Showing 255001 words to 258000 words out of 276165 words

Chapter 86 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

ya sanya Billy cewa,

"Wai ke Fadilah wannan rawar kan da kike yi na meye? Naga dai wani satin ne tarewa ta amma naga kina abu kamar yau zan bar maki gidan ki wataya."

Dariya suka yi kawai basu ce mata komai ba,da misalin ƙarfe uku na rana Any ta zauna ta tsarawa Billy kwalliya mai kyau da ɗaukan hankali,wata shadda ta bata ta sanya mai kyau da ta sha aiki tin daga sama har ƙasa,tana gamawa ta bata hijabi kalar aikin dake jikin shaddar ta sanya mata takalmi da kanta sannan ta bata ƴar ƙaramar purse da wayoyin ta ta ce,

"To amarya ki je waje yanzu haka angon ki na can na jiran ki a mota za ku je wani waje."

Baki Billy ta saki tana kallon Any da ta yi wujiga-wujiga da ita saboda aiki da ya yi mata yawa,Fadilah da Hauwa ne suka fito cikin nasu shirin sanye da manyan hijabai iri ɗaya,hannun Billy suka ja suka yi waje da ita. A sannan ne Any ta samu dama itama ta faɗa wanka,Ta Annabi na can na shiryawa za su tafi wajen walima tare da Any.

Lokacin da Billy tayi ido huɗu da Man sai kawai ta ji hawaye yana so ya zuba a idanun ta,kaya iri ɗaya suka sanya,fuskar nan tashi ta yi wani irin kyau annuri na fita a cikin ta,da kanshi ya buɗe mata mota ta shiga sannan abokin shi da ke ja ya wuce da su,Fadilah da Hauwa kuwa suna tsaye a jikin wata motar abokin Man suna jiran su Any su gama a kai su wajen walima.

Sanda Ta Annabi taga Any ta fito shirye cikin shadda da babban hijabi sai ta ji wani irin daɗi a ranta,lallai musulunci shine addini na gaskiya,wanda ya bar addinin shi ya kama hanyar shaiɗan ya halaka. A tare suka fita daga gidan,bayan sun rufe ne suka shiga mota abokin Man ya tuƙa su sai wajen walima.

Ko da suka isa sun tarar da Billy na ta kukan farin ciki,domin kuwa har Innah Laminde da su Abdul sun halarci wajen walimar,zuwan Innah Laminde ba ƙaramin abu bane a wajen ta duba da yanda bata taɓa jin labarin Innahr ta taɓa barin ƙauyen Ba Mugu ba a kaff tarihin rayuwar ta.

Billy na ganin Any ta shiga wajen walimar sai ta tashi da sauri ta isa gare ta ta rungume ta ta fashe da kuka,Any ma hawaye take yi daga ƙarshe ta janye Billy a jikin ta ta hau masifa,

"Ji wani iya shege Billy duk kin goge kwalliyar taki,nima kina so ki goge min tawa,dan Allah matsa ni na wuce raguwa kawai,komai kuka baki gajiya ke."

Dariya Fadilah tayi ta ce,

"Kedai Aunty Anam kina gudun kar ki ƙarar da hawayen ki ne tin kafin ki kai ƙanwar taki ɗakin miji.

Dariya suka yi,Any ta kama Billy ta maida ita wajen zaman ta,kujera ce babba ita da Man a zaune,sai ta samu gefen da mata suke zama ta zauna ita da su Fadilah,ɗayan gefen kuwa maza ne ke zaune a wajen. Suna nan zaune Malaman da aka gayyata suka iso suka hau yi musu wa'azi mai ratsa zuciya,babu wanda bai samu abinda zai amfana da shi ba a wannan wa'azi da aka yi,daga ƙarshe abinci akai ta baiwa mutane a abun take away, taro ya tashi kowa yana cike da farin ciki,dan kuwa yanda walimar ta gudana ta ƙayatar da mutane sosai.

Da magaribar driver ya karya kan mota ya wuce da amarya gidan ta. Suna isa Billy ta ga motar su Abdul da ke ɗauke da su Innah laminde ta riga tasu isa,mamakin yanda Any duk ta shirya wannan hidimar ta dinga yi,daga ƙarshe sai ta dinga yi mata addu'a da fatan alkhairi a cikin zuciyar ta,dan kuwa babu abinda zata yi mata ta biya ta akan alkhairin da ta ke ta yi mata.(Zama da turawa ne ya koyar da ita haɗa irin wannan abubuwan farin cikin dan faranta ran wanda kake tare da shi ba tare da ya sani ba)

Gidan Billy ya haɗu matuƙa dik da cewa ba wani babba bane sosai,yanayin ginin da tsarin gidan tare da kayan da aka zuba a ciki ne ya fitar da kyawun shi,ƴan kai amarya basu jima ba suka yiwa amarya sallama,tare da tarin addu'o'i da fatan alkhairi suka tafi. Billy kuwa duk baza idanun ta dan taga Any bata ganta ba,nan take ta gane bata biyo su ba,saƙon fatan alkhairi ta samu daga bakin Hauwa,haka ta ci kukan ta ita kaɗai Man na gefe yana lallashin ta suka tafi suka barta.

Yanda Man ke ririta ta yana lallaɓa ta har mamaki ya dinga bata,bata taɓa sanin yana da ilimin addini ba sai a wannan daren. Bayan ta gama kuka ya sa tayi alwala suka gabatar da sallar da ma'aurata ke yi a daren su na farko, addu'o'in da Man ya dafa kanta yana zuba mata ne suka sa zuciyar ta ta sake nutsawa cikin kogin ƙaunar shi,bayan ya kammala ne ta kalle shi tace,

"Man ashe ka iya addu'a haka ban taɓa sani ba?"

"Ni ɗin nan da kika ganni na haddace Alkur'ani mai girma,amma sakaci da shashancin da na sanya a gaba ne ya ja min zubewar hadda ta,domin kuwa shaid'anci baya taɓa gogayya da aikin alkhairi, dole ne idan ka kama ɗaya,ɗayan ya tafi ya barka."

Jinjina kai kawai Billy ta yi,kafin daga baya Man ya gabatar musu da abinci,babu wani jin nauyi Billy ta zage ta ci kazar amarcin ta ta kora da madara,hira suka fara yi suna tina baya suna yiwa junan su alƙawarin kasancewa mutanen kirki a gaban rayuwar su,daga haka salon amarya da ango ya sauya suka lula duniyar masoyan da auren sunnah ya haɗa su.

A can gidan Any kuwa ta sha kukan kewar Billy sosai sanda ta koma gidan ta ganta ita kaɗai,dawowar su Fadilah ne ya sanya ta goge hawayen ta ta shiga cikin su sukai ta farin ciki tare. Kwanan su uku suka shirya suka kaiwa Billy ziyara,daga ƙarshe suka wuce ƙauyen Ba Mugu.

***************************


Jikin Innoh yana ta sauƙi,dan kuwa tana iya magana a yanzu har a fahimci me take faɗi,tana iya dafa abu ta tashi tsaye,tafiya kuwa sai an riƙe ta,likitoci sun basu tabbacin idan suna ci gaba da zuwa gashi tana shan maganin ta yanda ya dace,sannan ana gujewa ɓacin ranta zata samu sauƙi da wuri.

Mommy duk ta rame ta jeme saboda wahalar kula da Innoh,Aunty Naja ta samu ta auri wani malamin makarantar allo mai mata biyu,suna zaune lafiya da mijin ta da matan shi,matsalar shi ɗaya kulle,wannan dalili ne ya sa Mommy take ta wahala ita kaɗai,Baaba kuwa ita ke yi musu girki a gidan dan sauƙaƙawa mommy wahalhalun da take yi. Duk kud'in maganin Innoh Alhaji Baban Gida ne yake bayarwa,wasu lokutan kuma Saddiqa na aiko da kuɗi a sai mata kalar abincin da ya dace ta dinga ci. Duk da hidimar iyali da karatun da take yi be hana ta kawo ziyara ba dan taga yanayin jikin Innoh.
Sule ma yana iyakar ƙoƙarin shi dan ganin ya bada tashi gudummawar wajen kula da Innoh shi da Ameerah ƙaura.

Bayan watanni biyu da bikin Billy aka sanya ranar bikin Abdul da Suhailah,Mommy na zaune a tsakar gida tana shan iska dan bata jima da kammala yi wa Innoh wanka ba har ta yi bacci,Sadeeq ne ya shiga gidan hannun shi riƙe da katin auren Abdul ɗin da Sultan ya bashi dan ya kawowa Ɗan Liti. Ba tare da tunanin komai ba ya tinkari Mommy dake binshi da kallo,yana zuwa ya miƙa mata katin ya ce,

"Yah Mommy kin ga abinda ke faruwa a wannan ƙauyen yau."

Tin kafin ta karb'i katin ɗaurin auren gaban ta ke fad'uwa,hannu na rawa ta karɓi katin,idanun ta ne suka sauka akan sunan Abdussaboor ɗin ta da na wata tare da ranar ɗaurin auren su,numfashin ta taji yana mata wahalar shaƙa,cikin wani irin mawuyacin hali Mommy ta saki katin ya faɗi ƙasa ta hau dafa gini zata shiga ɗakin ta,idanun ta sun rufe kirif da ruwan hawaye dan haka cikin rashin sani ta taka dutse ta faɗi a wajen.............


*Masoya Mommy a yi haƙuri kar na sha ruwan kalamai yau.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨










PAGE 104:










Kamar wadda ake ingizawa haka ta tashi ba tare da ta damu da kurjewar da ta yi a ƙafar ta ba. Hijabin ta ta sanya da nufin ta tafi gidan Sarkin ta tarar da Abdul ɗin ta roƙe shi ya yafe mata a maida auren su,da sauri Sadeeq ya riƙe ta ya ce,

"Dan Allah Yah Mommy ki kwantar da hankalin ki,kar ki manta da halin da Innoh ke ciki na rashin lafiya,kina tunanin yanzu idan taga halin da kika shiga hankalin ta zai kwanta ne? Kin ga ai se jinyar da ake yi mata ta koma baya ko? Sannan shi fa Baban Amir baya garin nan,Sultan ne ke rabon katin ya ce na kawo."

Waje Mommy ta samu a bakin ƙofar ɗakin ta ta zauna ta rintse katin ɗaurin auren a hannun ta da ƙarfi sai da ta ji ya yage,kuka mai matuƙar ƙona zuciya ta saki tare da juya kan ta cike da ƙunar rai ta ce,

"Na shiga uku ni Hadiza ina zan tsoma zuciyata taji sanyi ne? Shikenan yanzu Abdul aure zai sake yi da wata macen ba ni ba? Da na san haka zan sha wahala a rayuwa ta da ban yiwa Allah butulci ba akan ni'imar da ya yi min ta aura min nagartaccen namiji kamar Abdul da ya yi,tabbas Abdul namiji ne da kowacce mace zata so ta samu kamar shi,yana da kulawa,tausayawa,tare da shagwab'a mace,abun hannun shi be rufe masa ido ba,komai nashi nawa ne,me yasa na manta dika wannan alkhairin nashi na rufe idona na yi rashin mutuncin da ya janyo min wulaƙantacciyar rabuwa da miji na?"

Baaba ce ta fito daga ɗaki ta yafito Mommy da hannun ta,kamar Mommy ba zata tashi taje ba saboda yanda take jin jikin ta kamar na mara lafiyar da ta shekara tana jinya,a hankali ta miƙe ta isa ɗakin Baaba ta zauna a ƙasan carpet ta ci gaba da kukan ta,goro Baaba ta ɓantara ta watsa a baki sannan ta ja ruwan roba dake ɗakin ta miƙawa Mommy ta ce,

"Haƙuri zaki yi yanzu Mommy,saboda aikin gama ya riga da gama addu'a ce kawai zata karkato miki da kan Abdussaboor."

Cikin sauri Mommy ta ce,

"Dan Allah ki faɗa min kalar addu'ar da zan dinga yi har ya dawo gare ni Baaba."

Murmushi Baaba ta yi sannan ta ce,

"Dan Allah ki ga yanda ki ka koma yanzu Hadiza. Mu fa iyaye da muke yawan baku haƙuri idan kuka kawo mana ƙarar mazajen ku ba wai dan bamu son ku bane,soyayyar da muke yi muku ce ta jawo muke baku haƙurin saboda muma shi muke yi a namu gidajen,amma turawa sun nuna muku kar ku ɗauki raini wajen namiji daya yi maku ku rama,sannan kar ku wahaltawa namiji ba aikin ku bane. To ina son ki sani idan har a aure namiji baya dukan ki,baya zagin ki da iyayen ki,yana baki ci da sha ya ɗinka maki sutura ke da yara dai-dai ƙarfin shi,yana biya maki buƙata a gado koda ba koda yaushe bane,to kiyi haƙuri ki zauna a ɗakin ki,saboda duk wadda zata ce maki ki yi masa rashin kunya dan ɗan saɓani ya haɗa ku ba masoyiyar ki bace,tinda bata san rashin kunyar nan me zata jawo maki ba. Idan kuma ke da kan ki ne kike ganin bai isa ya ja zare ba ba tare da kin tsinka ba,to kin tafka babban kuskure,domin kuwa daga karshe zaki faɗa ƙaton ramin danasani ne a lokacin da ba zai yi maki amfani ba."

"Maganar ki gaskiya ne Baaba,ni a yanzu na yi nadamar dik abinda na yi,inshaa Allahu zan san hanyar da na bi na jawo hankalin Abdul waje na,ya taimaka min ya yafe min na koma ɗaki na na rungumi yaro na."

"Allah ya sa Mommy, idan hakan ta faru ai sai kowa ya yi farin ciki a gidan nan,dan kuwa kin yi dacen miji me son ki,kece kika yi wasa da damar ki. Na tabbata yanzu kinga illar mummunan kishi,daga ƙarshe kika ga illar bin bokaye da malaman tsibbu."

"K'warai Baaba na ga illar su,kuma har abada ba zan gushe ba face na ci gaba da neman gafarar Allah,idan Allah ya ƙara bani damar auren Abdul Baaba ko mata uku zai ƙaro bayan ni ba zan taɓa d'aga kai na kalle shi ba balle na hana."

"To da kyau,ni kuma na yi maki alƙawarin zan ci gaba da taya ki addu'a Allah ya dawo maki da shi ku komawa auren ku idan da alkhairi,idan babu alkhairi Allah ya kawo maki wanda ya fishi alkhairi."

A sanyaye Mommy ta amsa da,

"Amin Baaba,inshaa Allahu shine ma alkhairin."

Dariya Baaba tayi wadda ta sanya Mommy jin kunyar kalaman ta,cikin sauri ta miƙe tana faɗin,

"Bari naje na duba Innoh ko tana buƙatar wani abun."

Ba tare da Baaba ta ce komai ba ta ci gaba da taunar goron ta tana dariya. Mommy na fita kuwa sai ta leƙa Innoh taga tana bacci,ɗaki ta tafi ta kwanta a katifar ta tana tunanin Amir,cikin hawaye mai dauke da murmushi ta ce,

"Ko ya iya gudu yanzu? Idan mun haɗu da wanne suna zai kira ni? Ko yanzu ya kai girman wa? Anya kuwa ba zan je na ga yaro na ba gobe?"

Tashi tayi zaune ta na sake nazari akan zuwa ta ga ɗan nata. Daga karshe ta yanke shawarar ko ana muzuru ana shaho sai ta ga Amir a gobe, dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ta miƙe ta hau duba kayan ta, kuɗi ta d'akko ta fita tsakar gida,Sadeeq ta kirawo ta aika ya siyo mata kayan ƙwalama da ta san yaron na so. Cike da ladabi Sadeeq ya karɓi kud'in ya tafi shago dan siyowa Mommy abinda ta aike shi.

Kamar yanda ta ƙudirta kuwa washegari da rana bayan ta kammala gyara gidan, ta yiwa Innoh wanka ta sauya mata kaya,sai ta zauna ta bata abinci da maganin ta suka ɗan gwada tafiya a tsakar gidan,suna kammalawa ta kama Innoh suka koma ɗaki,babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta saboda maganin da ta sha da motsa jikin da tayi,tana ganin haka sai ta leƙa tsakar gida taga babu kowa, ledar da aka yo mata siyayyar tsarabar da zata kaiwa Amir ta ɗauka ta duba komai ya yi dai-dai,sai kawai ta fita tsakar gida ta shiga wanka daga nan ta yo alwala sannan ta yi sallar azahar. Tana idarwa ta hau kwalliya sassauƙa ta sanya wani material ɗin ta mai tsada da Abdul ya taɓa siyo mata a zuwan shi kaduna da ya yi saboda aiki,kalar material ɗin ta karb'i farar fatar ta,sai ta yafa mayafin ta ta zira baƙaƙen takalman ta ta ɗauki ledar tsarabar ta ta bar gidan.

Tafe take tana addu'a Allah yasa ta haɗu da Abdussaboor ta sanya shi a idanun ta ko zata ji sanyi a ranta,da wannan tunanin ta isa gidan Sarki. Da Innah Laminde ta fara cin karo a tsakar gidan suna hira da sauran matan gidan,ga goro da chewing gum da alawa nan ana ta ɗaurawa a leda za a kai gida-gida saboda a gayyaci mata auren Abdul ɗin.

Cike da dakiya Mommy ta durƙusa har ƙasa kamar yanda ta saba a baya ta gaishe da Innah Laminde da sauran matan Sarki,kallon ta kowa yake yi kamar sun samu sabuwar halitta,babu wanda ya taɓa tsammanin ganin ta a wannan lokacin,duba da yanda labarin auren Abdul ya karaɗe ƙauyen.

Tana nan duƙe ta jiyo ƙamshin turaren shi kamar a mafarki,kasa tashi tayi daga wajen da take tsugunne sai da Innah Laminde ta miƙe tsaye ta fara takawa ta ce wa Mommyn,

"Shigo ciki ku gaisa da ɗan naki mana."

Sarai Mommy ta gane Innah Laminde bata son Mommyn ta haɗu da Abdussaboor dake shirin shiga cikin gidan ne shi yasa ta yi mata tayin shiga ciki,dan haka tana miƙewa sai ta yi dabarar sakin ledar hannun ta a ƙasa har abun ciki ya watse a ƙasa,cikin wani irin salo Mommy ta duƙa tana kwashe biscuits da chocolates ɗin da suka zube tana mayarwa ledar su,Abdul kuwa da shigar shi gidan kenan idanun shi suka sauka akan Mommy wadda ta juya bayan ta tana kwashe abu a kasa.

Wani irin yawu ya had'iya sai da maƙoshin sa ya yi sama da kasa a fili kafin ya hau ƙyafta idanu da sauri da sauri kamar wanda yake son ya farka daga mafarkin da yake ciki. Mommy kuwa na gama kwashe komai sai ta yi gaba ba tare da ta juya ta kalli inda Abdul ɗin yake ba,tana shiga ɗakin Innah Laminde sai ta zauna a ƙasa tana wani sunne kai,murmushi Innah Laminde ta yi dan kuwa taga dik abinda ya faru,har da halin rikicewar da Abdul ɗin ta ya shiga akan ganin Mommy,gaisawa suka sake yi sannan ta k'wala wa mai aiki kira aka karɓo Abdul a wajen Baban shi aka kawowa Mommy.

Koda ta ɗauke shi ta zaci zai manta da ita ko kuma ya yi mata ƙiwa,sai taga yana ta shafa fuskar ta yana surutai irin na yara. Wasu irin zafafan hawaye ne suka dinga sauka a idanun ta wanda suka yi matuƙar karya zuciyar Innah Laminde har ta ji rashin kyautawar ta akan kaiwa Mommy ɗan ta da bata yi ba har na tsawon watanni masu yawa haka.

Cikin kuka Mommy ta fashe da dariya da ta ga Abdul ya tashi yana tafiya sosai da ƙafafun shi har yana haɗawa da gudu zai fita waje,ƙamshin turaren Abdul ne ya tabbatar mata da wanda yaron ya gani har yake son fita waje. Cikin sauri Mommy ta miƙe tsaye tana share hawayen ta ta ajiye ledar tsarabar da ta kawo a gaban Innah Laminde ta ce,

"Ni zan koma,sai kuma watarana,ina fatan za a dinga kawo min shi ina ganin shi ko da sau ɗaya ne a wata dan Allah."

Tausayin ta ne ya kama zuciyar Innah Laminde,cikin sanyin murya ta ce,

"Inshaa Allahu za a dinga kawo miki shi lokaci zuwa lokaci dan ku gaisa,fatan mu shine Allah ya raya shi ya yi masa albarka."

"Amin ya Allah na gode."

Da alamun sauri a tattare da Mommy amma Innah Laminde ta sake tsaida ita ta hanyar tambayar ta jikin Innoh,cikin sauri Mommy ta ce,

"Da sauƙi alhamdulillah,tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login