Showing 192001 words to 195000 words out of 276165 words
Chapter 65 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
A ci gaba da haƙuri watarana sai labari,shekaran jiya Sule yaje gida yake sanar dani haihuwar Ameerah da irin abubuwan da Innoh ke yi maki na rashin mutunci,Allah ya jiƙan Delu mutuniyar kirki,na rasa a ina yarinyar nan ta d'akko wannan mugun hali."
Cikin nuna hali na dattako Baaba ta ce,
"Amin, ai ni da Innoh mun zama abu ɗaya yanzu,muna nan tare da halin mu,ni nayi mata ne itama tayi min, dan haka kar ki wani damu da irin zaman da muke yi,yo dika rayuwar ma nawa take? Kina dai ganin yanda lokaci ke gudu yanzu,sai a kwanta da mutum lafiya,washegari a tashi babu shi,Allah dai ya sa mu dace ya raya mana kuma abinda aka samu."
"Hakane kam, to ameen ya Allah, a ci gaba da haƙuri,bari naje dare na yi."
Baabaa ce ta shiga ɗakin ta ta ɗan ƙullowa dattijuwar kayan ƙwalama da man shafawa da sabulu guda ɗaya,har bakin ƙofar fita daga gidan ta raka ta suna hira,Innoh kuwa banda bin Baabaa da harara babu abinda take yi, dan kuwa zargin ta ya gama bata Baabaa ce ta kai ƙarar ta wajen Goggon ta dan a hana ta zuwa birni.
Cikin sauri Sule yabi bayan Goggo dan yayi mata rakiya,sai da Baaba ta duba Ameerah da jinjirin ta sannan ta wuce ɗakin ta ba tare da ta kula ƙananun maganganun da Innoh keyi ba.
******************
Bayan kwana bakwai su Abbe da wasu daga ƴan uwan Innoh suka shirya tafiya suna zuwa gidan Mommy,Sule shine yayi musu jagora saboda shi kaɗai ne yasan gidan, Innoh kuwa tana ji tana gani suka tafi babu ita,baƙin cikin da taji kuwa baya misaltuwa.
Dik abubuwan da take yi Ameerah na ankare da ita,kuma ba kaɗan ba abun keyi mata ciwo,a wajen Baabaa kawai take samun cikakkiyar kulawar da ta dace ace mai sabuwar haihuwar fari tana samu.
A can gidan Mommy kuwa gida ya cika da jama'a,wanda hakan ba ƙaramin baiwa mommyn mamaki yayi ba,bata taɓa zaton za a taru haka ba duba da ko maƙotan ta bata shiga,amma dik da haka sai da suka zo mata suna har da kawo mata abun biki.
Gidan sarki ma mota biyu suka cika suka je suna,ciki har da mahaifiyar Billy sai da ta halarta,sai da mutane suka fara raguwa sannan Ta Annabi ta samu Mommy zaune a ɗakin Abdul, tana shayar da kyakkyawan jinjirin ta da suke kira da Amir kasancewar yaci sunan mahaifin Abdul,zama tayi tana kallon Mommy cike da sha'awar ɗaukaka da darajar aure da ta lulluɓe ta, cikin zubar da hawaye tace da mmmy,
"Hadiza dan girman Allah idan kin san inda Bilkisu take a garin nan ki sanar dani,ina so naje na ganta tinda ita taƙi zuwa ganin mu,ina kewar ta matuƙa Hadiza,dan Allah ki taimaka min ki sanar dani inda zan ganta na je na ganta."
Tausayin Ta Annabi ne ya kama Mommy,nan take ta hau tuna channel ɗin su Billy ta YouTube da ta gani ita da Any,shin yanzu ya zata yi ? Sanar da ta Annabi halin da Billy take ciki zata yi ko kuma ta ja bakin ta tayi shiru kawai?.....
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 78:
Kafin Mommy ta baiwa Ta Annabi amsa Hafsat ta shiga ɗakin,fuskar ta kawai zaka kalla kasan tana cikin farin ciki,zama tayi a kusa da Ta Annabi sannan tace,
"Innah ku taso muyi hotuna,Yah Abdul ya zo shi da Yah Bilal suna can waje suna jiran mu."
Wata sassanyar ajiyar zuciya mommy ta sauke, dan kuwa ba ƙaramin taimakon ta Hafsat tayi ba da ta shigo a dai-dai wannan lokacin,a tare suka jera za su fita Mommy ta miƙawa Ta Annabi jinjirin suka fita jikin ta dik a mace,kwalliya da shigar da Mommy tayi ne ya sanya Bilal haɗe fuska ya ce wa Abdul.
"Kana nufin a haka matar ka zata zo ta tsaya a gaban mai hoto ya dinga ɗaukar ta a hoto? Dubi shigar da tayi fa? Ko ni nan be kamata na ganta a haka ba balle wannan da babu dangin iya babu na baba,sannan ba abokin ka bane ko wani naka makusanci."
Sai da Bilal ya yi wannan maganar sannan Abdul ya kalli Mommy ya ga yanda shape ɗin ta ya fito daga ƙirjin ta har mazaunan ta a cikin dakakken leshin da aka yi wa matsattsen ɗinki,fuskar ta tasha kwalliyar zamani sai walainiya take yi,ga gashin doki da aka ƙara a saman nata ya zuba a bayan ta, dik inda ta gilma ƙamshi ne kawai ke tashi,tsaki Bilal ya ja sannan ya fita daga parlourn ya na yi wa mai ɗaukan hoto magana akan su je waje su jira mata su shirya,mai hoton ne ya kalle shi yana murmushi,dan kuwa ya gane abokin mai gidan na taya mai gidan kishi akan yanda matar shi ta fito babu suturce jiki da sunan wai suna ake yi.
Bayan tafiyar mai hoto da Bilal waje ne Abdul ya kira Mommy ɗaki, suna shiga ya ja ta a jikin shi yana yaba kwalliyar ta da kyawun da tayi,cike da jin daɗi Mommy itama ta hau yaba masa, cikin natsuwa Abdul ya yi wa Mommy bayanin yanda yake jin kishinta sosai, ta fito gaban maza babu mayafi,Mommy taji daɗin yanda ya nuna kishi akan ta, dan haka a tare suka zaɓi mayafi mai kyau a cikin kayan lefen ta da ya dace da leshin,Abdul ne ya yafa mata mayafin sannan ya zaro wayar shi ya hau yi musu hotuna da videos.
A can parlour kuwa sun gaji da jiran su, dan haka sai kawai Sule ya leƙa ya kira mai hoto su ya yi musu da jinjiri,Bilal ma ba a bar shi a baya ba wajen ɗaukan hoto da su Azizah, sai wani shisshige mata yake yi yana nuna mata yanda zata tsaya ayi mata hoton,ita kuwa sai noƙewa take yi tana jin nauyi da kunyar shi.
Suna tsaka da ɗaukan hotunan ne Mommy da Abdul suka fito,ganin Mommy da mayafi ne ya sanya Aunty Naja yin dariya ta hau tsokanar Abdul,murmushi kawai yayi aka miƙa musu yaro mai hoto ya hau ɗaukan su.
Ana daf da magariba mutane suka tattafi aka bar dangin ango da na amarya kawai,Abdul da Bilal kuwa sun yiwa kowa sallama sai ya bi Bilal gidan shi dan ya kwana a can, tinda gidan nashi babu wajen kwana.
Dik yanda suka so Sule ya bisu su tafi ƙi ya yi yace akwai inda zai kwana,sai da ya ci ya ƙoshi ya yi nak sannan ya shiga ya yi wanka ya wanke bakin shi ya musu sallama, tare da sanar da su sai da safe za su gan shi, yana fita ya danna No wayar wata budurwar shi da suka haɗa duk sanda ya shiga kano zai je ya taya ta kwana,mijin ta ba mazauni bane dan haka tana buƙatar wanda zai ɗebe mata kewa da dare,da kwatance Sule ya isa gidan matar.
Ko da ya isa ya tarar da gidan nata fiye ma da yanda ya yi zato,gida ne ƙato na alfarma mai ɗauke da manyan motoci,sai da mai gadi ya amsa wayar matar gidan sannan aka bar Sule ya shiga,baki ya saki yana kallon gidan cike da ƙauyanci.
Wayar shi ce ta yi ringing ya ɗauka, direction ɗin inda zai bi har ya shiga gidan matar gidan ta dinga bashi, ko da ya shiga tankamemen parlourn tsayawa ya yi yana kallon gidan,mamaki ne ya kama shi a dai-dai lokacin da ya ga wata hamshaƙiyar hajiya baƙa ta fito daga wata ƙofa,sanye take da wata shadda kalar maroon sai k'yalli take yi,fuskar ta tasha kwalliya da jan janbaki kamar wata aljana, cikin sauri Sule ya shiga WhatsApp ya hau duba profile picture ɗin budurwar tashi, sannan ya shiga chats ɗin su ya ga hotunan ƙirjin ta da gaban ta da take tura masa,nan take ya fita daga hirar a dai-dai lokacin da yaji hannun matar na shafa ƙirjin shi tana faɗin,
"Barka da isowa shalelena,bismilla muje ciki, abinci zaka fara ci ko wanka zaka yi kafin mu fara faranta ran junan mu?"
Zabura Sule yayi ya koma baya yana cewa,
"Ba..ban..ban gane ba, Hajiya ke ɗin wacece?"
Fari matar tayi sannan tace,
"Ni ce dai Baby nice ɗin ka da muke chatting,ni ce dai babyn ka dake kashe maka kud'ad'e,kuma ni ce babyn ka mai taya ka hira duk dare ta ɗebe maka kewa,a yau zan nuna maka zahirin hirar da kullum nake yi maka a waya,yau zan shayar da kai mamaki da farin cikin da baza ka taɓa mantawa ba."
"Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri suna nazo,sunan ƙanwata ake yi ko haƙiƙa ba a yanka ba ni kaɗai ake jira."
"Haba Baby meye haka? Ya kake abu kamar ba jarumi ba? Kar ka ganni haka kayi zaton wani tsufa nayi,rashin samun kulawa daga wajen miji na ne ya jawo nake neman irin ku suna share min hawaye na,ka amince mini ni kuma nayi maka alƙawarin zan baka dubu hamsin a kwana ɗaya,idan kayi min kwana biyu zan baka dubu ɗari,iya kwanakin da zaka taya ni iya kud'in da zan baka,dan haka ka bar maganar suna da yanka haƙiƙar da ba a yi ba a cikin wannan daren."
Yawu Sule ya had'iya yana nazari,kallon fuskar matar yayi ya hango tsananin munin da take dashi,wata zuciyar tashi kuma sai ta fara hasko masa irin tarin dukiyar da zai samu idan ya amince mata,cikin sanyin jiki Sule ya fara sakin jikin shi da ita sannan ya ce,
"To Hajiya yanzu kina ganin ba wata matsala? Idan mai gidan ya dawo fa?"
"Bama zai dawo ba saboda baya ƙasar ya yi tafiya Singapore,zai kuma kai a ƙalla wata ɗaya bai dawo ba, dan haka muna da lokacin farantawa junan mu kafin ya dawo."
A hankali Sule ya saki jikin shi,sai da ya ci abinci da kaji zuƙu-zuƙu sannan suka haura sama shi da Hajiyar, sai da komai ya kankama a tsakanin su ne Sule ya fara ji a jikin shi, dan kuwa dik wata basirar shi da ƙwarewa tare da jarumtar shi sai da suka ƙare wajen faranta wa Hajiya rai.
A jigace Sule ya ce,
"Wayyoo Allah na, dan girman Allah ki bari na huta, ki bari gobe mu ƙarasa na yi alƙawari zan yi maki kwana uku, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una."
Cikin ɓacin rai Hajiya ta miƙe ta kalli Sule ta wurga masa wandon shi ta ce,
"Ragon banza ragon wofi, ashe ma dik cika bakin da kake yi ƙaramin ƙwaro ne kai? Sau biyar ɗin ne ka gaji? Kai da ka ce dik sanda muka haɗu zaka kwana kana faranta min rai?"
"Na tuba,na tabbatar da ba zan iya kaiwa safiya da rai na ba idan muka ci gaba da wannan abun, mutuwa zan yi Hajiya."
Tsaki ta ja mai ƙarfi kafin ta tattare jikin ta ta sanya rigar baccin ta ta wuce band'akin dake cikin ɗakin,Sule na ganin haka ya miƙe cikin sauri ya saka kayan shi, sanɗa ya hau yi ya buɗe ƙofa ya fita parlour a guje, yana zuwa bakin ƙofar parlourn ya murd'a sai yaji ƙofar a rufe gam,wani irin marayan kuka ne ya kama shi kawai sai ya zube a wajen yana rera shi kamar marayan da bai jima da rasa iyaye ba.
Motsin Hajiya ya fara ji cikin sauri ya miƙe tsaye ya hau goge fuskar shi,bakin dinning table ya tsaya yana buɗe sauran abincin dake saman table ɗin,murmushin Hajiya yaji a bayan shi tana faɗin,
"Ragon maza kawai,yau dai naga ƙarshen cika bakin babyna,abinci za ka ci na zuba maka?"
Yage haƙora Sule ya yi sannan ya sunne kai ƙasa ya ce,
"Hajiya kenan,bari naci na ƙoshi na ƙara shan maganin nan da kika bani ɗazu wataƙila na iya taɓuka wani abu kafin gobe."
"Ko kai fa?"
Zama suka yi suka ci suka ƙoshi, sannan Hajiya ta ƙara banka wa Sule magani suka koma ruwa,ranar nan Sule ba ƙaramar wuya ya sha ba a hannun dattijuwar matar da ta isa ta haife shi.
Washegari da misalin goma na safe kowa yayi wanka, an gama raba naman suna an baiwa dangin Mommy da dangin Abdul nasu, sai kuma aka hau tunanin shin ina Sule yaje ne? An kira wayar shi tayi ringing har ta daina ringing ba a ɗauka ba, Aunty Naja ce tace,
"Idan zaku kama hanya ku tafi ku kama,dan kuwa Sule ba yau ya saba shigowa kano ba, ba zai ɓata ba inshaa Allahu."
Da wannan maganar su Abbe suka shirya dan tafiya ƙauyen Ba Mugu,bayan tafiyar su kuwa Mommy ɗaki ta tafi dan ta kwanta ta huce gajiyar suna,sai ta bar wa Aunty Naja Amir,tana shiga ɗaki ta ga wayar ta na ringing, koda ta ɗauka sai taga No Saddiqa, amsawa tayi suka gaisa,dan kuwa Saddiqa ta saba Kiran ta lokaci zuwa lokaci ta gaida ta, barka Saddiqa tayi mata sannan ta ce,
'Yah Mommy bamu samu zuwa suna ba saboda nima nayi nauyi yanzu,bana jin zan shanye wannan watan ban haihu ba,dan Allah ki tura min account No ɗin ki na turo abinda za a sai wa babyna wani abun.'
Murmushi Mommy tayi sannan tace,
"Saddiqa kenan, ke yanzu kina ganin har kina da kuɗin da zaki turo na sai wa ɗana wani abu da shi? Ki riƙe abin ki na gode da gaisuwar ma da kike kira muyi,Allah ya sauke ki lafiya "
Saddiqa ma murmushi tayi, dan kuwa ko babu komai yanzu tafi ƙarfin a kira ta da talaka, dai-dai gwargwado Munir na sakar mata kuɗi,cikin ƙasƙantar da murya tace,
'Aunty kar ki manta nima dai ɗana ne,dan haka komai ƙanƙantar abinda zan turo dan Allah a sai wa ɗana wani abun tinda ban samu zuwa ba,ina jiran ki ko kuma na kirawo Yah Sule ya tura min.'
Jin kalaman Saddiqa na kiran Amir da ɗan ta sai ya sanyaya ran Mommy,murmushi tayi sannan tace,
"To Shikenan tinda kin ce haka, zan turo maki Allah ya ƙara zumunci."
'Yauwa yayata ta kaina, Amin ya Allah na gode, a gaishe min da babyna da Yah Abdul ɗin.'
Suna yin sallama Mommy ta turawa Saddiqa account No,babu bata lokaci kuwa Saddiqa ta tura wa Mommy 50k,zaro ido Mommy tayi tana mamakin ina yarinyar ta samu kuɗi manya haka? Cike da tunani mommy tayi bacci.
*************************
Lokacin da Billy ta farka daga baccin wahalar da ta shane ta tarar da Any zaune a gefen ta,gaban ta ƙaramin table ne an shaƙe shi da abinci da abubuwan sha kala-kala,gefe ɗaya kuma wata jaka ce ƙarama an cika ta da kuɗi bugun kasar amurka wato dollars,sai makullin mota da kwalin sabuwar wayar da ake yayi.
Dik wata masifa da bala'in da Billy ta yi niyyar sauke wa Any sai ya maƙale,sai kawai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita a jikin ta, murmushin mugunta Any tayi sannan ta rungume Billyn a jikinta tana cewa,
"Shiii yi shiru my love, ki manta da komai ki fuskanci rayuwar ki ta gaba,kowacce mace tana rasa budurcin ta ta hanya biyu zuwa uku ne, imma ta rasa shi ta hanyar zina, ko ta hanyar aure, ko kuma ta hanyar yawan aiki,to ki godewa Allah ke ta hanyar neman kuɗin da yake gumin ki ne kika rasa budurcin ki."
Wani kallo Billy tayi wa Any wanda ya sanya Any miƙewa tsaye ta zuba hannayen ta a aljihun wandon ta tace wa Billy,
"A cikin wannan harkar tamu,ke kin san mata mun kasu kashi uku ne zuwa huɗu,akwai wadda maza kawai take bi,wata mata kawai take bi, wata kuma tana haɗewa dika ukun ta bi su,a cikin wannan kason na mata wadda take bin kowanne jinsi tafi kowa samun ariziƙi,Bilkisu ki sani ban tara wannan dukiyar da kike ta sha'awa da fatan ta zamo taki ba, sai da na rasa budurci na har sau biyu kamar yanda kika yi a yanzu,dan haka ki saki jikin ki wannan ciwon da kike ji na ɗan lokaci ne, da kin saba ke da kan ki zaki na nema."
Share hawaye Billy tayi sannan ta kalli kud'in dake shaƙe da jaka ta ce,
"Wannan na wanene,"
"Naki ne my love, ya danganta da yanda kike son su, a bar maki abun ki ne a gida ko a saka maki a banki."
Murmushi Billy ta yi,sannan ta sake buɗe baki Any ta ci gaba da ciyar da ita,sai da taci ta koshi sannan Any ta taya ta wanka,suna kammalawa ta shafa mata magani a bayan ta suka koma parlour suka zauna,Youtube channel ɗin su suka shiga suna kallon comments ɗin mutane akan last video ɗin su da suka saki, comment ɗin wata musulma kuma bahaushiya ne ya ja hankalin Any,cikin fushi ta miƙe ta d'akko camera ɗin su tace wa Billy.
"Babe bari muyi video yanzu, zaki iya ko nayi ni kaɗai?"
"No kiyi ke ɗaya bana son na nuna fuska ta haka babu kwalliya."
"Alright."
Nan take Any ta saita komai ta fara videon da ya sanya Billy sakin baki da dikkan wani abu mai motsi a jikin ta tana kallon Any, a hankali ta furta,
"Wacece ke?"............
*Hummmm na gaji wallah mu haɗu a next page mutane na,i kove reading your comments,dik group ɗin da suka ga bana tura masu pages sai dai link na wattpad basu comment ne a group, sai idan ban tura ba a tambaya ta PC, shin idan kun yi comment a group wani zai hana ku ko me? Ni dai na kasa gane kan wanga lamari. To dan haka na hutar da ku jama'a ta idan na daina tura pages a group to ku bi channel d'ina ta Whatsapp ku karanta ko kuma ku duba wattpad.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️ ✨
PAGE 79:
"Da farko dai ni suna na Anam,kin san me sunan yake nufi kuwa da harshen larabci?"
Kaɗa kai Billy tayi alamar bata sani ba,domin bata yi tsammanin Any ta ji tambayar ta bama balle har ta bata amsa,murmushi Any tayi tare da ƙarasa ajiye camerar tasu a saman center table ɗin dake gaban su,sannan ta zauna a kusa da Billy ta ci gaba da bata tarihin rayuwar ta a taƙaice.
"Anam yana nufin kyauta daga Allah,ko kice kyauta kawai,iyaye na sun zaɓar min wannan sunan ne saboda jimawa da suka yi basu samu haihuwa ba,har mahaifiyata ta fitar da ran samun haihuwa saboda shekarun ta da suka ja sai Allah ya azurta ta da samun ciki na,ana haka har watarana Allah yasa ta haihu lafiya, kasancewar mahaifi na babban malami shine dalilin da yasa ya zaɓar mani suna Anam,Billy na taso cikin wani irin gata da sangarta tare da kulawar iyaye na,