Showing 78001 words to 81000 words out of 276165 words
Chapter 27 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
tashin hankali, a ina wannan bawan Allah'n ya san sunan qanwar ta? Tayaya zai kalle ta ya ce itace ma Saddeqa bayan Saddeqa bata da wannan mugun bakin nasu na gado da suka gado wajen Ɗan liti? Cikin zuciyar ta take ayyana,
'Wataqila idanun mu ne suka yi masa kama, babu ja akan kamannin idanun mu saboda gaba ɗaya yaran gidan mu irin idon Baba muka d'akko'
Har suka isa Mommy bata dena zubar da hawaye ba da rawar sanyi, sanda suka shiga d'akin nasu na hotel ne taga Abdul na cire rigar shi ta sama sai wani irin tsoro ya kama mommy,nan take ta fara ja da baya ta na yarfe hannu, Bilal ne ya cire tashi rigar saboda tsabar tsokana sai ya fara taku ta saitin inda Mommy ta nufa wanda nan ne gadon shi yake, kafe ta yayi da ido yana murmushi, nan take Mommy ta kurma ihu ta zube a qasan wajen a sume,gaba ɗaya ta gama saddaqar da ta kawo kanta hannun masu fyad'e.
Abdussaboor ne ya ga abinda Bilal ya aikata sai ranshi ya baci ya hau yi masa masifa, shi kuwa dariya kawai yake yi yana kumawa, daga qarshe ya haye saman gadon shi yana dariya yace,
"Se ka watsa mata ruwa ta miqe sannan ka san yanda za ka yi da ita, ni ba ruwana a wannan chakwakiyar da kake neman jefa kan ka,kana da tabbacin gaskiyar abinda ta faɗa shine ya faru ba qarya take yi ba? Haka kawai na ji a zuciya ta akwai lauje cikin nad'i a maganar ta,ka dai bi a hankali, ka kalli jikin ta da kyau da surar da Allah ya bata, kana da tabbacin sato ta aka yi ba itace ta kawo kanta ba?"
Da sauri Abdul ya dakatar da Bilal ta hanyar nufar gefen gadon shi ya dakko ruwa ya watsawa Mommy, kafin ta farfad'o Abdul yace,
"Ka dinga kyautata wa mutane zato Bilal, kai a komai sai ka kawo nagetive though a ciki,wa ya faɗa maka jikin ta na da nasaba da zuwan ta qasar nan? Mu jira muji daga gare ta, iya sanina da yarinyar nan mahaddaciyar qur'ani ce kuma nitsattsiya, itace yarinyar danake faɗa maka na saka Sultan yi min binciken gidan Iyayaen ta,"
Tana gama buɗe idon ta taga Abdul tsaye a kan ta, da sauri ta hau taɓa jikin ta tana so ta ji shin kayan ta na nan a jikin ta ko sun cire mata,ji tayi kayan ta na nan a jikin ta sai ta yi wata ajiyar zuciya ta ja da baya ta shige lungun gadon su Abdul ɗin tana ci gaba da kukan ta, a hankali Abdul ya isa gaban gadon ya zauna yace,
"Sanar dani ya aka yi aka sato ki nan, iya sanina ke yarinya ce nitsattsiya mai ilimin alqur'ani na je gida na gan ki na kuma baro ki lafiya me ya faru?"
Kasa sanar da shi Mommy tayi ba itace Saddeqa ba sai kawai ta fara magana,
"Ni kaina ban san me ya faru ba, ina hanya ina tafiya kawai na ji kamar an shaqa min wani abu, ban sake farkawa ba sai a jirgin ruwa, daga nan ina ta kuka ina yi musu ihu suka sake shaqa min wani abu ban sake sanin inda kaina yake ba sai a wannan qasar, a gaban mu aka yi cinikin mu kamar kaji sannan aka sanya mu a mota,a gidan wani Bature mai suna Alex aka sauke ni, shine...shine...shine ya ke..."
Kuka sosai Mommy ta fashe da shi har jikin ta na rawa, da jin haka su Bilal suka fuskanci inda maganar ta ta dosa nan take Abdussaboor ya ji wani irin matsanancin kishi da baqin ciki sun mamaye shi, a fusace ya tashi yana faɗin,
"Zaki iya gane gidan shi?"
Da gudu Bilal ya sakko daga saman gadon shi ya damqe kafad'un Abdul ya girgiza shi da qarfi cikin d'aga murya yace,
"Kaii ka nutsu ! Nan qasar ba Nigeria bane ba kuma qauyen Ba mugu bane inda kuke mulka, nan qasar waje ne qasar wajen ma ta turawa, shawarata anan kawai ka zo mu duba online mu koyi yanda za a yi reporting b'atan passport ɗin ta, sannan mu yi dik yanda zamu yi mu tafi da ita shikenan,wani fushi da nuna jarumta ba naka bane a qasar azzaluman mutane irin wannan, yanzu ita se a sake ta su yi maka d'aurin goro,"
A hankali Abdul ya fara rage fushin dake cin zuciyar shi,sai suka kunna laptop suka duba yanda za su cike form din DS-11 dan su sama mata sabon passport cikin sauqi.
Suna kammalawa Abdul yayi waya aka kawo abinci da abubuwan sha da shayi, sannan ya duba a kayan shi ya samo mata T-shirt da wandon shi da zai iya yi mata, band'aki ta fara shiga tayi wanka sannan ta sanya kayan da ya bata ta fito tana rakub'ewa a jikin gini, Bilal banda kallon ta babu abinda yake yi, haka kawai yaji be yarda da ita ba, babu qarya yarinyar na neman taimako, amma zuciyar shi na sanar dashi akwai abinda take b'oyewa.
Haka Monmy ta qarasa gaban abincin nan ta zauna ta hau ci tana shan lemo da shayi dik a lokaci ɗaya,kana ganin ta ka san a wahale take kuma a yunwace take,bata kyale abincin nan ba sai da ta gama ci tasss sannan ta samu qasan gadon inda ta rakub'e ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.
Dik yanda Abdul yayi akan ta hau gadon shi zai koma na Bilal su kwanta tare qi tayi tace nan qasa ya ishe ta,Bilal na jin furucin ta ya gyad'a kai yace,
"Ka gani? Bata wani son gado kawai ka je ka kwanta abun ka malam ni kar ka wani matse ni,"
Abdul na jin haushin yanda Bilal yake magana a gaban Mommy yana nuna baya son zaman ta a tare da su,babu yanda ya iya dole ya kyale ta bayan ya wurga mata pillow da abun rufa, kasa qarasa rufe jikin ta tayi saboda baccin da take ji,munsharin ta me kama da husir ne ya sa Bilal dariya har yana fad'owa daga gado,tsaki Abdul yayi yace,
"Ka ji jiki kai dai,"
"Ahhh dole na ji jiki mana,ashe qauyen ku akwai qauraye ji yanda yarinya ke busa husur ɗin fita farauta,"
Duk yanda Abdul yaso ya haɗe rai kar ya yayi dariya amma da mommy ta ja wata sarewar munshari dole shima ya kece da dariya har yana hawaye, kusan raba dare suka yi suna dariya da tattaunawa akan yanda za a samawa Mommy takardar barin qasar cikin 'yan kwanakin da ya rage musu su tafi tare da ita.
Washegari da asuba Bilal ne ya fara tashi ya shiga band'aki ya kama ruwa yayi alwala sannan ya fito ya tashi Abdul domin ya yi alwala su yi jam'i a tare.
Abdul na fitowa daga band'aki sai ya tada Mommy dan ta yi alwala duk suyi sallar a tare, wani irin juyi tayi ta yaye bargon ta banqaro jikin ta tana miqa a suk'wane Abdul ya bar wajen yana zaro idanu waje be sake komawa inda take ba ya tada sallah Bilal ya bi bayan shi yana ayyana,
'Allah ya qara waya aike ka karambanin tashin mace daga bacci dama?'
Ko da suka idar da sallah sun jima zaune suna azkar still mommy bata farka ba,dik cikin su babu wanda ya sake bi ta kan ta suka yi wanka suka shirya suka bar mata takarda da rubutu jiki suka kulle d'akin suka fita yin abinda ya kawo su.
Mommy kuwa bata farka ba sai qarfe 11am ta tashi da miqa tare da hamma mai tsawo tana kalle-kalle, ganin inda take ne ya tuna mata da dik abinda ya faru a jiyan, da sauri ta tashi daga inda take ta ga babu kowa a d'akin,wata takarda ta gani a ajiye a saman gadon Abdul hannu ta sanya ta ɗauka,cikin kyakkyawan rubutun shi ya sanar da ita idan ta farka ta kira wannan No da ya rubuta a kawo mata abinci sannan tana iya duba cikin inda ya ɗaukar mata kayan sawa jiya ta ɗauki wanda zata sauya ba za su dawo ba sai dare.
Murmushi tayi sannan ta yi tsalle ta haye gadon Abdul ɗin tana juyi,a haka ta isa jikin landline phone ɗin dake ajiye a side drower ɗin gadon nashi ta sa hannu ta ɗauka ta hau duba takardar nan tana danna No dake jiki, tana gamawa ta kanga a kunnen ta, abinci ta sanar da akawo mata.
Cikin qanqanin lokaci ta shiga wanka ta wanke bakin ta ta duba kayan Abdul ta sauya zuwa wasu riga da wandon ta ninke wanda ta cire ta ajiye masa a saman gado.
Ba jimawa aka kawo abinci taci ta samu waje ta sake kwantawa a saman gadon ta hau bacci ko sallah bata yi ba.
Haka Mommy ta dinga rayuwa a cikin su Abdul suna kyautata mata, ita kuma ta na qoqarin nuna musu ita ta Allah ce dan su taimake ta ta koma Nigeria,a haka sai da suka shafe sati ɗaya ana cuku-cukun samawa mommy takardun da zasu bata damar barin qasar.
A can gidan Alex kuwa sun qudurta niyyar nemo Mommy ko ta halin qaqa dan kuwa be taɓa samun macen da ta yi masa ba irin ta, shi da abokinsa Mike sun qudiri aniyar ɗaukan mummunan mataki akan Alhaji da ya siyar masu da matsala a farashi mafi tsadar gaske.
*****************************
Alhaji na haɗa kan kud'ad'en shi ya sallami duk wanda zai sallama sai ya tattare ya koma Abuja da zama saboda ya b'atar da sawu kafin qura ta lafa ya sake shigowa kano ko kuma wani garin da ya tara mata irin su Mommy ya kwasa ya je turai ya siyar ya samu 'yan can jin shi, dan haka rayuwa yake yi ta kashin kuɗi da dukiya gaba ɗaya ya manta da wata Hajiya K'waisa da Mommy da tarkacen su.
Billy kuwa tinda ta dawo daga yawon ta da ta samo miliyoyin ta ta yi shirin komawa qauyen Ba Mugu dan kuwa a cewar ta Mommy ta buɗe musu hanyar nuna arziqin su ba tare da fargaba ba, a daren ranar da zata tafi sai da suka kai ruwa rana da Samuel yana yi mata masifa akan kar ta sake duk bala'in da qawarta ta shiga su nuna K'waisan alheri a matsayin wadda ta zama silar shigar su damuwa duba da cewa har yau ba a sami labarin inda Mommy ta shiga ba.
Itama cikin rashin kunya da masifa tace masa,
"Shi ɗan bariki dama yana da wanda zai riqe a matsayin wanda ya ingiza shi? Ai dik wanda ya yarda ya baro gida shi ya so, dan haka ka dena buɗe min ido kana zare min su kamar wani ubana,"
Da kyar Hajiya K'waisa da ke cikin jimami da alhinin rashin Mommy na kusan wata guda ta raba faɗan.
Lokacin da Billy ta isa qauyen nasu ita da saurayin ta da ya kaita a rantsattsiyar motar shi yara da manya ba abinda suke yi banda bin motar da kallo, manyan dake zaune qasan bishiya suna shan dumi a garwashin da almajirai suka bari na ragowar wutar karatun dare sai miqewa suke yi daga tsugunnon da sukai suna leqa motar su dawo suna faɗin,
"Ai kamar yarinyar nan ce Bilkisu 'yar gidan mai dusa,kalli wata iriyar sutura a jikin ta, yarinya sai kace anniya, a gaskiya Mai dusa be godewa Allah ba akan ni'imar da yayi masa, yana ɗaya daga cikin masu kuɗin garin nan amma wai ya bar 'yar cikin shi tafiya birni aikatau, ka duba ka ga yarinya ta isa haifar yara biyar tana yawo a titi tib'i-tib'i tsirara, yo tsirara mana ai wannan kayan na jikin ta da su da babu duk ɗaya ne meye ba a gani ba anan?"
"Babu kam, jibi wani uban gashin doki da ta saka yana reto har a saman mazaunan ta, kaiii subhanallahi Allah ka kiyashe mu aikin tab'ewa,"
"Ameeen ya Allah kai dai, yanzu ina ce 'yar ka Sarai shekaran jiyan nan ta haihu? Ba qanwar bayan ta bace? Itama da ta zauna ta fitar da miji an aurar da ita haka zata faru ne?"
"Ina fa,"
Haka suka ci gaba da hira har Billy ta gama ɗaukan kayan da zata iya ɗauka yara suka taya ta tashigar da sauran ciki, sake dawowa tayi dan tayi sallama da saurayin ta, cikin motar shi mai baqin gilashi suka shige ta zauna a jikin shi suna watsewar su, wani daga cikin dattijan nan ne ya leqa ta gaban motar dai-dai inda babu baqin gilashin ya hango Billy na sauka daga jikin matashin suna raba bakin su da suka haɗe tin shigar ta motar, wani irin salati ya ja ya dafe qirji ya na nuna wa sauran, kafin su gani Billy ta fito tana d'agawa saurayin ta hannu ya bar qofar gidan, juyawa tayi suka yi ido biyu da dattijan da ta ga sanda tsohon nan ya leqa ya ga me suke yi, cikin wani irin taku tana rausaya jikin ta ta isa gaban su ta durqusa kaɗan ta gaishe su.
Kaɗan daga cikin su ne suka amsa, sauran kuwa banda harara da surutan kar ta zo ta lalata musu tarbiyyar yara ba abinda suke yi,murmushi tayi ta miqe zata tafi ta ɗan karkace ta buɗe jakar ta ta zaro dubu goma ta miqa musu tace,
"Gashi a sanya mana albarka a kuma taya mu addu'a Allah ya shirye mu, shi d'a na kowa ne, idan kaga ɗan wani ya lalace ba aibata shi ya kamata ka yi ba addu'ar shiriya ya kamata kayi masa gudun kar kazo kana aibata na wani naka na can ya fi wannan da kake aibantawar lalacewa baka sani ba,"
Tana gama faɗa musu haka ta tafi ta bar su a wajen suna rabon kuɗi n da ta basu cike da zalama,tinda ta miqa kuɗin dama masu zagin nata suka yi shiru ba wanda ya sake cewa qala, a haka ta shige gidan su da ake ta murnar dawowar ta.
Ko minti goma sha biyar da komawa gidan bata yi ba aka dinga doka sallama kamar za a d'aga kwanon da aka rufe soron gidan nasu dashi..............
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 30:
Innoh ce ta qarasa shiga gidan tana ci gaba da banka sallama,Mahaifiyar Billy ce ta fito daga d'akin Billyn bakin ta a washe kamar gonar audiga tana faɗin,
"Lale maraba lale da qawata aminiya ta,irin wannan sallama haka kamar an koro ki? To bismillah shigo,"
"Ai dole ki ganni da tsakar ranar nan Saude ina banka sallama, ina can zaune na kwashe alale an fita da ita naji labarin 'yata ta dawo nace banga ta zama ba se na zo na ji labarin Mommiyata,"
Billy ce ta fito d'aure da towel a jikin ta da wata jaka me kyau da ke ɗauke da kayan wankan ta, ba tare da ta kula su Innoh ba ta k'wala wa qanin ta kira tana tambayar shi ya kai mata ruwan wankan? Ya bata ansa da eh ya kai, a sannan ne ta kalli Innoh taga yanda take binta da kallon burgewa, sake gyara jikin ta tayi da kyau tana murmushi tace,
"Innohn mu barka da war haka, ya gida ya su Ameerah da Baba?"
Cikin washe baki Innoh tace,
"Kowa na nan lafiya qlou Bilkisu, ina kika baro min mommyna uwar masu gidaaaa?"
Murmushi Billy ta sake yi sannan tace,
"Tana nan lafiya qlou alhamdulillahi, ai tana ta cewa a gaishe ku aiki yayi mata yawa da tini da ita za a zo ma ai,amma ta bada saqo na baki kafin ta iso, bani minti goma na watsa ruwa na zo,"
"Na baki arba'in ma idan zai ishe ki, a fito lafiya,"
'Masu shegen son abin duniyar tsiya tinda nake ban taɓa ganin tazo gidan nan ba idan ba haihuwa akai ba se gaisuwar rasuwsr Yabi amma jibe ta yanzu ta bugo qafafu kamar babur ɗin mijin ta ta zo yi min sannu da zuwa, ji yanda jikin ta ke rawa saboda tsabar kwad'ayi,'
Billy ta ayyana a ranta a lokacin da take wucewa bandaki domin ta yi wanka,Innoh na nan na sharhi akan al'amuran yau da gobe Billy ta gama shiri ta fito mata da wata atampa da leshi sai takalmi ta ɗora mata dubu goma tace na ɗinki ne wai inji mommy,murna Innoh ta dinga yi tana sanya musu albarka tare da fatan su fi haka arziqi, ba jimawa kuwa ta yi musu sallama ta tafi tinda ta karb'i abinda ya kai ta.
******************************
Abdul, Bilal da Mommy sun samu nasarar dawowa gida Nigeria lafiya ba tare da wata tangard'a ba, a gidan su Abdul ɗin mommy take zaune wanda zama da su ya sanyawa Mommy tsoron Allah duba da yanda suke gudanar da rayuwar su daga aiki sai ibada, sai su ci abinci da dukiyar da Allah ya wadata su da ita ta hanyar halal, sai kuma taimakon marasa shi da suke yawan yi.
Koda dai ba wani natsuwa take yi ba a wajen yin sallah yanzu tana samu ta yi su guda biyar ɗin a kan lokacin ta ba tare da an ce tashi ki yi sallah ba, a hankali Bilal ya gane wasu daga halayyar ta na rashin son ibada da son abun duniya amma sam Abdul be gane ba, dik sanda kuma Bilal zai yi masa bayani sai ya nuna masa cewar waye baya son abun duniya dama? Sannan ita mace dama tana da rauni yana daga cikin raunin ta wasa da ibada, amma idan aka tsaya akan ta aka dage da yi mata nasiha zata dena ne ta kama Allah da kyau ta yanda zata bawa wasu tarbiyya itama,da haka Abdul ke kashe bakin Bilal da be gama yarda da Mommy ba.
Tinda suka dawo ya ɗauke ta suka je shopping ya sai mata dogayen riguna irin na larabawan nan, ai kuwa Mommy ta yi murna da farin ciki sosai dik da cewa ta so k'warai ya barta ta ci gaba da sanya kayan shi, hakan na sanya ta nishad'i da jin wata iriyar shaquwa ta musamman na shigar ta game da shi, abinda take ji akan Abdul bata taɓa jin shi a kan wani namiji ba,yanda yake lelenta kamar k'wai ta gane tsantsar soyayyar da yake yi mata ba ta wasa bace,wanda lokuta da dama hakan na tada hankalin ta, tana tsoron ranar da zai gano ba itace Saddeqa ba kar ya juya mata baya.
Tana girmama