Showing 63001 words to 66000 words out of 276165 words
Chapter 22 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
K'waisa ce ta tura Zuby ta taso ta, sallah ta rama har ta jiya da bata yi ba sannan ta sauka qasa, anan ta tarar da masu gyaran jiki sun zo, abinci ta fara ci sannan suka gaisa da mutanen parlourn Hajiya k'waisa sai binta take yi da kallo, wata iriyar fata ce natural Allah ya yi wa Mommy me shegen kyau, murmushi kawai Hajiyan tayi tace,
"To a tafi a fara yin abinda ya kamata, so nake ku sauya min ita da kyau tafi haka kyau, na yarda da ku ba za ku bani kunya ba maza a je a yi aiki,"
Sama suka haye can dressing room ɗin Hajiya k'waisa aka fara sauyawa mommy kamanni da natural abubuwa na gyaran jiki irin na sudanis da sauran qasashen da suke martaba gyaran jiki da natural abubuwa.
Cikin awannin da za su kai uku da rabi Mommy ta fito daga wankan da suka sanya ta a cikin ruwa mai had'e-had'en kayayyakin gyaran jiki da na qamshi, jikin ta babu komai take takowa inda suke, Billy ce ta shiga d'akin a dai-dai wannan lokacin,da sauri ta zari wayar ta tana yi wa Mommy hotuna da videos, tana yaba kyawun da mommyn tayi ita kuma tana wani karairaya da juye-juye da shafa jikin ta ita a dole ga kyakkyawa,sai dariya suke cike da farin ciki.
Kwantawa mommy tayi a gadon da ake yin massage suka hau shafe ta da essential oils masu kyau da gyara fata,nan take Mommy ta qara ɗaukan sheqi da yalqi,Billy ce ta zauna a gefen ta tana shafa ta a hankali tace,
"A gaskiya ina kishi da fatar ki, ina kishin ta irin sosai ɗin nan, kin gan ki kuwa? Waye zai ce daga qauyen Ba mugu kika fito? Wayyoo Allahumma arzuquni minal fata me kyau wa shape irin na qawataaa,"
Billy ta faɗa tana sake murza fatar Mommy dake lumshe idanu saboda yanda ake yi mata massaging jikin ta, cikin murmushi irin na wadda bacci ke son kamawa tace,
"Na gode sosai, ai kema ki godewa Allah dan kuwa kina da kyawun ki masha Allah,"
"Himmm ba zaki hane ba, yanzu dai se ki tashi an gama na taya ki zaɓar kayan da zaki saka ko?"
Ba tare da ta yi wa Billy musu ba ta tashi suka hau duba kayan da zata saka, a haka har suka faɗa kan wata riga dark green mai kyau sosai qarama iyakar ta cinyoyin ta, dan ko cinyoyin bata gama rufe su ba hannun vest gare ta, ta na sanyawa kuwa ta dawo kamar wata babyn roba dan kyau, su kan su masu aikin sai yabawa suke yi, a haka ɗaya daga cikin su ta dawo da kayan shaye-shaye da ciye-ciye na kayan mata ta sanya ta a gaba ta bata ta hau ci.
Ba su jima da gamawa ba Hajiya K'waisa ta ce a sauka qasa a yi hotuna, babu musu kuwa suka sauka aka dinga kyasce mommy da hotuna kala-kala.
Da misalin qarfe biyar dai-dai Alhaji ya iso ya qi shiga gidan ya bada umarnin Mommy ta je su tafi kar su yi missing jirgin su, cike da mamaki tace,
"Ai ba yau bane tafiyar ko, me yasa aka ce yau?'
"Bani da masaniya akan haka Ma'am Alhaji yana jira a waje,"
"Ɗan ra'ayi kenan, to Mommy a je a shana a bawa ido abinci sannan a bawa jiki haqqin shi, kin karb'i magungunan da zaki yi amfani da su ko?"
"Eh hajiya na Karb'a,"
"Maza jeki jeki kar ya ga kin jima,"
"Kar ki manta da haɗa ni da abokin shi fa"
"An gama qawata, sai na dawo"
Sallama Mommy ta yi musu ta fita sanye da takalmi flat mai igiya kore kalar rigar ta, saman shi nada wasu golden stones masu kyau kamar yanda suke a jikin rigarta ta gaba,ta na isa motar ya buɗe mata yana yi mata murmushi, wani glass mai kyau da tsada ya bata mai duhu da face mask ta Karb'a ta sanya a fuskar ta sannan motar su ta tafi,tafiyar da da ta san qalubalen da zata fuskanta a cikin ta da ko miliyan ɗari yace zai bata baza ta amince da yin ta ba.........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
*Assalamualaikum mutanen k'warai masu albarka ina godiya matuqa da addu'o'in ku zuwa ga stepmom ɗina da Allah ya yi wa rasuwa, wanda a bisa wannan dalilin ne yasa ban samu damar ci gaba da rubutun ba, ko a yanzu ma ganin kun damu da ci gaban labarin ne ya sanya ni gwada ci gaba sai kuma aka yi sa'a Allah ya bani ikon rubutawa,a dai-dai lokacin da na san rasuwar na ɗora yatsuna zan ci gaba da rubuta page 23 ne dan har na ma fara,to shi yasa da na zo zan yi rubutun se na ji na kasa,amma alhamdulillahi gashi nan na samu dama zamu ɗora daga inda muka tsaya Allah ya sa mu gama lafiya... Wanda suka kira waya, messages da wanda suka je ta'aziyya har gida da masu niyyar zuwa ina godiya Allah ya jiqan magabatan mu baki ɗaya,Allah ya yi mana kyakkyawan qarshe idan namu lokacin ya zo, na gode sosai da kulawar ku a gare ni Allah ya qara mana lafiya da zaman lafiya a qasar nan da duniya baki ɗaya.*
PAGE 23:
A cikin filin jirgin Aminu Kano motar su Mommy ta tsaya, nan take ta kula da wasu manyan motoci guda uku na daban da suka sauke wasu mata wanda kusan rabin su sanye suke da facemask,dikkanin su qananan kaya ne a jikin su ana ajiye su suka ja akwatunan su suka shiga cikin airport ɗin, a zatan Mommy Alhajinta ne zai zagaya ya buɗe mata mota kamar yanda suka saba, sai ta ganshi ya maqale waya a kunnen shi ya yi gaba, driver ne ya buɗe mata motar ta fita,sororo tayi kafin daga baya ta gyara tsaiwar ta tare da kama qaramin akwatin ta tabi shi cikin airport ɗin,dik yanda taso ta tsaya kusa da shi sai ta ga ya kanga waya a kunne yana magana ya matsa daga inda take.
A haka aka gama dubawa da auna nauyin kayan su suka wuce dan zuwa cikin inda za su jira tashin jirgi,can saman bene ta hango Alhajin ya yi gaba ya barta a baya riqe da qaramin akwatin ta da 'yar jakar ta, cikin sauri ta bi bayan shi itama tana ta mamakin sauyawar shi cikin lokaci qanqani,zuciyar ta ce ta raya mata cewar,
'Mommy bawan Allah'n nan fa yana da iyali, kuma babban attajiri ne taya zai so duniya ta san yana mu'amala da matan da ba nashi ba? Kama kan ki kema yanda ya yi kawai,'
Siririyar jakar ta ta gyara a kafad'ar ta sannan ta hau yi wa kanta hotuna har ta isa can wajen da ta ga kujeru a jere ta samu nesa da Alhajin ta zauna, suna haɗa ido ya yi mata murmushi dan kuwa ya fahimci ta gane me yake nufi.
Cikin abinda be wuce minti goma sha biyar ba Mommy da sauran mutanen da ke jiran jirgi duk sun shiga jirgin kowa ya samu wajen zaman shi ya qame,mazaunin Mommy na bayan na wata budurwa da ta taɓa gani a resort ɗin Alhajin nata, cike da tsoro ta qanqame jikin belt ɗin da ta d'aure qugun ta tin kafin a bada umarnin a d'aura ɗin, kusan hawan ta jirgi na uku kenan kuma dik da Alhajin ta take yin tafiyar zuwa Abuja, ta rasa dalilin da ya sanya ta ganta a bangaren economy ba first classs ba kamar koda yaushe, da dikkan alamu Alhaji na can na jin daɗin shi ya barta a nan cakud'e da mutane kala-kala babu mai lallashin ta da kwantar mata da hankali a lokacin da jirgin zai lula sama.
Wasu hawaye ta ji masu d'umin gaske suna bin kuncin ta, bata san sanda zata dena jin tsoron hawa jirgi ba, maybe kuma ba za ta taɓa dena jin tsoron ba.
Tana nan tana ta tunani da addu'o'i tare da kiran mutanen gidan su kafff tana kuka jirgi ya daidaita a sararin subhana,mommy na nan kulle da idanun ta har na tsawon wasu mintuna kafin cikin sauke ajiyar zuciya ta buɗe idanun ta da ta kulle gam, wata mata ta gani riqe da ruwa cikin wani kofin roba fari tana yi mata murmushi jikin ta sanye da uniform, nan take ta gane ɗaya ce daga cikin ma'aikatan jirgin, da sauri ta karba ta kurɓe ruwan ta na sauke ajiyar zuciya.
Jirgi na nan na ta tafiya har mommy ta samu bacci, Alhaji kuwa na can shi da abokan harqallar shi suna tattaunawa akan business ɗin su,wanda kafin hakan ta faru yariga da ya bada umarnin a kula masa da ita dan kuwa ya san yanda take jin tsoron jirgi.
A Murtala Muhammad airport dake garin Lagos jirgin su ya tsaya, bayan sun fita ne Alhaji ya zo inda mommy take tsaye tana zare ido dan kuwa ta kasa gane ina ne nan ɗin, shin har sun iso Ugandan ne ko kuma ina ne nan ɗin?
"Baby kar ki damu, akwai wani saqo mai mahimmanci da zan karb'a ne shi yasa muka biyo ta lagos,daga nan zamu hau jirgi zuwa qasar Uganda kin gane? Akwai abinda kike so ne?"
"Eh ina so in yi fitsari,kuma ni yunwa nake ji abincin jirgin nan kasan baya wani isa ta ni,"
Cike da shagwab'a ta qarasa maganar ta wanda hakan da take yi yana burge shi sosai, cikin murmushi ya ja hannun ta ya kai ta inda zata yi fitsarin sannan yace ko da ta fito bata ganshi ba ta je ta samu waje a inda kujerun nan suke ta jira shi zai neme ta.
Tana shiga kuwa ya tafi wajen wani Inyamuri da ya isa filin jirgin da wasu zuqa-zuqan 'yan mata guda uku farare tass da su ba irin farin mai ɗin nan ba,kan su ya sha qarin gashi kowa da kalar nata, duk yanda suka kai ga kyawun fata da kyawun jiki sai Alhaji yaga Mommy ta fi su shape mai kyau, sannan fatar ta tafi tasu santsi da taushi,kallon su kawai yake yi dan kuwa ba haka yaso ba, cikin zuciyar shi yana ayyana,
'Yanzu dai dole ne sai na rabu da wannan 'yar shilan idan munje tinda ban samu replacement ɗin ta ba har yanzu'
Hannu suka yi shaking da wannan inyamurin suka yi sallama kowannen su ya kama harkonkin gaban sa kamar basu san juna ba, a haka mommy ta fito ta tarar har an fara kiraye-kirayen tafiya qasar Uganda.
Babu b'ata lokaci Alhaji ya yi wa Mommy alamar ta tashi su tafi, haka kuwa ta tashi ta bi bayan shi tana jin yanda take jin yunwa ta qudirta idan bata qoshi ba wannan karon in an bata abincin jirgi zata ce a qara mata ina dalili ai dai biya suka yi.
Daga turancin da ta ji ma'aikatan jirgin suna yi ta tabbatar da cewa lallai wannan ba irin turancin Nigeria bane, nan take ta sa natsuwar ta dan ta gane me ake faɗi amma ta kasa, dan kuwa turancin Nigeria ɗin ma ba kowanne take ji ba sai sama-sama.
Wannan karon ma sai da ta ji tsoro a lokacin da jirgin ke tashi, yana gama daidaituwa a sama ta sauke ajiyar zuciya ta lunshe idanun ta, kowa ka gani harkar gaban shi yake yi, wasu mata dake kusa da ita taji suna yin wani yare wanda bata ganewa,haka nan taji yaren ya yi mata daɗi,sai kawai ta jingina kanta a jikin kujera tana kallon su tana murmushi, zuciyar ta ce ta ke hango mata mahaifin ta Ɗan liti yanzu idan yasan ba aikatau take yi ba ta zama karuwa ya zai ji? Shin Innoh zata damu ma kuwa da lalacewar ta? Allah sarki Yadiko da tana nan tabbas taji ba aikatau take yi ba karuwanci take yi sai hankalin ta ya tashi, nan take ta hau yi mata addu'a a haka bacci ya ɗauke ta.
Duk rabon abincin da aka yi aka gama Mommy bata sani ba, tana can ta hangame baki cikin facemask tana zuba baccin ta cikin kwanciyar hankali
Tafiyar awanni shida ne cur ya tsaida jirgin su Mommy a Entebbe international airport dake capital city na Kampala dake qasar ta Uganda.
Dikkanin mutanen dake ciki ne suka hau sakko da kayan su daga inda suka ajiye su a saman kujerun jirgin, wanda basu da kaya kuwa haka suka dinga fita suna sauka daga jirgin,Mommy ma tashi tayi tana miqa tare da zabga hamma ta janyo akwatin ta ta jashi zata fita, a hanya ta haɗu da ma'aikatan jirgin suna yi mata murmushi da barka da zuwa qasar Uganda cikin turancin da ke cike da accent ɗin yaren su, murmushi kawai tayi ta sauka ta shiga motar dake tsaye ta kwashe su ta kai su bakin airport ɗin ta ajiye.
Da qafa suka taka suka je suka kammala dik wani abu da ya kamata su yi suka bar filin jirgin zuwa waje dan shiga abun hawa su isa masaukin su, ga mamakin Mommy wasu manyan motoci ta dinga gani suna layi matan nan da ta ga sun taho da su suka dinga shiga, ita kuwa tare da Alhajin ta suka shiga mota ɗaya suka lula sai cikin gari, tafiyar minti goma sha biyar ce ta isar da su Mowicribs hotel and spa.
Kalle-kalle mommy take ta yi, dan kuwa yanda ta zaci qasar da fari sai ta ga ba haka ta ganta ba, amma suna zuwa wannan had'ad'd'en hotel ɗin sai tunanin ta ya sauya ta hau washe baki tana shafa Alhajin tana faɗin,
"Allah ya sa muna isa abinci za a kawo min, muguwar yunwa nake ji, ban samu na ci abinci ba a jirgi ina ta bacci,"
"Kar ki damu, muna isa zaki ci abinci sai kin ture,ina yi maki maraba da zuwa Uganda qasar 'yanci,"
"Lallai na ga alama, dan kuwa su babu ruwan su kowa sai harkar gaban shi yake yi kamar kana kudu a Nigeria, ba ruwan ka da sa ido,"
"K'warai da gaske my love, ina fatan zaki saki jiki ki ji daɗin ki,"
"Sosai ma, kai dai mu je ciki na samu na huta tukunna ka ga sabuwar rayuwar da zamu gina, sai na sa wannan tafiyar ta zame maka tafiya mai kafaffen tarihi a rayuwar ka,"
Kafe ta ya yi da idanun shi da wani irin kallon da ta kasa gane kalar shi sannan yace mata,
"Ah ah ! Ni ne zan kafa maki tarihin da bazaki taɓa mantawa ba a wannan tafiyar Sweet H ! "
Bata san me yasa ba sai ta ji qirjin ta ya yi wata irin mummunar bugawa, shi kuwa Alhaji sai ya sakar mata murmushi mai qayatarwa har dai da Mommy ta saki jikin ta,a daidai wannan lokacin motar ta idasa tsayawa suka fita suka taka suka shiga cikin hotel ɗin.
*********************
Munir ne zaune a sabon office ɗin shi gaban shi takardu ne ko ta ina, dik da tsananin aikin da ya yi masa yawa be hana shi tunanin ta ba,a cikin sati biyu da dawowarsa daga Kano qawayen shi mata babu wadda bata san da zaman Saddeqa ba a cikin zuciyar shi.
A duk lolacin da ya yi yunqurin sanar da Ammin shi dan ta sanar da Alhaji Baban Gida Maganar Saddeqa sai ya kasa, ya rasa dalilin jin nauyin da yake ji a game da bayyana wa iyayen sa soyayyar shi,daga qarshe kawai sai ya sa a ran shi a dik sanda Alhajin ya bijiro masa da maganar aure to fa tabbas zai gabatar musu da Saddeqa a matsayin surukar su, murmushi ya yi mai sauti tare da danna saman biron dake hannun shi har sai da ya fidda sautin qara 'Qasss' sannan ya ja file ɗin gaban shi yace,
"Ya Allah ka mallaka min Beauty a matsayin matar da zata zamo uwar yara na,"
Da kanshi ya d'aga hannayen sa sama ya furta,
"Ameeen"
**********************
Cikin makarantar babu kowa dik ɗalibai sun tafi gidajen su dan cin abincin rana amma banda Saddeqa marainiyar Allah, ta na nan zaune cikin ajin su da ya bab'ure ta sama har rana ta samu nasarar hudowa ta haske cikin ajin ta yanda a dik sanda hakan ta faru d'aliban dake zaune a wajen za su dinga tashi suna neman mafaka.
Muryar ta ke tashi cikin suratul An'am tana rera karatun qur'ani cike da cikakken ilimin tajweed a ciki,qira'a mai daɗi take yi idanun ta rufe suke ta sanya qur'aninta ta rufe fiye da rabin fuskar ta,cike da natsuwa suke tafiya ana nuna masa dik ajujuwan da suka samu matsala suke da buqatar gyara shi kuwa ya na ta gyad'a kai gefe ɗaya kuma qanin shi Sultan na riqe da wani littafi da biro yana rubutu, tsayawa suka ga ya yi cak ba tare da ya ce musu komai ba, Sultan ne ya buɗe baki zai yi magana ya d'aga masa hannu alamar ya yi shiru, cike da natsuwa ya ci gaba da bin hanyar da yake jiyo muryar da ke ratsa zuciyar shi tana samun muhalli ta zauna, yana isa bakin qofar ajin nasu ya sanya qafar shi ta dama ya shiga, fuskar ta ya kalla wadda take fara tasss mai ɗauke da baqin gashin idanu da cikakkiyar gira mai yalwataccen gashi,ba tare da ya san sanda ya furta kalmar.
"Fatabarakallahu ahsanul khaleeqen,"
Ba ya fara takawa zuwa inda take,qamshin turaren shi da muryar shi mai amon sautin muryar cikakkun mazaje ne ta sanya Saddeqa buɗe kyawawan idanun ta ta sauke su akan fuskar shi mai ɗauke da dogon baqin gemu irin na ustazan asali.........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
PAGE 24:
Bai ce mata komai ba sai da ta kai qarshen ayar da take karantowa ta yi shiru ta na kallon shi sannan yayi gyaran murya yace mata,
"Assalamu alaikum,"
Cikin muryar ta mai daɗin sauraro tace,
"Wa'alaikumussalam...Ina yini?"
"Lafiya qlou alhamdulillahi,me yasa baki tafi gida ba kike zaune ke ɗaya duk yara sun tafi gida cin abinci kafin a shiga islamiyya?"
Sunkuyar da kan ta qasa ta yi a hankali ta furta,
"Babu komai,ina so na yi hadda tane,"
"Hummm"
Juyawa ya yi zai bar ajin ya sake tsayawa ba tare da ya juyo ba yace,
"Yaya sunan ki?"
"Saddeqa shine suna na,"
Gyad'a kai ya yi kawai ya fita ya ci gaba da duba duk inda ke da buqatar gyara a makarantar, basu bar makarantar ba se da yara suka fara zuwa islamiyyah, suna fita ya bawa Sultan