Showing 141001 words to 144000 words out of 276165 words

Chapter 48 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

gida, a tsakar gida ta tarar da Innoh da su Naja da Mommy da mutanen unguwa an baje lefen ana ta kallo ana yabawa,Innoh da bata da sirri sai da ta sanar da mutanen unguwa kafff yanda aka yi Shamsu ya bada kuɗin lefe, da yanda mijin mommy ya bada na akwati da karin kuɗin da suka ƙaro kayan lefen, takaici ne ya sa Naja jin haushin kanta da ta bawa Innoh labarin abinda ya faru, tashi tayi ta hau haɗe kayan tana faɗin,

"To jama'a muna gayyatar ku gobe da yamma za a kai amarya ɗakin ta, duk wadda take so a raka amarya da ita sai ta shiryo tazo,"

"To Allah ya kaimu, Allah yasa albarka,"

Haka mata suka yi ta sanya albarka, Ameerah kuwa ta zame ta wuce bangaren Baabaa ta zauna tana ta ciye-ciyen abubuwan da ta siyo a kasuwa, tana duba sauran tarkacen da ta siyo.

Bayan tafiyar mutane ne Naja ta kunna Icce ta haɗa ruwan wankan da ta zuba masa ganyen magarya a ciki kamar zata wanke gawa,sai da ruwan nan ya tafasa ya tafarfashe sannan ta kindima a ƙaton baho ta surka tace wa Ameerah ta zo suje ta wanke ta,shaving stick ne a hannun ta da sabulu da soso, sai kwalbar turaren almuski, kuka Ameerah ta fara yi tana faɗin,

"Alqur'an ni bana so ki barni nayi wanka na da kaina, haka kawai da girma na da komai ki tasa ni a gaba kice zaki yi min wanka?"

"Yasin se na miki wankan dan uwar ki,kin ji warin da kike yi kuwa Ameerah? Ke yanzu ba abun kunya bane namiji da kan shi yace ki sai turare da yawa saboda yana jin wari a jikin ki? Kin san Allah idan baki shige cikin bayin nan ba na ɗakko iccen can sai na dake ki dashi, kin san hali na ai,lokacin wasa a yi wasa, lokacin da ba na wasa ba a maida hankali a yi abinda ya dace haba,"

Tin Naja na faɗa sai da ta koma lallashin Ameerah kafin ta yarda suka shiga bandakin,ba ƙaramin daurewa Naja tayi ba wajen wanke Ameerah har tayi mata shaving,wani irin wari take yi mai maƙaƙi a wuya,ita kanta da aka gama yi mata wankan aka yi mata shaving hammata da ƙasan ta sai da taji iska na shigar ta, a bakin ƙofa ta tsaya ruwa na ɗiga daga kanta da ya sha wanki da omo da ruwan toka tsabar dattin da ya haɗiya.

Brush sabo Naja ta ciro da toothpaste ta baiwa Ameerah tace ta wanke bakin ta, babu musu ta karba ta wanke bakin ta tasss har tana ji wa kan ta ciwo, tana gamawa ta lakuci toothpaste ɗin ta sha tace,

"Aunty Naja wannan makilin ɗin akwai shegen zaƙi kamar an saka masa sikarin,"

"Ko uwar sikarin aka saka masa ba, dalla bani nan,gashi nan kullum da safe da dare ki dinga wanke bakin ki da shi, da kin ga gashi ya fara fitowa a hammatar ki da gaban ki ki saka irin wannan (shaving stick) ko reza ki aske gashin wajen saboda dik wankan da zaki yi idan da gashi a wuraren nan zaki ji kina bashi musamman idan da damshi a jikin su, Ameerah ko baki yin kitso ki dinga wanke kai kina gyarawa dan Allah, ki duba Mommy ki gani, bata kitso amma saboda gyara gashin ta da take yi gashi nan ya koma kamar na turawa,da da bata waye ba ana saka kumfar lox tana cinye gashin gashi yanzu an waye ana amfani da kayan kamfani ya dawo,"

Dariya Naja da Ameerah suka hau yi, ita kanta Mommy bata ji haushi ba ta tabbata maganar Naja gaskiya ne, dan dama tana da gashi danƙarewa da cinyewar da ya dinga yi a baya dik ta dalili rashin kulawa mai kyau ce,yanzu da yake samun kulawa gashi nan sai san barka,murmushi ta sake yi tace,

"Auntyn mu maganin kukan mu, Allah dai ya kawo miki miji ya mori wannan gayun naki, ni fa ina mantawa da shekarun da ke tsakanin mu dan sai in dinga jin ki kamar wata ƙawa ta Aunty Najancy,"

"Ehhh tinda ban kai uwar ku girma ba dole ku raina ni mana, da jikin Babar mu nayi bana Baba ba da kun isa ku ganni yar firit haka har ku raina ni?"

Innoh kanta ta ji daɗin yanda ƙanwar tata ta gyara mata Ameerah, godiya ta dinga yi mata, suna yin la'asar ta sa Mommy a gaba dan su tafi gidan ta ta ga ita kuma wace uwar take yi a gidan da ta kasa girka komai.

Kuɗi Innoh ta baiwa Naja ta ƙi Karb'a tace gudummawar ta kenan a matsayin ta na uwar Ameerah,godiya Ameerah tayi wa Naja wanda yin hakan yayi matuƙar basu mamaki, duba da yanda halin ta yake bata san tace wa kowa na gado ba.

Daf za su bar gidan ne suka haɗu da Sule suka gaisa ya wuce gida su kuma suka tafi gidan Mommy.


************************


Kwance take a saman makeken gadon da yake mallakin tane a yanzu in ji Baabaa, dan kuwa abinda yake mallakin Manniru ai na matar Manniru ne a cewar ta, ta yi wanka ta sanya rigar shan iska gaban ta dik littattafai ne da ta gama karantawa ba jimawa,wayar ta ce take ringing tana neman agaji,cike da murmushi ta sanya hannu ta ɗauka ta amsa kiran tare da karawa a kunnen ta.

"Hayyakallah ya ruhee,"

'Hayyakillah habibty,ya kike, ya yau? Ina fatan jarabawar yau bata baki wahala ba ko?'

"Alhamdulillah Zaujee, komai normal,jarabawa kam tayi sauƙi sosai dan kuwa ban zaci Physics ɗin nan zai min daɗi ba,"

'Alhamdulillah power of du'a kenan ake faɗa maki,ko kin manta kalar addu'ar da muka dinga yi?'

"Ban manta ba gaskiya, na gode sosai masoyi, ya su Ummina da Abbah da su Hafsat? Ina fatan kowa na lafiya? Ya office?"

'Dik alhamdulillah kowa na lafiya, office kuma babu daɗi,'

"Ayyaa ka ƙara hakuri, Allah ya sauƙaƙa lamuran,"

'Ameen, amma kam lamura ba wani saukin da za su yi kina nesa dani, na matsu ki gama jarabawar nan,wai ni sauran sati nawa ma ki kammala ne?'

Dariya sosai Saddiqa tayi kafin tace,

"Sauran wata biyu na kammala,"

A rikice Munir yace,

'What ! Wata biyu fa? Tabb lallai kuwa zan dawo Ƙauye na zauna har se kin kammala dika,'

Dariya ta sake yi sannan tace,

"Wasa nake yi maka, sauran sati biyu da kwana biyu inshaa Allah,"

'Ai na san tsokana ta kike yi, ko da bamu kai watannin da kika lissafa ba balle yanzu da abubuwan technology ya yawaita,Allah ya bada sa'a my love, i miss you so much,'

Lumshe ido Saddiqa tayi tana jin wata iriyar kewar Munir da shauƙin son ganin shi na taso mata a ran ta, hakan ne ya haddasa bugawar zuciyar ta ya ƙaru hawaye suka fito daga idanun ta, cikin murya mai rawa tace,

"I miss you too my love,ina son ganin ka sosai Hubby,"

'Da gaske kina son gani na? Kashe ki kunna data mu yi video call,'

Cike da murna kuwa tayi yanda yace, a lokacin da ta ga Munir kwance a gadon shi na Abuja sai da ta tsorata, tayi zaton ko a ƙasar waje yake, shanye mamakin ta tayi dan kuwa an ce dama Alhaji Baban Gida na da kuɗi sosai, shi kuwa Munir banda kallon surar jikin ta babu abinda yake yi, cikin furzar da iskar bakin shi yace,

'Alhamdulillah ya rab,'

"Na'am? Kayi magana ne?"

Da sauri yace,

'Ah ah ban ce komai ba, uhumm gani to kin ganni, me zaki yi min?'

Murmushi tayi cike da jin kunya sannan tace,

"Kallon ka kawai zan yi tayi har sai na ƙoshi,"

Ba tare da zato ko tsammani ba Baabaa ta afko d'akin tace,

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una Saddiqa ke da wanne aljanin kike magana nake jin muryar ƙato a dakin naki? Na shiga uku ni Baabaar Abbe me zan ce da Manniru idan yaji labarin matar shi tayi gamo da aljani na miji?"

Dariyar Munir ce ta karaɗe ɗakin ta sa baba kurma ihu tana salati tare da karanta kulhuwallahu ahad,dariya sosai Saddiqa take yi tana nuna wa Baabaa Munir ta screen ɗin sabuwar wayar tata, a hankali Baabaa ta natsu tace,

"Yanzu a haka zan iya ganin Baban Gida Shima?"

"Sosai ma, zaki iya ganin duk wanda kike so ta haka Baabaataaa"

Saddiqa ta faɗa tana rungume Baabaa da har a daidai wannan lokacin nutsuwa bata gama shigar ta ba, haka suka ci gaba da hira suna ta wayar wa da Baabaa kai game da video call.

A can gidan Mommy kuwa......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI










RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨












PAGE 56:






Idanun Naja akan gajeran wandon Abdul ya fara sauka, cikin sauri ta kauda idanun ta tana salati tare da tafa hannaye ta duba ƙasa inda bireziyar Mommy ke kwance kamar a nan ne ya kamata ace an gan ta, dik irin halin jin kunya da nauyin da Naja ta shiga bai dami Mommy ba dan kuwa cire mayafin ta tayi tare da yin wurgi dashi a ƙasa, sannan ta yarda takalman ta a tsakiyar parlour zata shige kitchen, cikin tsawa Naja tace mata,

"Kina shiga kitchen ɗin nan ba tare da kin kwashe kayan nan ba Hadiza zan ci maki mutunci, shashasha mara hankali da tunani kawai, yanzu da ace surukar ki ce tazo gidan nan haka zata yi wannan mummunan gamon?"

Cikin rashin fahimta Mommy ta juyo ta kalli Naja dake sababi tace,

"Aunty Naja wanne kaya zan kwashe kuma daga zuwan mu? Ki bari na d'akko maki lemo da ruwa ki dan jiƙa maƙoshin ki mana,"

"Abinda yafi lemo da ruwa zaki ɗakko min, Hadiza ki fita a ido na na rufe fa ! ba zaki wuce yanzu ki kwashe ɗan kamfan mijin ki dake zaune dafi'an bil amanati a saman kujera ba? Dibi rigar maman ki a ƙasa yanzu dik wanda ya shigo ya gani ya san me ya faru? Ke baza ki ji kunya ba ashe?"

Wata iriyar dariya Mommy ta kece da ita har tana zama, cikin dariyar ta hau kwashe kayan su ta nufi ɗakin ta ta wurga su a saman gado ta fito tana ci gaba da dariya tace wa Naja,

"Gaskiya Aunty Najanmu kina da matsala, to meye dan an ga boxer ɗin shi da bra d'ina a parlour? Naga dai ba mu aka gani tsirara ba ko?"

"Na yarda baki da hankali Mommy, abinda zuciya ta ke ta raya min ya tabbata, mu je kitchen ɗin mu fara ɗora abincin idan yaso sai mu dawo a gyara gidan lokaci na tafiya, yanzu ace gida ko sati ba a rufa ba da shigar shi dik kin halaka shi haka? Allah ya kyauta,"

Cikin ƙanƙanin lokaci Naja ta sa Mommy a gaba dan dole ta nuna mata yanda zata dinga kula da kayan miya da nama idan an kawo, da yanda zata dafa ta soya har ta dafa shinkafa da miya, suna gyaran gidan take koya mata yanda ake yin jalof ɗin taliya da na shinkafa,ta koya mata yanda ake soya dankalin hausa da na bature da yanda ake yin simple abubuwan da ta sani a matsayin ta na wayayyiyar da ta shiga garuruwa ta san abubuwan wayewa, a dik abubuwan da ake koyawa Mommy tafi gane na bedroom, dan bata da sauƙi ta wannan ɓangaren, a kullum so take ta dinga burge Abdul da salo-salon da zai zauna daram a zuciyar shi, gane hakan da Naja tayi ne ya sanya ta sakin murmushi ta samu locker ɗin dake gefen gadon Mommy da ta gama gyarawa ta zauna tace wa Mommy,

"Zauna Mommy na sanar dake wani abu da baki sani ba,"

Waje Mommy ta samu ta zauna ta baza kunnuwa tana son taji wani kayan matan da Naja zata sanar da ita dan ta haɗa ta sha ta gigita Abdul a gado, cike da zumud'i take kallon Naja, cikin kwantar da murya Naja tace,

"Hadiza ina so ki san cewa shi aure fa da kike gani ibada ne, ba wai dan kawai muna son mutum yana son mu ba sai kawai mu aure shi saboda wannan soyayyar, ah ah soyayya na da mahimmanci a cikin aure domin tana sawa a yi ibadar ta daɗin rai babu takura kamar auren da aka yi shi na dole.

Hadiza ina so ki sani ko da kika ga muna zuwa neman taimako ba wai hankali da tunani muka rasa ba, muna nan muna fatan watarana mu tuba mu dena dan babu bawan dake fatan ya dawwama a zunubi sai wanda bai san wanene Allah ba,idan kasan Allah kasan cewar in ka aikata kyakkyawa zaka haɗu da shi ta fuska kyakkyawa sannan idan ka aikata mummuna zaka haɗu da shi ta mummunar siffa to fa dole ne ka dinga addu'ar kar Allah ya kashe ka a kan hanyar ɓata, dan haka ki buɗe kunnen ki da kyau ki saurare ni, kar ki yi min kallon ban san me nake yi ba.

Hadiza ba kwanciyar aure bane kawai jigon aure,kina iya zama macen da tafi kowacce mace gamsar da mijin ta koda mata huɗu gare shi, amma yafi son wata akan ki, amfanin ki a wajen shi kawai shine ki kawar masa da kishin ruwan shi, da ya samu natsuwa dake ya komawa wadda yake asalin so,kin ga kenan ba kwanciyar aure ne kaɗai rayuwar aure ba ko ? tinda ana iya zama da wadda aka san ba za a iya kwanciyar auren da ita ba saboda wata lalura da take da ita, amma sai soyayya ta sa a kasa rabuwa da ita.

Mommy ki sani ita rayuwar aure ana so mace ta iya girki dai-dai gwargwado, ko da baki zama ƙwararriya ba kar a same ki sifili a bangaren girki wanda a yanzu a matakin da kike kenan,ba a son ƙazamar mace Hadiza, koda ba a same ki mai tsananin tsafta ta bada misali ba to fa kar a same ki ƙazama, sannan ana son mace mai ladabi da biyayya mai sanin ya kamata,macen da ta iya magana mai daɗi ba a tsaitsaye ba kamar shinkafar da bata dahu ba, sannan ana son macen da ke da kirki ma'ana mara rowa mai yawan fara'a da kamun kai, Hadiza a halayen ki kowa yana yaba maki baki da rowa sam, to dan haka ina so ki haɗe wadannan abubuwan da na sanar dake ki riƙe gam, saboda da su ne zaki juya Abdul koda bamu sake nemo maki taimakon komai ba,wannan Shagwab'ar da naga kina yi masa a mota ɗazu ki riƙe ta da kyau domin kuwa babban makami ce, Hadiza ba a ce sai kin zama 100% ba a gidan mijin ki, ana so dai ki zama kina da kaso 80% a ɓangaren kula da gida da mijin ki.

Dan haka ga wani haɗin zan sanar dake ki dage ki dinga yin shi, zaki sha mamakin yanda mijin ki zai gigice wajen son ki musamman in kina kula da cikin shi da tsaftace gidan ku.

Kaninfari
Citta
Minannas
Kabewa/kabushe
Madarar shanu/Ta gwangwani
Dankalin hausa
Kwakwa
Zuma
Dabino

Kinga da farko dai zaki samu kayan ƙamshin nan, citta busasshiya ko ɗanya ma idan kina so zaki saka ta ta ma fi ƙamshi da daɗi a wannan haɗin, ki daka kaninfari da minannas ko kuma ki deb'i kadan ki jiƙa dik yanda kika yi dai, sai ki samu kabewa ki mata tafasa ɗaya ki bari ta huce,sai ki fere dankalin hausa ki niƙa ki tace ruwan, ki niƙa kabewa ki zuba mata wannan ruwan dankalin, ki cire wa dabino k'wallo ki jiƙa ki niƙa ki juye a saman kabewar nan,ki zuba zuma,madara da wannan ruwan kayan ƙamshin ko garin nasu,ki samu kwakwa ki goga a ciki ki juya sosai, sai ki zauna ki sha ki ƙoshi,idan kina so kina iya sanyawa a ma'adanar sanyi har mai gidan duk ku sha,Hadiza dake da shi zaku yaba wa wannan haɗin sosai,"

Dik maganganun da Naja tayi wa mommy sun shiga kunnen ta, ta kuma fahimce ta sosai, dan haka ta ƙudirta gyarawa,ta d'aura ɗamarar siye zuciyar Abdul da kyawawan halaye da ɗabi'u, a tare suka koma kitchen suka sauke abinci suka zuba a inda ya dace, sannan Naja ta sa Mommy haɗa lemon kankana tinda ta ga suna da shi da lemon zaƙi, Mommy na gama haɗa wa suka jera komai a inda ya dace, kiran sallar magariba ne ya sa Naja kallon ƙaton agogon bangon dake manne a gefen qatuwar talabijin ɗin dake parlourn,gani tayi lokaci ya tafi sosai, da sauri ta tafi tayi alwala tayi sallah sannan ta ce wa Mommy to ita zata wuce,

"Tsaya mana ki ci abinci kin sha wahalar aiki kuma sai ki tafi baki ci ba?"

"Ah ah Mommy ni dai zuba min ɗan farfesun kifin na tafi da shi tinda da yawa,abinci kuwa watarana an gamu,"

Babu ɓata lokaci kuwa Mommy ta zuba mata farfesun har sai da Naja ta hana ta, ta hau yi mata faɗa,

"Ke fa matsala ta dake kyautar ki har tana neman yin yawa, ba a ce ki zama marowaciya ba, amma kar ki zama mai sake abun ki galala ki ƙarar da shi ki zo kina zare ido, komai zaki yi ki yi shi kadaran kadahan,"

Dariya mommy tayi sannan tace,

"Ina son ki Aunty Najancyn mu, Allah ya kawo miji na gari ya sa a gama da tsohuwa lafiya,"

"Ameeen Hadizatun Innoh, to na tafi sai mun haɗu goben wajen kai amarya ko? Dan Allah ki zo da wuri fa mu samu mu dan sake gyara waccan giliwi ɗin,"

"To Aunty Naja a gaida Kaka,"

"Za ta ji sai da safe,"

Cikin duhun daren da ya fara shiga Naja ta yi gida, Mommy kuwa ta kalli gidan taga yanda yayi fess da shi, sai tayi murmushi ta wuce wanka, tana wanka tana tunanin Abdul da ya jima be kira ta ba, a haka ta fito ta shirya cikin wasu ƙananan kaya dake cikin akwatin ta, ta gyara gashin ta ta feshe jikin ta da turare bayan ta shafa mai,bakin ta da ta wanke ta sanya wa chewing gum ɗin da ta gani a d'akin Abdul tin zuwan ta gidan, sannan ta fito parlour ta zauna riƙe da wayar ta tana gwada Kiran Abdul ɗin.

Dik wannan hidimar da Mommy tayi bata yi sallar magariba ba, sannan Naja bata nusar da ita akan wannan ba, a yanda Mommy ke da ɗaukan gyara da ace Naja ta nuna mata zuwa wajen boka da suke yi babu kyau su dena tabbas da za ta dena, amma sai ta nuna mata neman taimako ne kuma watarana za su dena, shin suna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login