Showing 111001 words to 114000 words out of 276165 words

Chapter 38 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

suka haɗu da Yah Abdul ya taimake ta daga hannun mutumin da tajewa yawon karuwanci tinda ya fi qarfin ta taga baza ta iya zama dashi ba sai ta gudu,da kuɗin karuwancin ta sai wa Ubanta adaidaita sahu ta sai wa Uwar ta injin niqa sannan take aikowa Sule yake shiga manyan suturu yake riqe babbar waya, yanzu haka da za a je gidan su a duba za a same ta da manyan kuɗi a tattare da ita, kuɗin kuwa dake shaqe a bankin ta ko Yah Abdul bana jin yana da su idan kuma qarya nake yi a bincika a gani,"

Idanun Innah Laminde ta kalla taga yanda suka kad'a suka yi jawurrrr suna zubar da hawaye,ganin ta samu nasara akan Innah Laminde sai ta zauna kusa da ita tana share mata hawaye tace,

"Yanzu ni babban tashin hankali na bai wuce ace Yah Abdul ya auri fasiqa ba ta sanya masa cutar nan ta zamani mu zo mu rasa shi, ni na hakura da shi tinda baya so na amma dan Allah kar ki bari wannan auren yayi tasiri, dan Allah Innata ki raba wannan mugun auren domin babu komai a cikin shi face cutarwa,"

Inna Laminde ce ta miqe tsaye tace,

"Ina zuwa Bilkisu kar ki je ko ina saboda hayaniyar danake jiyowa a waje ki yi zaman ki anan ki kwana gobe da safe zan sa a kira min Ta Annabi mu tattauna akan lamarin nan,"

Turakar sarki Inna Laminde ta shiga ta tadda shi zaune ya kashingid'a idanun shi a kulle,gaba ɗaya abinda ya faru yau ya zubar masa da qima da mutucin masarautar shi domin kuwa ya tabbata labari sai ya bazu zuwa wasu garuruwan, da wanne ido zai sake kallon sauran sarakunan da suke ganin qima da darajar masarautar shi? Me 'yan hassadar masaurautar shi za su yaɗa akan masarautar yanzu? Babban ɗan shi abun alfaharin shi ya auri karuwa? Da sauri ya kulle idanun shi dan jin labarin da Innah Laminde ke sanar da shi game da irin videos da hotunan da ta gani a wayar Bilkisu, cikin murya mai tsananin nuna damuwar ta tace,

"Allah ya taimake ka ka dubi girman Allah a raba wannan auren, ba zan so musamu  jikoki daga tsatson yarinyar da ta gama yawon dandi ba, ba zan so sunan masarautar nan ya ɓaci a idanun sauran masautun dake sama da qasan wannan masarauta ba,ban taɓa zaton halin yarinyar haka yake ba har na amince Abdul ɗin mu kamili ya aure ta,"

Kallon Sarki tayi taga ya sake kulle idanun shi yana taune haqoran shi,shi mutum ne da baya taɓa yanke hukunci cikin fushi ba dan komai ba saboda aiki da hadisin Annabi Muhammad da yake yin hani da fushi da yanke hukunci cikin fushin, cikin wata iriyar muryar da ta jima bata ji yayi magana a cikin taba yace mata,

"Ki je zan yi tunani akan matsalar da ta tinkaro mu,"

Buɗe baki tayi zata sake magana sai ta rufe kawai ta miqe dan ta riga da ta san halin shi idan dai ranshi ya ɓaci magana ɗaya yake yi, dan haka tana fita ta kalli Sailuba dake wanke hannu a pampo tace mata,

"Kira min yayan ku,"

Tana gama magana ta wuce d'akin ta ta shige quryar d'aki ta bar Billy zaune tana share hawayen munafurci.

Sailuba na zuwa kiran Abdussabour ta same shi a cikin wani irin mawuyacin halin da ya sanya ta fita da gudu ta nufi dakin Innah Laminde tana ihu,

"Innah ! Innah ki zo yayah ya na ta nishi da kyar a ɗakin shi,"

Cikin sauri kafin Innah Laminde ta fito daga ɗakin ta Billy ta yi ɗakin nashi da gudu, kwance ta ganshi a qasa yana murqususu yana numfashi da k'yar, d'ago shi ta hau qoqarin yi amma ta kasa, Innah Laminde ce ta shiga ɗakin taga halin da yake ciki da gudu ta koma ɗakin ta ta ɗauki waya ta kirawo Sultan,bata jima tana ringing ba ya ɗauka, cikin muryar dake bayyanar da tashin hankalin da take ciki tace,

"Sultan ka bar dik abinda kake yi kazo da mota mu kai yayan ku asibiti bashi da lafiya,"

"Gani nan zuwa ina qofar gida,"

Kashe wayar yayi ya shiga gidan cikin sauri, direct d'akin Abdussaboor suka nufa a tare da Innah Laminde dake ta salati da kiran sunayen Allah.

Koda suka shiga sun tarar da Billy na zaune a gefen Abdul tana ta kuka kamar ranta zai fita,da kyar Sultan ya iya kama Abdussaboor ya fita da shi zuwa mota, Innah Laminde ta so a tafi da ita amma tayi kawaici Ummah matar sarki ta biyu ta bi su ita da azizah.

***************************

Tinda Abdul yace wa Mommy da Innoh su wuce gida sai suka taka suka fara tafiya,basu bi su Baabaa dake ta'ajibin abinda ya faru a fada ba sai suka ratse gidan su Innoh, daga nan suka ɗauki Naja suka wuce gidan bokan su dan sanar dashi dik abinda yake faruwa.

Innoh ce ta sake muskuta manyan mazaunan ta ta kalli bokan su dake ta murmushi yana gyad'a kai tace,

"Ran bokan dik duniya ya dad'e muna godiya akan wannan babban aiki da ka yi mana, aiki naka nasara tamu, sai dai fa babban bokan duniya ina jin tsoro, ina jin tsoron abinda zai je ya zo a game da abinda ya faru na zuwan waɗannan 'yan daudu da karuwan,anya kana ganin lamarin nan ba zai lalace ba?.................."
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI


















RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨





















PAGE 43:
















"Kar ku ji komai ku dai kawai ku ajiye kuɗin aiki dubu hamsin idan kuna da shi, kafin safiya maganar nan zata zama kamar ba a taɓa yin ta ba, dik wani mai ganin aibun ki a gidan sirikan ki zai koma ganin farin ki, za su so ki, za kuma ki zauna zaman aure da ɗan su har ku hayayyafa ma,"

Cike da murna Mommy ta buɗe baki zata yi magana Innoh ta riga ta tace,

"Ran boka ya jima yayi qarko gaskiya bamu da wannan maqudan kuɗaɗen a yanzu amma..."

"Innoh kar ki damu ya bamu account No idan yana da shi zan tura masa, idan babu kuma muna zuwa gida zan bayar a bashi,"

Kallon Mommy Innoh tayi baki sake, ashe Mommy nada kuɗi a boye amma taqi bata duk irin faɗi tashin da take yi akan ta sama mata soyayyar Abdul? Ɗauke kai tayi cikin ɓacin rai tace wa boka,

"To kaji me tace,idan akwai afwun lambar se ka bata ta tura maka ko ba haka ba Naja? Masu abu da abun su kura da kallabin kitse?"

Naja ce ta gyad'a kai cikin sauri sannan tace,

"Aiko dai Yayah kin ga shikenan ma ta zo gidan sauqi,dake yanzu  kusan kowa na da wannan lambobin bankin sai kawai ta tura masa baki alekum,"

Boka be b'ata lokaci ba wajen karantowa Mommy account No ɗin shi, Mommy kuwa nan take ta lode a wayar ta, kafin su tashi a wajen ta tura masa dubu ɗari, sanda ya duba wayar shi yaga kuɗin murna ya hau yi tare da faɗin,

"Kar ku ji komai zan yi maki aiki yarinya har da wanda ma baki san da shi ba,nifa ina son mutumin da ya san darajar kan shi yanzu duniyar ai ba a zama sai da neman taimakon masana, ku tashi kuyi tafiyar ku a ci gaba da shirin biki, aure ya riga ya qullu mutuwa ce kawai zata raba shi,"

Cike da tsananin farin ciki suka tashi suka tafi, tin a hanya Innoh ta tura baki gaba ta wuce ta bar Mommy da Naja a baya ranta a matuqar haɗe ta isa gida, ko da ta shiga ta hango sashen Baabaa ba a buɗe ba sai bata kawo komai a ranta ba ta shige d'akin ta, Ameerah ta gani kwance a gado tana ta kukan baqin ciki, sai a sannan ta tuna da sanda Ameerah ta bar wajen taron cikin ihun kuka shamsu na biye da ita yana aikin lallashi,tausayin ta ne ya kama Innoh sai kawai ta qudirta a ranta dole ne ta aika Naja wajen boka ya san yanda zai yi ya raba Ameerah da soyayyar Munir amaye gurbin shi da soyayyar Shamsu, ta haka ne kawai zaman auren su zai yi daɗi a huta da tashin hankalin da Ameerah zata dinga b'allo musu a duk sanda tsiyar ta ta tashi.

Mommy da Naja sun iso gida shajaran majaran dan haka a tsakar gida suka zube, ganin Baabaa da tawagar ta basa nan ne ya sanya Naja buɗe baki tace,

"Ah ah Yayah ina wannan qarmasasshiyar tsohuwar tayi ita da ayarin ta kuma?"

Innoh ce ta fito tsakar gidan da d'aurin qirji kai ba d'ankwali ta zauna a dokin qofa ta ce,

"Ina na san inda take ni da na dawo yanzu? Naja dan Allah idan zaki wuce gida ki tuna min zan baki saqo wajen bawan Allah'n nan da ba a kama sunan shi a tsakar gida,"

Innoh na fad'ar haka Naja ta gane wa ake nufi sai suka sanya shewa, Mommy tace,

"Wai Ameerah har yanzu kuka kike yi baza kiyi hakuri ki sanya wa kan ki salama ba?"

Cikin faɗa Innoh tace,

"Taqi sanya wa kan nata salama mara mutunci,ai dama jira nake yi mu dawo gida na ci uban ki son rai na,ashe kina da waɗannan arnan kuɗin muke zaune haka ? Anya Mommy kina da tausayi kuwa? Da alama dai zuwan ki birni an sauya min ke dan kuwa a iya sani na dik cikin yaran nan kin fi kowa tausayi na, amma ace kina nan maqale da maqudan kud'ad'e ki kasa jifana da ko hamsin ɗin ce bayan a kan idon ki nake ta faɗi tashi dan kawai burin ki ya cika, maganar Ameerah dai ita ke neman zama gaskiya,ke da nake wahaltawa kece ke bani wahala,"

"Haba Innoh,yaushe ma hankali na ya kwanta balle har na hau baki kuɗi? Yanzu da amfanin su yazo ba gashi ana morar su ba? Ki kwantar da hankalin ki Sule ya dawo na bashi ya ciro wani abun sai na baki ke da Aunty Naja,"

Naja na jin maganar kuɗi ta ce,

"Habaa Innoh me yasa kike da gajen hakuri ne uhumm? Ai shi ɗan yau lallab'a shi ake yi ba wai ki kama yi mata faɗa irin haka ba, to yanzu dai ba wannan ba, tashi zaku yi na gyara maku jiki da abubuwan mu na amfanin yau da kullum tinda abubuwan sun zo a qurarren lokaci bamu samu damar yi muku gyaran amare ba,Yayah maza samo min waɗannan abubuwan a haɗa a gyara amare dasu,"

Lalle
Ganyen magarya
Farar shinkafa
Kurkur
Gishiri
Ruwan tsamiya/lemon tsami
Manja

Innoh ce ta miqe da kyar ta shiga d'aki tana ci gaba da mita akan yanda Mommy ke maqale kuɗi bayan ta san tana da buqatar su, dan wa take faɗi tashin idan ba su ba? Ita dai Mommy hakuri ta dinga bata da alqawarin bata dubu ɗari cash ita kuwa Naja tayi mata alqawarin dubu hamsin ita da Ameerah, Ameerah kuwa jin za a bata maqudan kuɗi masu yawa haka ne ya sanya ta fitowa tsakar gidan tana tura baki ta zauna dan ayi gyaran jikin har da ita.

Bayan an kawo wa Naja waɗannan abubuwan data nema ne ta miqe ta hade shinkafa, ganyen lalle, ganyen magarya,da kurkur ta sa a injin niqan Innoh ta niqe su tasss sai da suka yi laushi sosai sannan ta karb'i ruwan tsamiyar da ta sa Mommy jiqawa ta tace akan garin shinkafar nan ta zuba gishiri kaɗan,qaramar jarkar manja ta ɗauka ta karkata ta d'ebi marfi uku ta zuba sannan ta saka hannun ta ta juya sosai ta ajiye a gefe tace,

"To Yayah fa se kin yi hakuri dan kuwa dole ki bamu kaji biyu a kajin nan naki da bakya ci bakya sadaka da su mu yi amfani dasu,"

Wata harara Innoh ta makawa Naja sannan tace,

"Haka kawai sai in bada kajin da na sha wahalar kula da su suka yi girma haka babu ko sisi?"

"Innoh kiyi wa Kajin naki kuɗi zan siya,"

"Yanzu naji magana, gasu nan a bani dubu bakwai-bakwai idan an siya a haka a ɗauka idan ba a siya ba a aje min abuna babu shegen da ya taya ni watsa musu hatsi acikin ku ah toh,"

Babu b'ata lokaci Naja ta kame kaji ta yanka ta kira Mommy tace ta fige, cike da kyankyamin kajin Mommy ta toshe hanci tana kallon Ameerah bata ce komai ba,cikin zabgawa Mommy harara Ameerah tace,

"Kike wani kallo na dan kin siyi kajin wato ni se in fige ko? To kar Allah yasa a ci kajin a bar su, ke fa na kula wani jin kan ki kike yi kamar wadda tayi tashin turai ba qauyen Ba mugu ba, dika-dika watan ki nawa a birnin? Ko fa shekara baki yi ba rayuwar ki kaf a qauyen nan kika yi ta amma da an yi magana ki dinga maida mutane kidahumai, mtswww aikin banza kawai,"

Qarshe dai da Naja taga abun zai zama rikici ita ta zauna ta fige kajin ta daka kayan qamshi da attaruhu ta zuba daddawa sosai ta hura wuta ta dora su dan yin farfesu tinda lokaci ya qure da za su bazama neman kayan mata na musamman.

Suna ji ana kiran Sallahr la'asar amma dik cikin su babu wadda ta motsa dan yin sallar sai ma d'akko wannan haɗin farar shinkafar da Naja tayi ta sa su Mommy su tub'e ta gyara su, babu b'ata lokaci kuwa suka d'aura zani mommy ta ja under skirt ɗin ta zuwa qirjin ta Naja ta zauna ta murje su da wannan haɗin na shinkafar.

Shiru Mommy tayi tana tunano sanda tana gidan Hajiya K'waisa irin gyaran da ta dinga sha kamar wata sarauniya, k'wallar baqin cikin abubuwan da suka faru da ita a baya ne ta sirnano mata, cikin zuciyar ta take ayyana,

'Ko ya ake ciki a gidan su Yah Abdul yanzu? Anya Billy zata kyale ni na yi rayuwar aure cikin farin ciki kuwa? Bari na gama na kirawo Yah Abdul naji ya ake ciki dan naji shi shiru bai kira ni ba,'

Ameerah ta kalla taga yanda ta jingina kanta a jikin gini ta rintse idanun ta hawaye na zuba daga idanun nata dik da a kulle suke, tausayin tane ya kama mommy cikin sanyin murya ta dafa Ameerah tace,

"Ameerah kiyi hakuri da qaddarar data same ki, ina faɗa maki haka ne saboda ina son ki kuma na san ko auren ki Munir yayi ba zai kula dake da kalar soyayyar da kike yi masa ba sai dai ma ya wulaqanta ki,ni kaina badan wannan abin da aka yi wa Yah Abdul ba dan ya so ni na tabbata wahala zan sha a gidan shi bayan auren dik da cewar yana so na tin kafin mu dawo, amma kin ga shamsu na son ki sosai zaki murza kambun ki a gidan su, sai fa yanda kika yi dashi,ke ce zaki sama sitiyarin saita rayuwar shi sai abinda kika ce shi zai yi, ke yanzu dan Allah hakan bai fiye maki auren wanda zaki sha wahala a hannun shi ba?"

Cikin sharce majinar dake shatata a hancin ta Ameerah tayi murmushi mai ciwo tace,

"Humm Mommy kenan, ai yanzu aikin gama ya gama kawai ba yanda zan yi dole na karb'i qaddara ta, amma ni na tabbata dan bani da kuɗin da kike da shi ne yasa Innoh ke nuna mana banbanci, da ace nima ina da irin kuɗin ki ta san zata fanshe su ko ba jima ko ba dad'e nima da ta shiga ta fita na auri zaɓin raina, ke yanzu ba gaki kin samu farin cikin ranki ba?"

"Ameerah ba zaki..."

"Dan Allah Mommy mu bar wannan Maganar kawai, kema kin san gaskiya na faɗa,Allah ya bamu zaman lafiya kawai shine abinda zan ce,"

Cikin sanyin jiki Mommy tace,

"Ameeen,"

Ta ja bakin ta ta tsuke,suna nan zaune Mommy ta ja Naja zuwa d'akin Yadiko ta qirga kuɗi dubu ashirin ta bata tace ta je ta samo mata maganin mata mai kyau a islamic chemist din cikin kasuwar dare ta garin nasu, Naja ta sha mamakin lamarin nan sosai, ita kuwa Mommy ta riga ta saba da shan irin kayayyakin nan a wajen su Hajiya K'waisa kafin taje ta haɗu da maza,dan haka ta san darajar su,sune suke yi mata kallon ta Allah amma abinda ta sani a iya watannin nan su basu san shi ba.



****************************


Da misalin tara na dare Sultan ya tafi bakin tasha d'akko Bilal da ya iso daga Bauchi, dan kuwa tin bayan d'aurin auren Mommy da Abdussaboor Sultan ya sanar dashi komai ta waya anan take Bilal ya sanar dashi cewar dama ko bai sanar dashi maganar auren ba dole zai zo saboda abinda aka tura masa a wayar shi ya munana,direct asibitin da aka kwantar da Abdul suka je, zaune suka tadda shi yana shan lemo da ayaba Innah Laminde na ta jera masa sannu, ji take yi kamar ta zare masa ciwon ta mayar jikin ta, bayan sun gaisa da Bilal da jajanta abinda ya faru dan kuwa ba murna suke yi da wannan auren ba balle su taya juna murna, sai Innah Laminde ta kalli Abdul tace,

"Allah dai ya baka lafiya SARAUTA, ka kula da kan ka sosai dan Allah, ka dai ji me likita yace d'azu da ya zo,likita yace da alama ka shiga rud'ani ne na ji ko ganin wani abun da ya tada hankalin kane har yayi sanadiyyar da jinin ka ya hau kaɗan,se kuma ciwon dake kama mutum idan ya cika zirga-zirga, (stress) ita zirga-zirgar dama har ciwon ta ake yi Bilal, gaskiya baturen mutum sai dai a bar shi, Allah kuma ya baiwa mutanen qauye hakuri,mu nan mutum idan ya tashi tun safe ba sai ya wuni a tsaye ba yana lodar aiki be huta ba?"

Murmushi kaɗan Abdul yayi cikin muryar shi mai cike da natsuwa yace mata,

"Innah ai dole ciwo ya kama ni, ki duba fa ki ga hutu na zo yi amma abubuwa duk sun rincab'e min daga wannan sai wancan, na kasa samun hutun da nake so zuciya ta da gangar jiki na ta gaji Innah,gashi matar da nake so kuma ana so a raba ni da ita ko ta halin qaqa kin ga kuwa ai dole na kamu da ciwo,"

Hoton Mommy ne tsirara ya gilma a idanun Innah Laminde, nan take ta rintse idanun ta tana jin wata iriyar tsana da qin Mommy a cikin ranta,cikin haɗe fuska


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login