Showing 267001 words to 270000 words out of 276165 words
Chapter 90 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
gida,watarana ma sai ya yi mata magana akan hakan sai ta ce masa bata kula ba ta yi busy ne,bayan kuma yana ganin ta online kullum.
Da yamma Bilal ya kama hanyar ƙauyen Ba Mugu dan isar da saƙon Yariman ƙauyen zuwa fadar Sarkin ƙauyen,wanda yake fatan su amince da buƙatar da zai gabatar musu cikin sauƙi. Ya isa ana ta kiraye-kirayen sallar magariba,dan haka masallaci ya wuce ya yi alwala ya shiga cikin sahu aka yi sallah da shi,bayan an idar da sallah ne ya zauna ya gabatar da azkar ɗin shi kamar yanda ya saba,yana idarwa ya miƙe ya nufi gidan Sarki,kafin ya isa ya kira Sultan ya ce ya sanar da zuwan shi.
Direct turakar Sarki Sultan ya yi masa iso suka shiga a tare,sai da suka gaisa da Sultan ɗin ne Sultan ya fita ya baiwa iyayen nashi waje su gana da baƙon su.
Cike da ladabi da biyayya Bilal ya fayyacewa Sarki da Innah Laminde abinda ke tafe da shi,sannan ya ƙara da cewa,
"Dan haka muke neman alfarma a wajen ku da ku taimaka ku baiwa Sarauta izinin sake auren Hadiza a karo na biyu ko dan yaron su ya taso a gaban iyayen shi cikin kwanciyar hankali."
Murmushi Sarki ya yi sannan ya ce,
"Madalla da abokin gaskiya da riƙon amana irin ka Bilal,tabbas tarayyar ka da Abdussaboor alkhairi ce,Allah ya yi muku albarka,mun jima da sanin irin wannan ranar zata zo ko bajima ko ba dad'e,idan kuwa bata zo ba to fa ita yarinya ta ɗaura aure da wani,dan haka mun amince su sake kasancewa a inuwa ɗaya a karo na biyu,kuma kamar yanda yarinya ta buƙata zan aika ƙanne na da waziri tare da sarkin fada zuwa wajen iyayen ta dan su nemawa Abdussaboor izinin auren ta,fatan mu Allah ya basu zaman lafiya ya kuma kaɗe dikkan fitina da abun ƙi."
Innah Laminde ce ta gyara zama ta ce,
"Amin Ran ka ya dad'e,nima dai bani da abinda zan ce da ya wuce Allah ya sanya musu alkhairi yasa wannan karon a yi zama na mutunci da mutunta juna."
"Amin ya Allah, mun gode Allah ya ƙara girma,Azizah ta ce a gaishe ku,ta so ta biyo ni nace ah ah wannan tafiyar ba tata bace ta jira zuwa wani lokacin."
Murmushi Innah Laminde ta yi,Mai Martaba kuwa ya ce,
"Ai na kula baka haɗa hidimar abokin ka da kowa ba Bilal,Allah ya yi muku albarka."
Da wannan hirar suka rabu kowa na cike da farin ciki, Innah Laminde kuwa a zuciyar ta take addu'ar Allah yasa daga wannan karon Abdul ya rabu da matsalolin aure kenan,koda a gaba yaso ƙarawa Allah ya kiyaye kar a sake samun matsalar da aka samu a baya.
Bayan isha'i Bilal ya bar garin Ba Mugu,kafin ya isa gida Abdul ya yi masa missed call ya fi goma,yana gani ya ƙi d'agawa saboda ya fi so su haɗu ido da ido ya sanar dashi abinda ake ciki.
Washegari da sassafe ko karyawa Abdussaboor ya kasa tsayawa ya yi,duk yanda Suhailah taso ya tsaya ya sa wani abu a cikin shi ƙi ya yi, ƙarshe rabuwa ta yi da shi ta zauna ta karya kafin ta rufe gidan ta wuce wajen aikin ta.
Tinda Abdul ya isa office ya gane irin sammakon da ya doka,dan kuwa babu wanda ya zo da ya wuce mai gadi dake wajen a zaune,murmushi ya yi sannan ya shafa gemun shi ya ce,
"Da alama Bilal yau yana so na bishi har gida na ji saƙona."
Yana nan zaune mutane suka fara zuwa jefi-jefi,Bilal kuwa be zo ba sai da takwas ta buga,tin daga nesa Abdul ya hango sabuwar motar Bilal na shiga building ɗin,cikin sauri ya buɗe tashi motar tare da rufe ta da makulli ya isa wajen aminin nashi,gani ya yi Bilal ya fito fuskar shi a tamke kamar wanda aka baiwa wani mummunan labari,gaban shi ne ya yi wani irin faɗuwa har sai da ya jingina da jikin motar shi,jiki babu ƙwari ya fara takawa zuwa wajen Bilal,a hankali Bilal ya kalle shi ya yi masa nuni da ka su haɗu a office,Abdul ji ya yi kamar ƙafafun shi ba za su iya ɗaukar gangar jikin shi ba,a hankali ya furta.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,ya Allah ka bani wuyan ɗaukan duk abinda zan ji daga Bilal,mai kyau ko akasin hakan."...........
*Soyayya ruwan zuma ce...idan da Deejee a gefen Abdul ba zai ƙi murmushi baaaaa.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 108:
A office ɗin Bilal suka yada zango, Abdul dai sai zare idanu yake yi yana jiran Bilal ya sanar dashi abinda iyayen shi suka yanke game da auren shi da Hadiza. Bilal kuwa sai ja masa rai yake yi ta hanyar yin wasu ƙananun ayyukan da basu da wani mahimmanci a wajen Abdul,cike da ƙosawa Abdul ya ce,
"Wai dan Allah meye ka ke yi haka? Ka yi sauri ka sanar dani abinda kuka tattauna kada zuciya ta ta buga saboda zullumi."
"Lallai Abdul ka isa,yanzu a gabana ka ke ikirarin bugawar zuciyar ka saboda Hadiza? Hadiza fa."
Haɗe fuska Abdul ya yi sosai kafin ya ce,
"Ban gane Hadiza fa ba? Me kake nufi da maganar ka? Dan Allah ni ka ajiye maganar wasa ka sanar dani abinda Mai Martaba ya ce, ko dai basu amince bane?"
Ajiyar zuciya Bilal ya sauke kafin ya ce,
"To magana ta gaskiya dai haƙuri zan fara baka dan kuwa....."
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un ! Shikenan sun yanke min farin ciki na,Bilal ya zan yi yanzu? ina zan...."
Dakatar da Abdul bilal ya yi kafin ya ce,
"Ka taimake ni ka natsu Abdul,ina baka haƙuri ne akan ja maka ran da na yi ne,amma mai martaba da Innah duka sun amince da auren ku kai da Hadiza a karo na biyu."
Galala Abdul ya saki baki yana kallon Bilal,kafin daga baya ya miƙe tsaye cike da farin ciki ya rungume Bilal yana murna,cikin sauri ya fita daga office ɗin Bilal ya faɗa nashi,sai da ya kulle ƙofar da makulli dan kar ma a dame shi sannan ya samu waje ya zauna a kujera. Wayar shi ya ɗakko daga aljihun rigar shi ya nemo No Hadiza da ya mayar mata da sunan ta na da wato Baby. Bata wani jima tana ringing ba Mommy ta ɗauka,cikin kashe murya Abdul ya ce,
"Baby ya kike?"
Jimm Mommy ta ɗan yi tana wani lumshe idanu saboda jin sunan da ya kira ta da shi,ta jima tana mafarkin sake jin wannan sunan a bakin shi,ashe dai da rabon mafarkin ta zai zama gaske,shirun da ta yi ne ya sanya shi gane halin da ta shiga,wani murmushi ya saki dake can ƙasan maƙoshin shi,har sai da Mommy ta ƙanƙame wayar saboda vibration ɗin murmushin da ya sauka a kunnen ta,cikin sake maƙale murya yanda ya san yana rikita ta a baya Abdul ya sake cewa,
"Baby ko baki jina ne? Hello?"
A sanyaye Mommy ta ce,
'Ina jin ka mana,kawai ina mamakin saurin zaƙewar ka ne bayan babu wata ƙwaƙƙwarar maganar iyaye a tsakanin mu.'
"Ki kwantar da hankalin ki Babyna,Mai Martaba da Innah sun amince ki sake zama surukar su,uwar jikokin da zaki sake haifa musu anan gaba,dan haka idan kin bani dama ko yau ɗin nan ma sai aje nema min auren ki."
Zaro ido tayi waje,sannan ta karɓe hannun ta da ake zanawa baƙin lalle ta tashi tsam daga wajen ta koma ɗaki,saman gado ta haye ta na lumshe idanu ta ce,
'Sorry ka jini shiru ko? Na ɗan tashi ne daga wajen mutane,ammm game da amsar abinda kace,ka ɗan jira har mu dawo daga tafiyar da muka yi,saboda har Baban muka taho Abuja.'
"Wait ! Dama kina nufin bada saurayi ki ka tafi ba da Baba ne?"
Dariya Mommy ta yi kafin tace,
'Ni dama na ce maka na yi tafiya Abuja da saurayi ne? Daga ni sai Baba se Yah sule muka tafi.'
Shiru ya yi yana nazarin maganar ta,nan take ya gane me ta yi masa,murmushi kawai ya yi suka ci gaba da zubawa junan su kalaman soyayya kamar ba za su rabu ba,da ƙyar mommy ta yi nasarar bashi haƙuri suka yi sallama tare da alƙawarin kafin ya koma gida za su yi waya.
Wunin ranar Mommy da Abdul sun yi shine cikin farin ciki,a haka aka ci gaba da hidimar bikin su Anisah da Khaleesat,ranar Juma'a na zuwa aka ɗaura aure washegari aka yi dinner,sanda aka tashi daga dinner angwaye suka kwashi matan su da kansu babu ƴan rakiya suka wuce da su gidajen su. Tin a daren ranar Ɗan Liti ya ce wa Mommy da sule su shirya da sassafe za su koma, zai ɗauki fasinjan kano a tasha,dan haka kar su ɓata masa lokaci.
Ranar Mommy a gidan Saddiqa ta kwana ita da Sule da Sadeeq,sun sha hira sosai,inda Sule yake basu labarin abokin shi da ya ɗana masa tarko a nan Abujan,ashe neman maza abokin yake yi ya b'oye masa,duk tsawon lokacin da suka ɗauka a baya suna abota a Facebook shi son Sule yake yi ba tare da Sule ya sani ba,dan haka shida abokan shi sun gama haɗa duk ranar da Sule ya shigo gari to fa za su haɗu a yi party da murnar haɗuwar su ta farko. Ganin Sule ya jima da haƙura da rayuwar da ya yi a baya ne ya ga bashi da dalilin haɗuwa da abokan shi na Facebook har a haɗa party da mata da maza,wannan dalilin ne yasa duk yanda suka yi ya je ya ƙi,ƙarshe shine abokin ya kira shi ya dinga ɗura masa ashar yana sanar da shi da ya kuskura ya je da sai an yi masa ɗinki a bayan shi,domin kuwa kaca-kaca ya yi niyyar yi masa ya kauda kwad'ayin sa akan Sulen. Tinda Sule ya ji wannan mugun tanadin da suka yi masa sai ya ƙi zuwa koda wajen ɗaurin auren ne,bashi da burin da ya wuce ya wayi gari ya ganshi a ƙauyen Ba Mugu.
Dariya Mommy da Saddiqa suka dinga yi masa,domin kuwa har a wannan lokacin da yake basu wannan mugun labarin zufa yake yi,duk da sanyin Ac dake parlourn.
Suna tsaka da dariyar sule ne Mommy ta sanar da su abinda ke tsakanin ta da Abdul,murna suka taya ta sosai,Sule ya hau yabon Abdul sannan yana yiwa Mommy faɗa akan yanda zata zauna da mijin ta da abokiyar zaman ta lafiya,shiru tayi tana sauraron shi, dan kuwa ko be faɗa ba yanzu ta yi karatun ta nutsu,kishi ba nata bane tinda a yanzu wata zata tarar,sannan ta yi zama da Meron Malam da Tsahare ta koyi yanda zata yi controlling kishin ta akan Abdul.
Tsaraba sosai Saddiqa ta haɗa musu,sannan ta bada wanda za su baiwa Sadeeq da ya maƙale wajen Munir,ba ta manta da su Innoh da Baaba ba a tsarabar ta,har ma da Amir. Alƙawarin zuwa auren Hadiza ta yi koda kuwa kwana ɗaya zata yi ta juyo a jirgi duba da yanayin karatun ta baya buƙatar wasa.
Suna nan suna hira Sadeeq da Munir suka dawo,suma zama suka yi aka dasa sabuwar hira da su,kafin daga baya kowa ya wuce makwancin shi.
Washegari da asubar fari bayan sun yi sallah Munir ya kwashe su ya kai su gidan Alhaji Baban Gidan,koda Sule ya leƙa ɗakin baƙi sai ya tarar da Ɗan Liti dake ta faɗan da sassafe za su wuce ya baje a ƙatuwar katifa yana bacci abun shi. Dariya ya yi ya ja masa ƙofa,Ummi ce ta fito sanye da wani ɗanyan leshi a jikin ta sai baza ƙamshi take yi, idanun nan nata duk sun zurma ciki,da alama bata samu isasshen bacci ba da dare,jikin ta duk babu wani kuzari suka gaisa da su Mommy,cike da tausayawa Mommy ta ce,
"Ummi ya kewar su Anisah kuma? To Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a masu albarka,ya kamata yanzu da basu nan ki samo masu aiki saboda ki samu masu ɗebe maki kewa da taya ki aiki."
Kallon gidan Ummi ta yi sannan ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ta ce,
"Ke dai bari Mommy,ji nake yi kamar na rabu da wani ɓangare na jiki na,ban shiryawa tafiyar yaran nan gaba ɗaya ba a lokaci ɗaya,tsakanin jiya da yanzu da na fito na san tabbas zan sha wuya kafin na saba da rashin su."
"Inshaa Allahu komai zai zo maki da sauƙi Ummi,ga ƙaramin mai gidan ki nan yana taya ki hira ai baki da matsala."
Murmushi Ummi tayi kafin ta ce,
"Dama Baban ku zai bar min ke koda na sati biyu ne,da na ji daɗi."
Cike da zaƙewa Sule ya ce,
"Tabdijam ! Ai idan Baba ya bar maki ita na wata ɗaya ma tsohon mijin ta ba zai bar maki ita na sati ɗaya ba,dan kuwa ya dawo da zafin shi,so yake a sake ɗaura musu aure kwanan nan."
Mommy ce ta sunne kai cike da jin kunya kafin ta ce,
"Kaiii Yah sule faɗi ba a tambaye ka ba sannu da aiki,kai Sadeeq je ka ka taso Baba kar ya ga laifin mu kuma ya ce bamu tada shi ba."
Murna sosai Ummi ta taya mommy,kafin ta miƙe ta shiga ɗakin da ta tara gift ɗin su Anisah da suka yi saura,kaya ta dinga ɗibarwa Mommy har bata san iyakar su ba,ta dai san zannuwan gado sun fi yawa a ciki,sai da ta cika mata wata babbar jaka sannan ta kira Sadeeq ya je ya fito da jakar,albarka ta sanya wa Mommy sannan ta yi mata alƙawarin zuwa auren ta idan lokaci ya yi,cike da murna ta ce,
"Za mu zo har da Sadeeqa itama ta ga gida,ta jima bata zo ba saboda makaranta,gashi yanzu lokaci na ta tafiya ta yi nisa da karatun,Allah ya nuna mana lokacin,kar a manta a sanar damu da wuri."
Shiru Mommy ta yi tana jin kunya,Sule kuwa ya amshe addu'ar sannan ya ce,
"Da kaina zan sanar dake Hajiya Ummi,"
Munir ma ba a barshi a baya ba wajen baiwa Mommy kuɗi yace ta sayi wani abu,da ƙyar ta karɓa saboda nauyin shi da take ji,Ɗan Liti na fitowa sai ya hau masifa yana zagin yaran tare da faɗin,
"Idan na rasa fasinja a tasha dik se kun biya kud'in mota."
Dariya suka hau yi masa,kafin Ummi ta ce,
"Ai kuwa duk saurin ku kun tsaya ku ci abinci ko? Ina nan da sauran abinci Mommy biyo ni mu dumama kowa ya ci ya koshi,akwai abubuwan da na tanada saboda Baaba da Innoh da basu samu halartar bikin ba."
Bayan ta Mommy ta bi suka je suka haɗa abinci suka dawo,kowa ya zauna ya ci ya ƙoshi suka ɗebi wanda za su ci a hanya,suna tsaka da shiri Alhaji ya sakko suka gaisa, kuɗi mai yawa ya baiwa Ɗan Liti ya ce a sha mai, godiya sosai suka yi musu har da shi aka fita raka su Ɗan Liti,motar shi ya buɗe ya shiga ya kunna, nan da nan Sule da Saddiq suka zuba kaya a bayan motar ta cika famm,sannan suka zauna a baya,a haka ya wuce dasu tasha ya kwashi mutum biyu da za su je kano, ɗaya a baya, daya a gaba sannan suka bar garin.
*************************
Tafiya ta yi kyau dan kuwa da misalin karfe ɗaya suka isa kano,direct tasha Ɗan liti ya nufa ya ajiye mutanen nan,sannan ya yi lodin ƙauyen Ba Mugu,daga nan suka sake kama hanya sai gida.
Sun isa garin Ba Mugu ana kiran sallar la'asar,Ɗan Liti har cikin gari ya shiga da mutanen nan ya ajiye su a ƙofar gidan shi,kowa ya ɗauki dan ƙullin kayan shi da babu wani yawa ya wuce gidan shi,suna shiga gidan suka tarar da Ameerah zaune tana ta tsartar da yawu saboda sabon cikin dake tattare da ita,cike da murna suka hau gaisawa da mutanen gidan,nan suka baje a tsakar gidan aka raba tsaraba,Baaba sai murna take yi da farin ciki,ƙarshe sai da ta yi kukan murna jikokin ta sun samu mijin aure a lokaci ɗaya, addu'a ta yi musu sannan ta ce,
"Hadiza kema Allah ya fitar maki da miji na gari ki yi auren ki."
Cike da zumuɗi Saddiq ya ce,
"Ai Baban Amir ya ce zai turo a yi maganar komawar ta gidan shi in ji Yah Sule."
Takalmi Mommy ta ɗauka ta jefe shi da shi kafin ta miƙe da jakar kayan da Ummi ta bata ta wuce ɗakin ta,dariya Sule ya kwashe da ita ya ce,
"To ai gashi nan kin kwashe kayan auren naki da aka baki,idan baki son auren se ki faɗa mana amma ba ki hau jifan yaro ba dan ya faɗi gaskiya."
Kowa ya taya Mommy murna banda Ameerah da Ɗan Liti,Ɗan Liti jira yake yi ya ji shin Mommy ta amince da sake auren Abdul? Ita kuwa gwaskiya Ameerah takaicin ta bai wuce na Abdul yana da wata matar a gidan ba,Mommy zata je a ta biyu kenan,nan take ta karkace baki ta ce,
"Ai da mun san haka zata kasance da baki kashe auren ki ba kin yi zaman ki a ɗakin ki,gashi nan yanzu zaki koma a ta biyu."
Innoh ce ta ce,
"To bismillahi zaki fara halin ko? Ki raba ni da kunji-kunji Ameerahh,ai yanzu dai magana ta ƙare,abinda ya faru ya riga ya faru sai a tari gaba,Allah ya basu zaman lafiya."
"Amin"
Shine abinda kowa ya ce kafin su tashi zuwa yin sallar la'asar.
Da misalin shida na yamma wazirin sarkin garin Ba Mugu da sarkin Fada da wasu baffanin Abdul ne suka zo har ƙofar gidan Ɗan Liti a mota,rasa inda zai saka su Ɗan Liti ya yi,koda ya shiga gida ɗakin Baaba ya wuce direct,ita ce ke da carpet da babbar tabarma,kwasar su ya yi bayan ya sanar da ita me ke faruwa, ya wuce soro ya shimfiɗa musu suka zauna,sai da ya tabbatar sun zauna sannan ya koma ciki dan sama masu ruwan sha,Baaba ce ta bashi ruwan roba da Alhaji Baban Gida kan siya mata guda sha biyu,komawa ya yi ya ajiye musu sannan ya zauna dan a gaisa,suna tsaka da tattaunawa akan neman auren Hadiza da suka zo Baaba ta baiwa Sule dake ɗaki yana hutawa sauran snacks ɗin da suka kai mata tsaraba ya kai soro,sai da ya saka shaddar shi da ya yi niyyar sakawa ranar ɗaurin aure tsoro ya hana shi fita sannan ya kai musu snacks ɗin, godiya suka dinga yi suna washe baki,dan kuwa wasun su basu taɓa cin kayan fulawa irin wannan ba.
Babu ɓata lokaci Ɗan Liti ya kira Alhaji Baban Gida a waya akai komai akan kunnen shi,dan