Showing 117001 words to 120000 words out of 276165 words
Chapter 40 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
dinga faruwa da Abdul suka dinga dawo masa akan shi,yanda Salwah ke qi sam ta tura hoton ta har fuskar ta,da yanda take qin suyi waya ko suyi audio sai dai shi ya dinga yi ya tura mata, ashe dik ta tara waɗannan abubuwan ne ta ajiye dan su zama abinda zata yi blackmailing ɗin Abdul dasu.
Cikin fushi Bilal yace,
'Kai dan uwar ka ka san wa kake yi wa wannan shirmen kuwa? Zamu sa a nemo ka a kamo mana kai dik inda ka shiga mu ci uwar ka'
Cikin dariya matashin yace,
'Kafin ku nemo ni ni kuma zan wulaqanta ka domin kuwa nan da awa ashirin da huɗu idan banga million uku a account ɗina ba hotunan tsiraicin ka zai shiga duniya zaɓi yana gare ka, kar ka tsaya dogon nazari ai ko ba komai na ɗebe maka kewa da hotunan budurwa ta da take turo min ka kalla ka ji daɗin ka,nima kuma ka turo min naka ina nan na adana su a waje mai tsaron da babu wanda ya isa ya taɓa su in ba ni ba, da wannan sokiburutsun da kuke yi dama kud'in kuka turo min dan kuwa nasan kafi qarfin su ko babyna? da ka zaci a banza zaka hau social media kaga hoton kyakkyawar mace a profile ka kama soyayya da ita? Komai na duniya yana da price ni kuma na yanka maku nawa dole kuma ku biya,'
Yana gama fad'ar haka ya kashe wayar shi ya bar Bilal da Abdul cikin tashin hankali,Bilal kallon Abdul yayi yaga yanda nadama da tashin hankali suka baibaye shi, damuwa da tsoro suka shige shi,tinanin shi bai wuce yanda iyayen shi za su ji ba a duk sanda suka fahimci ya aikata zina ta waya har hotunan shi da videos ɗin shi suka watsu a duniya, me zai sami aikin shi? Wacece zata aure shi anan gaba idan tsiraicin shi ya fita duniya?
*Bature yace never judged a book by its cover. Masoyan Abdul a yi hakuri kar a canye ni d'anyaaaa haka labarin yazo, kowa yana da rayuwar shi da ta gabata, walau mai kyau walau mara kyau, fatan kawai shine kar mumini ya dawwama a aikin sab'o.*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 45
Kamar yanda Abdussabour yayi ƙoƙari yayi gini a garin kano da qauyen su na Ba Mugu, haka ma Bilal yake ƙoƙarin yin gini a can garin su na Bauchi saboda yana so idan ya kammala ya tattara har iyayen shi su bar gidan da suke ciki su koma sabo,kasancewar Iyayen shi ba masu qarfi bane ya sanya d'awainiyar gidan su dik ta rataya akan shi, wannan shine dalilin da ya sanya bai iya baiwa Abdul gudummawar kud'in da za su isa a biya wannan bawan Allah'n da ke neman lalata sunan Abdul a idon duniya.
Dik yanda mutum yake komawa idan ya shiga tashin hankali da damuwa to fa Abdul ya koma hakan ko ma fiye da hakan, saboda magana ake ta tsiraicin shi zai watsu ya bazu a duniya,gaba ɗaya abun har mamaki yake bashi yanda hanyoyin samun shi suka toshe, dan kuwa tin ana abun 24 hours sai da aka kai 72 hours Abdul bai haɗa kan million biyu bama balle a kai ga ukun,ganin haka ne ya sanya Bilal shawartar shi da ya je gida wajen iyayen shi musamman mai martaba ya tambaye shi koda aro ne wataqila ba za a rasa ba a wajen su,nan take Abdul yayi na'am da wannan shawarar, da rana tsage-tsage ya shirya ya hau motar shi ya wuce garin Ba Mugu, direct gidan su ya nufa ya tarar da mahaifin shi a fada da mutane ana wani case tsakanin manoma da makiyaya, bai tsaya a fadar ba bayan ya kwashi gaisuwa sai ya shiga cikin gida wajen Innah Laminde wadda ke zaune a kujerar ta ta shan iska suna hira da kishiyoyin ta da yaran su 'yammata cikin nishad'i.
Innah Laminde na ɗora idanun ta akan fuskar gudan jinin nata gaban ta yayi mummunan faɗuwa,domin kuwa a cikin kwana biyu Abdussaboor ya rame, idanun shi sun yi zuru-zuru kamar wanda yayi shekara yana jinya, shiru tayi tana bin shi da kallo har ya gama gaishe da iyayen nashi yayi wa qannen shi wasa ya isa gaban ta ya durƙusa ya na gaishe ta, da ido ta kafe shi tana son sanin abinda yake damun shi, nan take idanun shi suka kad'a suka yi jajawur, miqewa yayi ya shiga ɗakin ta ya wuce uwar d'aka,Innah Laminde na ganin haka ta tabbatar da babu lafiya, dan haka cikin sauri ta miqe tabi bayan ɗan nata, a tsaye ta gan shi yana sintiri idanun shi na bayyanar da damuwar shi,kafaɗar shi ta dafa ya juyo, suna haɗa idanu ya saki wata iriyar ajiyar zuciya mai qarfi, zama tayi a bakin gado ta nuna masa gefen ta tace,
'Zauna SARAUTA ka sanar dani abinda ke damun ka,'
Cikin jin kunya ya zauna a qasan qafafun ta kan shi a qasa yace,
"Innah nayi wa Ubangiji na laifi mai girma,gashi tin a duniya zan fara biyan laifin nan da na aikata da farashi mai girma, dan Allah ku taimaka min idan akwai kuɗi a wajen ku koda dubu ɗari biyar ne ku bani in tafi yanzu, rayuwa ta na cikin hatsari,"
'Hasbunallahu sa'yu'utinallahu min fadhlihi inna ilallahi raghiboon,Allah ubangiji yayi maka gafarar zunuban ka da mu baki ɗaya, tashi ka zauna anan, ka sanar da mahaifin ka abinda ke faruwa kuwa?'
Har ya bud'i baki zai yi magana Sultan ya shiga ya isar da saqon mai martaba akan yana son ganin Abdussaboor a turakar shi, domin kuwa ya kula da halin da gudan jinin nashi ya shiga shi yasa ya sallami kowa ya shigo ciki sannan ya aika a kira masa shi dan ya ji damuwar shi.
Abdussaboor na gab da fita Innah Laminde ta tsaida shi tace,
'Kar ka b'oye wa mahaifin ka damuwar ka, domin kuwa shi kaɗai ne zai taya ka kokawa kuma ya sama maka mafita,ka zo ka karb'i dubu dari biyu a waje na kafin ka tafi, Allah ya kyauta ya kiyaye dikkan abin qi, ina mai yi maka nasiha da ka ji tsoron Allah a dik inda kake, sannan a koda yaushe ina sanar da kai ka dinga bin dokokin Allah,'
Jinjina kai kawai Abdussaboor yayi yana tunanin ta inda zai fara sanar da mahaifin shi abinda ya aikata a rayuwar shi,cike da damuwa ya isa turakar Mai martaba, a zaune ya gan shi an kawo masa abincin ranar shi ya buɗe ya na kallon kwanikan kawai ba tare da ya sa hannu ya ci ba, Abdussaboor na shiga ya samu waje ya zauna ya sake gaida mahaifin nashi, bayan mai martaba ya amsa ne ya kalle shi cikin kulawa yace,
'Bismillah mu ci abinci kafin ka sanar dani damuwar ka,'
Hannu Abdussaboor ya wanke ya matsa jikin kwanikan abincin ya jira saida mahaifin shi ya fara sanya hannu ya ɗebi tuwon farar shinkafa da miyar taushen da ta ji gyad'a da naman rago, sannan shima ya sanya nashi hannun, sun fara cin abincin su ba tare da kowa yace uffan ba wayar Abdussaboor ta hau ringing, nan take gaban shi ya tsinke ya faɗi,cike da damuwa ya zaro wayar ya kalli mai kiran nashi, hannun shi ne ya fara rawa sannan ya kalli mahaifin nashi da yayi kamar be ga halin da yake ciki ba, dan kuwa lomar tuwon shi kawai yake sakawa a bakin shi yana taunawa a nutse.
Gefe Abdussabour ya koma ya amsa wayar, cikin yin qasa da murya yace,
'Malam ka jira lokaci ya cika mana idan kaga ban baka kud'in ba sai ka kirani,habaa sai faman damu na kake yi, sannan ba zai yuwu na baka million uku ba dole na rage dubu ɗari biyar dan kuwa ban samu dika ba,'
Cikin dariyar shaqiyanci bawan Allah'n nan yace wa Abdussabour,
'Calm down mana, ai tunatarwa bata zama laifi ba ko?'
Tsaki Abdussabour yayi sannan ya kashe wayar ya koma ya zauna, kasa ci gaba da cin abincin yayi, shi kuwa Sarki bai daina ci ba har sai da ya qoshi sannan ya wanke hannun shi, Azizah ce ta shiga ta kwashe kwanukan sannan tayi waje, gyara zama Mai Martaba yayi kafin yace,
'Bismillah Babana sanar dani damuwar ka kar ka b'oye min komai,'
Cikin in'ina da kame-kame Abdussabour ya labartawa mahaifin shi duk abinda yake faruwa da kuma matsalar da ta kunno masa kai, faɗin yanda ran Sarki ya baci ma ba abu bane mai yuwa, amma da yake mutum ne shi mai shanye damuwar shi, sai yayi shiru bai ce komai ba na tsawon wani lokaci kafin daga baya yace,
'Ina No mai kiran naka take?'
Jiki na rawa Abdussaboor ya miqawa mahaifin shi No a wayar shi sannan ya koma gefe, Sarki wayar shi ya ɗauka ya danna kira tare da bada umarnin a nemo masa mai wannan No a duk inda yake, sannan a sanya jami'an tsaro su mamaye shi su kama shi yana so ya b'ata wa masarautar shi suna ta hanyar blackmailing babban ɗan shi.
Nan take kuwa wanda Sarki ya kira suka bashi tabbacin za su tsananta bincike ya basu wani ɗan lokaci,bayan ya kashe wayar ne ya ƙurawa Abdussabour ido har sai da Abdul ɗin yaji wani irin tashin hankali da damuwa na mamayar shi a hankali, a hankali Sarki ya fara magana,
"ABDUSSABOUR ka bani mamaki, ka karya min yarda ta da amincin da na baka, ka kunyata ni a idon ubangiji na, ba tarbiyyar da na yi maka ba kenan ni da mahaifiyar ka,a zato na a iya ilimin da muka baka idan sha'awa ta dame ka kasan yanda zaka magance ta ba tare da ka kauce hanya ba, Abdussabour ina ka bar aure bayan kana da gidaje har biyu, kana da abun hawa, kana da salary da zai iya riqe maka mata huɗu idan kana so? Abdussabour ina ka bar azumin nafila idan kana ganin baka son kayi aure saboda baka shirya yin auren ba? Abdussabour me ya kai ka buɗe zuciyar ka ma mutanen banza har su hilace ka ka afkawa zina? Abdussabour me ya kai ka kallo da karance-karancen banza da ya kai ka aikata zina da girman ka da qimar ka da mutuncin ka?"
Hawaye ne ke zuba sosai a idanun Abdussabour, banda istighfari babu abinda yake yi, hakan da yayi ne ya sanyaya ran mahaifin shi, domin kuwa a qallah Abdussabour ba shi yake baiwa haƙuri ba, yana neman gafara ne daga wajen Allah ya fahimci Allah yayi wa laifi, dan kuwa shi laifin zina haqqi ne na Allah,idan bawa ya aikata shi da zarar ya nemi gafarar Allah shikenan, sai dai kuma mutum idan yana da aure to fa ya haɗa da hak'k'in abokin zaman shi, sai ya san hanyar da zai bi ya nemi yafiya ba tare da ya tona asirin kanshi ba gudun lalacewar auren shi gaba ɗaya.
Abdul bai samu damar yin magana ba har sai da mahaifin shi ya gama yi masa nasiha mai ratsa zuciya, sannan ya samu damar cewa,
"Tinda abun nan ya faru na gane illa da munin abinda na aikata, na kasance ina mai cike da nadama da danasani tare da kaico akan wannan abu dana aikata,ina neman afuwar Allah sannan ina neman gafarar ku akan kaucewa tarbiyyar da kuka yi min,inshaa Allahu irin haka ba zata sake faruwa ba har abada, zan kuma dage na nemi mata nayi aure,"
"Allah ya karb'i tuban ka babana, kafin lokacin auren naka ina mai yi maka nasiha da ka riqe azumi da yawan karanta alqur'ani da kuma zama a majalisin da ake koyar da ilimi na addini, Allah ya qara yi wa tarayyar ka da Bilal albarka, tabbas shi ɗin aboki ne na gari wanda za a yi fatan a ƙarasa rayuwa dashi har abada,yanzu ka tashi kaje zan kula da wannan kar ka sake ɗaukan wayar shi,sannan ko ya sauya no ya kira ka da kaji shine kar ka kula shi,"
Dik da har a wannan lokacin zuciyar shi na cikin tashin hankali amma ya samu natsuwa da salama kaɗan,yana fatan asirin shi ya rufu har abada a samu nasarar yin maganin wannan mutumin dake neman zubar masa da mutunci.
Abdussabour bai bar garin Ba Mugu ba sai bayan magariba,a lokacin Mai martaba ya sanar dashi bawan Allah'n nan ya shiga hannu, yana ofishin 'yan sanda dake Yakasai a garin Kano da ya isa ya wuce can a kashe case ɗin,baya so ya aika kowa daga nan saboda baya son kowa yasan me ya faru ciki kuwa har da mahaifiyar shi, godiya Abdussabour ya dinga yi wa mahaifin shi sannan ya yi sallama da iyayen shi mata ya bar garin Ba Mugu ya koma cikin garin Kano, direct Yakasai ya nufa yana zuwa ya tarar da Bilal da yayi wa waya tun a hanya,rungume Bilal yayi cike da farin ciki kamar an ce masa case ɗin ya qare.
Ko da aka nuna masa matashin da yayi masa wannan abun sai da ya nemi waje ya zauna saboda shiga damuwa,nan take ya tuna sanda matashin yazo masa shajaran majaran yana neman taimakon abinda zai ci da qanwar shi da mahaifiyar shi kasancewar shi maraya, Abdul ɗin bai yi qasa a guiwa ba wajen taimaka masa da maqudan kud'ad'e sannan ya bashi No shi yace a duk sanda yake da buqatar taimako ya neme shi, tin daga nan yake taimaka wa yaron ba tare da sun sake haɗuwa ba,amma shine ya biyo masa ta wannan hanyar zai cutar dashi.
Nan take Bilal yayi tsalle ya falle matashin da mari, dik faɗa da tsoratarwar da hukumar 'yansandan ke yi wa Bilal be hana shi lallasa yaron ba, yana zagin shi, cikin takaici yace,
"Matsiyaci dogon banza, dube ka kamar na Allah, ashe ƙwallon shege ne, kai yanzu ka rasa wanda zaka zalunta sai wanda ya taimake ka? Dan Allah ku bari na ci uwassa in yaso ku rufe ni na kwana anan tare dashi,"
DPOn da ya dena hana Bilal dukan yaron ne ya riqe shi yana dariya yace,
'Aboki na gaka gajere amma sai masifar tsiya, ana hana ka kana qara daka tsalle kana falla masa mari, tin ina jin haushin qin jin maganar mu da kake yi har ka fara bani dariya, to yanzu ba wannan ba dai, a iya binciken da muka fara mun gano qarya yake yi bashi da wani abu daya b'oye na game da abinda ya faɗa akan ka, hasali ma dik maganar da kuka yi dashi goge ta yake yi saboda qanwar shi na amfani da wayar tana assignment shi yasa baya barin komai da zai sanya mata zargi akan yayan nata,iskanci ne kawai irin na ɗan yau, amma dik da haka zamu sake bincikar shi na sati biyu dan tabbatar da bai ajiye wata shaida ba a wani wajen,'
Cike da d'imuwa da gigicewa matashin nan yace,
'Sati biyu ! Dan girman Allah kar ku ajiye ni har tsawon wannan lokacin mahaifiya ta zata iya mutuwa dan baqin ciki idan ta neme ni ta rasa aka ce mata ina nan, ba irin tarbiyyar da tayi mana ba kenan, ni kaina tsautsayi ne da rashin godiyar Allah yasa na aikata abinda nayi, dan Allah me gida kayi hakuri ka sa baki a sake ni na koma, yau tin safe bamu ci abinci ba dikan mu har mahaifiyar mu, gashi bata da lafiya tana da ciwo zuciya magungunan ta sun qare,bana so na rasa ta, bana so na rasa ta dan Allah ku taimaka min,'
Kuka matashin nan ya dinga yi kamar zai shid'e, wani irin tausayin shine ya kama Abdussabour,tabbas Allah yana son shi da shiriya ne shi yasa ya turo masa wannan bawan Allah'n dan ya tsorata shi ya ganar dashi abinda yake yi ba mai kyau bane ya daina, dan haka godiya ma zai yi masa sannan ya bashi tukuicin fargar dashi irin halakar daya tsoma kan shi a ciki,cike da fara'a Abdussabour yace,
"Ranka ya dad'e na janye case d'ina da wannan bawan Allah'n,ina mai nema masa afuwa akan abinda yayi,zamu je na ga mahaifiyar shi idan da gaske yake akan duk abinda ya sanar damu to fa zan taimaka masa da jarin naira dubu ɗari biyu dan ya samu yanda zai yi ya kula da mahaifiyar shi da qanwar shi, idan kuma qarya yake yi zamu dawo nan akai shi kotu a yanke masa hukuncin abinda ya aikata,'
Cikin sauri matashin nan yace,
'Na amince, na amince mahaifiya ta na zaune a can 'yan kaba, idan qarya nake yi ni ku harbe ni ma na yarda,'
Bilal ne ya dalla masa harara yace,
'Ni da kaina zan harbe ka sai dai a d'aure ni, kai kuma Allah yasa hakan shine yafi alkhairi haka ake son mutum mai yawan saka alkhairi ga wanda yayi masa sharri, muje a tabbatar da gaskiyar maganar shi, dan ni har yanzu ina da tantama akan shi,kasan fa dogon mutum ba hankali ya cika ba,'
DPO ne ya kalle shi cikin dariya yace,
'Ah ah fa kar ka sake ka zage mu dogaye, dan kana gajere sai ka yi mana kud'in goro?'
Murmushi Bilal yayi suka fita a motar Abdul, yaron nan kuma a motar 'yan Sanda, bayan tsananta bincike ne suka gano gaskiyar maganar da ya faɗa musu,babu b'ata lokaci Abdussabour ya bashi kud'in da yayi masa alqawari suka koma gida,tin daga wannan ranar Abdussabour ya koma yin azumin litinin da alkhamis, idan ma ya tashi da tsananin buqatar mace to fa zai iya zarcewa da azumi a ranar,a hankali rayuwar shi ta koma ina ka fito aiki, ina zaka je aiki, me kake yi ibada.
Abdussabour na nan kwance bai yi aune ba yaga Bilal ya farka daga baccin da ya ɗauke shi a saman kujerar da yake zaune, band'akin dake d'akin da aka kwantar da Abdul ɗin ya shiga yayi alwala ya zo ya shimfid'a abun sallah ya fara nafila.
Wannan halin na yawan ibadar Bilal na qara sanya wa Abdul qaunar zama da shi dan kuwa ba kaɗan yake nuna masa hanyar gaskiya ba,zama da Bilal alkhairi ne a wajen shi.
Washegari da safe.......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 46:
Baabaa ce ta dage ita zata yi musu qosa idan yaso Ummi ta dama kunun gyad'a irin wanda take cika masa kindirmon nan yayi shar da shi