Showing 102001 words to 105000 words out of 276165 words
Chapter 35 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ta tashi ta kama hannun Abdul da yake a firgice ta zaunar da shi kusa da ita tace,
"Ka ga ka sa ta ji kunya ta wani takure waje ɗaya kamar gaske, ai murna zaki yi ba wai kunya zaki ji ki yi shiru ba, alhamdulillahi, alhamdulillahi, alhamdulillahi,SARAUTA Allah yayi maka albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka, ina alfahari da kai d'ana,banda abinka kuma ai da leqowa kayi ka ce taje tinda bata amsa wayar ba, kai da qanwar ka?"
Billy ce ta sake duqar da kai tana murmushi ta kalli Innah Laminde ta sake sunkuyar da kai tana saka hannu a baki ita a dole taji kunyar suruka, kallon su Abdussaboor yayi yace,
"Innah ina take? Yaushe tazo gidan ban sani ba? Dan Allah kirawo min ita tazo na gan ta ko zan ji sanyi a rai na,Innah bana son na rasa Hadiza a rayuwa ta ina son ta, na yarda ta yi min qarya ta cutar da zuciya ta, amma na amince da soyayyar ta da ta dasa a raina zan aure ta, soyayyar ta itace qaddara ta, Innah ki yi wa Mai martaba maganar auren mu da Hadizana dan Allah,"
Wani irin ashar Billy ta saki a gaban su ta yi tsalle ta dire sannan tace,
"Lallai kuwa soyayyar ta zata yi ajalin ka, dan kuwa na tabbata Innah Laminde ba zaki yarda ki haɗa zuri'a da karuwa ba, da ka auri Mommy ka barni da dakon son ka gwanda a mutu har liman................*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 39:
D'akin Innah Laminde ta wuce cikin kuka ta ɗauki mayafin ta da jakarta ta fito babu ko sallama ta shuri flat shoes ɗin ta baqaqe masu kyau ta bar gidan, dik kiran da Innah Laminde ke yi mata be sa ta juyo ta saurare ta ba balle ta ansa ta, haka Billy ta sa kai ta bar gidan, ba ta tsaya ko ina ba sai a tasha,tana zuwa ta samu mota babu mutane sosai se ta kirawo driver tace ya zo su tafi a haka za ta biya shi kuɗin har da qari ma tana so ya kaita kano, cike da murna kuwa driver ya yi sallama da abokan shi ya shige mota ya bata wuta suka bar qauyen Ba Mugu.
Innah Laminde ce ta kalli Abdul dake ci gaba da yi mata magiya kamar bai ga sanda Billy ta bar wajen cikin kuka ba, shi yanzu baya kallon kowa a gaban shi da idanun zuciyar shi da idanun saman fuskar shi da ya wuce Mommy, cikin ɓacin rai Innah ta kalle shi tace,
"Yanzu Abdul abinda ka yi ka kyauta kenan? Yarinya na son tin tana qarama har wa girman ta amma kake wulaqanta ta? Anya Abdul haka ake rayuwa? Kai fa da bakin ka kace ba zaka auri Hadizan baka tsane ta baka ko son ganin ta, to yanzu me ya sauya ra'ayin ka akan ta?"
"Ni dai a bar tuna baya a fuskanci gaba dan Allah Innah, koda da nace ba zan auri Hadiza ba ai nace ba zan auri wannan mara kunyar ba ko? Ni fa dama can bata yi min ba, yarinyar nan kwata-kwata bata da tarbiyya ke ce baki ga abubuwan da take yi ba idan ta ganni,yanzu dai Innah in dai farin ciki na nada mahimmanci a wajen ki dan Allah ki shige min gaba a nema min auren Hadiza,Innah taɓa qirji na ki ji yanda yake bugawa (nan take yaja hannun Innah ya ɗora a saitin zuciyar shi), a dik bugun zuciyar dake qirji na ina jin yanda soyayyar Hadiza ke qaruwa a raina,"
Ajiyar zuciya Innah tayi sannan tace,
"Abdul dole na so farin cikin ka domin kuwa a kaff yaran gidan nan kai ne yaron da yafi kowa kyautata mana yake son ganin mu cikin walwala da wadata da farin ciki, ba iya ni da mahaifin ka ba kaɗai, gaba ɗaya iyayen ka na gidan nan da dangin mahaifin ka da nawa duk kana kula da kowa, tin baka da shi har Allah ya azurta ka,dan haka zan yi wa mahaifin ka magana a nemo mahaifin ta a yi maganar aure a tsakanin ku,Allah ubangiji ya sa hakan shine yafi zama alkhairi, Allah ubangiji ya kare dikkan sharrin dake cikin tarayyar ku,"
Wani irin kwanciyar hankali ce ta ziyarci Abdussaboor wanda ya samu kanshi da murmusawa tare da duqawa a gaban mahaifiyar shi ya hau godiya kamar zai koma cikin ta, tin bata murmushi har sai da ta murmusa ta sanya masa albarka.
"Yanzu yanda za a yi ka kira min Azizah tazo ta je gidan Mai dusa ta ga ko Bilkin ta je ta sanar da Ta Annabi tazo ina son ganin ta da gaggawa, saboda bana so maganar nan ta b'ata zumuncin dake tsakani na da qanwata,"
"To Innah bari na aika ta yanzun nan, to ya zancen yi wa Mai martaba maganar Hadizan?"
"Ohhh wannan wutar ciki da kake nunawa na bani mamaki Abdul, ai ka bari washegari da safe sanda yafi karb'ar qorafi ko sauraren duk wata magana mai mahimmanci sai na sanar da shi ko? Kai dai ka dage da addu'ar neman zaɓin Allah alkhairi a game da auren ka,"
Cikin sauri ya katse Innah Laminde da fad'in,
"Hadiza ce alkhairi na Innahr mu,"
Sultan ne ya shigo ya samu waje ya zauna yana furzar da iskar bakin shi sannan ya gaida Innah Laminde ya kalli Abdul dake cikin shauqin qauna yace,
"Yah broth how far na, anything for me?"
"Hummm Sultan kenan kai dai kullum baka da magana sai ta anything for you kamar kai nake yi wa neman,"
Dariya Innah tayi tace,
"Ahh toh yaro ka girma amma kullum kana maqale a jikin yayan ka, shi da zama yayi zai kai haka ne?"
Suna tsaka da hirar ne wayar Abdussaboor ta yi ringing, har ya kai hannu zai ɗauka ta katse,da sauri ya miqe ya bar d'akin yana fara'a ya sake bin kiran,ba a ɗauka ba har sai da ta katse, gaba ɗaya duk wani kamewa irin tashi duk ya zubar a cikin qanqanin lokaci, sake kiran wayar yayi yaji baturiya na sanar da shi wayar da ya kira a kashe take, a kid'ime ya shiga d'akin shi ya shirya cikin manyan kaya yana zabga qamshi ya sanya takalmin shi ya bar gidan riqe da wayoyin shi da makullin motar shi.
A qofar gida ya tarar da mutane suna zaune ana hira, suna ganin shi suka hau miqa gaisuwar su gare shi, hannu kawai ya d'aga masu ya faɗa motar shi, nan take wasu suka hau gulmar ya fara girman kai wanda ba halin shi bane, wani mutum ne yace,
"Ahh dama zaka rasa basarake da girman kai ne? Ai kai dai kawai ayi sha'ani,"
Wani bawan Allah dake zaune yana jin hirar su da suke tin ɗazu wadda bata wuce zagin mutane da gulma da annamimanci ba ne ya kalle su yace,
" Kuna da abun mamaki gaskiya, me yasa baku yi tunanin ko wani abune yake damun shi ba tinda kun dai san halin shi da fara'a da son mutane, yanzu kai da kake maganar girman kai kasan me kalmar girman kai take nufi a musulunci kuwa? Ana kiran mutum da me girman kai ne idan aka faɗa masa gaskiya yaqi ɗauka saboda yana ganin wanda ya faɗa masa gaskiyar be isa ya faɗa masa ba ya fi shi ɗaukaka ta kuɗi ko matsayi ko kuma ya girme shi,dan haka kaga baka sanya kalmar ma a muhallin da ya dace ba, mu dinga yi wa juna uziri dan Allah, dan kuwa ko babu komai kasha karb'ar 'yan kud'ad'en da yake bayarwa,"
Cikin dariyar yaqe wanda ya kira Abdul da mai girman kai ya hau cewa,
"Ahhh abun kuma ya zama 'yar gori?"
Shima bawan Allah'n cikin dariya yace,
"Babu maganar gori tinda bani na baka ba, nasiha kawai nayi maka Allah yasa mu dace,"
Gaba ɗaya sai suka haɗa baki suka furta, Ameen.
Abdul na isa qofar gidan su Mommy sai ya kirawo wani yaro dake wasa a qofar gidan ya aike shi yace yaje ya kirawo masa ita, cike da murna da farin ciki yaron ya tafi kiran Mommy dan kuwa ya gane waye Abdul, abun farin ciki da alfaharin shine ace mutum kamar Abdul ya aike shi.
Yana shiga ya tadda Ameerah na ta kuka a tsakar gida tana rantsuwa babu wanda ya isa ya aurawa Saddiqa Munir ko za a yi yaqin duniya ne ba baɗe ta da barkono ba, dik wannan mintunan da ta ɗauka tana kuka babu wanda ya kula ta balle yace tayi shiru.
Shi kuwa Munir takaicin yanda ma aka yi yarinya mara hankali kamar Ameerah ke son shi yake yi, a ganin shi a jerin mutanen da ya kamata su so shi Ameerah bata cikin lissafin su, dan haka da b'acin ran ta ya koma gidan su shi da Sadeeq da ke cike da murna da farin cikin hukuncin da Baabaa ta yanke.
Cikin fara'a yaron yace,
"Wai inji Yarima SARAUTA yace a kira masa Hadiza,"
Cikin takaici Ameerah ta kalli yaron bata ce masa komai ba ta miqe ta zaro iccen dake cikin wuta ta bishi a guje, nan take kuwa yaro ya kwasa da gudu ya bar gidan yana faɗin,
"Wayyoo Allah na mahaukaciya 'yar macukule ta biyo ni da wuta,"
Ko ta kan Abdul be bi ba yayi gidan su da gudu,ganin haka ne ya sanya Abdul zuwa bakin k'ofar gidan ya dinga bugawa yana zabga sallama, ya kai kimanin minti biyar yana bugawa kafin Mommy ta fito sanye da doguwar riga baqa mai manyan flowers gaba da baya a jiki, sai ta yafa mayafin rigar a kan ta gashin kanta baqi sidiq ya bayyana ta gaban goshin ta, leb'en nan sai ɗaukan ido yake yi saboda man da ta sanya, idon ta kuwa sanye yake da kwallin su na sihiri rambad'ad'au har wani ado tayi dashi a saman idon,cikin takun ta mai ɗaukan hankali ta isa gare shi ta tsaya a jikin qofar gidan su tana jifan shi da wani irin kallo mai sace zuciyar wanda ake kallon, lumshe idanun shi kawai yayi tare da sauke wata wahalalliyar ajiyar zuciya mai qarfi, jingina yayi da qofar motar shi yana jifan ta da kallon da yake narkar da duk wata gab'a ta jikin ta, cikin sanyin shi da kamewar shi yace,
"Anya Hadiza kin san cewa kece nutsuwa ta a yanzu? Sannan kece zaman lafiyar zuciya ta da kwanciyar hankalin gangar jiki da ruhi na, Me yasa kika qi amsa kira na kuma na kira kika kashe wayar ki ko so kike zuciya ta ta buga na rasa raina gaba ɗaya ne?"
Cikin wata iriyar murya mai sace zuciyar mai saurare Mommy tace,
"Babu caji ne shi yasa ta mutu,"
Ajiyar zuciya ya sake saukewa dan kuwa muryar ta dama yake so yaji, ya rasa me yake fusgar shi gare ta da yake sanya shi jin kamar zai haukace akan ta, a hankali ya fara takawa zuwa ɗaya gwfen na motar shi ya buɗe mata sannan ya koma mazaunin direba ya shiga yayi mata nuni da ta shiga itama, qin shiga Mommy tayi sai ta samu gefen inda ya zauna ta jingina kawai tana ci gaba da lumshe ido tana ware su akan fuskar shi, dik wani salon da zata yi dan ya kalli cikin idanun ta yi take yi,Abdul fito da qafafun shi yayi yana shaqar wani qamshi na musamman a jikin ta, (qamshin turaren wajen boka ne da aka tsaface dan ya so ta).
"Please ki yi magana mana kin barni ina ta surutu ni kaɗai kamar aku, ko baki ji daɗin gani na bane, da alama na takura ki da yawa ko? Hadiza bana jin zan iya bacci idan ban sake ganin ki ba yau,"
Murmushi tayi ta sunne kai ita a dole taji kunyar shi, a zahiri bata son yin magana saboda kar ta rusa musu plan ɗin su ita da Innoh, amma a cikin ranta tana son ta furta masa kalmar so gwargwadon yanda kunnuwa da zuciyar shi zata iya ɗauka,tana tsaka da tunani taji yace,
"Ina fatan dai idan aka zo neman auren ki gobe mutanen gidan ku ba za su ce na yi sauri ba? Domin kuwa da za su taimake ni su bani ke yau ma da babu abinda zai hana ni auren ki Hadiza, ban san yanda zan kwatanta miki yanda nake jin ki a raina ba, amma ni dai na san ina son ki, kuma ba zan iya dena son ki ba har qarshen numfashi na,"
Murmushi Mommy ta saki sannan tace,
"Da gaske kana so na Yah Abdul? Akwai abubuwan fa da baka sani ba a game da ni, idan ka sani daga baya kana ganin zaka iya ci gaba da sona har ka aure ni kayi rayuwar aure dani?"
Kallon ta yayi da kyau dan ya bata tabbacin yana son ta yace,
"Hadiza ina son ki zan aure ki, kuma ko wanne irin hali gare ki zan jure na zauna dake a haka, Hadiza bazaki gane yanda nake jin ki a raina ba saboda ke baki sona kamar yanda nake son ki shi yasa,"
"Humm Yah Abdul kenan, ta yaya mace lafiyayya mai hankali zata ga namiji kamar ka tace bata so? Ai idan dai ba ciwon hauka take yi ba ba zata taɓa qin ka ba,balle ni mai hankali, Yah Abdul na fara son ka a ganin farko da na yi maka dik kuwa da irin tashin hankalin da ka riske ni a ciki be hana ni yabawa Ubangiji ba akan Kyakkyawar halittar sa ba"
Hamdala Abdussaboor kawai yake zubawa yana kallon Mommy, ji yake kamar ya sace ta ya gudu da ita ya b'oye ta a waje mai kyau ya dinga bata kulawa kamar sarauniyar dik duniya.
Haka Mommy da Abdul suka wanzu suna bayyana wa junan su irin yanda suke so da qaunar junan su tare da fatan kasancewa a inuwa ɗaya.
******************************
Basu isa cikin garin kano ba sai da aka gabatar da sallar magariba sannan suka isa,bayan driver ya sauke mutane a tasha Billy ta bashi kuɗin da ta yi masa alqawari ta bar tashar, a bakin hanya Man ɗin ta da suke ta waya da chatting ya ɗauke ta sai gidan Hajiya k'waisa, suna isa mai gadi yaqi buɗe musu qofa dan hango Billy a mota da yayi, cike da masifa Billy tace,
"Ba zaka buɗe gate ɗin bane ko me? Ko kai makaho ne ko kurma da ka tsaya qiqam kamar icce ka qi budewa?"
"Ranki ya dad'e Hajiya ce da kanta tace kar na sake na sake buɗe maku gate ke da wannan me bakin dorinar ruwan,"
"Ka buɗe min na shigo ko kuma idan na kira ta a waya ta baka tabbacin ta cire dokar ta na kore ka qauyen ku da kai na,"
Cike da tsoro mai gadi ya wangale gate, nan take Man ya shige da motar shi gidan k'waisa ya ajiye a ma'adanar ajiye motoci, cikin isa Billy ta fito dan kuwa bata son su Sallau su kawo mata raini,buga qofar da zata sada su da cikin gidan suka yi kafin daga baya Zuby ta buɗe musu ta ja ta tsaya a bakin qofar tace,
"Hajiya bata nan sun fita da Oga Sam,kuma ta jima da bada umarnin kar a barku ku shigar mata gida ke da Mommy, ban san me yasa aka buɗe muku gate ba ma yanzu,"
"Lallai ne Zubaidah, wato wuyan ki har yayi kaurin yanka ko? Da kyau bari na kirawo Hajiyan na sanar da ita me kike yi min, a sannan ne zaki gane cewa Uwa bata fushi da ɗan ta sai dai ta ladabtar da shi,"
Cike da b'acin rai Zubaida ta matsa tana qunquni tace,
"Ai kuwa anyi asarar uwa da haihuwar ma baki ɗaya,"
Da jin Hajiya bata nan Billy ta ja Man suka wuce d'akin ta suka kulle dan ɗebe wa juna kewar da suke tattare da ita kafin Hajiya ta dawo.
Kusan awanni uku suka ɗauka a gidan kafin Hajiya ta dawo ita kaɗai,cike da gajiya ta hau kiran Sallau dan ya kawo mata abin sha, cikin sauri Sallau ya tafi cika umarnin ta, kamar abun almara haka Hajiya k'waisa ya d'aga kai sama ya hango Billy da Man ɗin ta na sakkowa daga saman benen ta manne da juna kamar suna cikin gidan su na kan su..............
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 40:
Cike da mamaki Hajiya k'waisa ta miqe tsaye tana ganin ikon Allah, cikin kama hab'a da dafe qugu da hannun hagu yace,
"Lale maraba gasasshe kura taga baqin jaki,mata k'urasa dangin shaid'an to ni K'waisan alheri me na ci na asham da zan yi ramuwar azumi kuma yau? Sallauuu! Sallauuu! Je ka kira min mai gadin nan mara amfani ka kuma tattaro min kan ku da kai da su Ruby ku zo nan na ji shegen da ya buɗe musu gida na da ban yi wahala da kowacce tsinanniyar qaramar karuwa na samo abina ba,"
Har Sallau ya taka da sauri zai fita Billy ta qarasa da sauri gaban Hajiya K'waisa ta fashe da kuka ta dafa qafar ta tana faɗin,
"Dan girman Allah'n da kike wa Sallah ki dakatar da shi ki ji uziri na,"
"Toooo wata sabuwa in ji 'yan caca ! ehh lallai dole na saurare ki dan kuwa maganar ki ta tuna min ko sallar asuba ban ba ga kuma duhu ya riske ni, uhumm ina jin ki, ina son sanin dalilin zuwan ki gida na bayan kun yanke wa kan ku hukuncin aure kun ajiye karuwanci? Sannan kin kawo min 'yar daba ko kuma in ce mayya dangin masu shan jini gida har taso zuqe mana jinin jijiyar wuya da tsintsiyar hannu har gida, sannan yanzu ki zo ki ce zaki hau yi min kukan da na san na makirci ne irin na karuwa?"
Hannu k'waisa ya d'aga wa Sallau yayi masa nuni da yatsan shi mai dogayen farata akan ya koma bakin aikin sa ya bar su da Billy, yana tafiya yayi wa Billy da Man dake tsaye yana jinjina kaidin mace nuni da wajen zama kafin shima ya zauna a kujerar da ya tashi ya harɗe qafa ya dora zaratan hannun shi a saman qafar tashi yana jijjiga su yace,
"Uhumm se aka yi yaya?"
"Hajiyata na zo ne in baki hakuri akan dikkan abinda ya faru a baya wanda ban taɓa tunanin zai faru ba, na ɗauki hakan a matsayin