Showing 150001 words to 153000 words out of 276165 words
Chapter 51 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
kawai Amy take yi tana farin cikin samun Billy a matsayin matar da zata aura.
Shagwab'e fuska Billy tayi tace yunwa take ji,ba ɓata lokaci Amy ta ja hannun ta suka wuce wajen cin abinci, daga nan suka koma gida suka ci gaba da shirye-shiryen bikin su.
Da misalin ƙarfe goma na safe wajen da za a yi bikin nasu a bakin ruwa cike yake da mata kala-kala masu shiga iri-iri,wasu tare suke da matan su wasu kuma 'yammatan su,iskar ruwan dake wajen mai sanyi sai kaɗa gashi da tufafin su yake yi, wajen ya sha kwalliya da fararen furanni, hatta da kujerun wajen farare ne,wata mata ce tsaye a jikin wani ɗan gini tana jiran ma'auratan su ƙarasa ta ɗaura musu auren.
Hannayen su sarƙe dana juna suka taho, Amy na sanye da suit farare tas masu matuƙar tsada kan nan ya sha gyara ta d'aure shi a tsakiyar kanta kamar yanda Billy ke so, ƙafafun ta sanye suke da wasu fararen takalma sau ciki masu matuƙar tsada,hannun ta d'aure da agogo rolex sai ɗaukan idanu yake yi,wuyan ta kuwa wasu sarƙoƙi ta saka guda biyu suna ta ɗaukan ido,dik wanda ya ga Amy a wannan yanayin ba zai taɓa ɗauka ta haɗa hanya da zuri'ar musulmai ba, babu mai ɗaukan ta a matsayin mace sai dai a kira ta da namiji.
Billy ce ta kalli Amy ta saki murmushi, rigar ta fara ta ɗan ja dan ta ƙara sauka dik da cewa ta riga da ta san ba saukar zata yi ba tinda iyakar tsawon ta kenan,gashin ta ne ke ta kad'awa saboda iskar ruwan dake kad'awa a hankali,riga ce guntuwa a jikin ta mara hannu ta fitar da shape ɗin ta da ta kashe miliyoyin kud'ad'e domin samar da shi.
Fuskar ta ta sha kwalliya sab'anin ta Amy da hoda kawai aka shafa mata sai man baki da maskara,an yi mata gyaran girar da ya dace da doguwa kuma siririyar fuskar ta.
Cikin abinda bai fi minti goma sha biyar ba aka gama d'aura musu abinda suka kira da aure, waje ya kaure da ihun murna da party.
Tin daga wannan rana Amy da Billy ke rayuwa kamar mata da miji a ƙasar turai,daga wannan ƙasa su je waccan suna honeymoon ɗin su.
***********************
Cikin shirin ta tsaf Saddiqa ta fito parlour ta samu Baabaa da ke zaune sanye da atampa ta yafa mayafi tana jiran ta, Sadeeq ne ke ta b'ata rai yana cin magani shi a dole an takura masa baya son zuwa ko ina, kallon shi Baabaa tayi tace,
"Bindiga zaka yi ka fashe sai na san kaji haushi mara kirki kawai, ni shi yasa nafi son Saddiqa akan ka,dan kuwa komai lalacewar uban ta da 'yan uwan ta tana son su, amma kai sai shegen riƙo, na rasa a inda ka ɗakko wannan mugun halin dan ba halin uwar ka bane ba kuma na uban ka ba."
"Wai har yanzu b'ata rai yake yi ba za shi ba?"
"Iyy wai, rabu da d'annema dole ne kaje ka ga ɗakin 'yar uwar ka ka gaishe ta dik da basu gayyace mu ba,kin rufe ko ina ko?"
"Eh Baabaa na rufe, ga makullin da za a rufe gidan na d'akko,"
"Da kyau to mu je yamma na yi, tinda Allah yasa an gama jarabawa lafiya ai sai aje a sada zumunci gobe-goben nan kina ganin wannan me ƙaton kan ya iso,dan na san kin faɗa masa kin kammala yau,"
Cike da jin kunya Saddiqa ta hau borin kunya tace,
"Ni fa Baabaa ban sanar da shi ba, shi da kan shi yake lissafi d'azu yace zai zo goben,kuma ma nace masa kar ya zo yayi zaman shi shine yaƙi,"
"Uhumm muje ni kinibabbiya bana son ƙarya,ke ɗin ce zai ce zai zo ki hana?"
saddiqa bata sake magana ba suka fita suka rufe gidan suka kama hanya dan zuwa gidan Ameerah su ga gida, wanda Baabaa bata san Saddiqa ta jima tana leƙa Ameerahn ba idan an tashi makaranta, tin tana zuwa tana yi mata rashin mutunci har ta dena zagin ta da yi mata habaici......
*Mutanen k'warai masu albarka a yi min kara a zo a sayi littafai na na kuɗi,kar fa a dinga wasa tare ci banban.....*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
*SANARWA !*
*Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....*
*MAZAUNA GIDA 300*
*ƳAN ABUJA 300*
*A GARIN MU 300*
*KAI NE JARUMI 300*
*KUN MAKARO 300*
*TAUBASHI 300*
*KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻*
*IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.*
*Kar ku manta akwai kayan gyaran jiki kamar su;*
*Face oil*
*Hair cream/oil*
*Hair mask*
*Skin oil*
*Body scrub*
*Domin gyaran jikin ku a wannan lokacin na sanyi.*
PAGE 59:
A hanya Baabaa ta baiwa Saddiqa kuɗi ta ce ta shiga shago ta ɗan yi wa Ameerah siyayyar abinda ta san tana so na ƙwalama, dan ta san halin mutuniyar tata kura ce uwar kwad'ayi, dariya Saddiqa tayi ta karb'i kuɗin ta tafi shagon, tana zuwa ta hau saiwa Ameerah tarkacen su biscuits da sweets har da indomie, tana isa inda ta bar su suna jiran ta suka rankaya suka yi gidan Mai Dusa.
Sai da suka gaisa da shamsu dake shago sannan suka shiga gidan, da sallama Baabaa ta shiga gidan Ummahn Billy na tsakar gida tana shan iskar maraice ta amsa tare da yi musu marhabun da zuwa,ciki tace su shiga Baabaa tace,
"Ah ah nan ma ya isa ba jimawa za muyi ba almuru ya gabato,"
Gaishe-gaishe suka yi a tsakanin su sannan Saddiqa da Sadeeq ma suka gaishe ta, tinda suka shiga Ameerah taji muryar su ta miƙe ta hau kwashe tilin suturun da ta loda a saman kujera ta watsa a cikin wardrobe ba tare da ta ninke ba, tana tsaka da kwashe kwanikan da ta bari tin na jiya da bata kwashe ba suka sallama ƙofar ta, cikin tura baki ta amsa ta ƙarasa fitar da kwanikan ta koma ta zauna, gaishe da Baabaa tayi taga Baabaan na yatsina fuska,Saddiqa da Sadeeqa ma sun gaishe ta amma sai taƙi amsawa da kyau tace musu,
"Ya kuke?"
Ɗauke kai Sadeeq yayi sai Saddiqa ce ta amsa mata da,
"Muna nan lafiya ƙalu alhamdulillah,"
Ledar da Ameerah ta ƙyalla idanu ta hango a hannun Saddiqa ne ya sanya ta cewa,
"Ya kuka tsaya anan ku shigo ku zauna mana, ko aikin soja za kiyi kin fasa na likitan?"
Murmushi Saddiqa tayi sannan ta samu waje a ɗaya daga cikin kujerun da suka fara sauya kala ta zauna,Baabaa ce ta kasa hakuri da yanayin da ta tadda Ameerah na ƙazanta da wari a ciki tace,
"Ke yanzu Ameerah uwar ki bata zame miki ishara ba ashe? Ko da yake ai lokacin da uban ku yayi mata kishiya kina ƙarama, Ameerah ke fa amarya ce amma d'akin ki ƙasa lamar ba ki share ba, Allah ma kaɗai ya san iya kwanakin da kika yi babu sharar,ki duba ki ga kaya yanda kika watsa su ko rufewa baki yi ba da alama baki jima da watsa su ba dan kar a gan su a barbaje kika ɗaga, ke yanzu irin rayuwar Innoh zaki yi ko? Kalli kan ki yanda ya tuje kamar ana ball a wajen, ji yanda kike tsamin hammata Ameerah ko kunyar kar mijin ki ya shaƙa baki ji,"
"Na yi wanka fa na shafa turare ni, kuma ni ki dena zagin uwa ta."
"Ashe kin san abinda kike yi bashi da kyau idan har zaki ɗauki gyaran da nake yi maki a matsayin zagi? To dan uwar ki Innoh kar ki fasa yin ƙazanta kina ji kina gani mijin naki zai yi maki irin yanda uban ki yayi wa Innohn taki, ko bai auro kyakkyawar bafulatana irin Yadikon sule ba, da ya auro mai hankali, tsafta da kula da kanta irin Yadikon sule kin koma gida zawarci dan kuwa mazan yanzu ba irin na da bane da yana ganin inda zai more ya tsaya akan ƙazama ballagaza ku ku tashi mu tafi,"
Ajiye mata ledar da suka kawo mata suka yi suka tafi Baabaa na ci gaba da zagin Ameerah har a tsakar gida dan ta tabbata kowa na ganin abinda take yi amma ba a gyara mata, meye amfanin zama da manya idan ba za a yi wa yaro gyara ba? Har ƙofar d'akin Ummahn Billy ta je tana masifa, da sauri ta fito daga ɗakin tana baiwa Baabaa hakuri,cikin yin ƙasa da murya tace,
"Ai Baabaa Ameerah addu'a kawai za a bi ta da ita, bayan ƙazanta lamarin ta har da rashin kunya,kina yi mata gyara a inda tayi kure zata buɗe baki ta faɗa maki mai zafi,shi kanshi mijin ma baya ganin laifin ta, to kai bawa ba sai ka koma gefe ba kayi kallo?"
"Kwarai da gaske tinda ba zaka sa mutum yin abinda bai niyya ba dole, ai kuwa zata ci malafar uban ta in dai namiji ne,gata gashi Allah bamu alheri,"
"To Ameen Baabaa a gaida gida mun gode."
Bayan tafiyar su Baabaa ne Ameerah ta hau shara, tana yi tana mita tare da yiwa surukar ta habaici akan abinda taji tana faɗa wa Baabaa,Ummahn Billy na jin ta ta kyale ta, Fadila ce ta gaji da jin yanda take yi wa mahaifiyar su rashin kunya ta fita tsakar gidan ta take tsintsiyar hannun Ameerah tace,
"Kin san Allah kina sake magana akan Ummar mu zan kifar dake anan wajen sai dai dik abinda zai faru ya faru,mara mutunci kawai."
"Keee dakata min ! Dakata min ba da ke nake yi ba da me dattin ɗankwali nake yi dan haka matsa ki bani waje."
Dariya sosai Fadila tayi kafin tace,
"Ko ba mai dattin ɗankwali ba? Ai kin baro ta a can GIDAN ƊAN LITI GATSO, kowa ya san Innoh bata wanka sai sati ba kuma ta kitso sai shekara wanki kuwa sai sa'a kin ga kuwa a wajen ta dattin ɗankwali ya ƙare,"
Ameerah na gama jin zagin da ake wa mahaifiyar ta ta yarda tsintsiyar tayi kukan kura ta cafki Fadila suka hau dambe, Ummah ce ta fito da gudu tana faɗin,
"Subhanallahi abun har ya kai haka?"
Cikin haki Ameerah ta k'wace daga riƙon da fadila tayi mata ta zabga wa Ummah harara sannan tace,
"Yama fi haka, ai ke kika turo ta ta yi min rashin kunya, to ki sanar da 'yar ki da tayi kwantai ba mashinshini dik sa'o'in ta na ɗakin miji da yaran su ta fita a sabga ta, idan ba haka ba se na ci uwar da ta kawo ta duni..."
Wani b'arin makauniya Fadila tayi wa Ameerah a fuska na bazata, nan take kuwa Ameerah ta tsaga uban ihu kamar ana zare mata rai,bata gama dawowa hayyacin ta ba Fadila ta yarɓar da ita a ƙasa ta hau kirɓar ta, dik yanda Ummah taso ta janye ta kasawa tayi,a guje suka ga shamsu ya baro shagon shi ya shiga gidan,cikin tashin hankali yayi kan Ameerah yana ƙoƙarin janye Fadila daga kan ta yana faɗin,
"Wannan wanne irin abune Ummah zaku haɗu ku tarar wa yarinya ƙarama ku yi ta duka haka? Ke fadila ɗaga ta ko na kifa maki mari."
Cikin haki Fadila tace,
"Sai dai ka kashe ni, amma tinda ta zagi uwa ta a gaban uwar tawa sai na dake ta na fasa mata wannan shegen ruɓaɓɓen bakin nata idan yaso gobe in ta tashi zagin uwa ta ta tanadi ruwan zafin gasa shi."
Shamsu na jin kalaman Fadila sai ranshi ya ɓaci yace,
"Ummah ta zaga?"
"Eh mana kuma an mata magana take yi wa mutane iskanci har tana min gorin aure, da bamu san yanda aka yi naki auren bane sai ki yi wa mutane gori, a yanda kowa yasan Innoh da shegen asirin tsiya na tabbata kaima asirin aka yi maka,"
Cikin tsawa Ummah tace,
"Fadila na ce ki ɗaga ta ko? Kai kuma ba za ka janye ta ba daga saman matar ka kana gani sai dukan ta take kamar ta samu ganga?"
"Barta Ummah ta koya mata yanda ake yi wa iyayen wasu ladabi,ni na koma shago sai anjima,"
Fita yayi ran shi a matuƙar ɓace, ya jima yana jin haushin yanda Ameerah ta raina mahaifiyar shi,dik sanda yayi mata faɗa sai ta hau fushi, to gwanda ya ƙyale Fadila ta gyara mata zama gobe idan an ce ta zagi mahaifiyar shi zata kiyaye.
A haka ya ci gaba da turawa wasu 'yan mata videos na batsa da ya mayar sana'a,ba ƙaramin samu yake yi ba da wannan sana'ar dan kuwa har maza manya zuwa suke yi su zauna a tura musu ko kunyar Allah basu ji balle ta mutane. Dik daren duniya sai shamsu ya shiga da ɗan ƙunshi gidan na mahaifiyar shi da ƙannen shi daban sannan na Ameerah da shi kan shi daban, yau kuwa ya ƙulla yi mata tsiya tinda ta zagar masa uwa.
A cikin gidan kuwa da ƙyar Ummah ta samu ta d'aga Fadila daga saman Ameerah, dik jikin ta yayi futu-futu da ƙura, hancin ta da bakin ta sun fashe sai ɗigar jini suke yi, yawu na tarara ta miƙe tana kuka tace,
"Allah ya isa ban yafe ba matsiyaciya kawai,"
Ganin Fadila ta zabura zata yi kanta sai ta taka da gudu ta shige ɗakin ta, kyacci Fadila tayi tace,
"Matsoraciyar banza mara kunya, da ki tsaya mana ki ga yanda zan yi dake,da na baki mugun mamaki,"
Ameerah zama tayi a bakin gadon ta tana tuna sanda ta daki Saddiqa a soron gidan su bata ji ba bata gani ba,takaici ne ya kama ta ta miƙe da ƙyar ta fita kitchen ta ɗora ruwan zafi a risho, tana gamawa ta juye a bokiti ta shiga wanka.
Bayan ta fito ne ta wuce d'aki ta shirya cikin wani material ɗaya daga cikin na lefen ta da ba a jima da ɗinko mata su ba,kalar material ɗin baƙi mai ratsin green a jiki yayi wa farar fatar ta kyau, turare ta fesa babu shafa mai balle roll on ta koma ta zauna tana ci gaba da kukan bakin cikin shamsu ya ƙi bin bayan ta,ƙwafa tayi tana jiran dare yayi ya zo zata yi maganin shi tinda ta san lagon shi.
Da dare kuwa bayan Shamsu ya dawo taga ya zo da ƙullin leda ya zauna a kujera mai cin mutum ɗaya ya buɗe ledar ya fara cin tsiren shi shi ɗaya ba tare da ya yi mata tayi ko ya zauna inda zata iya zama su ci tare ba,dik yanda taso ta ɗauke kai ta kasa dan haka cikin b'ata rai ta isa gaban shi ta kama ƙugu tace,
"Ina nawa hak'k'in ko ba za a bani bane?"
"Gashi kin faɗa me kuma kike son kiji? Ai in dai zaki zagi uwar da ta kawo ni duniya Ameerah kin gama samun komai daga waje na, ina sane da ƙazantar da kike yi min bakin ki ya dinga wari kamar mushe,hammata tsami,gaban ki wari Ameerah ɗakin ki sai yayi kwana uku baki share ba, sutura babu wanki balle kiyi wanka,dik na hakura na shanye na ji na gani zan zauna dake a haka amma iyaye na basu da mutunci a wajen ki musamman mahaifiya ta,to daga yau an gama irin wannan ɗan iskan zaman a gidan nan kin ji na faɗa maki, dan haka wuce ki bani waje kan na tashi na tattakaki wawuya kawai,"
Kuka ne ya k'wace wa Ameerah ta haye gado kuwa ta dinga rizgar shi, wato a dake ta har a fitar mata da jini a jikin ta amma ya dinga yi mata ihu har da cinye nama ya hana ta? Babu komai Allah zai saka mata ne.
Shamsu kuwa yana gamawa yayi gyatsa me ƙarfi sannan ya nannaɗe ledar ya yar awajen sannan ya cire rigar shi ya haye gado,dama bai dawo gidan ba sai da ya gama kallon fina-finan shi da baya gajiya dan haka a buƙace da ita ya dawo.
Cikin zafi-zafi ya fara taɓa ta saboda yau yaji sauyi, babu wannan mugun warin tayi wanka sai ƙamshin turare ke tashi a jikin ta, cike da tsiwa ta juya zata yi masa rashin mutunci ya samu wannan damar ya rufe mata bakin dan dole ta yi shiru, dik yanda taso ta hana shi kan ta dan ta hukunta shi kasawa tayi da kan ta ta miƙa kai bori ya hau.
**************************
A daren ranar nan Saddiqa bata yi bacci ba sai da ta gyara farar shinkafa ta wanke ta jiƙa saboda tana so tayi sinasir, zob'o ta dafa mai daɗi ta tace ta haɗa ta saka a fridge, Baabaa na ganin ta tana ta murmushin jin daɗi,ta tabbatar da cewa Saddiqa bata baro dik wani kyakkyawan halin Yadiko ba,ta ɗauke su tsaf a kan ta wanda da alama ma za ta iya fin mahaifiyar ta a komai.
Da safe kuwa tinda ta tashi ta saka Saddiq sharar harabar gidan zuwa ƙofar gidan, ita kuma ta hau gyaran gidan, bata samu zama ba sai da ta gama girki ta gyara ko ina tayi wanka sannan ta zauna tana hutawa, Baabaa ce tace,
"Sannu da aiki, Allah yayi maku albarka,Allah kuma ya dawo da shi lafiya,sai dai naga ana ta tuya amma an manta da albasa,"
"Ameen Baaba, amma ban gane me kike nufi ba?"
"Ahhh kin gyara gida tsaff kin yi wanka kin yi kwalliya hannu fari tasss ƙafa fara fat ido babu kwalli,kin kuwa san tasirin yin lalle da sanya kwalli a wajen mace?"
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi, dan kuwa ita a ranta ma har lalle taso taje to nauyin Baabaa ne ya hana ta, kar a ga zaƙewar ta ace ko tarewa bata yi ba tana rawar kai,cikin yin murmushi irin na manya Baabaa tace,
"Koda yake ma gwanda kar ki yi lallen ki jira a yi maki na tafiya ɗakin mijin ki dan na san tinda ya kamo hanya yau ba zai tafi ba sai dake,"
Sake yin ƙasa da kan ta Saddiqa tayi, daga ƙarshe da taji farin cikin yayi mata yawa sai ta miƙe ta bar wajen ta wuce d'akin ta da gudu, a gaban madubi ta tsaya tana kallon shigar ta ta atampa riga da skirt, d'aurin ɗankwalin da ta kafa ya yi dass akan ta kamar an kafa hula, ƙeyar ta kuwa gashin tane irin na Yadikon Sule kwance