Showing 42001 words to 45000 words out of 276165 words
Chapter 15 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ba.
"Ya salam kula kar ki faɗi,"
"Waye kai ka shigar mana bayi? Innoh Yadiko ku zo ku ga wani ya shigo mana gida"
Baabaa ce ta zo ta ga abinda ke faruwa cike da washe baki tace,
"Ke Yayan ku ne na Habuja da na ce maki zai zo tun kwanakin baya, ai shine ya zo"
Da sauri Saddiqa ta sake kallon shi da kyau, a sannan ne ta gano kamannin da yake yi da Baabaa, cikin jin kunya ta durqusa ta ɗauki butar da ta faɗi ta mayar gefe ta gudu d'akin su na 'Yanmata, Ameerah ta tarar a kwance ta na ta bacci wanda da dikkan alamu ta jima tana yin baccin babu wanda ya d'aga ta,labulen windown d'akin su ta d'aga dan kuwa kyawun Munir ya burge ta, ta na so ta sake yin ido huɗu da sumar kan shi, ta na buɗewa ta leqa a hankali idanun su ya sarqe a cikin na junan su, murmushi ya sakar mata mai kyau, ita kuwa nan take ta saki labulen ta maqale a jikin ginin d'akin ta na qanqame jikin ta tare da sakin murmushin da bata san tana yi bama, a hargitse cikin hargowa da hayagaga Ameerah ta farka ta na faɗin,
"Wanne ɗan iskan ne ya taka min hannu? Ke Saddiqa uban wa yace ki taka ni ko baki da ido ne?"
Da sauri Saddiqa ta matsa ta na zaro ido dan bata ma san ta taka Ameerah ba,
"Dan Allah Yah Ameerah ki yi hakuri ban san na taka ki ba"
"Sannu balama, ina hankalin ki yake har da zaki taka ni amma kice baki sani ba? Dalla malama matsa ni na wuce"
Tashi Ameerah tayi ta fita tsakar gida ta tsartar da yawu sannan ta yi miqa tare da zabga wani ihu a cikin miqar tata ba Kiran sunan Allah babu komai ta nufi d'akin Innoh dan kuwa yunwa take ji.
Munir da ya koma d'akin Baabaa duk ya ga abubuwan da Ameerah ta yi kafin ta shige d'akin Innoh, cikin magana kamar ta me rad'a yace,
"Ikon Allah, lallai gidan granny ya haɗa mutane kala-kala,Allah yasa na gama ganin mutanen gidan kenan kar daga baya kuma na ci karo da me haqoran zarto"
Cike da dariya Sadeeq da baya magana sosai yace,
"Ai bata nan ta na can birni aikatau ba lallai ku haɗu ba ma,"
"Kana nufin akwai me haqoran zarto a gidan nan?"
"K'warai da gaske Yah Mommy kenan,ta na can kano aikatau ai bata jima da tafiya ba ka zo dan bana jin ta cika sati yanzu da tafiya"
"Allah me iko, to ita waccan beautyn da na gani da uniform fa?"
"Yah Saddeqa kenan,"
"Hummm, tashi muje ka raka ni can gidan na dan watsa ruwa kafin a yi magariba dan na ga lokaci ya kusa,"
Sallama Baabaa ta yi ta shiga ta ajiye masa fura da nono da ya sha damun hannu sannan tace,
"Ga fura fa ko zaka ɗora ka danne abincin da ka ci da ita"
Zaro ido waje Munir ya yi sannan yace,
"What ? No alhamdulillahi na qoshi gaskiya ina ki ke so na zuba ta?"
"A cikin ka mana, ku fa mutanen birni baku son cin abinci shi yasa gaka nan kamar a hure ka ka faɗi,"
"Kar dai ki zagi qaramin jiki na dan kuwa ke na gado,kema da kike ci da yawa baki wuce ni ba ai, gwanda ma ni na fi ki qiba, ba wannan ba ma na ce ina keys ɗin gidan can suke zan je na watsa ruwa"
"Ina me?Kai ni idan zaka yi min yaren da na sani kayi, idan ba zaka yi ba mu sha zaman kurame dani da kai ah toh"
"Yi hakuri Granny ki bani makullin gida zan je na yi wanka an kusa Kiran sallah"
"Yanzu na ji magana,gasu nan, amma ka jira Saddeqa ta sake share maka waje dan tun sanda baban ka yace zaka zo na sa aka share ba a sake bud'ewa ba, Saddeqa ! Saddeqa ke !"
"Na'am !"
"Zo taho da shijabin ki ki share gidan Baban gida yaron nan ya samu ya je ya huta an shawo hanya"
Ameerah ce ta fito tana sud'e hannun ta, Munir ya fito shi da Sadeeq daga d'akin Baabaa, tsayawa ta yi hannu a baki tana kallon Munir ɗin da Innoh ta gama gargad'in su akan kar ta kurkura ko da wasa taga ɗayan su ya kula shi,kallo ɗaya Munir ya yi mata ya wuce ta ya miqa wa Saddeqa keys ɗin gidan, a kunyace ta Karb'a saboda ta kula da kallon da Munir ɗin ke bin ta da shi, har zata fita Munir ya kirawo sunan ta ta tsaya cak, a hankali ya taka wajen ta yace,
"Mu je na ajiye ki a gidan ko? Tunda nima can ɗin zan je, Sadeeq taho ka raka mu ko?"
Suna fita waje Ameerah ta koma d'akin Innoh tace,
"Ke da wancan balaraben kike ta zagi kina d'ebewa albarka kike cewa kar mu kula shi? To alqur'ani ni dai na yi mijin aure anan, ko za a kahye ni ba zan qi kula hyi ba ni hyi zan aure,"
Cikin Fushi Innoh ta ce,
"Ai kuwa se dai ki mutun dan kuwa in dai ina numfashi ba zaki aure shi ba shegiya matsiyaciya, mutanen da ba qaunar mu suke yi ba shine kike so ki jawo min matsala, ki dube ni ki ga yanda kakar shi taso sabauta min baya Allah ya taqaita wahala shine kike maganar kina son jikan ta? To sai dai kuwa ki mutu,"
Cike da rashin kunya da qunquni Ameerah ta bar d'akin ta wuce nasu ta kwanta tana rusa kuka tare da cin alwashin duk rintsi duk wuya sai ta ja ra'ayin Munir ya fara son ta har ma ya aure ta.
************************
A cikin kwanakin da Mommy tayi Billy bata nan duk sai ta ji gidan ya yi mata girma, Hajiya K'waisa na yawan fita bata da lokacin zama a gida sai tsakiyar dare ake dawo da ita watarana,haka zata dawo da damman kuɗi ta shige d'akin ta tana rawa tana shewa,dan haka daga ita sai masu aiki da masu koya mata kwalliya da tafiya,magana da dai duk wani abu da ya kamata ace ta iya.
Lokuta da dama cikin dare idan ta fito zata tarar ana tsarawa Hajiya k'waisa kwalliya ta garari, ana gamawa za a ɗauke ta hotuna masu kyau ta ɗora a shafukan ta na internet sannan ta yi vidoes nan ma ta yi posting, watarana sai daf ana kiran sallar asuba zata gama abubuwan da take yi ta kashe wi-fi a goge mata kwalliyar ta ta wuce sama, Allah ne masani tana sallah bata sallah take kwantawa bacci sanin gaibu sai Allah.
Kwanan Mommy takwass cif a gidan da dare ta fito daga d'akin ta kamar koda yaushe dan ganin yanda Hajiya K'waisa ke gabatar da lamuran ta cikin dare ta ji Hajiyan na waya da wani wanda bata san ko wanene ba, cikin rausaya da fari kamar wani mace yake faɗin,
"Eh gaskiya she is not ready yet, dan kuwa wannan kifin ba a kowanne ruwa yake rayuwa ba, ka jira idan aka gama bikin new year wataqila ka samu shiga,"
Hajiya K'waisa ta jima ta na sauraron me ake faɗa daga ɗaya bangaren kafin ta tashi zaune da ga kishingid'ar da ta yi ta yarfa hannun ta ɗaya sannan ta mayar ta kama hab'a tace,
"Da gaske zaka iya bata waɗannan maqudan kud'ad'en a lokaci ɗaya? To indai haka ne babu damuwa sai ta fara da kai, kaine first customer ɗin ta kenan, amma kasan ni yarana fa ba kamar saura suke ba, pay before service ne su,ka yarda zaka tura kuɗin ne yanzu ko kuwa?"
Shiru ta sake yi na wasu daqiqu kafin tace,
"An gama na waje na, Heeeee ragassss ! Ni fa shi yasa kake burge ni dan baka wasa, duka d'auka ne kai, Allah dai ya biya na waje na masu kashe kuɗi a sab'on Allah a jefa kaɗan a aikin Allah"
Mommy na jin wannan hirar ta tabbata akan ta ake yin wannan maganar, cikin sand'a kamar yanda ta saba lab'ewa ta kalli Hajiya k'waisa ta koma d'akin ta yau ma haka ta yi, tana shiga d'akin ta maida qofar ta a hankali ta rufe ta na maida numfashi,kallon kanta ta yi a madubin dake gaban ta ta juya jikin ta ta sake, bakin ta da ya sha man leb'e ta kalla taga yanda yake sheqi idanun nan sun sha eyelashes, ga uban gashin doki an saka babu mai cewa ba nata bane saboda yanda ya mannu da kan ta, shape ɗin ta mai kyau cikakke ta kalla ta ga yanda qirjin ta ya sake cika saboda supplements ɗin da ake bata tana sha na gyaran fata da jiki.
"Ohh ni Mommy yanzu da gaske harkar karuwanci zan faɗa tsundum? Ko nawa bawan Allahn nan zai biya akai na kuma oho? To ko dai shine wanda yake ta yi min naci a TikTok d'ina ne?"
Da sauri ta nufi wayar ta ta kunna ta shiga TikTok ɗin ta, Dm ɗin ta ta duba, da messages ɗin mutumin da ya nace mata ta fara cin karo kamar haka.
*Sweet H da alama ni ne na yi nasarar samun ki a matsayin wadda zata taya ni yin hutun weekend*
Sai stickers na banza da ya tura mata kala kala wanda ya sanya ta shiga wani yanayi na tsananin buqatuwa da abinda ya nuna matan, cikin rawar hannu ta shiga wajen yin reply ta danna masa heart ta tura sannan ta kashe wayar ta gaba ɗaya ta faɗa gado tana murna, dan kuwa tayi kewar shamsu sosai tunda tazo sai dai ta ga kowa na jin daɗin shi amma banda ita,ita ko ba za a bata sisi ba kawai ta samu biyan buqatar ta ya wadatar, da wannan tunanin Mommy ta kwanta bacci.
Washegari tun da asuba Hajiya K'waisa ta aika Ruby kiran ta wanda hakan ba qaramin mamaki ya bata ba............
*To nima dai na yi mamaki mutumin da baya tashi domin sallar asuba ya doka wannan uban sammako haka?*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 16:
Saida mommy ta yi sallar asuba sannan ta nufi hanyar d'akin da Hajiya k'waisa ke jiranta, ta na shiga ta ga Hajiyan kashingid'e a saman wata royal chair mai hannu ɗaya,ta na sanye da wata had'ad'd'iyar kimono a jikin ta, kanta d'aure da ƙaramin towel kalar kimono ɗin jikin nata, gefe ɗaya Zubaida ce duƙe a saitin ƙafafunta ta na matsa mata su, cikin isa da izza ta miqa hannu ta ɗauki Apple juice ɗin da Ruby ta kai mata, ganin Mommy na shiga d'akin ne ya sanya ta ɗauke kai tare da jan guntun tsaki yace,
"Ai da yanzu nake so na sake aika Sallau ya gano min me kike yi a d'akin da ba za ki zo dan amsa kira na ba,"
"Ki gafarce ni Hajiya, ai na yi zaton tashi na aka yi dan gabatar da sallar asuba shi yasa na yi sallar, ina idarwa Ruby tace min ni kaɗai kike jira shi yasa na zo nan ɗin yanzu"
Kallon Ruby Hajiya K'waisa ta yi, sai yanzu ta gane dalilin jimawar ta ashe sai da ta sake bi ta wajen Mommy ta kirawo ta, fari ya yi da idanun sa sannan ya kur'bi juice ɗin ya mayar kan side table ɗin dake wajen sannan ya tattare rigar shi ya miqe tsaye yana rangwad'a, kallon su Sallau ya yi da Zubaida da ke tsugunne har a wannan lokacin tana jiran Umarnin Hajiyan, tafa hannayen sa ya yi sau uku sannan yace,
"To Zuby, Ruby da Sallau a bamu waje ko?"
"An gama Hajiya"
A tare suka bar wawakeken dressing room ɗin suka bar Mommy da ke jin d'akin ya yi musu kaɗan tsabar yanda take jin ta a takure, kallon Mommy Hajiya k'waisa ta tsaya yi daga sama har qasa, sannan tace,
"To alhamdulillahi komai ya ji baki da matsala a iya inda idanuna suka kalla, amma duk da haka crue ɗin dake yi min gyara na musamman a lokacin da nake da fita ta musamman kamar dai wadda zaki yi a yau za su zo su gyara min ke ciki da waje, za kuma su baki kayan gyara na mata wanda zaki sha ki maida quruciyar ki dan na riga na ji labarin kema 'yar hannu ce,"
Mommy na jin maganar Hajiya k'waisa ta qarshe ta buɗe baki tare da dafe qirji, Hajiyan ma baya ta ja ta yarfa hannu tare da mere baki tace,
"Meye zaki wani buɗe baki kina kallo na kamar na yi miki sharri ko qarya ne ba a gama rabawa gayun qauye ba kafin ki zo nan?"
"Hajiya duk wanda ya faɗa miki haka gaskiya yayi min qarya saboda ni saurayi na ɗaya ne kuma bamu taba yin....uhummm...bamu taba..."
"Dakata min ke ! An faɗa maki dole sai namiji ya kwanta da mace ne budurci ke guduwa? Shi fa budurcin nan ba wani nama bane mai kauri, bashi da k'warin da za ai ta fitar da ruwan jiki kuma ace ba zai tab'u ba, idan har zaki zauna ki yi wasa da jikin ki buqatar ki ta biya to ki sani tabbas budurcin ki yana cikin hatsari, haka zalika idan har zaki na barin namiji ya yi wasanni da ke to tabbas kina taɓa budurcin ki ne, dan haka dole ne a ɗauki matakin gyara dan ba zaki je ki sa naji kunya ba ah toh, bawan Allahn nan kuɗi ya bada wuri na dukan wuri kimanin miliyan biyar akan ki ke kaɗai, babu qaramar karuwar da ta zauna a waje na ta yi darajar ki a fitar farko, dan haka ina so ki gyara jikin ki da kud'in, gyara mai kyau ma kuwa, ke koda dika kud'in ki ka kashe a gyara ba laifi bane saboda gaba zaki samu fiye da haka, mu a bariki kud'in mu wajen gyaran jikin mu suke tafiya kin gane?"
"Na gane Hajiya, amma wanne mutumi ne wannan kike magana akai"
"Heeeee ragassss ! Keee yarinya gyara kimtsi mana da fa hajiyar karuwai manyan asshoshi kike magana, ko a zaton ki ban san kina yi min lab'e ba kina ji da ganin duk abinda nake yi a gidan nan?"
Wata iriyar fad'uwa gaban Mommy ya yi, da sauri ta sunkuyar da kan ta qasa ta hau kame-kame da bada hakuri,
"Ki yi haƙuri Hajiya....rashin Billy ne ya sa gidan yi min girma shi yasa nake fitowa, amma inshaa Allahu ba zan sake ba,"
"Be dame ni ba, shi yasa ki ka ga ai ban taɓa kula ki ba, anyways mu koma kan maganar mu, wannan bawan Allahn dai da kuka yi magana ta TikTok shine yake gayyatar ki zuwa resort ɗin shi sabo daya buɗe yana so ya yi weekend da sabon jini,dan haka dan Allah kar ki bani kunya, ki saki jiki ki ci arziqi ki bar arziqi a mazaunin sa, idan ya ji dai-dai ma wataqila ya qara kuɗi kin ga kema daga nan zaki faso gari ko?"
"Hakane Hajiya ina godiya da d'awainiya dani da kike yi,"
Kallon Mommy Hajiya k'waisa ta yi tana murmushi, yarinyar na burge ta da yawan godiya fatan ta Allah ya sa Mommy ta ɗore da biyayya ta kuma zama me riqon amana.
Qarfe tara na safe dai-dai kamfanin da ke zuwa har gida su yi wa Hajiya K'waisa gyara na musamman suka iso, nan take suka hau sama suka shiga dressing room ɗin Hajiya K'waisan, anan suka tadda su suka kwashi gaisuwa dan kuwa sun san shegen son girma irin na ɗan daudun ko dan ya sallame su da kyau dole su saki jiki suma su girmama shi kamar yanda yake so.
Nan take suka bawa Mommy housecoat mai santsi ta saka suka hau mulke mata jiki da kayan gyara kala-kala na zamani,ɗaya daga cikin su ta shiga bathroom ta haɗa ruwan wankan da ya ji kayayyakin gyara da turarukan qamshi kala-kala da flower.
Hajiya K'waisa na zaune tana latse-latse a laptop ɗin ta tana kora juice, Zubaida ce ta shiga wajen da kayan motsa baki ta ajiye, kafin ta fita Hajiya ta kalli ɗaya daga cikin matan tace,
"Ki bi ta kuje kitchen ɗin duk abinda ya dace a dafa mata a dafa a kawo nan taci na ci ta sha na sha dika anan a gabana ina kallo, ba maganar ba daɗi ko da d'aci,"
"To Hajiya, balle ma yanzu kayan namu duk an sake inganta su babu masu bauri a ciki,dik suna da daɗin su"
"Whatever"
Hajiya k'waisa tace tare da yin fari ta ci gaba da danna laptop ɗin ta, a tare ma'aikaciyar suka fita zuwa kitchen da Zubaida, nan ta shiga dafa kaza da sauran tarkacen magungunan mata, ta sa aka haɗa juice kala-kala duk na gyaran jiki ciki da waje tace a kai mata sama gata nan zuwa da sauran.
Sanda Mommy taga kazar nan guda wai kuma ita ɗaya zata cinye, sai wani farin ciki ya kama ta, ga wata jahilar yunwa dama tana ji, nan da nan kuwa ta zauna ta gyara zama ta hau cin kazar nan da sauran kayan madara da juices kala-kala da aka kai mata,tun tana ci ba mai kallon ta har sai da ta ja hankalin Hajiya k'waisa,ya kuwa buɗe baki yana yi mata kallo cike da harara, da ya gaji da kallon yanda mommy ke cin abinci ba aji ya daka mata tsawar da ta firgita ta yace,
"Ke ! Meye haka kike yi kina wani cin abinci se kace balama? Kin gan ki kuwa? A haka ne ki ke so ki zama wata a cikin wannan sana'ar tamu da ke yaye mata masu aji da k'walisa? To bari kiji ba inda zaki je ki kai labari in dai haka zaki dinga cin abinci hayam hayam,mu a sana'ar mu ana so mace ta zama mai aji, mai natsuwa da iya takun ta, ana son mace mai taqama da k'walisa, ana son mace mai juriya mara gazawa wajen biya wa customers buqatun su,ana son mace da bata da rawar kai, mai iya shagwab'a da lank'wasa jikin ta duk inda aka lauya ta,ana son mace wadda ta iya kallo ta iya sarrafa kallon ta, ana son macen da ta iya sarrafa bakin ta ta hanyoyi da dama, shi yasa na faɗa maki bakin ki kadarar ki ce, dan haka ki natsu dan Allah kar ki firgita shi yaga kina gatsa kaza irin haka ya tsorata, ina dalili irin wannan kaftu da kike