Showing 96001 words to 99000 words out of 276165 words
Chapter 33 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
qoqarin rufe zanin ta kar Mommy ta gani, sai dai ta makaro saboda Mommy ta haska ta da hasken wayar ta da ta toshe da hannun ta ta sauke a gaban Ameerah,nan take tayi mugun gani kuwa, baki ta toshe tana kallon Ameerah tace,
"Ameerah meye zan gani? Qonewa kika yi ko me? Wa ya faɗa maki ana kara wannan wajen a wuta idan ana so a cire gashin wajen? Ki yi amfani da reza ko shaving stick ko shaving cream mana, ki duba ki ga dan iskanci yanda kika babbake jikin ki ba dole ki dinga wari ba kamar mushe tinda kin kama waje kin qunshe babu wanda kika sanarwa, ko Innoh ta sani?"
Cikin kuka Ameerah tace,
"Ku yi wa Allah ku rufe wannan maganar ku sama min mafita na dena jin azabar nan da nake ji,"
"Ke meye wannan baqi kika haɗa mata da tsakar daren nan?"
"Yah Mommy magani ne irin wanda Yadiko ke samu tsarki da shi idan mun gama al'ada, ba kuma qonewa tayi ba ina zargin Infection ne ya kama ta,"
"Na shiga uku wanene Infeshon? Maye ne? A wanne gida yake ni Ameerah,"
Baki ta wage zata yi kuka da qarfi Saddiqa tace,
"Yah Ameerah shiga ruwan kar ya huce zan yi miki bayani daga baya,"
Cikin daddafe robar ta shiga ruwan da sauri ta miqe tsaye zata yi ihu Mommy ta damqe mata baki da qarfi sannan ta sake danna ta cikin ruwan,tin Ameerah na kuka har ta natsu ta zauna saboda daɗin ruwan da take ji yana ratsa ta, Saddiqa ce tace mata ta sa hannu ta wanke wajen da kyau idan yaso sai ta juyo mata wanda ta sake sakawa ta d'auraye, haka kuwa ta sanya hannu babu musu ta wanke wajen tana hawaye, tana gamawa ta fita Saddiqa ta ɗauki ruwan taje rariya ta zubar, gaba ɗaya jin cikin ta take yi yana hautsinawa saboda wari da qarni amma babu yanda zata yi dole ta koma ta d'auraye robar ta sake zuba mata wani ruwan ta sirka ta kai mata, wannan karon bata ji zafi ba sai ma daɗin ruwan da taji, har wani bacci me daɗi ne ke fizgar ta a ruwan Mommy ta talle mata qeya tace,
"Tashi dan uban ki bacci zaki yi mana muna tsaye sauro na cizon mu?"
Hamma Ameerah tayi zata tashi ta maida zanin ta, sai taga Saddiqa tana jan ruwa a bokiti hannun ta riqe da sabon sabulun wanka da reza,miqawa Ameerah tayi tace,
"Yah Ameerah idan kina so ki warke dika dole ki aske gashin hammatar ki da na gaban ki,sannan kiyi wanka ga ruwa nan na saka maki mai zafi ki yi wanka ki zo na baki sabuwar atampar Yadiko ta sallar data wuce ki saka,"
Ameerah dai tinda taji wajen nan yayi mata daɗi bata yi wa Saddiqa musu ba ta wuce ta fara aske gashin hammatar ta sannan na gaban ta, ta yi wanka me kyau ta fito d'aure da sabo kuma wankakken zanin da Saddiqa ta bata, d'akin Yadiko suka koma gaba ɗayan su Saddiqa ta cika alqawarin ta na baiwa Ameerah atampar Yadiko ta saka, cikin zuciyar ta tana jin kewar mahaifiyar ta sosai, addu'a tayi mata sannan ta d'akkowa Ameerah man zaitun tace ta shafa a gaban ta sannan tace,
"Yah Ameerah kiyi hakuri amma dole ne zan faɗa maki wata gaskiya koda baza ki ɗauka ba,kuma koda zaki ji haushi na saboda na jima ina neman hanyar da zan yi maki magana na rasa, yanzu kuwa Allah ya bani dama dole ne in sanar dake gaskiya,"
"Ke bana son iyayi kar ki ga kin taimaka min ki ji cewar kina da damar zaunar dani ki ishe ni da surutun banza,"
"Yah Ameerah ba surutun banza bane, kar kiyi mamaki idan nace maki nasan me ya jawo maki wannan mummunan ciwon infection ɗin,"
Cikin tsawa Ameerah tace,
"Ke wai shi menene wannan shegen Infeshon ɗin da kika dame ni da shi ne?"
Mommy wadda bata manta da bayanin infection da ciwon sida ba daga bakin Hajiya k'waisa ce ta amshe tace,
"Ciwon sanyi kenan wawiya,ciwo ne da ake ɗauka ta hanyar saduwar mace da namiji, ko mace da mace, ko kuma ta hanyar amfani da hannu ko wani abu mara tsafta a biyawa kai buqata a yayin sha'awa,sannan ana iya ɗauka a band'aki mara tsafta, ko kuma sanya kayan gwanjon da ba a tsaftace ba kafin amfani dasu, ko kuma sanya wando ko zani ko skirt ɗin wanda ke ɗauke da ciwon,to ke garin yaya kika kamu da wannan mugun ciwo dan ni ban taɓa sanin yana irin wannan abun ba, waje ya sale kamar an qone ga wari kamar an buɗe shaddar gidan gandu da safe,"
Saddiqa ce tace,
"Ni na san ya akai ta kamu da wannan ciwon,kema Allah ne ya kare ki a lokacin da kike gida kafin ki tafi aikatau baki kamu da shi ba, saboda ke kina kwatanta tsafta ita kuwa Yah Ameerah hannun ta da datti da komai take sanyawa a gaban ta wajen biyawa kanta buqatar sha'awar ta,wannan halin da kuke aikatawa ba abu bane mai kyau, bayan ciwukan da yake tattare dashi akwai zunubi da azabar Allah da zata riski mai aikatawa, kar ku manta akwai malaman da suka haramta biyawa kai buqata saboda shi abinda yake cutarwa tafi amfanin shi yawa to a musulunci an haramta shi,saboda a dik abinda Allah yake haramta mana babu ɗaya da zai amfanar da Allah da komai ko ya cutar da shi face abun nan cutarwa ne a gare mu, saboda soyayyar da Allah yake yi mana shi yasa yake haramtawa saboda masoyan shi na gaskiya bayin shi masu yi masa biyayya su guji abun dan kar su cutu, bayin Allah kuwa da basu son Allah bakuma su bin dokokin sa sai su qi bi hakan yayi sanadiyyar cutuwar su,ina mai yi maku nasiha a koda yaushe ku guji dik abinda aka ce zina ne, domin Allahu subhanahu wata'ala ya haramta kusantar ta balle ma a aikata ta,kar ku manta masu biyawa kai buqata ba kowa ke wankan tsarki ba gudun kar a gano shi,to wanda be tsarkake jikin shi ba ta yaya zai yi ibada?
Ina jiye maku ranar qin dillanci ranar da wutar Allah mai tsananin duhu da azaba da firgici da tsoro zata zama mazaunin ku idan baku tuba ba, yanzu dan Allah akan jin daɗin minti ɗaya ko biyu ko uku sai ku yi wa kawunan ku tanadin mazauni a wuta? Ku fa duba ku gani hayaqin nan na duniya kawai aka barmu dashi ya ishe mu azabtuwa, mutane dake kashe kawunan su wasun su na amfani da wuta su kashe kan su saboda sun san zafin ta ba abune da bawa zai jure mata ba,to dan Allah ku faɗa min me yasa zaku yi abinda zaku shiga wutar qiyama wadda a cikin ta aka d'ebo hayaqin ta bayan an wanke shi a ruwa sannan aka bamu shi a nan duniya muke girki da sauran buqatun mu? Kun shirya karb'ar azabar Allah ne ? Kun shirya shiga wuta ne?"
Cikin tsananin firgici Mommy ta sauka daga saman gadon da ta zauna a gefen Ameerah wadda tinda Saddiqa tayi nisa a nasihar ta bacci ya ci qarfin ta ta kirifce tana baccin ta,mommy kuwa katifar ta ta hau ta kwanta tare da qanqame jikin ta tana tuna yanda ta dinga bari maza na saduwa da ita saboda kuɗi da son abun duniya har ta kai kanta inda aka nuna mata fin qarfi,kuka ta dinga yi kamar zata haɗiyi zuciya,ta kasa shaqar numfashi saboda yanda take jin kamar ana shaqe mata wuya za a ɗauki ranta, a tsorace ta miqe tana janyo numfashi da kyar tana wani irin tari, ina zata iya ɗaukan azabar Allah? Haqiqa ta cuci kanta dan kuwa bazata dorawa kowa laifi ba tinda babu wanda ya d'aure ta a lokacin da taji cewa ba aikatau zata yi ba karuwanci zata yi.
Saddiqa ce ta isa gaban ta ta zauna tana shafa bayan ta tare da yi mata firfita, cikin murya mai sanyi tace,
"Yah Mommy kar ki d'aga hankalin ki dan Allah har ki samu wata matsalar,kin manta a bayan dik wata azabar Allah akwai rahamar shi mai tarin yawa? Kin manta cewa Allah mai gafara ne kuma mai afuwa ne idan ka nemi gafarar shi da afuwar shi zai shafe zunuban ka su zamo kamar baka taɓa aikata su ba? Dan haka dena kuka ki yi ta istighfari da hailala da kuma yin sayyidil istighfar, wallahi Allah ba zai barki ki wulaqanta ba face ya gafarta maki zunuban ki duk girman su kuma ya maye gurbin su da lada,"
Cikin kuka Mommy tace,
"Ke yarinya ce Saddiqa bazaki gane me na aikata ba a rayuwa ta ba, na tabbata Allah ba zai yafe min ba, kar ki manta tun ina gidan nan nake karanta littafan batsa na kalli films ɗin batsa, na saurari audios na batsa, na yi soyayyar da bata dace ba da shamsu sannan da natafi birni...dana tafi baki san...."
Kuka ne yaci qarfin ta ta kasa qarasa maganar ta,cikin sigar lallashi da kwantar da hankali Saddiqa tace,
"Allah afuwwu ne, zai yafe maki kuma ya shafe su a Littafin ki matsawar kin yi tuba irin tuban da ake so mumini yayi, ma'ana ka fara nesanta kanka daga zunubin, ka nemi gafarar Allah, sannan kayi niyya bazaka sake komawa wajen aikata zunubin ba balle ma ka aikata shi, shikenan zaki zamo kamar wata jaririya dan kuwa Allah zai shafe zunuban naki,"
Cikin sauri kuwa Mommy ta hau istighfari, jin an fara kiran sallar asuba ne ya sanya Saddiqa tashi ta fita ta sanya ruwan zafi da gishiri ta wanke robar da Ameerah ta zauna a ciki da kyau ta ajiye tayi alwala ta koma d'akin su.............
*Matasa ina mai kira a gare ku da ku ji tsoron Allah ku kyale jin daɗin mintuna qalilan, idan kai saurayi ne baka yi wa kan ka fatan kayi aure? Ko idan mutuwa zata riske ka ta riske ka kana a halin saurayi nagari ta yanda matan hurul ini zasu tarbe ka su jiyar da kai daɗin da babu irin shi a duniya? Idan ke budurwa ce baki son ki tadda mijin ki na aljannah ya jiyar dake daɗin da babu irin sa a duniya? Zaɓi na wajen mu 'yan uwana masu albarka*
*Unedited page a yi hakuri da abinda aka gani.*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 37:
A cikin sati ɗaya Saddiqa ta gama jinyar Ameerah ba tare da Innoh ta gane ba, da rana kuwa haka Ameerah zata yi ta yanka mata rashin mutunci amma da dare da kanta take zuwa qofar d'akin ta ta kira ta tazo ta haɗa wuta ta dora mata ruwan magani ta zauna a ciki ta bata na shafawa, Mommy kuwa ta cire kuɗi ta bata ta siyo na asibiti tana sha,dake bata da qan jiki nan da nan qurajen sun mace sai dai har a wannan lokacin akwai qaiqayi da take ji a gaban ta tinda ba dena muguwar dabi'ar da take yi tayi ba.
Bangare Mommy kuwa dik ta bi wayar ta ta goge kafff videos ɗin banza da hotunan dake cikin wayar ta, tana yi tana istighfari, films ɗin dake ɗauke da soyayyar da bata dace ba duk ta goge daga laptop ɗin ta, abu ɗaya ke damun ta shine matsananciyar soyayyar Abdussabour da har yau be neme ta ba bai kuma turo gidan su ba kamar yanda ta sa a ranta zai yi ɗin tinda yana matsanancin son ta.
Yau Saddiqa ta tashi cikin murna da farin cikin Saukar qur'anin su da za a yi wanda suna kammalawa da wata biyu kuma za su fara rubuta jarabawar su ta qarshe,babban abinda ya dame ta rashin kulawar Ɗan liti akan saukar tata, dan kuwa da ta sanar da shi ma cewa yayi,
"Allah sa alheri akan sauka ba zan fasa nemo wa iyali na abinci ba"
Yayi ficewar sa zuwa wajen sana'ar shi,masu taya ta murnar gaskiya a gidan basu wuce Baabaa, Sadeeq ,jikokin Baabaa da su Abbe 'ya'yan Baabaa da suka so zuwa amma basu samu dama ba sai suka aiko yaran su sai kuma Sule, Innoh kuwa banda sukar abun babu abinda take yi,daga qarshe ma cewa tayi,
"Allah dai yasa dan Allah'n aka yi saukar ba b'ata lokaci akai ba ana ta yawon zuwa makaranta,dan dai mutum yasan riya haramun ce ah toh,"
Babu wanda ya kula ta dik da cewa maganar ta tayi wa Saddiqa zafi sosai kasancewar dama ta tashi da kewar Yadiko sosai a zuciyar ta, haka ta shanye baqin cikin ta ta jawo farin cikin da ke qasan ranta ta gama shiri ta nufi d'akin Baabaa, tana shiga ta tarar da Baabaa itama ta cakare cikin atampa riga da zani ta sanya sky blue ɗin hijabi, murmushi suka sakar wa junan su Baabaa tace,
"Rabu da ita baqin ciki ke damun ta da hassada,yaran ta kafff babu wanda ya haddace daga fatiha zuwa sabbi shi yasa take haushi kamar karya,Allah ya jiqan Yadikon Sule da tana a raye tabbas da yau zata zamo rana mafi soyuwa a gare ta domin kuwa ta ci burin ganin wannan ranar a rayuwar ta fiye da ranar auren ki, kar kiji komai kina tare da albarkar ta a duk inda kike, muje kar mu makara,"
Saddiqa hannu ta sanya ta share hawayen ta fuskar ta ɗauke da wani irin murmushi na farin ciki, hannun Sadeeq ta kama suka fita tsakar gida Baabaa na kulle d'akin ta ta hango Mommy sanye cikin abaya mai bala'in kyau kalar maroon sak hijabin jikin Saddiqa, mayafin abayar ta yafa a saman kanta ta saka baqin takalmi mai tsini wanda ya dace da jakar hannun ta, Baabaa ce ta qanqance ido ta kalle ta tace,
"Ke kuma ina zuwa haka?"
Kafin Mommy ta bata amsa Sule ya fito daga nashi d'akin sai kallo ya koma kan shi, sanye da farar shadda sabuwa gadagal fara sol tana ɗaukan ido ya fito,hannun shi sanye da baqin agogo qafar shi da takalmi sau ciki baqi kan shi babu hula, yayi matuqar kyau kamar ba Sule ba, Saddiqa ce ta fashe da dariya tace,
"Yah Sule dama kana saka manyan kaya?"
Murmushi yayi yace mata,
"Gashi yau kin gani Za a je ne ko ya ? naga kun wani tsaya kuna kallon juna,"
Baabaa ce ta mere baki tace,
"To ni dai ban san tafiyar har da marasa hijabi za ayi ba da na yi gaba abuna, dan ba zan jera da zangareriyar mace kamar wannan ba babu hijabi,ni ba 'yar iska bace ah toh,"
Innoh ce ta fito tana kumfar baki tace,
"Wacece 'yar iskar to? Kema Allah ya qara babu wanda ya gayyace ki amma saboda shegen iyayi zaki je gashi nan ana zagin ki a banza,Ameerah da tasan ciwon kanta ai gata can bata ce zata je ba ma balle ta shirya zuwa,"
Mommy bata kula kowa ba ta yi gaba dan ta san plan ɗin da suka riga suka haɗa da Innoh a bayan fage wannan duk buyagi ne dan bata so a gano su, a qofar gida ta tsaya ta zaro kwallin da Innoh ta bata ta sanya ta ɗauki baqin gilashi ta toshe idanun ta da shi ta tsaya jiran su Saddiqa su fito.
Baabaa na ta masifa ta tattaro kan Saddiqa da jikokin ta dika suka yi gaba, a qofar gida suka tadda Mommy na jiran su, gaba Baabaa tayi tace duk shegiya mara hijabin da ta biyo ta bata yafe ba ta barwa Allah ya musu hisabi ranar gobe,ci kan ki Mommy bata ce mata ba dan abinda ke gaban ta kawai take son aiwatarwa ta bar taron ta dawo gida.
Sun isa wajen taron sun tarar mutane sun zo har an fara gabatar da manyan baqin dake wajen, da gudu Saddiqa ta isa wajen da ya dace ta zauna dan kuwa ita zata riqe abun magana su gabatar da karatuttukan da za a gabatar na farko kafin a fara bikin saukar tasu, zaman ta ke da wuya Munir ya shiga makarantar tasu ya qarasa cikin taron, tana karb'ar abun magana idanun ta suka sauka a cikin nashi, wani irin daɗi ne ya mamaye zuciyar ta har sai da k'walla ta taru a idanun ta, murmushi ya sakar mata ya d'aga mata yatsu biyu,sauke kanta qasa tayi sannan ta kalli gaban ta ta d'aga kai zata fara karatu, karaf idanun ta suka shiga cikin na Abdussabour da ya sha rawani yana zaune a wata royal chair mai cin mutum biyu shi kaɗai cikin shiga ta alfarma,domin kuwa shine babban baqon taron nasu, ba zata iya tantance yanayin da yake ciki ba, amma tabbas kallon da ya kafe ta dashi yana huda naman jikin ta yana zama.
A hankali ta fara a'u'ziyyah kafin ta yi basmala ta fara karatun ta mai tsananin daɗin sauraro cikin suratul Rahman, shiru wajen ya ɗauka kafin daga baya sauran d'aliban su ɗauka su ci gaba dayi a tare,kabbara ce kawai ke tashi ko ta ina saboda yanda karatun nasu ke sanya tsigar jiki miqewa dan daɗi.
Wani mai hoto ta gani wanda babu irin shi kaff garin nasu yana ta ɗaukan ta a hotuna har ta fara jin ta takura, lura da hakan ne ya sanya Munir da ya kawo shi yayi masa waya ya bashi umarnin ya yi nesa da ita da alama ta takura da ganin shi yana yi mata hoton, babu b'ata lokaci kuwa ya bar wajen yayi nesa da su ya ci gaba da aikin shi.
A haka taron ya ci gaba da gudana har lokacin da babban baqo ya karb'i abun magana ya yi wa ɗalibai nasiha akan su riqe qur'ani kar ya zamo abun wasa abun mantawa a gare su, sannan su dinga aiki da shi ba wai su karanta a baki ba kawai, yana kammalawa aka dinga baiwa d'aliban kyaututtuka, Saddiqa itace yarinya ta farko da ta karb'i kyauta mafi yawa a taron gaba ɗaya, ta karb'i kyautar tsafta, tafi kowa k'ok'ari sannan tafi sauran ɗalibai tarbiyya da kamun kai, daga qarshe ta karb'i kyautar wadda tafi kowa iya hadisai da tafsirin alqur'ani, Baabaa kuka ta dinga yi tana murna tare da faɗa wa mutanen dake wajen ai 'yarta ce,nan fa aka dinga taya ta murna, Munir kanshi sai da yaji wani irin alfahari da ganin wannan itace matar da