gan ka, a tunanin ka da waye yake bani kud'in da nake kashewa irin ku idan ba shi ba? He was never around,zan yi ta zama ne a haka ba ɗan ɗebe kewa?"

Wani yawu Sule ya haɗiya cikin sauri ya ja akwatin shi ya bar gidan,hankalin shi har a wannan lokacin bai kwanta ba,ga yanayin unguwar irin ta masu hannu da shuni ce ko machine ɗaya be gani ba ballantana adaidaita sahu,tafe yake yana magana shi kaɗai kamar wanda ya zare,cikin tsananin mamaki ya furta,

"Amma dai mijin matar nan mugun kidahumi ne,ta yaya zai dawo daga tafiya yaga namijin da bai sani ba a gidan shi kuma ya ƙyale shi? Idan ni ne ai sai na yi ajalin duk wanda na gani a gida na da sunan kwartanci."

Ƙarar mota yaji a bayan shi ta tsaya da ƙarfi, a kiɗime ya juya ya na rarraba idanu,ƙartin da ke takewa Alhaji baya ya gani sun buɗe mota sun fito, ɗaya daga cikin su ne baƙi tittirna ya yi wa Sule fito tare da nuna masa ya shiga su tafi,sakin akwatin hannun sa Sule ya yi ya durƙusa a ƙasa yana kuka,cikin tsananin tashin hankali ya ce,

"Dan girman Allah ku yi hakuri,ba zan sake zuwa gidan nan ba,yanda na bar nonon uwa ta har abada na bar maku gidan ku har abada,dan Allah kar ku kashe ni."

Fitsari ne ya fara tarara a jikin Sule bakin shi kuwa ya ƙi dena bada hakuri,wani gigitaccen mari yaji an sauke masa, ko uffan bai sake cewa ba ya shiga motar ya na hawaye tare da wani irin nishin damuwa da tashin hankali,yana shiga motar sauran mazajen da suka fito suma suka afka suka ja mota da ƙarfi suka bar unguwar da Sule.

Waya suka yi wa Alhaji yana ɗauka suka ce,

"Alhaji gashi fa mun damƙo ma shegen a kai shi can ma'ajiya ko?"

'Eh a ajiye min shi ina da wasu tambayoyi da zan yi masa,domin kuwa da alama nema na ne na wata da watanni yazo ƙarshe,dik yanda aka yi yaron nan na da alaƙa da Sweet H.'

"To Alhaji an gama."

*****************************



Da la'asar sakaliya su Baabaa suka isa garin Abuja,tinda Baaba take zuwan ta bai fi biyu ba,shi ma da ƙyar da siɗin goshi ta je,dan haka sai taga wajen kamar an sauya mata shi,gidan ya haɗu matuƙa,cike da murna Ummi da su Khaleesat suka fito tarbon su,itan ma banda washe baki babu abinda take yi.

Drivern da ya yi wa su Ɗan Liti jagora ne bayan sun yi waya sun sanar da sun shigo Abuja ne ya tintsire da dariya,kallon yanda Ɗan litin ke sake buɗe haƙora yana kallon gidan ya yi,cikin dariya yace wa Ɗan liti,

"Aboki na rufe bakin ka kar ƙuda ya faɗa,ko da yake shi ƙudan Abuja daban yake da na ƙauye."

"Ai dole ya zo daban da irin wanda muka sani, ka duba ka ga waje aljannar duniya malam,ashe haka Baban gida ke da arziƙi muke ƙauye muke fama da na masara?"

Sadeeq ne ya ce,

"Ai Baba kowa na duniya da arziƙin da Allah ya rubuta masa zai ci in ji malamin mu,dan yana da kuɗi be zama dole sai ya yaye maka rayuwar talaucin da kake ciki ba, shi Allah ya zaɓa ya baiwa dukiya saboda ta zame masa jarabawar shi,idan ya yi amfani da ita yanda ya dace ta yi sanadiyyar shigar shi aljannah,idan kuma ya kauce hanya saboda yana da dukiya zata iya kai shi wuta,haka abun yake a ɓangaren dik wani talaka,idan talaka ya zama mai wadatar zuciya ya yi ibada tsakanin shi da Allah, sannan ya yi hakuri da abinda Allah ya hore masa to sai ta kai shi aljannah,idan ya yi akasin haka wuta zata kai shi,ai Abbah na ƙoƙari ma Baba,yana fitar da zakka ya baiwa dangin shi,ya na yi mana ihsani, sai dai duk wannan abubuwan da yake mana ba zai taba yanke mana talauci ba idan Allah bai nufa ba."

"To suda ya isa haka,ahhh nace to suda ya isa haka,mu je ciki mun tsaya anan wajen masu aikin gida."

Kayan jikin Ɗan Liti mai gadi ya kalla suka haɗa ido da driver sai suka bushe da dariya suka tafa,Sadeeq gaba ya yi cikin sauri dan baya son yaji me za su faɗa akan Mahaifin nashi,ko da ya shiga sai ya tarar da Saddiqa zaune daf da Baaba kamar wata ƙaramar yarinyar da ta ga mahaifiyar ta,da sauri ya isa gare ta ta tashi cikin sauri itama suka rungume junan su,a tare suka sauke ajiyar zuciya kafin Saddiqa ta ɗaga kan Sadeeq ta kalle shi,gani tayi ya ƙara girma ya yi haske sosai fiye da da,ga wasu ƴan kumatuttuka da ya yi,hamdala tayi a zuciyar ta dan kuwa dik wanda ya ga Sadeeq zai gane yana cikin kwanciyar hankali.

Munir ne ya ce,

"Hello malam Sadeeq ko har an manta dani ne?"

Da sauri Sadeeq ya je wajen Munir ya bashi hannu suka gaisa cike da farin ciki, Baaba ce ta miƙawa Ɗan liti jaririn a dai-dai lokacin da Saddiqa ta durƙusa a gefen shi tana gaida shi,ƙarbar yaron yayi yana mai jin ƙaunar shi a cikin ran shi,kallon Saddiqa ya yi ya ce,

"Allah ya jiƙan Yadikon Sule, da tana nan da nasan ba za ta zo ba saboda kunya,amma kuma na san zata so shi kamar ta maida shi cikin ta,zuciyar ta cike take da soyayya,bata ƙin kowa, bata nufin kowa da sharri sai alkhairi."

Kuka ne ya ƙwace wa Ɗan liti wanda hakan yayi sanadiyyar sanya mutane da dama matsar ƙwalla, ciki har da Sadeeq da yake tsananin kewar mahaifiyar tashi a koda yaushe.

Munir ne ya zauna a gefen Ɗan liti ya ce,

"Ka san sunan da muka sanya wa babyn kuwa?"

Girgiza kai Ɗan liti ya yi yana share hawaye da hannu ɗaya,

"Sunan shi Zubair amma za mu dinga kiran shi da Suhail."

Washe baki Ɗan liti ya yi ya kalli Saddiqa dake bin Munir da kallon mamaki,dan kuwa ba haka suka yi da shi ba, sunan Abbah za a saka wato Alhaji Baban gida, sai gashi ya sauya ya ce sunan shi Zubair,cike da farin ciki Ɗan liti ya hau godiya mutanen parlour duk sai suka hau yi masa dariya.
Saddiqa kuwa kallon Munir take da tsantsar so da ƙauna tare da girmamawa,Baabaa ce tace,

"Alhamdulillahi Ɗanli an yi takwara,Allah ya raya mana ya sanya albarka, to ba wannan ba, wai ni ba cewa aka yi yau ne suna ba da an gama a yau zamu juya?"

Dariya kowa ya hau yi mata a wajen, Ummi tace,

"Ai ba yau bane suna Hajiya Baabata sai gobe in Allah ya kaimu,goben da an gama suna sai kawai a maida ke gidan ki tinda dai dama darajar jinjiri muka ci aka zo mana."

"Ahh toh, gwanda a hanzarta a yi abinda za a yi a maida ni ɗakin miji na."

Tashi tayi tana takawa tare da neman inda zata shiga bayi, Anisah ce ta kama hannun ta tayi mata jagora har ɗakin da aka gyara mata,ko da Baaba ta shiga ɗakin sai ta tsaya turus tana kallon yanda aka tsara shi,ɗaki ne da ya ji kayan more rayuwa an kafe ƙaton hoton Baaba kamar a kirawo ta ta amsa,washe baki tayi ta zauna a bakin gado tace,

"Allah sarki Baban Gida, tinda na ƙi dawowa nan sai ya ajiye hoto na ya dinga gani yana jin daɗi."

"Ah toh ba dole ba Baaba, ke da gidan ɗan ki amma kin ƙi zuwa ki sakata ki wala ki bararraje,kowa so yake yaga yana da wani makusanci me kuɗi a Abuja ya zo,amma ke kin kafe kin nace sai dai a bar ki a ƙauye."

Murmushi Baaba tayi kafin tace,

"Yaro yaro ne,ai bari ki ji ƴannan,a yanda zamani ya koma yaran yanzu basu son zaman surukan su a gidan su,ke ko ma ana so a gani na uwar miji idan tana da nata muhalli to tayi zaman ta a can shine mutuncin ta, shi kuma ɗan nata da matar shi su ji tsoron Allah su dinga kyautata mata, su dinga kai mata ziyara akai-akai,abun duk da suka ci ko da ba za su baiwa mahaifiyar mijin sak irin shi ba to su kwatanta,idan akai haka kowa sai ya zauna a inda yake cikin aminci,kai baka takurawa surukar ka ba, itama bata gaji da kai ba ta takura maka."

Gyad'a kai Anisah tayi cike da gamsuwa da bayanin Baaba, banɗaki ta raka Baabaa ta cika mata ruwa a buta, sai ta haɗa mata na wanka ta fito.

Kafin Baaba ta gama wanka da alwala ta fito an kawo mata abinci kala-kala, an jere a saman carpet,ga abun sallah nan an shimfiɗa mata,jin daɗin karamcin da aka yi mata ne ya sanya ta dinga sawa surukar ta ta albarka,a haka ta tada sallah ta yi azahar da la'asar dika,sannan ta zauna ta yi addu'a,tana idar wa ta hau duba abincin,sai taga tuwon alkama ne da miyar ɗanyar kuɓewa ya ji ganda da kifi ga nama a ciki kamar ka musu magana su amsa,kunun shinkafa da zob'o kuwa suna nasu mazubi suma,sai farfesun kan rago da ya sha kayan ƙamshi,hamdala Baabaa tayi ta zuba dai-dai cikin ta sannan ta hau ƙwalawa Sadeeq kira.

Saddiqa ce ta shiga ɗakin riƙe da jariri a hannun ta ta zauna a gadon Baaba ta fara shayar da shi,sai da ta gama mannawa yaron abincin shi sannan tace,

"Baaba ki ci abincin ki, in dai Sadeeq ne shima yana can shi da Baba suna cin nasu,ai kowa an zuba masa."

"Auu to shikenan,ai na zaci ko dama mu biyu ne tinda na ga da yawa."

"Ah ah naki ne ke kaɗai,Ummi ce da kan ta ta dafa maki,su kuma nasu Anisah da Khaleesat ne suka dafa."

"Allah sarki, Ya Allah ka yi wa yarinyar nan albarka,yarinya mai ladabi da biyayya, a wannan zamanin da surukai suka raina surukan su ita bata da burin da ya wuce na ta ganni cikin farin ciki, Allah yasa ki yi koyi da halin ta ki dinga kyautata mata."

"Amin Baaba, ai Ummi ta daban ce, dik yanda naso na kyautata mata sai ta ninka min abinda na yi mata sau goma,haka nan Allah ya yi ta mai yawan kyautatawa ce ga duk wanda Allah ya haɗa ta dashi,har maƙotan ta bata bari ba wajen yi musu mu'amala mai kyau."

Haka Baaba da Saddiqa suka dinga tattaunawa kafin daga baya su Khaleesat su sallama su shiga suma, da misalin ƙarfe biyar da rabi mai ƙunshi ta zo,babu jimawa aka fara yi wa mai jego ƙunshi,sai da aka gama da ita ne aka yi wa su Khaleesat,daga karshe ta yi wa Ummi ta sallame ta ta tafi.

Washegari Baaba ce ta yi wa jinjiri wanka irin na tsofaffi,yaro kuwa yaji ruwan zafi sai bacci yake zubawa,mai kwalliya ta musamman Ummi ta ɗakko tazo ta tsarawa mai jego da su Anisah kwalliya, Hajiya Sa'a da sauran ƙawayen Ummi duk sun halarci suna,taro ya yi taro mai jego ta samu gift sosai daga ƙawayen Ummi da abokan aikin munir da Abbah, Saddiqa ta ji daɗi sosai tayi murna da farin ciki, Innar ta ce ta kira ta a waya ta taya ta murna tare da yi mata alƙawarin idan sun dawo daga kudu za su zo barkar haihuwa.

Da misalin ƙarfe uku na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login