Showing 57001 words to 60000 words out of 276165 words
Chapter 20 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ta a wata duniyar ta daban,sannan abu na gaba murna da farin cikin alqawarin samun damar ci gaba da karatun ta da ta yi.
Bayan sati daya da kwana biyu da rasuwar Yadiko, Sadeeq da Saddeqa sun saki jikin su sun koma makaranta suna ci gaba da karatun su lafiya,sai dai abu ɗaya ne yanzu ke tsananin damun su, wannan abun kuwa shine yanda Ɗan liti ya koma sam be damu da rayuwar su a gidan ba, sai dai ya dinga bin su da ido da baki, baya ce musu ta tafasa balle yace ku sauke,ko gaishe shi suka yi baya amsawa kuma baya d'aure musu fuska.
Innoh kuwa banda mulkin kama karya ba abinda take yi a gidan, a duk sanda ta ga dama take zuba wa su Saddeqan abinci, sanda bata ga dama ba sai ta ce idan tana so ta ci abinci sai idan an tashi a boko ta dawo kafin lokacin Islamiyyah ya yi ta yi girkin dare idan yaso ta koma,ranar da Saddeqa ta yi gangancin dawowa girkin dare dan ita da qanin ta su samu abincin dare a gidan ubanta kafin ta koma har anyi qarin karatu babu ita, gashi ana son a haɗa saukar su da bikin gama secondary ɗin su lokaci ɗaya, Baabaa ta yi kuka, ta tada aljanun ta yi borin amma babu abinda ya sauya.
Hasali ma duk sanda Innoh ta k'yalla ido ta ga Baabaa ta ba wa su Saddeqan abinci to ranar sun shiga uku, dan kuwa haɗe su zata yi a d'aki ta yi ta jibga har sai sun yi da sun sanin karb'ar abincin da suka yi, Munir kuwa ya sha yunqurin cewa zai haɗa ta da human right a k'watar wa yaran haqqin su Baabaa ke hanawa watarana ma cemasa tai,
"Babu wanda wahalar kishiyar uwa ta kashe Manniru, idan kuwa ka ga mutum ya mutu to lokacin shi ne ya yi, fata na da roqo na shine Allah ya nuna min ranar da alhakin marayun nan zai bibiyi Innoh,"
Baqin cikin hakan ne ya sanya shi yi musu sallama ya tafi Abuja, ranar da zai tafi kuwa Sadeeqa ta sha kuka dan kuwa har ta raka shi bakin mota ya kasa furta mata kalmar da take ta fata da son ya furta mata, shi kan shi daurewa kawai yake yi, ya so k'warai ya bayyana mata sirrin zuciyar shi, amma sai ya ga kamar idan yayi hakan zai hana ta cika burin ta saboda yawan tunani da tsarabe-tsaraben da hakan ke tafe da shi,kuɗi ya bata yace ta b'oye ta dinga siyan abinda suke da buqata a b'oye,sannan duk abinda bata da shi ta tambayi Baabaa, zai dinga kiran ta ta wayar Baabaa suna gaisawa, haka Munir ya tafi Sadeeq na kuka Saddeqa na yi babu mai lallashin wani a cikin su.
Tin daga ranar azabar Innoh ta ninku akan su, gashi Saddeqa na tsoron taɓa kud'in da Munir ya bata,saboda bata son Innoh ta gano ta shiga bala'i, dan haka sai kawai ta bankad'e katifar Yadiko ta ajiye su ta manta da su.
Sule ne kawai ke ɗan yin faɗa idan yaga ana yi musu mugunta, watarana su ci sa'a idan ya shigo da 'yan canji a kyale su, watarana kuma idan baida ko sisi ta haɗe su duk ta cinye musu mutunci.
Wata ɗaya kenan cif da tafiyar Mommy Innoh bata ji daga gare ta ba, dan kuwa Sule ko a social media ya dena ganin ta, duk yanda suka so su haɗu da ita ta waya abun ya gagara, idan sun kira wayar Billy sai tace musu gidan aikin su ba ɗaya bane basu tare amma idan sun haɗu zata sanar da ita ta nemi mutanen gida.
Hankalin Innoh ya fara tashi sosai da rashin ji daga Mommy, musamman yanzu da take buqatar kud'ad'en da za a kai wajen boka a qara kame mata Ɗan liti da kyau ya zama sai yanda ta yi da shi.
*********************
A can kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa kuwa a gidan Hajiya K'waisa wato K'waisan Alheri.....................[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH
PAGE 21:
"Billy na shiga uku Number bawan Allahn nan bata tafiya, ita kan ta 'yar iskar yarinyar ta kashe wayar ta ba a samun ta, daga taje ta yi weekend shikenan sai ta b'ata shiru kamar an aiki bawa garin su?"
Murmushi Billy ta yi cikin ran ta tana fatan ace wani mugun abun ne ma ya samu Mommy kar ta dawo, dan tinda take harkar nan babu wanda ya taɓa bada million uku nan take akan ta balle wuri na gugar wuri har millon biyar se dai a ba wa sauran yaran da suka yi zama tare, kafin ta haɗa million biyar sai ta sha yawo wajen qatti da mata,duk qarya take zubawa mommy dama akan samun kuɗin da take yi dan ta aminta da harkar sosai, se gashi ya tabbata ta shiga da qafar dama bugu ɗaya ta samu million biyar zuwait, cikin yaqe tace,
"Hajiyata don't stress yourself out akan wannan lamarin, ke fa ki ka faɗa min bama kamfanin ki na gyaran jiki kika kirawo aka yi mata gyara ba, kamfanin uwar Daba ki ka kirawo, matar da a kullum itace madubin ki kamar yanda kike madubi na, kin kuwa san ta sha gyara dole Alhajin ya riqe ta,"
"Kuma da wannan ma fa, to amma me yasa ba za su bar waya a kunne ba idan an kira a same su? "
"Kar ki damu, yanzu se ki fara quraje a fuska ki b'ata skin ɗin ki,"
Wata qara me cike da yanga Hajiya K'waisa ta saki sannan ya hau shafa fuskar shi ya na wani karairaya yace,
"Hakane kuma fa, bari na kwantar da hankali na shi ɗan bariki duk inda yaje dole gida zai dawo tinda shi ya sa kan shi a harkar,amma kuwa duk sanda mutumin nan ya dawo da ita se na ɗauke duk wani nauyin shi da nake ji na cinye masa guntun mutuncin shi da ya rage a ido na, sannan kuma dole ya qara kuɗi akan wanda ya bayar dan ba qaramar mace na aika masa ba, yarinya full option double engine? Ke baki ga yanda ta haɗu bane Billy na san da kin ganta sai aljanun kan ki sun tashi kin ja yarinyar mutane d'aki, hahaiiiii ragassss, zo zo na nuna miki hotunan da sa a yi mata ba tare da ta ma sani ba,"
Nan take wani irin qunci ya qara kama Billy, da dikkan alamu dai Mommy na neman kwace mata fada a wajen K'waisa,in kuwa haka ne lallai mommy ta zama 'yar yankan baya, kwana nawa ta yi da tafiyar har ta samu wajen zama a gun Hajiya K'waisa? Jiki babu k'wari ta matsa kusa da Hajiyan shi kuwa ya hau nuna mata hotunan Mommy har waɗanda aka yi mata tana cikin kwamin wanka ba tare da ta sani ba, da shi Hajiyan ke so ta yi amfani wajen yaudaro babban ɗan siyasan da take so ta haɗa ta da shi, wajen kuwa da ake shafa mata mai a jikin ta babu kaya video ta sa aka yi mata, wani yawu Billy ta had'iya dan ganin yanda Mommy ta kere ta a komai da komai,nan take zufa ta fara karyo mata na wani mixed emotions da take ji game da videon, hassada, baqin ciki, kwad'ayi da so da qaunar kasancewa da mommy, sannan uwa uba k'yashi da jin dama ita ce ke da jiki irin na mommyn.
Kallon ta Hajiya K'waisa tayi taga yanda Billy ta gigice, dariyar mugunta ya saki har da buga qafa sannan ya daki kafad'ar Billy yace,
"Wani kaya sai amale, ramin kura kuwa sai 'ya'yanta, wannan ita ake kira da cib'iri nannagi babban kaya,ba abinda zan ce miki sai godiya,kar kuma ki damu babu mai k'wace matsayin ki a waje na har abada, ke fa 'yar amana ta ce,kin manta faɗi tashin da muka yi tare? Kin manta irin taimakon da kema kika bani a rayuwa? Ai ba zan taɓa juya miki baya ba,kar ki ji komai wai mace ta mari mijin ta, tace kar ka ji komai duk a cikin so ne,"
Nan da nan Billy ta ji zuciyar ta ta wanke da kaso mafi tsoka daga baqin cikin dake addabar zuciyar ta, sannan ta wani bangaren ta cika fal da mamakin yanda aka yi wannan karon Hajiyar ta gano yanda take hassada da Mommy, kafad'ar ta ta ji an dafa Hajiya K'waisa tace,
"Dalilin da ya sa na gane me ke zuciyar ki baya rasa nasaba da bincike da na sa aka yi min game da abinda ya raba ni da sauran asshoshi da 'yan balaja'un da muka yi rayuwa da su a baya,na gano wani abu game da ke Billy wanda baki taɓa zato ko tsammanin zan gano ba,tabbas babu qarya a cikin soyayya da riqo da halaccin da na yi maki a baya,kina ɗauka ta a matsayin wanda ya ceci rayuwar ki daga qaramar kuma maqasqanciyar rayuwa na dawo da ke cikin daula, na yarda na amince kina bani wannan girman, hakan ne ya sa bakya so ko kaɗan ki ga wata ko wani ya rab'e ni har na fifita shi sama da ke, shi ne yasa a baya ki ka dinga haɗa manaqisa da kissa da tuggun da na rabu da kowa banda Any wadda ita da kanta ta yi sanadiyyar rabuwar mu,kina daga cikin wadda ta sa na dinga salwantar da ɗaukakar yaran da ni na rene su da hannu na ba tare da na ankare ba, Baby shine ya haska min fitila akan ki tun ina qi har na bashi dama ya yi bincike kuma ya gano komai game da ke, ya so na kore ki na qi saboda har yanzu ina son ki,kuma ina jin daɗin yanda kike nuna min soyayya da qauna kamar mun fito ciki ɗaya, wannan shine dalilin da yasa kika ga Baby baya son ki,saboda ya san ko ke wacece.
Ina neman alfarma Billy wannan karon kar ki shiga tsakani na da Mommy, saboda na kula yarinyar na da nasibi, da ni da ke zamu amfana da ita sosai kafin mu bata dama ta kafa kanta itama,sannan na kula bayan qin ta da kike akwai wata iriyar wutar sha'awar yarinyar a zuciyar ki, me zai hana ki kauda qiyayyar ki mori yarintar ta tun kafin ta rabawa gayu?"
Banda karkarwa babu abinda jikin Billy ke yi a daidai wannan lokacin saboda bata taɓa zaton cewa Hajiya ta san komai game da ita ba kyale ta kawai take yi, wata iriyar zufar tashin hankali da kunya ce ta mamaye saman bakin Billy da hancin ta,cikin yaqe tace,
"Ki yi hakuri Hajiyata ba zan maimaita abinda na yi a baya ba ko ba komai Mommy kamar 'yar uwa take a waje na, duk abinda na yi mata ni za a zarga saboda qauyen mu ɗaya, kuma ta sanadi na ta zo nan da sunan aikatau,bayan haka ma dai ina son ta sosai itace ta qi bani had'in kai,ta yi rantsuwa ita ba zata yi mu'amala da mace 'yar uwar ta ba, kuma ba zata bar namiji ya neme ta ta baya ba, ta ce a barta da zunubi ɗaya ta ji da shi, na yi duk abinda zan yi yarinyar nan ta qi amince min,"
"Kar ki damu, idan ta san wata ai bata san wata ba ko? Bari dai ta dawo zan sama maki duk abinda kike so a wajen ta, kema kin sani ba zan taɓa barin ki da buqatar abu a ran ki ba ko menene shi ba tare da na sama maki abun nan ba,"
Murmushin farin ciki Billy tayi sannan ta rungume Hajiyan tata saboda murna, cikin tsananin farin ciki tace,
"Na gode na gode na gode Hajiya ta, na san ba zan taɓa neman abu na rasa ba a wajen ki, "
Wata tsawa suka ji an buga cikin tsananin tsoro Billy ta saki Hajiya K'waisa da ta saki qara a tsorace tace,
"Babyyyy meye haka zaka sa na kashiye 'yan hanji na?"
Cike da rangwad'a Samuel da aka kira da baby ya isa gaban Billy yana qanqance ido yace,
"Mena faɗa miki game da Babyna? Ban ce ki nesanta kan ki daga gare ta ba uban wa ya ce ki rungume ta?"
Wani irin wawan mari Samuel ya sakar wa Billy me bala'in zafi sai da ta matse qafarta sakamakon fitsarin da taji ya kub'uce mata, cikin kuka tace,
"Allah ya isa na azzalumi mugu kawai, kasan me yasa na rungume tan ne da zaka ci zalina? Ba zan taɓa yafe maka ba se Allah ya saka min,"
Da gudu Samuel ya bi Billy zai qara dukan ta Hajiya K'waisa ya bi shi yana wani rangwad'a shi a dole ana faɗa akan shi, da kyar ya yi nasarar riqe Samuel da ke cika yana batsewa,
"Habaa babyna meye haka kuma? Bafa kasan dalilin da yasa ta yi hugging ɗina ba, wata 'yar shila take so na yi mata alqawarin sama mata ita shine take murna har ta rungume ni,"
"Ke yanzu wanna macijiyar kike karewa? Ok bari na tafi na bar ku tunda kin fi son ta akai na, dan uban ki ke kuma da kike cewa Allah zai saka maki marin da na yi miki ai kin dai san muka je lahira duk wuta zamu je to meye na neman sakayyar?"
Cike da fushi Samuel ya fita ya bar gidan,har mota Hajiya K'waisa ta bi shi tana bashi hakuri amma haka ya shige mota zai kunna ya tafi shi a dole kishi yake yi da Billy, a son shi ma Hajiyan ta raba gidan zama da Billy amma ta kafe ta nace bazata raba ba,sannan kuma ya zo ya gansu rungume da juna? Inaaa zuciyar shi bazata iya ɗauka ba.
Har ya tada motar shi ya ga an wangale gate ɗin gidan, wata had'ad'd'iyar mota ce ta shiga gidan, nan take Hajiya K'waisa da Samuel suka hau tambayar juna meye sunan motar? Yaushe ta fito kuma waye a ciki, nan take gulma ta haɗe soyayyar da kishi ke so ya raba, ba zato ba tsammani Samuel ya fito a motar shi yana so ya ga waye mamallakin motar.
Sai da motar ta gama tsayawa Hajiya K'waisa ta ga Alhajin da ya tafi da Mommy ya fito cikin sauri ya buɗe ɗaya bangaren Mommy ta fito cikin wata iriyar shiga mai ɗaukan hankalin mai kallo rataye da wata arniyar jaka mai mugun tsada,da gudu Mommy ta tafi zata rungume Hajiya K'waisa Samuel ya yi wata sufa ya sha gaban ta ya na wata jijjiga da fari tare da kad'a mata yatsan shi manuni alamar gargad'i ,dariya sosai Alhajin nan ya yi shi da Mommy, K'waisan Alheri kuwa ya wani shagwab'e fuska yace,
"Babyyyy ! Itan ma kishi kake da ita? Wannan ita ba ruwan ta da layi uku ko biyu, layi ɗaya ta zab'a kuma ka ga alama da idanun ka, ji yarinya yanda ta dawo wata tarwad'a?"
Nan take Mommy ta hau juyi ta na dariya Alhajin ta ya rungume ta suna zuba soyayya a gaban su K'waisa, ihu da shewa K'waisa ta yi tace,
"Hahaiiiii Ragassss! Dole neee yarinya, mu shiga ciki, muje muje da alama bakin nan naku akwai labari, kai Ahaji haka muka yi da kai?"
Cike da dariya da farin ciki suka shiga cikin gidan kowa na faɗin albarkacin bakin sa, Billy ce ta sakko daga bene tana shan juice, idon ta ta sauke akan mommy dake manne da Alhajin ta, wani irin kishi ne ya kama ta, nan take Hajiya K'waisa ta yi wa Samuel rad'a a kunne, kallon Billy ya yi ya kalli Mommy a hankali yace wa Hajiya K'waisa,
"Shegiya kalar mayu, in Allah ya yarda ba zata amince mata ba,"
Dukan kafad'ar shi kwaisa ya yi yace,
"Babyyy"
A tare suka samu waje suka zauna a babban parlourn qasa, Mommy na wani irin yauqi a jikin Alhajin nan,cikin gyaran murya ya kalli K'waisa da ke jiran jin bayani daga gare shi na neman su shi da Mommy a rasa.
"To da farko dai ina mai neman afuwa a wajen uwar d'akin mu Hajiya K'waisan Alheri,lallai na yarda ke ɗin alkhairi ce dan kuwa kin haɗa ni da alkhairina,yanzu haka ita ta matsa sai na dawo da ita ta gan ku sannan ku ji cewar ta na lafiya,amma ba dan haka ba na so sai mun yi wata guda sannan mu zo,"
"Lallai kafin nan zuciyar mu ta gama bugawa da fargaba ko Billy?"
Billy da ta samu waje ta zauna a qaramar kujerar dake facing ɗin su Mommy ce ta kur'bi lemo dan ya danne mata abinda ke taso mata wanda ita kan ta ba zata iya fassara menene shi ba,sannan tace,
"K'warai kuwa, ai da kafin wannan lokacin ka ji sammaci a kotu dan kuwa rashin ta a gare mu babbar illa ce,da fatan dai ka dawo mana da ita kenan dan kuwa mun yi kewar ta sosai,"
Billy ta faɗa tana kafe mommy da idanu, da sauri Mommy ta ɗauke kan ta tana murmushin yaqe dan bata son irin kallon da Billy ke yi mata ko kaɗan,ita da a son samun tane ma kar wajen kwana ya sake haɗa su, da a son tane a ce gidan da kowaccen su take kwana ya zama daban, bazata iya da wannan qazantar da Billy ke so ta aikata ba da sunan soyayya ko jin daɗi, bayan duk abinda suke da ilimin su ta san cewa zunubin mace ta nemi mace ya fi zunubin namiji ya nemi mace, to ta yarda ta aikata qaramin daga baya ta nemi gafarar Allah.
(Niko na ce idan kuma baki riski lokacin neman gafarar ba fa mutuwa ta riske ki sai ki ce wa Allah me? )
Ganin yanayin da ya ɗan gifta a tsakani ya ɗan yi tsauri sai Hajiya K'waisa ta buɗe murya ta hau kiran Sallahu da Ruby akan su kawo abun motsa baki, nan take kuwa suka shiga hidima da su kamar dama can jira suke a basu umarni.
A cikin hirar su ne Alhajin nan ke cewa Hajiya K'waisa,
"A gaskiya ba dawo muku da ita na yi ba, na zo ne dai na sanar da ku za ta yi min rakiya Uganda zan halarci wani taro,da mun dawo zata dawo itama, sai kuma wani lokacin na sake dawowa idan na samu hutu irin haka,"
"Hahaiiii Ragasss !