Showing 177001 words to 180000 words out of 276165 words
Chapter 60 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
hau yi wa Alhajin kafin ya buga shewa ya daki cinyar shi yace,
"Ashe rai kanga rai wai tsohuwa ta ga abun nan da ba a kama suna, kai bawan Allah haka ake rayuwa sai kawai kayi ɓatan dabo?"
Murmushi Alhaji yayi sannan yace,
"To ai gani na dawo yanzu,baki da masaniyar mune muka yi organizing wannan taron? Shi kanshi Ministern da kika kawowa yarinya ni na bashi labarin ki,amma a ganin ki shaharar ki ce ta haɗa ku ko? Na jima da sanin ki kece baki sanni ba sai ta sanadin TikTok da nake shiga dan haɗuwa da irin su Sweet H da irin ku masu connection da mata irin ta,ammmm ina baby na take? Ina so ki haɗa mu muna da unfinished business da ita."
Baki sake K'waisa ke kallon Alhaji, sai da taji an yi maganar Mommy ta yatsine fuska tace,
"Kai ni rabani da wannan haihuwar asarar haihuwar rage jinin,ni ina na san inda take yanzu? Ai ni rabona da ita tinda suka kwakushe mu nida tawaga ta muka je ƙwatar wa Billy ƴanci a ƙaucen su karnuka suka raka mu babu azziƙi na cire ta a cikin yarana,kai ƙarshe yarinyar nan fa har gidana tazo ta illata mu nida babyna kaga kuwa ai ni sai dai na nemi tsari da sake ganin ta ko?"
"I don't care about how you guys get separated,yanzu zan baka wani aiki ne na musamman, dole ne dik inda take ka nemo min ita, dole ne na kashe auren nan nata na maidawa Alex ita saboda kuɗi ya biya maƙudai masu yawan gaske,da su nake sha'anin dik da kika ga yana gudana anan dama wasu da ba zan iya lissafawa ba,yanzu haka shiga new york ya gagare ni saboda su Alex na nema na ido rufe, ya bada umarnin da an ganni a kashe saboda tsinanniyar yarinyar nan,dan haka ki nemo ta dik inda take ko kuma a bakin taki rayuwar."
Wani irin zillo K'waisa yayi tare da dafe qirjin shi,idanu mazajen dake zagaye da shi suka hau zaro masa suna gyara zaman bindikar su a jikin su,yawu mai kauri ya had'iya sai da Adam Apple ɗin shi ya motsa, nan take jikin shi ya hau rawa,cikin damuwa da marairacewa yace,
"Yau na shiga uku na ni K'waisan alheri,ni dai sanin wannan matsiyaciyar yarinyar be zame min komai ba sai tashin hankali da bala'i da masifa,yanzu ta ina zan fara nemo ta?"
Alhaji kafaɗun shi biyu ya d'aga sannan yace,
"Ban sani ba,ban kuma damu da yanda zaki yi ki samo ta ba, i just want her back,do what ever it takes and bring her back to me,you can go back to the party and enjoy your self."
Miƙewa K'waisa yayi yana sharce zufa yace,
"Yo wane enjoyment bayan ka katse min shi? Ashe ƴan kud'ad'en da naci na nan na bibiya ta zan biya su ta hanya mai wuya, na shiga uku ni K'waisan alheri."
Haka Hajiya K'waisa ta koma cikin taron mutanen da suka fara buguwa da giya suna ta timɓele da aikata masha'a,Sam ta hango shi da wani saurayi suna magana daf da juna kamar za su shige jikin junan su hannayen Sam na yawo a jikin matashin, kallon shi kawai tayi ranta na ƙuna saboda wani azababben kishi da ya taso mata,kaɗa gashin kanshi yayi ya damƙe ƴar jakar shi ya hau wurga ƙafa zai bar wajen,hankalin Samuel ne ya kai kan k'waisa,cikin sauri ya janye daga jikin saurayin yabi bayan masoyin nashi,kafin ya isa gare ta har ta isa inda motocin mutane ke ajiye ta kunna wadda suka zo a ciki ta tada,da wani azababben gudu ya take motar ya bar harabar wajen,tin a hanya ya fara kuka saboda kishin da yake ji,idan bai manta ba wannan ne karo na biyar yana kama Sam da yunƙurin cin amanar shi,banda text messages da yake gani yana soyayya da wasu mazan,kenan lalurar da ta fara damun shi ce take ƙoƙarin nesanta su? Ashe alƙawarin kasancewa da juna har ƙarshen rayuwa da suka yi wa juna ba zai tabbata ba?
A haka ya isa gida yana kuka tare da fatan Sam ya biyo bayan shi dan ya bashi hakuri,sai dai har dare ya raba babu Sam babu dalilin shi,ya rasa da wanda zai tattauna game da matsalar da ta kunno masa kai na nemo Mommy.
Kaff cikin sabbin yaran shi babu wanda ya sakewa suka shaƙu balle ya basu labarin abinda ke faruwa dashi,agogon dake manne a jikin bangon ƙaramin parlourn shi ya kalla yaga ƙarfe biyu na dare tayi,tunanin ta inda zai fara nemo Mommy yake wayar shi ta hau ringing, a tunanin shi Sam ne sai yaga baƙuwar lamba, yana ɗauka aka ce masa.
'Kar ka shagala da dogon tunani,muna nan muna bibiyar ka har sai ka kawo wa Alhaji abinda ya buƙata zamu ƙyale rayuwar ka.'
A tsorace ya kashe wayar yayi wurgi da ita jiki na masa rawa,cikin tsananin tsoro ya furta,
"Na shiga uku ni ƙwaisan alkhairi,wannan mutumi ya zame min masifa da bala'i,na zaci na yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda tinda na rabu da Hadiza da Billy ashe an rabu da bukar ne an haifi habu."
Safa da marwa yake tayi kafin yaji ƙasan shi na yi masa ƙaiƙayi, kuka ya fashe dashi sannan ya kwashe wayoyin shi da jakar shi ya haura sama, band'aki ya shiga ya tub'e kayan shi gaba ɗaya, wani ƙaton pampas ne a jikin shi irin na manyan nan,a hankali ya hau ƙoƙarin cirewa yana toshe hancin shi, dik da ƙoƙarin dunƙule pampas ɗin da yake yi dan kar yaga ƙazantar dake ciki hakan bai hana wasu daga cikin tsutsotsin dake ciki fad'uwa ƙasa ba,cikin kuka ya buɗe trash bin ɗin dake cikin banɗakin ya wurga pampas ɗin ya tara ruwa a bathtub mai dumi ya zuba su Dettol da sauran abubuwan kashe ƙwayoyin cutuka,yana gama haɗa ruwan ne ya hau saman toilet ya zauna,ya jima sosai yana zazzage cikin shi kafin yayi tsarki ya shige cikin ruwan ya zauna.
Wata iriyar ajiyar zuciya ya sauke kafin a hankali ya sanya hannun shi yana wanke bayan shi da kyau har sai da ya tabbatar ya wanke wajen da kyau,ruwan ya tsiyaye ya sake haɗa wani ya zauna, Hajiya K'waisa bai samu fitowa daga band'akin ba sai da ya zauna a ruwan zafi sau uku, d'aure da towel ya fito yana jin daɗin yanda ya gasa jikin shi ya fitar da ƙazantar da ta taru masa.
Kwance ya tarar da Sam a gado yana surutai irin na bugaggun mashaya,tsaki yaja ya wuce gaban madubi ya shafa mai da turaruka sannan ya maida pampas jikin shi ya saka kayan bacci ya bar d'akin ya koma wani dakin,kwanciyar yayi da tunanin yanda zai nemo Mommy.
********************************
Tsabar murnar ganin Naja ce ta sanya mommy rasa inda zata saka Auntyn nata taji daɗi,hakan da Naja ta gani sai ya wanke mata baƙin cikin da Innoh ta dasa mata a rai kafin tazo,nan take ta maida komai ba komai ba ta rungumi ƴar ƴar'uwar tata da ta gama wulaƙanta ta da yi mata gorin haihuwa.
Abinci kuwa gashi nan kala-kala Naja taci ta ƙoshi,tana tsaka da shan fruit salad ne ta kalli Mommy tace,
"Wannan ɗin daga hotel aka siyo? Dan dai na san baki iya girki kamar haka ba Hadiza."
Dariya Mommy tayi sannan tace,
"Habaa Auntyna ai wannan sanin da kika yi min,ai tinda muka dawo garin nan ya saka ni a classes na koyon abinci,banda online classes ɗin da na shiga na koyon girke-girken zamani da na gargajiya,Aunty Naja nafa gane yanzu komai zaka yi wa namiji dan ka riƙe shi idan baka gyara kan ka ba aikin banza ne."
Hannu Naja ta baiwa Mommy suka tafa kamar wasu ƙawaye sannan Naja tace,
"Amma kuwa ba ƙaramin farin ciki wannan sauyin dana gani a tattare dake ba ya sanya ni, inama waccan sokuwar itama ta fahimci rayuwa ta yanda kika fahimce ta da ta mori zaman gidan miji, dan kuwa yanzu shamsu a kafff matasan ƙauyen Ba Mugu da suka yi aure babu yashi wajen kula da iyalin shi,matsala ɗaya da yake fuskanta shine samun ballagazar mata, kaya duk tsadar shi Ameerah zata kashe shi,abinci dik kyan shi da tsadar kuɗin da aka saka aka siyo shi zata bari ya lalace ko wajen girka wa ta ɓata, dole sai dai a azubar,Allah ya nuna min Ameerah ta zama mutuniyar kirki."
"Ohhh kice har yanzu Ameerah na fama da wannan shiriritar?"
"Humm ai sai dai addu'a kawai, sauƙin da aka samu yanzu ita kanta warin hammatar da take yi na sata amai cikin jikin ta baya son wari, shine fa ake wanka akai akai,amma banda haka kar ki daɗa kar ki raga tana nan a Ameerahn da kika san ta "
"Gaskiya na tausayawa Shamsu yana fama waiiii,idan ban manta ba shamsu fa baya son wari ko kaɗan,uhummm bari dai a bar tuna baya Aunty Allah ya yafe mana,Aunty me kika kawo min neeee."
Dariya suka sake yi suka tafa tare da shewa, cikin yin ƙasa da murya sosai Naja tace,
"Sai anjima idan na shiga ɗaki ki biyo ni, akwai wani taimako da na amso maki wajen malam,a ruwan sha ake sakawa wannan, yanda yasha ruwan nan haka soyayyar ki zata yi ta ninkuwa a zuciyar shi,ba zai ga kowacce mace a matsayin mace ba bayan ke,na tabbata maki babu ke babu kishiya ko a waje balle a cikin gidan auren ku."
"Kaiiii amma Aunty Naja banda kamar ki,kin gama min komai Auntyna Allah ya biya ki, dole ne nayi maki kyauta ta musamman Auntyna."
Murmushin jin daɗi Naja tayi sannan suka ci gaba da hirar cikin da ke jikin Mommy da irin tanadin da tayi na suna da kayan da suka fara siyowa.
Haka rayuwar gidan su Abdul ta ci gaba da kasancewa cikin farin ciki da nishad'i, sai dai ta ɓangaren shi ya samu tawayar nishad'in da yake tsananin buƙata a tattare da Mommyn tinda cikin ta ya shiga wata takwas,gaba ɗaya Mommy yanzu gudun Abdul take yi bata bashi haɗin kai a duk sanda ya neme ta.
Tin suna yin abun nasu su biyu babu wanda ya sani har saida Naja ta sani, ai kuwa babu zancen jin kunya ko nauyi haka ta zaunar da Mommy tayi mata faɗa sosai akan hakan, rimi-rimi ta fara bin umarnin Naja tana daurewa kamar abun zai ɗore,ana haka wata rana da safe ta gaji da dauriyar da take yi ta fara masifa da balai'n yana takura mata yayi hakuri har ta haihu ita baza ta iya da jarabar shi ba.
Cikin fushi Abdul ya sanya tufafin shi ya ɗauki makullin motar shi ya bar mata gidan saboda samun natsuwar ranshi,wanda da ace Mommy tasan abinda take aikatawa zai jawo mata shiga damuwa da tashin hankali tabbas da ta haƙura ta jure dikkan buƙatun Abdussaboor ɗin..........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
*A yi haƙuri a daina tambayar pages ɗin da akai missing saboda na riga na tura,idan baku gani ba ku duba wattpad ko WhatsApp channel,ko ku jira a gama a haɗa document.*
PAGE 72:
Tin a mota yake saƙe-saƙen inda zai samu biyan buƙatar shi da matar shi ta halalin shi ta hana masa,mamakin yanda Mommy ke gudun shi yake yi,a baya kafin cikin ta ya tsufa ko al'ada take yi ta san yanda zata yi ta bashi nishad'i har ya samu gamsuwa da ita, amma a yanzu dan cikinta ya kai wata bakwai take gudun shi? Ta san halin da yake shiga kuwa a dik sanda ta nesanta daga gare shi? Me yasa take sanya shi tunanin rayuwar shi ta baya?
Dukan sitiyarin motar tashi yayi tare da faɗin,
"Baby me yasa kika sauya daga romantic wife zuwa wata mace ta daban da ban sani ba?"
Da ire-iren wannan maganganun da tunanin ya isa office ɗin shi, ko da ya isa ya tarar da Bilal da sauran ma'aikatan wajen sun saka sabbin ƴan bautar ƙasa a gaba suna yi musu bayanin abubuwan da ya kamata su sani.
Ba tare da ya kula kowa ba ya wuce zuwa office ɗin shi ya buɗe ya shiga ya zauna a kujera,juya kanshi ya dinga yi daga wannan ɓangare zuwa wancan, idanun shi kulle suke saboda yanda yake jin shi a matuƙar buƙace da matar tashi har a wannan lokacin,tinani yake anya ba zai koma yayi mata ta ƙarfi ba? Baya so ya komawa zunubin da ya tuba yake fatan har abada ba zai kuma aikatawa ba,to amma ya zai yi?
Wani irin sassanyan ƙamshin turare ne ya daki hancin shi,a hankali aka fara buga ƙofar kamar ana jin tsoron bugawar,ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya buɗe jajayen idanun shi yayi gyaran murya, murya na rawa ya furta,
"Yes..come in."
Tura ƙofar kyakkyawar budurwar tayi ta shiga, idanun ta ta zube fesss a saman fuskar Abdul dake ta ƙoƙarin daidaita natsuwar shi,doguwa ce baƙa mai matuƙar kyau, idanunta masu ɗaukan hankalin mai kallo ta zuba masa, cikin ƙanƙanin lokaci Abdul ya sake rikicewa, leb'en shi na ƙasa ya cije ya kalle ta yace,
"Lafiya? Kin shigo kin zuba min idanu baki ce komai ba."
Cikin sauri da basar da abinda ta ɗarsawa ranta game da kyakkyawan mutumin dake gaban ta ta isa gaban shi ta miƙa masa takardun dake hannun ta tace,
"Sir Bilal ne yace na kawo maka wannan ka saka hannu, sannan nice wadda zan dinga taimaka maka akan dikkan ayyukan ka daga yau inshaa Allahu."
"Ok...meye sunan ki?"
"Suna na Maimooon Salis Ubaid."
"What a nice name...Maimoonnn, ok Maimoon ina fatan an yi maki bayani akan dik wasu abubuwa da muke gudanarwa anan kamfanin ko? Idan ba a yi maki ba zaki min hakuri sai zuwa ko gobe ne na yi maki saboda a gaskiya yau bana cikin yanayi na yin kowanne irin aiki."
Cikin yanga da rausaya ta isa gaban table ɗin da yake ta ɗora dika hannayen ta tana wani kashe masa idanun ta kyawawa,harshen ta ta ɗan zaro ta lashe labb'an ta sannan tace,
"Yess na kula da hakan tin da ka shigo kamfanin nan,na kula da inda hankalin ka ya karkata Sirrr,idan zaka bani dama zan yi maka kowanne irin aiki kake da buƙata,idan nace kowanne irin aiki ina nufin....ko wanne irin aiki."
Tana ƙarasa maganarta sai ta hau kallon shi daga sama har ƙasa sannan ta zube idanun ta a wajen da bai kamata ace ta kalla ba a jikin shi,nan take kuwa Abdul ya fahimci abinda take nufi, wani irin ziga da kururuwa shaid'an ya dinga yi masa yana ingiza shi akan ya kashe ƙishin dake damun shi da wannan tsaleliyar budurwar da ya fara gani a yau,ƙamshin dake tashi a jikin ta da saƙon da take aika masa da idanun ta yafi komai fizgar shi a game da ita,ganin tana neman jan ra'ayin shi ne yayi hanzarin cewa,
"Okk to bari mu gwada wani abu mu gani idan zaki iya yin kowanne aiki na saka ki."
Kafin ya rufe bakin shi ta zagaya inda yake zaune ta hau shafa kafad'ar shi tana matsawa a hankali,nan take tsikar jikin Abdul ta tashi ya sake dulmiya cikin wani yanayi,a hankali Maimoon ta kai bakin ta saitin kunnen sa tace,
"I can do anything for you sir,ka gwada ni ka gani."
K'wank'wasa ƙofar da aka yi ne ya sa Maimoon saurin barin inda take tsaye ta dawo gaban table ɗin Abdul ta tsaya tana kafe shi da wani Shu'umin kallo da murmushi,murya a sarƙe Abdul ya amsa wa mai buga ƙofar tashi,Bilal ne ya shiga yana masifar me yasa Maimoon ta jima,Abdul ne ya haɗe fuska yace,
"Kai bana son iskanci meye haka zaka hau yi wa ƴar mutane faɗa daga zuwa yau? Dalla zauna ka jira nine na tsaida ita, tambayar ta nake yi wasu abubuwa,ni yau fa gaba ɗaya bana ma jin daɗi."
"Subhanallahi me yake damun kane Sarauta? Na kwana biyu ina ganin yanayin ka yana sauyawa a hankali daga farin ciki zuwa damuwa,ko dai damuwar Madam ta kusa sauka ne? Ko kuma matsala ce daga gida?"
"Noo ba haka bane man,akwai dai wasu ƴan matsaltsalu here and there da suka taso ni gaba, amma inshaa Allahu na kusan samun mafita akai, na gode da kulawar ka,ya kana waya da mutanen gida ko? Ina fatan kowa na lafiya?"
Abdul ya ɗauke hankalin Bilal daga son sanin matsalar shi, dan kuwa ya tabbata in dai za su ci gaba da hirar to fa zai sanar da Bilal damuwar shi,kuma yasan hakuri kawai zai bashi,shi kuma ba hakuri yake nema ba a yanzu,biyan buƙatar shi kawai yake nema,hannu ya sanya a takardun ya miƙawa Maimoon dake tsaye kamar ta Allah, Karb'a tayi ta faki idanun Bilal ta kashe masa ido, cikin sauri Abdul ya kauda kanshi daga kallon ta,tafe take tana juya mazaunan ta da suka zauna dass a cikin wandon nata na ƴan bautar ƙasa, faffad'an ƙugun ta Abdul ya kalla,tabbas tana da diri, amma ko kusa bata kai ya Mommy ba,Mommy wata iriyar halittace ta Allah mai kyawun dirin da bai taɓa cin karo da ita ba,murmushi yayi a lokacin da ya tuna da ita,Bilal ne ya kalle shi da tausayawa, a yanzu ya tabbatar da abokin nashi na cikin damuwa, dan haka dole zai dage da taya shi addu'a Allah ya kawo masa mafita mafi alkhairi,dan shi gaba ɗaya zargin Mommy yake yi akan halin da abokin shi yake ciki, Fatan shi dai Allah yasa ba wani rashin gaskiyan take aikatawa ba,shi a yanda yake ganin ta ma kamar tana yi wa abokin nashi sihiri, anya ba maganin karya sihiri zai fara kawowa Abdul ba?
Abdul bai tashi daga office ba sai da lokacin tashi yayi,lokacin da kowa ke tafiya shi kuma yana nan zaune yana nunawa Maimoon abubuwan da suka kamata ta sani a ranar farko na zuwan ta kamfanin nasu.
Basu suka bar kamfanin ba har sai ƙarfe biyu na rana,a motar shi ya ɗauke ta da niyyar rage mata hanya, tin a motar ta fara aika masa da saƙonnin da ya kasa jurewa sai da ya sauya hanya ya kai su wani hotel mafi kusa.
A wannan ranar ne Abdul ya koma ruwa tsundum,bai tashi sanin ɓarnar da yake aikatawa ba har sai da komai ya lafa hankalin shi ya dawo jikin shi sannan ya gane lallai yayi kuskure nadama da danasani mai girma ne suka mamaye shi, hankalin shi ya tashi matuƙa,babban abinda ya bashi mamaki bai wuce samun Maimoon a matsayin budurwa da yayi