Showing 30001 words to 33000 words out of 276165 words

Chapter 11 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

bi anya zata iya yin wannan rayuwar irin ta su Billy kuwa? A hankali jiki babu k'wari ta fita,Billy na ganin ta fita bata ce mata komai ba ta yiwa karan sigarin ta doguwar zuƙa ta fesar sannan ta yar ta bi ta take ta sa kai suka shiga shopping mall ɗin,wajen da ake saida qananan kaya na mata suka nufa, Billy ta dinga kwasar wa Mommy ta na kara mata a jikin ta, da ta ga sun yi mata sai ta ɗaukar mata, a haka saida ta ɗebar mata kala goma sannan ta kwashi takalma biyar da purse uku masu kyau ta wuce wani d'aki ta sa mommy ta shiga ta dinga gwad'awa, daga qarshe ta bar wata bingilar riga kalar purple mai duhu wadda take iyakar ta guiwa da siririn hannu ta qirjin ta an tattare ta kaɗan, murmushi Billy ta yi ta daki mazaunan Mommy ta ce,

"Da kyau Hadizan Ɗan liti, mu je na san yanzu Hajiya na can ta dawo,mu je ki bata mamaki qawata, yanzu ace Baba D'an liti ya gan ki a haka ai sai ya tsine miki ya haɗa da ni da zuri'a ta dika,"

Ganin Billy ta saki ranta har tana murmushi da jan ta da wasa ne ya sanya Mommy itama sakin ranta kaɗan, dan kuwa a da duk ta takura ta damu, ga jimamin sanin Billy ba aikatau take yi ba karuwanci take yi ga kuma Billyn na fushi da ita saboda ta yi maganar lokacin sallah.

A hanya ne Mommy ke jinjina lamari irin na mutanen duniya, ashe dai komai iskancin ka kana samun wanda ya fi ka?

A da da tana gidan su sallah sai ta ga dama take yi, ko kuma ta haɗe azahar, la'asar, magariba, watarana se zata kwanta ma ta haɗa duk har da isha'i,sai gashi anan yin maganar lokacin sallah ma ya zama tashin hankalin da ake d'aga jijiyar wuya akai,lallai rayuwar duniyar nan ta na da ban ta'ajibi.

Sun isa gida a matuqar gajiye, dan haka suna isa Billy ta fito ta wurga wa Sallau makullin motar tace ya fitar da kayan ciki ya kai d'akin Mommy, da sauri ya cafe makullin motar ya fara bin umarnin ta, Mommy kuwa na biye da ita kamar raqumi da akala.

Suna shiga suka ga Hajiya K'waisa da wani kyakkyawan matashi suna manne da juna kamar mata da miji, Hajiya K'waisa sai shagwab'a take yi wa matashin shi kuma yana lallashin ta tare da sumbatar ta a duk inda ya samu a jikin ta.

A kasalance Hajiya K'waisa ta d'aga kan ta daga jikin kyakkyawan matashin ta na duban Billy wadda ta b'oye Mommy a bayan ta ta na murmushi,cikin wani irin yanayi Hajiya K'waisa ta miqe a ɗan firgice bayan Billy ta matsa Mommy ta bayyana.

"Ke Billy wannan halittar daga ina haka? Ke..ke...tsaya, kar ki ce min...laaa kar ki ce min wannan wagirarriyar yarinyar ce ta koma haka? Allah mai iko ! Ahayyeeee washhh Allah maraba gasasshe wai kura ta ga baƙin jaki"

Dariya Billy kawai take yi ta jin daɗi dan kuwa ta san idan Hajiya ta yaba dole a yi mata ruwan nerori.

"Billy ina motar can da kike maita na hana ki? To ki ɗauka na baki kyauta"

Ihun murna Billy ta sanya ta tafi da gudu zata rungumi Hajiya Saurayin Hajiya ya zabga mata harara, harar da ta dakatar da Mommy daga dariyar da take yi ta farin ciki, dan kuwa a ganin ta ko za a kashe ta ba zata iya yin wannan hararar ba a matsayin ta na mace.

Cikin wata muryar da Mommy ta zata mace ce ke magana matashin yace wa Billy,

"Ke dakata anan, na yi maki iyaka da wannan naman, domin kuwa naman giwa ya fi ƙarfin kaza ta ja shi,tsaya can kiyi murnar ki bana son gwalangwason banza"

Kafin Billy ta yanko tata maganar Hajiya K'waisa ta shiga tsakanin wannan 'yar qaramar taqaddamar dake son ta kaure tsakanin Billy da saurayin Hajiya K'waisa,

"To ya isa haka, table ɗin mu is ready mu kaɗai abinci ke jira tun ɗazu mu je mu ci kar ya yi sanyi,Billy kin cancanci wannan kyautar shi yasa na yi maki ita, na sani kina so ki wanke min bakin cikin da Any ta sanya min a raina ne kafin ta bar gidan nan, na tabbatar ke da kan ki a yanzu idan kin so zaki iya kafa taki harkar amma halacci ya sanya ki ke ci gaba da zama a qarqashi na,dan haka ba abinda ba zan yi maki ba dan ki ji daɗi kema sai abinda bani da shi"

"Ina godiya Hajiya ta,dole ne na ci gaba da yi maki biyayya domin kece ki ka tsamo ni daga mummunar rayuwar zama a gidan qananan karuwai ki ka ɗaukaka daraja ta na dawo ina zama a irin wannan mashahurin gidan, kuma ki ke yi min duk abinda nake so dan haka dole ne nima na faranta maki....ai baki sani ba, mun haɗu da yaran Any a saloon har da yada min magana,"

"Rabu da su, zan basu mamaki a taron new year na Abuja ina nan ina wani babban tanadi,Mommy nake so ta yi mana wannan babban kamun saboda ita sabuwar fuska ce,da ita zamu yi amfani mu kece raini"

Yaqe Billy tayi dan kuwa ta jima tana targeting wannan babban taron da za a yi na manyan 'yan duniya irin su,kuma a wannan taron ne ake saka ran zuwan babban matashin ɗan siyasan nan mai suna Alhaji Yasir Mai Nasara,matashi ne mai ji da kyau da nera, a taron ne zai zaɓi yarinyar da zai dinga hutawa da ita a wannan shekarar, a tunanin ta Hajiya K'waisa za ta aika ta sai kuma ta zaɓi Mommy, wani irin yawu ta had'iya mai d'aci ta wuce gaba tana yaqe,kujera ta ja wa Mommy Mommyn ta zauna a d'arare, dan kuwa sauraron su kawai take yi amma tabbas tana buqatar fashin baqi dalla-dalla akan lamarin nan da suke magana akai.

Murmushi Hajiya K'waisa ta yi tace wa Mommy,

"Kar ki damu da sannu zaki gane inda komai ya dosa,watarana ke zaki gayyato wasu suma su dangwali arziqi kamar yanda Billy ta yi miki"

Yaqe Billy ta sake yi dan ita wannan yabon be wadatar da ita ba sam.

Abinci suka fara ci Mommy na ta kallon yanda kowa ke sarrafa wuqa da cokali mai yatsu ita dai ko da cokali mara yatsun ma ba zata iya zagewa ta ci yanda zata qoshi ba, dan haka sai ta faki idon su ta sanya hannu ta damqi nama ta jefa a baki ta hau muzurai,Hajiya K'waisa na kallon ta amma ta kauda kai ta yi kamar bata gani ba, da ido ta kalli Billy ta yi mata alama da,

'A koya mata cin abinci a table'

Itan ma da ido ta amsa mata da,

'An gama'

Wayar Mommy ce ta hau ringing wadda gaba ɗaya ta ma manta tana tare da wayar a cikin qaramar purse ɗin ta da suka fita da ita, qarar ce ta razana Hajiya K'waisa har sai da ta zubar da abincin da zata kai bakin ta a jikin ta ,cikin ɓacin rai da haɗe haqoranta waje ɗaya ta kalli Mommy, da sauri Mommy ta miqe tana bada hakuri ta nufi hanyar sama dan zuwa amsa wayar ta...............[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI












PAGE 11:







Wayarta ta fara sokewa a jikin ɗan qaramin wandon dake jikin ta, kafin ta doka doguwar bismillah ta kama qarfen jikin matattakalar ta fara takawa sannu a hankali har ta samu nasarar hayewa can sama, ko da wasa bata yi gangancin sake leqa kan ta qasa ba,direct d'akin ta ta shige ta samu doguwar riga daga cikin kayan ta da mayafin kayan ta sanya a jikin ta tare da d'aure kan ta da kyau ta yanda ba mai gane yanda gashin ta ya koma.

Tana qoqarin kiran su Sule ne kiran shi ya sake shiga wayarta, katse kiran ta yi ta kira shi video call a WhatsApp, cike da washe baki Sule ya ɗauki wayar dan dama ya qagu ya ga muhallin da take zaune a ciki, ko da suka ɗauki wayar sai Sule ya rud'e dan ganin qayatuwar d'akin da Mommy ke ta haska musu kafin ta yi magana da kowa, cikin zumud'i yace,

"Wai kina nufin duk wannan d'akin naki ne ke kaɗai?"

"Iyyyy, kai se ka ga ma sauran cikin gidan za ka gane ba gidan qananan mutane bane,yanzu haka abinci muke ci da matar gidan ka kirawo ni se da na hawo bene na shigo nan fa, bari dai mu gama gaisawa da su Baba zan maka videon gidan ka gani da kyau,"

"Shegiya mommy ta taka leda"

Ɗan liti ne ya amshe wayar ya na b'ata rai yace,

"Dan uban ka ya zaka ce mata shegiya bayan gani a tsaye?  Ke mommy kin isa lafiya dai ko?"

"Lafiya qlou na isa Baba,bana ganin ka sosai Baba, Sule haska min shi da kyau, Baba ashe zan yi kewar ku haka? Tunda muka zo nake ta son na gaishe ku na faɗa muku mun iso lafiya kuma na sauka a gidan masu akwai, inshaa Allahu kuma bana zaku fara shan jar miya, ina Innoh?"

Innoh na gefe ta k'wame ita a dole ta yi fushi ba a fara bata wayar ba, cike da dariya Sule yace,

"Inno ki karɓi wayar ko kuma katin ta ya qare ke da ku sake gaisawa se qarshen wata idan an yi mata albashi"

Da jin haka ta yi wuf ta karɓi wayar ta hau qorafi,

"Iyyyiii in ba dan an mai dani mara mahimmanci ba ace se kowa ya gama magana za a bani? To ni irin wannan rashin bani mahimmancin ne ke damuna yan....."

"Innohta kwantar da hankalin ki,indai waya ce yanzu muka fara, albashi na na farko zan sa a sai maki waya mu dinga ganin juna kullum"

"Alhamdulillahi,amma ba wayar nake so ba dai, kina ji ko...."

Nan Innoh ta zauna ta dinga rattab'a wa Mommy duk wani abu da take so wanda ta sani sarai ya fi karfin arziqin Mommy ko nawa kuwa za a bata a matsayin ta na sabuwar zuwa aikatau,sannan gashi ko albashin ma ba a yanke mata nawa za a bata ba, daɗin dad'awa bata ma san wanne irin aiki Mommyn zata yi ba a biya ta, hatta da Ɗan litin bai tambaye ta wanne kalar aiki zata fara yi ba, fatan su kawai da burin su bai wuce na ta cika musu burikan zuciyoyin su ba da duk kud'in da zata samu, cikin lissafe-lissafen kuwa ba a bar Ameerah a baya ba ita da Sule.

Dan kuwa Sule yace babbar waya yake so ta b'aro masa dal a leda saboda shima ya dinga ɗaukan hotuna mai kyau, dan kuwa yanzu a social media daga hoton ka ma ana iya gane wace iriyar waya kake amfani da ita.

Wayar Mommy ce ta fara nuna ba caji kafin su hakura suka yi sallama da juna, bayan ta yi musu alqawarin biyawa kowa buqatar shi da zarar ta samu kuɗi, qasa ta koma wajen su Billy nan ta samu har sun gama cin abincin sun koma wani parlour na daban, kwalabe ne masu arnen kyau da kofunan gilasai a gaban su suna zuba wani abu ja dake cikin kwalaben suna sha a hankali cikin yanga da k'warewa.

Ita dai ta san bata qoshi ba, yaqe haqora ta yi ta na kallon su, da sauri Hajiya K'waisa ta ajiye nata cup ɗin ta na wani fari da yarfa hannaye ta ce wa Billy,

"Billy jata can dan Allah ta ci ta qoshi kar ta yage ni"

Cike da dariya Billy ta ce,

"Kai Hajiyata wanne irin ta yage ki sai kace wata kura?"

"Ke Mommy ki ke ko wa? Dole ne fa ki koyi sarrafa leb'en ki da haqoran ki ta hanyar da zaki burge masu kallon ki ba wai ki dinga yaqe su yanda kike yi ki na firgita jama'a ba, bakin ki bai da munin da za a dinga magana akan shi a koda yaushe amma rashin iya sarrafa shi shine matsalar ki, nawane masu irin bakin ki maza ke nema ke har da shegun mata irin su Hajiya Badariyya? To ki sa kunnen ki da kyau ki saurare ni, idan har ki na so ki mori sabuwar rayuwar nan da kika shigo to ki kimtsa kan ki, ki dinga gyara bakin ki, ba koda yaushe bane zaki dinga sakin gandar leb'en shafatataaaa ki na yaqe haqori kamar zaki sari icce ba kin gane? Billy ku je can bana son hayaniya zamu huta da baby please"

"To Hajiyata yanda kika ce haka za a yi, kuma zan koya mata yanda zata yi ta gyara duk abinda ya dace ta gyara"

"Good ! Na san zaki iya bana jin ki ta nan wajen ai"

Direct dining table suka nufa Billy ta k'wala wa Ruby kira tace a kawo abinci da dikkan cokula da wuqaqen da ake amfani da su wajen cin abinci.

Bayan an kawo dik abinda ya dace a kawo ne Billy ta zauna ta dinga nuna wa Mommy yanda ake amfani da cokula da wuqaqen har ma da cokula masu yatsu babban da qaramin,hatta da kala-kalan kofuna na shan ruwa da lemo da giya duk sai da Billy ta yi wa Mommy bayanin yanda ake amfani da su, Mommy ta riqe wasu, wasu kuma bata riqe ba, na giya kuwa ko sake bi ta kan shi bata yi ba dan kuwa a cewar ta me zai haɗa ta da giya tana musulma? Cikin nuna k'ware wa da taqama Billy tace,

"Ai kuwa dole ki iya amfani da su Mommy idan har Babbar yarinyar ki ke so ki zama ba mai riqe wa Babbar yarinya jaka ba, domin kuwa wani wajen ma idan kin je giya ita za a baki a matsayin ruwan da za a tarbe ki da shi musamman idan kin yi dacen zuwa Abuja ko qasar waje,"

"Giya dai giya da muke jin ana cewa haramun ne shan ta Billy?"

"Mommy bana son abinda kike min fa? Haramun nawa ki ka aikata kafin ki zo nan? Ke har tsoron haramun kike yi dama? To bari ki ji na faɗa maki,idan zaki cire wannan tsoron ki cire idan baza ki cire ba kuma sai ki yi ta yi, ba inda ɗaukakar ki zata je zata b'are,"

Shiru Mommy tayi, kafin daga baya ta kai hannu zata yagi naman kazar da ke gaban ta, da sauri Billy ta sanya hannu ta dakatar da ita ta yi mata nuni da wuqa da cokali mai yatsu, b'ata rai Mommy ta yi tace,

"Ki wa Allah ki bari na ci na yau kaɗai,"

Murmushi Billy ta yi sannan ta kyale Mommy ta koma gefe ta dasa wayar ta tana yi wa Mommy video ba tare da Mommyn ta kula da hakan ba,gaba ɗaya ta maida hankalin ta kan cin kayan daɗin da ke gaban ta, hannu bibbiyu ta sanya tana cin abincin kamar tsohuwar mayunwaciya,lemo ta ɗauka ta kwankwad'e na cikin cup ɗin da aka zuba gaba ɗaya, ta na cire cup ɗin a baki ta saki wata muguwar gyatsa mai qarfin gaske, sannan ta kalli Billy wadda ta yi saurin kashe camera ɗin ta ta miqe ta na murmushi tace wa Mommy,

"To an ci an qoshi sai mu je ko?"

Murmushi Mommy ta yi sannan ta duqa zata fara tattara kwanikan da ta ci abincin da su da niyyar kai su kitchen Billy ta ce,

"Idan baki nuna wa masu aikin gidan nan sama ki ke da su ba to tabbas watarana sai Sallau ya aike ki, mu je za su tattara"

Kallon inda Zubaida ke tsaye Mommy tayi ta sakar mata murmushi, da sauri Zubaida ta b'ata rai ta ɗauke kan ta daga kallon Mommy ta hau tattare kayan wajen, mommy kuwa cikin ranta ta ke ayyana,

'Da alama idan na samu dama a gidan nan yarinyar nan zan fara kora, dan na ga ta tsane ni tinda na zo gidan nan take harara ta'

Sama suka wuce basu sake komawa wajen su Hajiya K'waisa ba da ke can ɗaya parlourn suna shan barasa da saurayin ta.

Suna shiga d'akin Mommy Billy ta buɗe wardrobe ɗin mommyn ta ga yanda Sallau ya jera mata kayan da suka siyo d'azu,murmushi ta yi sannan ta koma saman gadon Mommyn ta kwanta tana faɗin,

"Washhh Allah na na gaji,bari na huta"

Mommy ma zubewa ta yi a gefen ta suka kwanta, wayar su suka d'akko suka kunna data kowa ya shiga inda ya fi kauri, Billy direct TikTok account ɗin ta ta shiga, Mommy kuwa ta shiga WhatsApp ɗin ta, Messages ta gani suna ta riqe-riqen shiga wayarta sai ta juya ta na so ta tashi ta sanya caji,Billy na ganin haka ta nuna mata gefen gadon tace,

"Ba sai kin je ko ina ba, cajar ki kawai zaki d'akko ki jona,"

"A gaskiya Billy kuna jin daɗin ku, sai yanzu na ke ganin wauta ta ta qin biyo ki tun farko."

"Ai gaki yanzu kin biyo ni, lokaci bai qure maki ba ki maida hankali kema ki zama wata abar kwatance kamar wannan baiwar Allahn"

Da sauri mommy ta qarasa saka caji ta kwanta a kusa da Billy suna gogar jikin junan su, nan Billy ta dinga nuna wa Mommy manyan 'yan mata dake rayuwa a social media da kuma boyayyiyar rayuwa irin tasu ta 'yan bariki,mamakin irin dukiyar da matasan matan ke kashewa har ma da mazan ne ya sanya mommy yin shiruuuu ta na hango kan ta ta zama mai hamshaqin kuɗi irin su, ta tabbata ita iyayen ta ba za su qi ɗaukakar da zata samu ba ba kuma za su damu da sanin daga ina ta samo kud'in ta ba, dan haka jawo su zata yi a jiki da kyau su ci arziki su bar arziki a mazaunin sa.

Daga nan sai Billy ta qara shiga shafukan wasu zafafan mata da samari nan take Mommy ta sake mannewa da jikin Billy ta na kallon hotuna da videos tare da tambayar Billy,

"Yanzu wannan ma musulma ce? Ko dai arniya ce ne baku sani ba tun farko?"

Dariya Billy tayi sannan tace,

"Musulmace mana, Sunan ku ɗaya da ita amma ana kiran ta da Pretty H, kuɗi ne da ita dan ita ruwa biyu ce, ke watarana ma takan rikid'e ta zama ruwa uku, irin su ba qananan kuɗi suke samu ba, dan kuwa sai ta iya sai maki irin gidan nan sama da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login