Showing 60001 words to 63000 words out of 276165 words

Chapter 21 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

Lallai Alhaji duniya ta yi maka daɗi dole ka je qaraye, to ba wannan ba yaushe ne tafiyar?"

"Ina ga nan da 3 days ne zan yi tafiyar,"

"To yanda za a yi ka yi hakuri ka barta ta kwana gobe da yamma sai ka zo ka ɗauke ta, ka san mu fa mata 'yan kwalliya da gyara ne, kuma ka san yanda tsari na yake bana son yarinyar dake waje na ta samu gazawa ta kowanne fanni, dan haka ina so ta zauna gobe da yamma ka zo ka ɗauki kayar ka ku yi ta tafiya in ma bangon duniya zaku je se kun dawo,"

Cike da jin babu daɗi Alhajin nan ya nuna qin amincewar shi, da kyar K'waisa da Samuel har ma da Mommyn suka shawo kan shi ya amince ya ce to zai tafi ya barta amma kuma da qarfe biyar na yamma a tabbata idan ya zo zai gan ta ta zama ready, tabbacin zai samu yanda yake so Hajiya K'waisa ta bashi, nan take ya karb'i account No ya sake tura wa Hajiya kwaisa million biyar yace shi zai wuce,

Har mota Mommy ta raka shi, sun jima a cikin motar divern shi na waje yana jiran su kafin daga baya ta fito ta na d'aga masa hannu, ta na shiga ciki ta samu su Hajiya K'waisa na yaba sa'ar mommyn cikin hauragiyar hirar da suke yi K'waisa tace,

"Keee yarinya zo ki faɗan gaskiya ko dai kin haɗa dangi da matsafa ne suka tsaface bawan Allah'n nan haka yake maki b'arin nera ? Taho nima ki haɗa ni da kakan ki a tsaface min Babyna?"

Dukan wasa Samuel ya kai wa K'waisa daga nan suka tafa suna dariya, mommy tace,

"Ai Hajiya baki ga komai ba sai kin ga wannan,"

Waya sabuwa dall ta zaro a jakar ta ta miqa wa Hajiyan,waya ce da ake yayi mai shegen kyau da tsada, cikin wani irin kwad'ayi da nuna maitar wayar Billy da ke gefe tana kallon su ta cafki wayar ta na washe baki ta doka wani uban ashar sannan tace,

"Mommy kin san nawa ake saida wayar nan kuwa? Mommy yana da aboki ki haɗa ni da shi? Wayyooo Allah shegiya qawata kin shigo bariki a sa'a,ya kamata Baba Ɗanli ya dangwali wannan arziqin shi da Innoh"

Nan take jikin Mommy ya yi sanyi, dan kuwa tun tana can take yawan tunawa da gidan su da iyayen ta da ta ha'inta tace aikatau zata yi tazo tana aiki da jikin ta tana samun kuɗin haram.

(Kwad'ayin su ne ya kawo ki nan tun farko)

A haka Billy ta ja Mommy sama tana bata labarai kala-kala, suna isa d'akin Mommyn ta sauya murya ta rage sauti tace,

"Mommy ina so na sanar dake wani abu, amma dan Allah ki kwantar da hankalin ki, kar ki tada hankalin ki idan na faɗa maki har wani ya gane, sannan kar ki ce zaki sanar da kowa a gidan nan abinda zan sanar dake yanzu,"

Cike da rud'ani da tsantsar son jin me ya faru a gidan da bata nan Mommy ke kallon qofa dan kar wani ya ji me Billy zata sanar da ita ta kama hannun Billy suka zauna a gefen gadon ta tana jiran ta ji me zata sanar da ita.................

*Kowa ya baza kunne zuwa gobe da yardar Allah sai mu ji me Billy zata qulla kuma*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊANLITI




RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH






PAGE 22:




Cikin yin qasa da murya Billy tace,

"Abinda zan sanar dake ba wai anan gidan ya faru ba, a can qauyen Ba mugu ne, kuma a gidan ku can gidan ƊAN LITI abun ya faru,na ce ki natsu ne saboda nan gidan ko iyayen ki ne suka rasu ba wanda zai damu dake ke kaɗai zaki yi jinyar zuciyar ki ki gama, sannan ki ci gaba da harkar gaban ki,saboda Hajiyata ta jima da rasa nata iyayen,in fact bai san iyayen shi na haihuwa ba, tashi ya yi yana watangaririya, marigan shi kuma sun azabtar da shi matuqa anan aka koya masa neman maza saboda harkar mariqin shi kenan,wannan shine dalilin da ya sa ya taso zuciyar sa a qeqashe baya tausayin kowa sai karuwa ko d'an daudun da be san yanda zai d'aga darajar kan shi ba, to fa zai tsaya maki ko ya tsaya maka har se ka zama wani abu saboda kar ka ɗauki wulaqanci ko raini a wajen kowa kin gane?"

"Na gane Billy zuciya ta sai tsinkewa take yi waye ba lafiya Innoh ko Baba?"

"Lafiyar iyayen ki qalou sai dai kin yi rashin kishiyar uwa, dan kuwa Yadikon ku ta mutu, sa ido ya qa...."

Wata iriyar bangaza Mommy ta yi wa Billy, cikin hawaye da kukan da ya k'wace mata tace,

"Dakata Billy ! Kar ki sake ki faɗi wani mummunan abu akan matar da a kullum bata da burin da ya wuce na ta ga ni da 'yan uwana har ma da mahaifiyar mu mun gyara rayuwar mu, aikatau kawai aka ce zan zo amma bata amince ba,dik da haka ta bada shawara ba a ɗauka ba,da zan taho ta bani guziri ba tare da ta san mummunar rayuwar da zan zo ina yi anan ba,wayyoo Allah Yadikon Sule Allah ya jiqan ki, dan Allah Billy kar ki sake kiran ta da uwar sa ido,ko wani mugun sunan bana so"

Cikin shanye baqin cikin da Mommy ke qunsa mata Billy ta rungume ta tana lallashin ta, a haka ta samu har Mommy ta saki jikin ta da kyau ta kwanta a kafad'ar ta tana ci gaba da kukan ta,ita kuwa ta yi amfani da wannan damar tana ta shafa jikin ta da sunan lallashi.

Suna can cikin d'aki suna jimanta rashin Yadiko, Hajiya K'waisa da babyn ta na nasu d'akin suna aikata abinda idan ance mutum mai natsuwa da ya san Allah zai iya zare ran shi yana tsaka da wannan mummunan aikin ya aikata ba zai yi ba, Zuby da Ruby kuwa su suka gyara inda aka b'ata a parlour.

Hajiya K'waisa bata samu kan ta ba sai da Babyn ta ya yi mata sallama ya tafi bayan ya ajiye mata maqudan kud'ad'e, dan kuwa shi da US dollars yake sallamar masoyin nashi.

Wanka ya ci ya sanya gashin dokin shi mai kyau sannan ya saka rigar da aka yi masa na musamman na jikin mata wanda idan ya saka babu mai musu akan cewa shi ɗin ba a cikin jinsin mata yake ba, sannan ya ɗauki wasu arnan kaya masu kyau ya saka iyakar su guiwa, ya ɗauki wayar shi ya hau yin waya da kamfanin da ke gyaran jiki na role model ɗin shi,nan take ya yi booking gobe za su zo da safe su gyara Mommy sannan ya tura musu da kud'in su ta account ɗin su nan take babu b'ata lokaci.

Jakar shi ya ɗauka ya sauka qasa ya duba inda suke ajiye makullan motar su ya ɗauki na motar da yake sha'awar hawa a ranar ya bar gidan shi kaɗai ba tare da driver ba, sannan ba tare da kowa ya sani ba.

Mommy kuwa na can ta samu bacci Billy ta kai qololuwa wajen son kasancewa da Mommy amma babu hali, haka ta janye ta a jikinta ta rufi mommyn ta bar d'akin nata, tana fita ta shige nata d'akin ta tsaya tana tuna yanda abubuwa ke neman jagule mata, ita bata samu biyan buqatar ta ba, ga mommy ta zo tana neman finta da komai a gidan da ma rayuwa baki ɗaya, dole ne ma ta ɗauki babban mataki akan hakan.

Laptop ɗinta ta kunna ta shiga social media dan ganin inda zata faɗa ta samu biyan buqatar ta da kyar ta tsaida hankalin ta a wani sabon page da ta gani ana neman irin ta guda uku da za a ɗauka a babban wani sabon Hotel su yi kwana biyar a biya su million bibbiyu, hamdala ta dinga yi kamar wadda aka yi wa kyautar makka ita a ganin ta hanyar ɗaukakar ta ce itama ta zo, dariya ta yi ta buga cinya sannan tace,

"Bana nima zan yi wulaqanciiii, million biyu a kwana biyar kacal ina laifi? Da kyau TikTok, TikTok gidan kawalci gidan zabga sab'on Allah kala-kala,a gaskiya wanda ya qirqiri TikTok har aka kawo shi Nigeria ya shigo mana arewa shegen kaya ne,da alama sun gane mu mutanen Arewa bamu da wayo da dabarar amfana da irin waɗannan kafofin sadarwar da ya wuce mu yi ta wauta muna zagin juna da tozarta juna dan neman followers, sun gane mu ko kasuwancin namu ma da aka sammu da shi baqin ciki muke yi wa juna ba saya muke ba se wanda Allah ya tsaga da rabon shi, mun gwammace mu sa data mu hau muyi ta hayani da saida jikin mu muna samun 'yan canji, shi yasa suka bamu duk wani abinda muke buqata dan shoshalewar mu, Allah dai ya biya TikTok gidan bad'ala da cin gashin kai,"

A wajen waɗanda basu san me suke yi ba ba? wanda suka san kan su ai suna can suna saurarar wa'azin malamai da kuma tallata kasuwancin su da qirqirar content masu amfani da amfanar da al'umma,akwai girke-girke kala-kala wanda mata da maza dika zasu amfana da su, dan haka kowacce kafa ta social media na da amfani da kuma rashin amfanin ta ya danganta da yanda mutum yake so ya amfana da ita, zai yi amfani da social media ne ta hanyar da zata kai shi aljannah ko kuma zai yi amfani da ita ne ta hanyar da zata kai shi wuta? Zaɓi yana hannun ka kai me waya da data, komai naka se yanda ka yi da abun ka.

Tsakiyar dare Mommy ta farka da matsanancin ciwon b'arin kai wanda da kyar take iya buɗe idanun ta, rayuwar da suka yi da Yadiko ce kawai take dawo mata, mace mai mutunci da mutunta kowa, duk yanda za su qulla mata sharri ko su yi mata rashin kunya ba zata kula su ba, abu ɗaya ta sani duk sanda ta daki Saddeqa ko Sadeeq Yadiko na magantuwa kuma tana nuna ɓacin ranta kwarai akan hakan, dan haka Mommy ta yi alqawarin aika wa yaran da kuɗi idan ta tashi yi wa Iyayen ta aike,a haka ta shiga ta yi wanka ta gasa jikin ta da kyau har ta samu ta ji ciwon kan ya yi mata sauqi, wayar ta ta ɗauka ta dannawa Sallau kira tace ya kai mata abinci,amma a saka naman kaza a ciki sannan ya haɗa mata da fresh milk,dan kuwa Alhaji yace mata daga fruits sai naman tsintsaye da madara ne suka kamaci jikin ta dan ta qara murjewa ta yi kyau,shi yasa bashi da aiki daya wuce na siyo naman talo-talo da yawa sai kaji haka masu aikin resort ɗin shi za su yi ta sarrafa mata abincin nan kala-kala,wani ta iya ci wani ta kasa ci saboda ba irin na qasashen mu bane na Africa, girki ne irin na turai tana kallon ragowar jinin naman sai ta gagara ci ta sha fruits da madara tace ta qoshi.

Sallau na bacci ta taso shi, haka ya fito yana zagin ta a ran shi dan ya kula yanzu tana da wani matsayi a gidan me girma be isa ya nuna mata ɓacin ranshi ba a fili idan yana son aikin shi.

A cikin daren ya sarrafa mata kaza ya haɗa mata duk abinda take da buqata ya haura sama ya kai mata, cikin wasu qananan kaya masu bayyana tsiraici ya ganta da sauri ya kauda kai ya ajiye mata ya bar d'akin dafe da qirjin shi.

"Iko sai Allah ji baiwar Allah'n nan yanda ta koma cikin qanqanin lokaci? Sanda tazo banda uban baki da idanu a lungu na me jin yunwa se uban warin talauci babu abinda take yi, amma yanzu ji ta har ta fi me gidan murjewa, shegiya nera me abun mamaki,"

Cikin son yin gulma ya sauka qasa sai da ya isa kitchen ya tuna ashe tsakar dare ne yanzun su Ruby basu nan balle ya guntsa musu, kama baki ya yi ya wuce d'akin shi ya rufe yana sake jinjina kyawun da mommy ta yi.

Ita kuwa yana fita ta ja abincin gaban ta ta hau ci tana danna waya,dan kuwa yanzu mommy an dena cin abinci hayam-hayam duniyar yanzu ta buɗe mata ba sauran yunwa da babu a tattare da ita.

Account balance ɗin ta ta duba ta ga tana da maqudan kuɗi a ciki, dan kuwa Alhajin ta da kan shi ya kai ta suka buɗe account a cewar shi tana buqatar privacy ba dole ne sai Hajiya K'waisa ta san samun ta gaba ɗaya ba, dik da cewa acikin zuciyar ta tana ganin kamar bata kyauta ba, amma kuma ta ji daɗin ganin yanda take da kuɗi ko tana son yi wa dangin ta abu ba sai ta jira Hajiyan ta bata ba.

Whatsapp ta duba ta ga tarin messages na wasu mutanen da suka dinga nuna suna son ta a resort ɗin Alhaji har ta basu No ta ba tare da ya sani ba,a hankali tana dubawa ta ga tarin messages ɗin shamsu, murmushi tayi dan tunawa da tsohuwar zuma, ba tare da ta duba ba ta ci gaba da duba saqonnin ta, No Sule ta gani ya bar mata tarin saqonni dan haka cikin sauri ta buɗe saqonnin nan taci karo da saqon rasuwar Yadikon da ma wasu tarin matsaltsalun da Sule ya sanar da ita.

Tashi ta yi zaune ta danna masa kira dan ta san shi a wajen shi dare shine ranar shi, yana ganin sabuwar lamba kuwa ya ɗauka a zaton shi 'yan matan sa ne da kan kira dan ya ɗebe musu kewa da kalaman shi na rashin d'a'a a cikin dare, sai ya ji muryar Mommy, da sauri ya tashi zaune ya ce,

'Ke dan uban ki ina kika shiga ake ta neman ki ba waya ba saqo ba aiken inda kika shiga? Kin ga abinda ya faru damu ko?'

Sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace,

"Na gani Sule, wayata ce ta samu matsala shi yasa baku ji ni ba, kuma gidan aikin mu ba ɗaya bane da Billy, se yanzu na sake waya na saka lambobin mutane a ciki,"

Ta faɗa ne kawai dan kar a gano halin da take ciki, tin sanda Billy ta kaita suka sayi waya take bata shawarar ta sake sabon layi,bata samu dama ba sai da Alhaji ya kai ta ta sai sabo a take a wajen ta loda No shi shida Samsunta.

'To ya ake ciki? Shiru shiru babu wani motsi?'

"Humm ai da kyar na yi bacci sanda na ga rasuwar Yadiko Allah ya jiqan ta, dan Allah gobe da safe ka yi min flashing zan kirawo ka mu gaisa da su Innoh na yi musu ta'aziyyar Yadiko,"

'Humm ki dai yi wa Baabaa ta'aziyya, dan yanzu gidan ba irin wanda kika tafi kika bari bane komai ya sauya,duk yanda zan yi miki bayani ba zaki gane ba se dai kin gani kawai da idon ki,'

"kon Allah! to ina Baba?"

'Na faɗa miki ba zaki gane ba se kin gani da idanun ki, Innoh ita ce ke mulkin gidan se abinda tace, Baba ba ya gane ma su Saddeqa yanzu ko sun gaishe shi sai dai ya amsa kawai ba dan ya san su ba, Yadikon kanta idan kika yi masa zancen ta se ya yi shiruuu kamar me tuna ina ma ya santa?'

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una me ya ke faruwa to?"

'Ahhh se kin tambaya ma? Ku ne fa kuke zuwa karb'o saqon irin qullin nan wajen Innah Naja ko Kaka ko har kin manta ne? ko da yake muryar ki kawai ta gama sanar dani irin wayewar da ki ka samu Sweet H,'

Qiris ya rage wayar hannun ta bata sub'uce ta faɗi ba a dai-dai lokacin da ta ji sunan ta na bariki a bakin Sule, in ina ta fara yi zata yi magana yace,

'Kar ki wani damu ba wanda zan sanar wa, nima ai kin san suna na a social media na taɓa jin kin sanar da wani? Dan haka kowa ya riqe wa kowa sirrin shi,amma ina jiye maki tsoron kar wani da ya sanki ya san gidan nan ya kawo rahoton ki,abun ba zai yi maki kyau ba idan Alhaji Baban Gida ya ji labari, dukan dakan sakwarar legas ze yi miki se kin yi laushi kamar gandar raqumin da aka dafa,to yanzu meye labari akwai wasu 'yan canji a qasa ne na sake waya?'

Wani yawu ta had'iya bayan ta gama jin kalaman Sulen,ajiyar zuciya ta sauke me qarfi sannan tace,

"Kai labarin da nake so na baka yana da tsawo, amma dai a taqaice shine ba aikatau nake yi ba, wasu 'yan harkoki ne dai ake yi ake samun miliyoyi...."

'Me milliyoyi ba ma nerori ba?'

Sule ya faɗa a zabure har yana miqewa zaune,

"Kwarai, yanzu haka ma jibi qasar zan bari amma dan Allah kar ka sanar da kowa kaji Yayana? Yanzu ka tura min account No d'in ka zan baka dubu ɗari da hamsin ka sai waya, sannan zan baka kuɗi masu yawa  ka sake wa Baba Machine a saka masa mai full tank, kuma zan baka wanda zaka bawa Innoh da Baabaa da sauran 'yan gidan,"

'Doleee yarinya se da keeee ! Muna godiya Allah sassaka, amma me zai hana ki saiwa Baba adaidaita sahu ya huta da machine ɗin nan, ko ruwa ko iska yana nan yana neman kuɗi da shi,Innoh kuwa ki bata tsurar kud'in tafi saka maki albarka,'

"To amma me zamu ce musu? Ina nufin a ina zamu ce an samu kud'in?"

'Ki bar wannan a hannu na yarinya zan ji da komai, ke datse waya na tura maki account No ta, gimtse ta nace,'

Sule ya faɗa yana wata iriyar murna, cikin dariya kuwa Mommy ta kashe waya, ba jimawa sai ga qarar message nan har ya turo account No d'in shi, nan take kuwa ta yi masa transfer na kud'in da zai isa ya yi duk abinda suka tattauna akai, qarshe ta ce ya riqe amana saboda ta haka ne zata ji daɗin kashe masa kuɗi,duk wanda tace ya bawa to fa ya basu banda k'wange.

Daga nan kuma Mommy ta gyara kwanciyar ta ta hau hamma, a haka bacci ya dauke ta bata farka ba sai qarfe takwas na safiya,a hakan ma Hajiya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login