Showing 243001 words to 246000 words out of 276165 words
Chapter 82 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
sanda suka saba da Bilal ba,ina yawan jin suna waya da shi,kun san da hakan?"
"Eh mun sani,ai ko wancan satin ma yazo wajen mai martaba."
"Lallai zan nuna wa yaron nan ni zan aurar da ƙanne na da kaina,wato shine yake bin bayana yana soyayya da ƙanwata ban sani ba ko?"
Dariya Innah Laminde ta yi sannan ta ce,
"Kun fi kusa,ni kar ku saka ni a shiriritar ku,yarinya ubanta na da rai haka kawai se a ce yayanta ne zai aurar da ita?"
Da haka ta katse wayar ta bar Abdul na mita tare da neman Bilal a waya.
***********************
Tinda Mommy ta kwanta take murƙususun ciwon baya da ƙafadu saboda wahalar da ta ci wajen tuƙa tuwon dawa a ƙatuwar tukunya irin ta gidan biki,hawaye ke zuba a idanun ta wanda ta rasa yanda zata yi ta hana su zuba,jin su take yi kamar ruwan dalma a duk sanda suke taɓa kuncin ta. Wani lokacin tana jin ciwo a zuciyar ta na zubar hawayen nata tinda dama ai duk wanda ya sai rariya ya san zata zubda ruwa,wanda kuwa ya ƙi yin sharar masallaci,to fa dole zai yi ta kasuwa,haka zalika wanda ya ƙi jin bari tabbas zai ji hoho,gashi nan yanzu rayuwa ta yi mata d'aurin damin minti,ko kuma in ce d'aurin goro mai wuyar kwancewa.
Tsaki tayi ta sake sanya hannun ta na dama a kafaɗar ta ta hagu tana matsawa a hankali,lumshe idanun ta ta yi a lokacin da ta ji tsokar wajen ta yi mata tsami,tana nan kwance ta ji agogon ɗakin nata ya buga ƙarfe goma na dare ta yi,kukan da cikin ta yake yi ne ya tuna mata da rashin cin abinci da bata yi ba,rabon ta da abincin arziƙi tin washegarin ranar da za a kawo ta ɗakin miji,sai da safe kuma da ta sha koko jug ɗaya.
A galabaice ta yunƙura zata tashi,ƙarar taɓa ƙofar ɗakin ta ne ya sanya ta tsayawa dan taji wanene ke taɓa mata ɗaki da wannan daren,muryar Malam taji yana faɗin,
"Hadiza buɗe ƙofar nan mana mu yi sallama."
Wani irin takaicin shi ne ya sake turnuƙeta a karo na babu adadi,a tsiwace ta ce,
"Sai da safe ba sai ka shigo ba,ni na kwanta ma bacci zan yi."
"Idan na koma da safe zaki yi dakin sanin ƙin buɗe min ƙofa fa !"
Tana jin haka ta dire ƙafafun ta a ƙasa ta taka cikin sauri ta buɗe masa ƙofar,leda ce a hannun shi baƙa,cikin haɗe fuska ya miƙa mata ya ce,
"Wannan saboda ƙoƙarin da kika yi ne ya sa na kawo maki tukuici,karɓi nan,mu kwana lafiya."
Ɗan tsayawa tayi tana shawara da zuciyar ta akan shin ta karɓa ne ko kar ta karɓa? Kar fa taje ya yi mata wani barbaɗen tinda ta kula yanda mata da yara har da mahaifiyar shi ke tsoron shi ba banza ya bar su ba. Ganin ta ƙi karɓa ne tana ɓata masa lokaci sai ya sa kai zai wuce ba tare da ya ce mata komai ba, cikin sauri Mommy ta miƙa hannu ta warce ledar,murmushi ya yi sannan ya ce,
"Lallai Hadiza har yanzu baki san wanene ni ba shi yasa kike irin waɗannan abubuwan,sai da safe."
Waje ya yi ya barta tsaye tana maimaita kalaman shi,to me yake nufi da hakan? Zama tayi a ƙasa ta buɗe ledar,gurasa ce irin ta wajen masu balangun nan,ta naɗi romon nama da narkakken kitse,sai nama yanka uku,da gani ma ci ya yi ya rage mata,kamar mayunwaciyar da ta shekara bata ci komai ba haka ta dinga tura gurasar nan tana korawa da ruwa,sai da ta zo cin nama ne ta fashe da kuka,cikin kuka baki a cike da gurasa ta ce,
"Ohhh ni Hadiza na ga ta kai na ! Wai yau ni ce nake cin nama yanka uku kacal kamar wata mayya? Allah ka kawo min sassauci,Allah na tuba akan dikkan laifukan da na aikata dan nasan sune dalilin shiga ta wannan rayuwa ta ƙasƙanci."
Kuka sosai Mommy ta sha har sai da ta fara tinanin anya bata samu matsala a kanta ba kuwa? A haka ta gama cin abincin ta ta miƙe ta haye gado ta hau baccin gajiya. Da asuba ta tashi ta yi sallah,kafin ta haye gado ta maida bacci Tsahare ta aika yaro a kira ta ta hura murhu a dora ruwan koko,dan shi ake fara damawa kafin dumame,idan kuma sabon tuwon da ake yi wa Malam ne dik safiya Tsahare ce ke yi masa,domin ita kaɗai ya yarda ta dinga yi masa abincin da zai ci da safe.
Kuka Mommy ta sanya kafin ta hau buga ƙafa a ƙasa tana jin yanda idanun ta ke rufewa kamar wadda tasha maganin maye,jiki babu ƙwari ta fita ta hau ɗiban ledoji a tsakar gidan,har da plate ɗin su na roba sai da ta saka ta ƙone kafin wutar ta kama,tana gamawa ta debo ruwa ta zuba a ƙatuwar tukunya,a wajen ta zauna ta rakuɓe a jikin gini tana bacci. Malam na shigowa ya ganta zaune ta saki leɓe tana bacci,murmushi ya yi ya wuce ɗakin mahaifiyar shi ya gaishe ta,ruwan na tafasa Tsahare ta nuna mata yanda ake dama kunun gidan yawa irin nasu,tana gamawa ta ce,
"To ina sugar?"
Dariya Asabe dake gefe ta yi ta buga cinya sannan ta ce,
"To kema wanda kika sha jiya rabon ki ne ya tsaga saboda amarci,kowa na gidan nan haka yake shan kunu babu sugar,idan uwar yaro nada kuɗi sai ta sai masa mazarƙwaila ya saka a ciki,in bata da shi sai ya kalli sauran ƴan'uwan shi dake da shi suna sha."
Shiru Mommy ta yi ta ɗauki tuwon da ta tarar an yanka an zuba a miya, da alama Tsahare ce ta yi mata haka ko kuma ta saka yaranta su yi mata hakan,dan tana da yaƙinin yanda Mero da Asabe ke nuna mata kishi a fili baza su yi mata hakan ba,godiya ta yi sosai sannan ta ɗora tuwon ta ja gefe ta zauna tana jiran ya yi,nan take ta tina da nata da bata ci ba a daren jiya, ɗakin ta ta tafi da azama ta ɗakko ta yanka ta zuba.
Saida Malam yazo wucewa ta durƙusa tana gaida shi,gani tayi yana yi mata wannan mayen murmushin nashi da kan faɗar mata da gaba, itama yake ta yi masa,ko babu komai jiya bata yi kwanan yunwa ba.
A gaban idanun ta Asabe ta kwashi abincin Malam da Tsahare ta gama jerawa ta wuce dashi ɗakin ta inda Malam ɗin ya shiga,anan ta gane kenan a ɗakin Asabe ya kwana,yatsine baki ta yi sannan ta kauda kai gefe,dan kuwa ko a jikin ta wai an tsikari kakkausa da mashi.
Tana kammala ɗumamen tuwon ta zubawa kowa nashi yanda Tsahare ta koya mata,da kanta ta ɗauki abincin surukar su ta kai mata har ɗakin ta sannan ta fito ta wuce da nata ɗakin ta,zaune take ta rabka uban tagumi tana tunanin Amir ta ji Tsahare ta sallama ta miƙa mata man shanu ta ce,
"Ki tsiyaya wannan kin fi jin daɗin tuwon,idan kina son yajin daddawa ma sai na kawo miki duk ina da shi."
K'walla ce ta taru a idanun Mommy,godiya ta dinga yi wa Tsahare sannan ta ce,
"Ina so a kawo min yajin Iyah,ko kuma muje na karb'o da kaina ba sai na wahal da yaran ba."
"Ah ah yi zaman ki kawai bari na baiwa Abashiyya ta kawo miki."
Tafiya ɗakin ta tayi,ta bar mommy na jin daɗi a ran ta, dan kuwa ko babu komai man shanun zai sa ta ji daɗin abincin,babu jimawa Abashiyya ta kaiwa Mommy yajin,zama ta yi ta dinga cin tuwon kamar ta samu nama,tana gamawa ta kora kunun cikin sauri ta haye gado dan ta rama baccin dake kanta,ga shi har a wannan lokacin jikin ta be bar ciwo ba.
Da rana dambu Mommy tayi musu,ta ji daɗin hakan sosai dan kuwa itama ta ci mai yawa,Ameerah ma da ta kai mata ziyara sai da ta ci ta ƙoshi,kamar ta san Mommy na cikin babu haka ta kai mata kayan maƙulashe da dakakken yaji mai daɗi,sai kuɗi dubu uku wanda Ɗan Liti ne ya bayar yace ta kai mata. Mommy ta yi farin ciki sosai sannan ta godewa Ameerah, cikin damuwa ta zayyanewa Ameerah dik irin zaman da take yi a gidan. Ameerah kuwa sai ta kada baki ta ce,
"Ai Allah ya kara tinda baki ɗaukar shawarata sai ta Aunty Naja,lokacin da kika sanar dani irin auren da zaki yi ban hana ki ba? Na san ni ba wani ilimi gare ni ba kamar ku,amma da jin sunan auren ma AUREN KISAN WUTA bashi da kyau,ki cire ran ki ki akan zaki rabu da mijin ki, ki tuba ga Allah, sannan ki faɗa masa ke kin tuba baza ki ci gaba da wannan auren kisan wutar ba,idan ya ga dama ya barki a ɗakin ki haka ƙaddarar ki tazo,zaki rungume ta hannu bibbiyu,kina dai ganin yanda aure na ya kasance da Shamsu,na ƙi auren shi ne? Ai ban ƙi ba,a haka na zauna dashi har na haihu,gashi yanzu ina jin son shi a cikin zuciya ta,shi kan shi idan kika ji yanda yake yabo na tare da furta min kalaman soyayya zaki sha mamaki,dan haka ki saki ran ki shi Abdul na can amaryar ma ta gudu,to ta ji bashi da kayan aiki shine ta gudu,yanzu dai baida aure babu kuma wadda zata aure shi tinda ya rabu dake akan gaskiyar ki."
"Na ji shawarwarin ki Ameerah inshaa Allahu zan ɗauka,amma kuma kar ki manta Abdul fa ba abun zagi bane a wajen mu,ya yi min halacci, ni ce dai na ƙi yarda na danni zuciya ta,gashi ta kaini ta baro,Allah ya bashi wata matar ta gari,ni dai kam na riga na yi asarar miji mai so na."
Hawaye ta fara zubarwa har sai da ta karyawa Ameerah zuciya,ita kuwa bata iya lallashi ba, dan ko ɗanta ke kukan banza a ƙananan watannin shi zazzane shi take yi balle wata Mommy,goya yaronta tayi ta miƙe tana faɗin,
"To ni dai na yi can,sai kuma wani lokacin idan Allah ya nufa, duk abinda kike so wanda be fi karfi na ba ki min waya zan kawo miki ko na aiko shamsu ya kawo miki."
Godiya Mommy ta yi mata sannan ta raka ta bakin ƙofa,da harara Ameerah tabi ɗakin da Malam ke aikin bokancin shi kafin ta wuce ta bar gidan,Mommy na dawowa ta haye gado ta hau bacci kafin la'asar tayi ta ɗora tuwon dare.
*************************
A hankali shagon su Billy yake ta buƙasa,mutane na ta zuwa siyayyar kayan gyaran jiki,amare kuwa anan ake yi musu gyaran jikin sannan su sayi kayan mata wanda su Billy ke haɗawa da natural abubuwa marasa cutarwa da kan su,kayan su na matan aure ne zalla a cewar Any banda ƴan mata ko zawarawa,dan kuwa sun yi alƙawarin babu budurwar da zata zo siyan kaya su sayar mata,tinda su sun san yanda ƴan mata ke siyan maganin mata har sun fi matan auren ma siya,wasu kuma zawarawa ne ma kuma ba wani auren za su sake ba,haka kawai za a siya a sha a dinga rabawa mazan aure da samari jiki a waje.
Watarana haka suke faɗa kaca-kaca da ƴan mata ko zawarawa,amma hakan baya damun su ko kaɗan,da suna da ikon daƙile karuwanci a duniya ma baki ɗaya tabbas da za su yi hakan,dan kuwa su sun san illar shi.
Gefe ɗaya kuma duk wani taro ko wa'azi da za a yi da ya ƙunshi mata zalla,ba a barin su a baya,mataimakiyar shugaban Hisba kan kira su a waya ta sanar da su,sai suma su dunguma a tafi wa'azi,ba su dawowa gida sai an gama komai tare da su.
Soyayya ce mai tsafta ta ƙullu tsakanin Man da Billy,sai dai babbar matsalar da suke fuskanta,iyayen shi sun ce ba zai auri yarinyar da ta gama yawon bariki ba,sannan sun ji ƙishin-ƙishin ɗin videon tsiraicin ta na yawo a duniya.
To ni anan ina da tambaya makaranta,shi wai iskancin nan kashi-kashi ne ko kuwa dik abu ɗaya ne? Na ga dai abinda Billy tayi shi Man ya yi,to me yasa ita Billy ake ƙyamar auren ta shi kuma ba a jin wata damuwa game da abinda ya aikata?
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 99:
Kwana Billy ta yi tana kukan baƙin ciki tare da data sanin baƙar rayuwar da ta zaɓi ta yi a baya,da kanta ta ɗauki kanta ta jefa a masifa da bala'in da ba zai taɓa gogewa a idanun mutane ba. Bawa zai iya aikata babban zunubi koda kuwa shirka ne ya tuba zuwa ga Allah,Allah ya yafe masa,amma mutane sam basa yafiya,ba kuma sa mantuwa musamman akan mummunan abinda ya shafi rayuwar wasu. Cikin kuka ta miƙe ta shiga toilet ta gabatar da uzirin ta ta fito tana dafe gini saboda yanda take jin jiri na ɗibar ta,sakamakon rashin cin abincin da bata yi ba a gaba ɗaya wunin ranar. Any ce ta kalle ta cike da takaici tace,
"Wai ke kashe kan ki zaki yi akan mutane da basu damu da rayuwar ki ba? Wani shege yana da wuta ko aljannah ne a cikin su? Idan babu mai son ya bar ɗan shi ya aure ki ba akan ki aka fara zama kuma a ƙare rayuwa babu aure ba,ki tsaya ki nemi gafarar Allah akan abinda kika yi a baya har iya tsawon rayuwar ki,sannan ki nemi kuɗi ki huce takaicin talauci da babu,ki fi karfin abinda zaki ci da abinda zaki sanya a jikin ki,dama duk dan me ake fita karuwancin da yawan zinace-zinace a cikin gidajen? Ina ce saboda a ci abinci me kyau dangin su nama da kayan ƙwalama da maƙulashe ne? Sai kuma a sanya sutura ta kece raini a hau manyan motoci,to a yanzu idan kika dage da sana'a ta halal i promise you zaki fi karfin dik abinda kike nema,dan haka ki jajirce ki kama Allah ki rabu da duk wani shegen da zai dami zuciyar ki da kwanciyar hankalin ki."
Any na gama masifar ta ta ɗauki wayoyin ta ta bar ɗakin ta koma wani ɗakin ta kwanta tana ci gaba da mita,Billy kuwa a wajen ta samu ta tsugunna ta ci gaba da rusa kuka. Ba da wasa take son Man ba,tin fil azal shine namiji na farko da ta fara so,kafin son zuciya ya shige ta su ƙulla soyayya da Any,da shiriya ta shige su kuwa nan take suka gane ba soyayya bace sha'awa ce da ingizawar shaid'an kawai a tsakanin su,soyayyar da ta yi wa Abdul kuwa ta gano har da hassada da baƙin ciki da take yi wa Mommy,sannan a tinanin ta zata iya yiwa Allah wayo ne,ta gama bariki sannan ta je ta auri miji kalar nunawa sa'a. Cikin kuka ta miƙe tsaye tana layi kamar wadda ta shawu,wayar ta ta ɗauka ta hau neman layin mahaifin ta,tinda suka baro garin Ba Mugu bata fasa neman shi tana bashi haƙuri ba,da fari baya ɗauka,amma daga baya yana ɗauka daga gaisuwa babu wani abu dake sake shiga tsakanin su,mahaifiyar ta kuwa tini ta yafe mata,sai dai ta ce tayi zaman ta anan inda take ba sai ta koma gida ba,dan kuwa har yanzu a garin ana zancen ta da abinda ta aikata.
Cikin sa'a bata jima tana ringing ba ya ɗauka,sallama ya yi cikin dakewar murya kamar koda yaushe,kukan da ya ji Billy nayi ne kamar zata rasa ranta ya sassauta masa fushin sa,abinka da ɗa da mahaifi,nan take ya ji wani irin tausayin ta ya lulluɓe zuciyar shi,murya na rawa ya ce,
"Bilkisu ki daina kukan haka ya isa,idan bera na da sata to fa bahaushe ya ce laifin daddawane,dan kuwa itama tana da wari,da bamu barki sakaka babu tarbiyya ba,da haka bata faru ba,sannan da bamu rufe ido muna ta karb'ar abun hannun ki ba tabbas da bamu kawo wa yau ba,dan haka na yafe miki da zuciya ɗaya,ban riƙe ki da komai a raina ba sai alkhairi,ki yi shiru ki dena kukan haka ya isa."
Nan take Billy ta sake ɓarkewa da wani sabon kukan da ke nuni da farin cikin da take ciki, cikin tsananin murna ta ajiye wayar ta yi sujjada ga Allah tana gode masa kafin ta sake ɗaukar wayar ta ce,
"Hello Baba kana...ji...na?"
"Ina jin ki Bilkin Baba duk murna ce haka?"
Dariya ta saki hawaye na zuba a kuncin ta sannan ta ce,
"Baba a yau na haƙura da Man tinda iyayen shi sun ce ba zai aure ni ba saboda ni lalatacciya ce,iyakar yafe min da ka yi ta wanke min baƙin cikin rasa shi da na yi, alhamdulillah na godewa Allah Baba,yanda ka yafe min Allah ubangiji ya gafarta min ya yi min afuwar zunubai na."
"Amin Bilki,ina Anam ɗin take yau bata ce a gaishe ni ba? Ki kwantar da hankalin ki,duk inda mijin ki yake zai zo har inda kike ya same ki,ko kuma ke kije ki same shi."
"Humm Anam fushi take yi dani Baba,saboda ina kuka akan dangin Man sun ce ba zai aure ni ba."
"Subhanallah fushi kuma? Ko da yake ai dole ta yi fushi dake,dan kuwa a duniyar nan kowa yana aikata zunubi,wanda Allah yafi so shine wanda idan ya aikata ya gane ya yi kuskure ya gyara,sannan ya tuba ga Allah,dan haka ki rabu da su tinda ba kwaɗanta shi za su yi ba su cinye,Allah zai kawo maki wanda ya fishi albarka kin ji?"
Godiya Billy ta yi sosai kafin ta tashi ta je har ɗakin da Any take,tana zuwa ta ƙwanƙwasa ta miƙa mata wayar,nan take ta washe baki suka gaisa da Baba mai Dusa kafin daga baya ya basu Ta Annabi su kafa sabuwar hira,sun jima sosai suna hira irin ta sabo da shaƙuwa tsakanin uwa da ƴar ta kafin daga baya su yi sallama.
Da dare bayan Billy da Any sun yi wanka sun sha gayu da dogayen abaya sun buɗe shago suna zaune ana ta ciniki,sai ga Man ya zo a hargitse kamar wanda aka koro,cike da murna ya fara rawa a gaban Billy,kallon shi kawai suke yi ita da Any suna jiran su ji ƙarin bayanin murnar da yake yi,hamdala ya yi sannan ya ce,
"Alhamdulillahi Baby you are going to be my wife very soon ishaa Allah,ai nake faɗa maki na kasa jure tsaurin da Daddy ƙarami ya ɗauka akan maganar nan,ina tashi tin safe na