Showing 90001 words to 93000 words out of 276165 words

Chapter 31 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

haka...uhum uhummm me yake wari haka mun shiga uku,"

A galabaice Saddeqa ta janye jikin ta daga na Ameerah dake cika tana batsewa tana jin kamar ta shaqe Baabaa itama, wanne wari take yi haka har da kowa ke magana akai ne? Ita fa bata jin warin da ake magana akai,ta sani wulaqanci ne kawai ake yi mata ba komai ba.

Da sauri Baabaa ta duqa ta ja Saddeqa dake kwance cikin tab'o da datti,ruwa ta ja a rijiya ta dinga kwara mata daga qarshe ta shiga d'akin Yadiko ta samo mata wasu kayan ta ce ta shiga tayi wanka ta sauya.

Baabaa da kan ta ta ɗora masu abinci tace se dai a haɗa da na dare dan ba shegen da zai sake saka marainiyar Allah girki da almuru.

Saddeqa ta jima a band'aki dan kuwa tana tsugunnawa a shadda ta dinga zawo, cikin ta gaba ɗaya ya burge, da kyar ta samu ta gama abinda zata yi tayi wanka ta yi alwala ta wuce d'aki sanye da kayan da Baabaa ta bata,sallah ma a zaune tayi ta saboda rashin k'warin jiki, Ameerah kuwa na nan tsakar gida tana qunquni da zage-zage,Baabaa ce ta juya ta qanqance ido tace,

"Idan baki deb'i ruwa kin shiga wanka ba ruwan nan na tafasa zan d'iba da zafin shi na yi miki wanka Ameerah, kin dai san idan aljanu na suka tashi ko uwar ki da take ji da qiba ba qarfi na tafi ba ko? Shashashar yarinya kawai, a hakan ne Mannirun zai so ki kina wannan mugun warin?"

Tana jin Baabaa ta ambaci sunan Munir Ameerah ta miqe ta kindimi ruwa ta wuce bayi tana zumb'ura baki,a haka ta samu ta yi wanka sama-sama ta fito, ko kallon inda take Baabaa bata yi ba ta ci gaba da aiki, fatan ta taci qarfin aikin kafin Innoh ta dawo daga yawon nata ta hau Saddeqa da masifa.

Zaune suke gaban Boka ya gama dube-dube da tsubbace-tsubbacen da zai yi ya kalle su cike da tashin hankali yace......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI














RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH ✍️✨














PAGE 34:








"Ran boka ya dad'e akwai matsala ne?"

"Gagaruma ma kuwa, domin kuwa wannan yarinya Ameerah auren ta da wannan yaron Manniru zai yi wahala indai dole sai an mallake kakar shi za a yi auren, amma ba zan ce ba zai yuwu ba gaba ɗaya saidai ko zai yuwu ɗin to fa za a sha wahala,"

"Boka wai waye zai sha wahalar ne? Ni ko 'yata ko kuma su iyayen yaron ko wannan matsiyaciyar Saddeqar?"

"Kece wadda zata fi shan wahala a lamarin kafin 'yar ki ta biyo baya,amma kuma kar ku manta maganar bahaushe da yace...yi yafi rashin yi wai qazama tayi tsarki da ruwan d'orawa,daga qarshe dai za a ce tayi tsarki,"

"Da ruwan ɗorawar boka? Ai gwanda ta zauna babu tsarkin,ina sam ba zata sab'u ba,a bar wannan aikin a kama na babbar 'yata boka, ina so 'Ya ta Mommy ta auri wannan yaron Abdussaboor ɗan sarkin garin nan, sannan idan an sake binciko wata hanyar mai sauqi a taimaka min a na Ameerahn ma yarinyar nan kashe kanta take so tayi akan yaron nan Boka,"

"Kar ki damu ai ke kina sakin kuɗin aiki dan haka za a yi miki aiki da kyau,ko da ba ta samu auren wannan da kuke so ta aura ba za mu yi mata abinda zai sa ta manta shi ta samu wani tayi auren ta baki alekum,"

"Ni dama haka za a yi da nima hankali na yafi kwanciya dan har yanzu zuciyata bata son haɗa zuri'a da tsohuwar nan,idan yaso ita yarinyar nan Saddeqa a hana yaron auren ta kowa ya rasa,"

"Zamu yi me yuwa ku dai ku saki kuɗin aiki ku ga aiki,"

Su Innoh basu baro wajen boka ba har sai da suka tabbatar da za a sama masu mafita akan matsalolin su domin sun yi imani da shi, muddin suka kai masa damuwar su komai girman ta yana yi masu maganin ta,dan haka suka baro wajen shi ran su fess Naja ta wuce gida Innoh ma ta yi nata gidan.

Ko da ta iso gidan la'asar ta jima da wuce wa, domin kuwa qarfe shida na maraice yayi, Sule ta tarar yana zaune yana cin abinci sai zuba santi yake yi yana fad'in,

"Ni fa Allah na gani nafi son girkin Yadikona tin da can, sai kuma na Saddeqa da Baabaa, in dai Innoh tayi miya se ka ji gishiri ya zarce ko kuma wajen son a burge baba se a zabga mata shegen maggi, watarana kuma kaga mai nashe-nashe kana leqawa ka hango fuskar ka kamar madubi, tuwon kuwa idan ka yanko zaka iya jifa da shi goshi ya tsage tsabar tauri kaii....."

"Goshin uban ka na jefa da lomar tuwo ya tsage sule, nace goshin uban ka na jefa, shege sallamamme kwasasshe,ina can ina fafutukar yanda zan samawa 'yan uwan ka farin cikin su kai kana nan kana ɗebe min albarkar abincin da dashi ka ci ka girma, Sule idan baka fita a ido na ba na rufe se na....."

"Assalamu alaikum, Mommy na nan?"

Billy ta katse Innoh dake ta faɗa ta hanyar doka sallama, faram-faram ta shiga gidan kamar babu abinda ya faru ɗazu,Innoh na ganin ta da qatuwar jaka itama ta washe baki ta hau fad'in,

"Lale maraba da Bilkin Mai dusa, bismillah tana cikin d'aki na ko Sule? "

Ta qarasa Maganar ta da tambayar Sule inda Mommy take dan kuwa bata da masaniyar inda take a yanzu tinda itama dawowar ta kenan gidan daga yawon bin bokaye,Mommy ce ta fito tsakar gida ido yayi mata luhu-luhu saboda kukan da ta sha,tsayawa tayi tana kallon Billy da wani mugun kallo tace,

"Billy me ya kawo ki gidan mu kuma? Kin ga dan Allah ki tattara dik wani abinda ya kawo ki ki bar min nan bana son ganin ki,bana so na sake yin wata alaqa dani da ku har abada, kun koyar dani darasin rayuwar da ba zan taɓa mantawa da shi ba, dan haka bana buqatar duk wani abu dana same shi daga wajen ku,ki juya ki koma ki kaiwa wannan qaton banzan kayan nan dan kuwa bana so,"

Cikin wani irin yanayi Billy ta isa gaban Mommy ta riqe hannun ta ta qura mata idanu, kafin ta buɗe baki tace,

"Mommy ki kwantar da hankalin ki,shi kan shi k'waisan ya kore ni da kan shi, Man ne ya kawo mana kayan mu na gidan ta, ki Karb'a ki duba na tabbata duk wasu kuɗin ki suna ciki dan kuwa nima na ga nawa a ciki, kuma ATM ɗin ki ma na ciki kar ki yi wa kan ki da 'yan uwan ki asarar dukiyar da na tabbata basu taba riqe irin ta ba, ki...."

Wufff Innoh tayi ta amshe jakar ta na risinawa kamar zata duqawa Billy ta hau fad'in,

"Mun gode kedai 'yar albarka, Allah ya saka da alkhairi mun gode ki gaida min aminiyata Allah ya saka da alkhairi sai da safe,"

Billy ce ta kalli Mommy taga shigar dake jikin ta, wata riga ce mai siririn hannu an riqeta ta sama ta qasa ta baje amma dik da haka ana ganin shape ɗin Mommy fatar nan luwai da alama qasar da taje ta karɓe ta,tini ta cire gashin dokin dake kan ta asalin gashin ta ya sha parking, dan kuwa Mommy na da gashi dama rashin gyara ne ya sa yake danqarewa ta qeya ta gaba ya kwanta luwai, yanzu kuwa da ake gyara mata shi ya tashi ya miqe ya yi kyau, yawu Billy ta had'iya a ranta tana ayyana.

'Allah yasa Yah Abdul ya aure ni sai daga baya in sa ya auro ki Mommy in haɗa ku ku biyun ina morewa ta'

A zahiri kuwa sai ta dafa kafad'ar Mommy ta ɗan shafa tace,

"To Sweet H sai da safe, ki yi tunani da kyau wannan kuɗin halal ɗin ki ne ke kika nema da jikin ki, idan ma kin qi Karb'a an mayar musu a banza za su cinye ke kikai asara,dan haka sai da safen ku,"

Haka Billy ta tafi ta bar Mommy na gasgata maganar ta, dan kuwa ta san ta wahala da jikin ta kafin ta samo kuɗin to me zai sa ta bar wa su K'waisa? Da sauri ta fizge jakar a hannun Innoh ta shige d'akin Innoh ta zauna a bakin gado,ganin Innoh ta biyo ta d'akin ne ya sa tace,

"Dan Allah Innoh ki ɗan bani waje mana ina buqatar sirri kika san meye a jakar tawa? In kuɗi ne ni ba da kaina na fita nema ba dan na baku ku mora me zai sa na hana ki yanzu da aka kawo min har gida? Dan Allah ni ki fita idan na gama zan kira ki,"

Babu musu kuwa Innoh ta fita tana washe baki, Sule ne ya yage murya yace,

"Qanwata idan an gama nima ina nan ina jiran a yaga min wata salalar,"

Ba tare da Mommy ta amsa shi ba ta buɗe jakar waya da laptop ta fara gani a sama sannan ATM ɗin ta da ta bari a lokacin da zata bi Alhaji Uganda,hawaye ne suka sirnano mata saboda tunawa da Alhaji da cin amanar da yayi mata.

Tana d'aga rigar farko taga bandir ɗin dubunnai guda huɗu da sauri ta mayar ta rufe tana zare ido, leqa window tayi ta hango Sule da Innoh tsaye suna ta safa da marwa a tsakar gidan, shawara ta yanke akan bari ta d'akko bandir biyu ta boye sauran, dan haka cikin sauri ta boye kuɗin ta ta kira Innoh da Sule,kamar su yi tsuntsuwa su gan su a gaban Mommy suke ji,suna shiga suka samu waje suka zauna kowa ya zuba mata idanu, cikin yanayi na rashin son hayaniya ta zari dubu goma ta miqawa Sule sannan ta zari dubu talatin ta miqawa Innoh, sai ta ware kuɗin da zai isa a sai mata katifa ta bawa Sule tace ya siyo mata a yau ɗin nan, dan bazata kwanta a qasa ba ta wuce wannan yanzu, har zai tafi ta sake zare dubu ashirin tace ya siyo mata akwati da kwad'o da makulli,tana faɗin haka Innoh ta tsume ta hau masifa,

"Iyyy ga gidan b'arayi da 'yan banga da fashi da makami dole a sai kwad'o da makulli,"

Ko kulata mommy bata yi ba ta d'akko wayar ta ta kunna, ba jimawa ta kunnu nan take ta duba accounts ɗin ta na social media kafff an goge mata su,nan take ta sayi katin dubu uku dan ta loda data.

Sanda ta ga alert ɗin kuɗin ta dake banki sai da ta saki wayar ta ta kurma ihu, nan fa ta manta da ma me ya sanya ta siyan katin wayar,ashe dama ta tara waɗannan manyan kuɗin bata sani ba? Ya aka yi to Hajiya k'waisa ta dawo mata da komai ba tare da ta taɓa ba? Anya ba wani tarkon aka sake d'ana mata ba kuwa?

"Ke me ya faru kike ihu haka?"

Cikin son ɗauke tunanin Innoh tace,

"Babu komai b'era na gani qato ya wuce qasan gado,"

A sheqe Innoh ke kallon Mommy tace,

"B'eran kike yiwa Ihu haka mommy? Yaushe kika fara tsoron shi? Ko da yake ke yanzu ai 'yar birni ce rayuwar ki ta sauya an ga kano,"

"Hummm Innoh ni fa ba iya kano na gani ba, ni nan da kika ganni har wasu qasashen na je, na je america na je Uganda idan kin taba jin sunan wajen,"

Zama Innoh tayi ta kama hab'a tace,

"Ke 'yannan faɗa min gaskiya, da gaske kin je america! Can qasar turawa fa masu jar fata,"

"Ai a can muka haɗu da Abdul ya cece ni daga hannun wasu 'yan iskan qasar,Innoh zauna na baki labarin gaskiyar abinda muke aikatawa a wajen aikin mu naga baki damu da sanin meya faru da rayuwa ta ba lokacin da na bar gida, burin ki kawai a kawo kuɗi kin san ta hanyar da na samu kuɗin kuwa?"

Sadeeq ne ya shiga d'akin Innoh yana kuka ya zube a gaban ta yace,

"Innoh ki taimaka min Yah Saddeqa ke ta zawo a kwance tin d'azu, na bata magani ta sha tayi amai"

Toshe hanci Innoh tayi tace,

"Za me? Zawo? Inaaa Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni nan da ka ganni rabona da wankin kashin yara tin Ameerah na qarama ba jika gare ni ba balle na wanke masa kashi dan haka maza tashi kaje ka sanar da waccan k'yarmadasshiyar tsohuwar me kama da busasshen Kilishin ta taya ta gyara jikin nata kaji,"

Mommy ce tace,

"Habaa Innoh ki taimaka mata mana a fa dalilin Ameerah ta kamu da amai da zawon nan,"

"Ke ki je ki taimaka mata mana uwar iyayi, haka kawai ina zaune a sani jinyar kashi? Ni Allah na tuba kashi na ma dan ya zama dole na wanke ne da ba zan saka hannu ba,"

Cikin dariya mommy tace,

"Kuma in faɗa miki Innoh a america akwai wani waje idan kikai ba haya ruwa ne kawai zai wanke maki shi ki tashi ki kab'e jikin ki kiyi fitowar ki,"

"Dan Allah ki bari,"

"Da gaske nake,"

Muryar Baabaa suka jiyo tana mita ta wuce zuwa wajen Saddeqa tana faɗin,

"Ke dai Innoh kin yi asara, uwar yarinya ta mutu kin koma kishi da ita saboda asara akan ki ta qare,  kai Saddequ deb'o min kuka a madafi da ruwa da cokali kaga,"

Da sauri Sadeeq ya kawo duk abinda ake da buqata ya bawa Baabaa ya riqe Saddeqa dake mulmula a qasa saboda ciwon ciki yana ta jera mata sannu, Baabaa kuwa kuka ta d'iba cokali biyu ta kwab'a da ruwa ta bawa Saddeqa ta kafa kai ta shanye, tana shanyewa ta taimaka mata suka fita tsakar gida Baabaa ta wanke mata jikin ta kafin su koma d'aki Sadeeq ya gyara d'akin ya kunna turaren wuta na tsinke ya fitowa da yayar tashi kayan sakawa.

Sai da yaga Saddeqa ta ji dama sannan ya wuce masallaci ran shi na matuqar quna akan halin da suke ciki a gidan, Saddeqa kuwa sallar magariba tayi ta koma ta kwanta a wajen ko abinci ta kasa ci,abinda yafi damun ta dama amai da gudawar ya tsaya kuma ta dace tinda ta sha kukar nan bata sake yi ba.

Sabuwar katifar da Sule ya shiga da ita ce ta sanya Ameerah da ko sallar magariba bata yi ba ta fito tana tambayar na waye,ko kula ta Sule beyi ba ya yada katifar a tsakar gida ya wuce d'akin shi da baqar ledar shi guda biyu.

D'akin su na da Mommy taje dan  ta share taji yana tashin wani irin mugun wari a guje ta fita tana haki tace,

"Alqur'an bazan koma d'akin nan ba se dai na koma na Yadikon sule, kan bala'i Ameerah wanne irin wari ne wannan a d'akin? to wai kashi kike yi a ciki?"

"Ban sani ba wulaqancin banza kawai, kar fa ki ga kin je birni kin dawo ki dinga yi wa mutane iskanci na ga dai aikatau kika je yi a birnin ma ba wata tsiyar ba aikin banza kawai,"

Ameerah ta faɗa tare da tsirtar da yawu ta koma d'akin ta ta kwanta tana jin zafin yanda kowa ke gudun ta,mommy kuwa na fita d'akin Yadikon Sule taje babu neman izinin Saddeqa ta maida kayan ta cikin akwati ta kulle da makulli sannan ta yada katifa ta roqi zanin gado wajen Innoh,nan take Innoh ta kuwa bata har da pillow ta yada ta kwanta, dan kuwa a gajiye take tana buqatar bacci sosai har ta fara lumshe ido taga Saddeqa zaune tana lazimi tana jiran ayi isha'i ta yi, sai Mommy ta fita waje dan tayi alwala ta yi sallah itama, saida ta fara yin wanka sannan ta yi alwala ta wanke bakin ta sannan ta koma d'akin tayi sallah.

A can gidan su Billy kuwa basu rabu da Man ɗin ta ba sai da ta sama masa natsuwa da kyau ta hanyoyin da matar aure ce kawai ya fi dacewa tayi wa mijin ta hakan musamman idan tana a halin rashin tsarki, sai gashi Billy da bata da aure ta k'ware tsafff har ta fi wata matar auren ma k'warewa ta sallami Man ɗin ta ya cika ta da nera ya tafi abun shi.

Tana komawa gida ta tarar da Ummahn ta bata nan ta tafi gidan Sarki,murmushi tayi ta kwanta a gadon ta tana faɗin,

"Wo ni Billisious 'Yar Sanata, in yi bariki son raina sannan in auri ɗan sarki in na ji kwad'ayin qawata ya dame ni in sa a auro min ita in haɗa su su biyu a gida ɗaya ina mora,Allah ka kai damo ga harawa ko be ci ba yayi birgima, Mommy ina mai baki shawara ki hakura da Yah Abdul ki barmin shi na fara auren sa ko kuma dani da ke dika mu rasa ayi biyu babu, idan kunne yaji?...........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI













RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨















PAGE 35:













Kishiyoyin Innah Laminde ne suke zaune a parlourn ta bayan sallar magariba suna tattaunawa game da abinda ya faru da safe, kowa na kawo tata shawarar Innah Laminde na sauraron su, guda biyu sun fi yarda da Abdussaboor ya auri Bilkisu tinda an san asalin ta kuma gida bata qoshi ba ba a kaiwa dawa ba, ɗaya daga cikin su kuwa ta ce ai sam Mommy da Bilkisu basu dace da Abdul ba, Abdul yafi qarfin auren yaran da suka yi aikatau a wani gidan a matsayin shi na ɗan sarauta kamata yayi ya auri 'yar manyan mutane kamar shi, dan haka tinda ya rasa kamilar yarinya kamar Saddiqa to a barshi ya zaɓi wadda ranshi yake so,idan kuma a cikin su Allah ya nufa akwai matar shi sai a yi masa addu'a da fatan alkhairi, Innah Laminde tafi aminta da wannan shawarar dan haka sai ta kulle zancen da cewa,

"To Allah yayi masa zaɓin alkhairi, ni babbar damuwa ta ma yanda ya ɗora ran shi akan wannan yarinyar me zumb'utun baki kamar duwaiwan kaza,dik ya fita hayyacin shi bashi da zance sai na irin son da yake yi mata, yanzu ma sai da Bilal yayi masa wankin babban bargo sannan ya dena maganar ta suka tafi masallaci,"

"Babu komai a hankali watarana idan an ce yaa taɓa son ta ma ba zai yarda ba, mu yi ta taya shi da addu'a watarana sai labari,"

In ji wadda ke bi wa Innah Laminde, hira suka ci gaba da yi tare da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login