Showing 180001 words to 183000 words out of 276165 words

Chapter 61 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

ba,me ya aike ta sadaukar da budurcin ta a gare shi a ranar farko da haɗuwar su? Shin bata kishin kanta ne a matsayin ta na macen da ta gama jami'a da budurcin ta har ta kai matakin bautar ƙasa? Mene ne shirin ta ko ƙudirin ta akan shi?


Mommy kuwa na can gida hankalin ta duk ya tashi saboda rashin komawar Abdul gida akan lokacin da ya saba,kiran magariba ake tayi amma ta kasa zuwa ta gabatar da sallah tana nan zaune tana ta gwada layin shi shiru bai ɗauka ba.

Naja ce ta fito daga d'aki har ta yi sallah da carbi a hannun ta tace wa Mommy,

"Hadiza kije kiyi sallah inshaa Allahu zai dawo lafiya."

Hawaye ne suka kwaranyo a idanun Mommy cike da nadama tace,

"Aunty Naja ba zaki gane bane, laifi nayi masa ɗazu shi yasa ya fita yana fushi, da na sani naji faɗan ki na dena hana shi hak'k'in shi,yanzu ga abinda na jawowa kaina nan, ya tafi tin safe ko karyawa bai yi ba har yanzu be dawo ba."

Kuka ne yaci ƙarfin ta sosai ta samu waje ta zauna tana ta rera shi cikin d'aga sautin muryar ta,Naja ce ta zauna a gefen ta ta dafa ta tace,

"Irin wannan nake guje maki,ki gode Allah mijin ki ma mutumin kirki ne,da wani ne neman matan banza zai tafi idan kina hana shi kan ki,ke bari kiji shi kanshi mutumin kirkin yana iya kauce hanya idan dai shaid'an da gajen hakuri suka gifta a rayuwar shi."

"Allah kar ya nuna min ranar da Abdul ɗina zai faɗa tarkon shaid'an Aunty Naja, dik sanda Abdul ya aikata zina da auren mu Aunty sai na illata shi,sai na kashe yarinyar ko ƴan matan sai dai a kashe ni."

Ido Abdussabour da ya buɗe ƙofa ya zaro waje yana jin kamar ma ta gama ganin abinda ya aikata ne yasanya ta yin wannan furucin,cikin sanyin jiki ya ƙarasa shiga parlourn,Mommy na ganin shi ta miƙe a guje ta nufe shi ta rungume shi sosai a jikin ta tana ƙara fashewa da kuka, Naja na ganin haka ta miƙe ta bar parlourn ta wuce d'akin da yake a matsayin nata.

A hankali Mommy ta fara janye jikin ta daga na Abdul tana wani sunsunar shi kamar kare da uban gidan sa,nan take idanun ta suka kad'a suka yi wani irin jaaa kamar jan ƙyalle.

Kallon shi take yi daga sama har ƙasa tana so ta karanci yanayin shi,jikin Abdussabour ne ya yi bala'in yin sanyi kamar kazar da aka watsa wa gishiri a talle,kallon kallo suka fara yi,cikin sauri ya janye jikin shi yace,

"Meye haka kike wani kallo na kamar na yi wasu kunnuwan a jiki na? Matsa ni naje na ci abinci na huta,idan kin san ba biya min buƙata ta zaki yi ba ki daina kusantar inda nake daga baya ki barni cikin buƙatar da zan rasa yanda zan yi da kai na."

"Rasa yanda zaka yi da kan naka ne ya kai ka ga yin mu'amala da wasu matan banzan Abdul? Ji kake yi bazan gane ba ko? Wannan ƙamshin turaren wace tsinanniya la'ananniyar Allahn ce, wannan wanne janbakin wace matsiyaciya mai ƙarar kwanan ce? Wacece take son uwar ta ta haifi wata? Abdul wace shegiyar ce ta janye min kai tun safe har dare? Ka bani amsa kafin in kashe ka in kashe abinda ke ciki na da ni kai na !"

A matuƙar tsawace Mommy ta ƙarasa maganar ta har sai da hakan ya janyo hankalin Naja ta fito a guje, jikin Mommy ne ke wata iriyar rawa kamar mazari, nan take cikin jikin ta ya hau naushin ta,da ƙyar Abdussaboor yayi ta maza yace,

"Kar ki sake kiran matar da zan aura da tsinanniya,tinda kin gaza wajen kulawa da buƙatu na dole ne na ƙara aure saboda na samu nutsuwa,ba zai yu ki kasa sauke haƙƙin aure na dake kan ki ba kuma ki hana ni auren wata."

"Rashin biya maka buƙata ne ya sanya ka zuwa aikata zina da auren mu?"

"Ni ban aikata zina da kowa ba Hadiza, kar ki sake accusing d'ina da aikata zina abun ba zai yi mana kyau ba ni da ke,matsa ki bani waje."

Ture ta gefe yayi da niyyar ya wuce Mommy tayi kukan kura ta ɗauki glass cup ɗin dake saman table ta saita shi ta wurga masa...................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI









RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨









PAGE 73:









A hannun Aunty Naja kofin ya sauka,wani irin tsoro ne ya dira a zuƙatan su gaba ɗaya,a guje Mommy ta nufi Auntyn nata tana mai duba hannun ta,cikin sauri Abdul ya janye ta kafin ƙafar ta ta sauka akan kwalaben kofin da ya tarwatse a ƙasa,wani irin mugun kallo ta watsa masa sannan tace,

"Ina ruwan ka da abinda zan taka? Abdul zan iya bi takan jerarrun wuƙaƙe da tsinin mashi akan na hana ka karuwanci ko ƙara aure, Abdul ina so ka saka a ranka har abada baka da matar aure sai ni ɗaya a duniyar nan, kai baka isa ka ƙara aure ba da raina da lafiya ta, kai ko bayan mutuwa ta baka isa ƙara aure ba ni na yi maka wannan alƙawarin, ka rubuta ka ajiye."

Naja da ke tsaye cike da kaɗuwa da jin tsoron irin kishin da Mommy ke gwadawa ne ta kama hannun Mommyn suka shiga d'akin ta,suna shiga Mommy ta zauna a bakin gadon ta ta fashe da wani matsanancin kuka,numfashin ta taji yana yi mata wahalar shaƙa saboda azabar da take ji na kishi a ƙirjin ta,cikin kukan da take yi ta kalli Naja dake goge ɗan jinin da ke fita daga bayan hannun ta da tissue tace,

"Aunty Abdul fa zina yaje yayi da auren shi,me yasa ba zai yi hakuri na haihu lafiya ba? Shi shaida ne akan yanda nake bashi kulawa ta musamman,ashe laifi ne dan na saba masa da kalar soyayyar da bai taɓa ji ko ganin irin ta ba? Akan Abdul yayi min kishiya Aunty Naja gwanda na rasa raina."

Haƙuri kawai Naja ke bata,dan kuwa bakin ta na ɗauke da maganganun da ta san idan tace zata yi su a irin wannan lokacin mommy sake rikicewa zata yi, dan haka sai kawai tace,

"Kiyi haƙuri Hadiza,na yi miki alƙawarin har abada Abdussaboor ba zai auri kowa ba a duniyar nan har bayan ranki,ke kaɗai ce matar shi,bayan ke babu wata mace da zata sake burge shi a duniyar nan,ki kwantar da hankalin ki kin ji ko? Sannan ni kina bani mamaki,a zato na ke mai fahimta ce,kuma mai ɗaukan shawarace, duba da yanda kika ɗauki wasu shawarwarin nawa kika yi aiki da su kuma Alhamdulillahi gashi kin samu nasara a gidan auren ki, me yasa da na baki shawara ki dinga biya masa buƙatar shi koda da dabaru ne namu na mata kika gaza? Namijin da ya saba da kulawa baya da juriya, maza ƙalilan ne masu tsoron Allahn da za su tsare maki mutuncin ki da nasu idan basu samun yanda suke so, a yanda soyayyar nan ta zamani tayi yawa ma ba sai dai ki hango wani a waya yana lalata da matan banza ba? ke kin san komai ai ba sai na tsaya ina maki dalla-dalla ba, dan haka yanzu kiyi haƙuri ki haihu za mu ɗauki mataki mai girma."

"Aunty yanzu ba za a iya ɗaukan matakin ba har sai mun jira na haihu?"

"Hadiza ke da ake ta lafiyar ki kuma yaushe zamu rankaya ƙauye wajen malam a haka? Ji fa girman cikin jikin ki kamar ba cikin fari ba."

Cikin sauri Mommy ta miƙe tsaye ta kalli Naja tace,

"Aunty zan iya zuwa ko nan da birnin sin ne akan biyan buƙata ta,dan Allah gobe idan ya fita aiki muje mu dawo da wuri,tinda babu nisan da har zai gane mun fita in dai ba dawowa yayi ya tarar da bamu nan ba."

"To shikenan yanzu dai ki tashi ki tafi ɗakin ki, bana son fushin nan naki kina bani tsoro, ba haka halin ki yake ba Hadiza, ke yarinya ce mara rigima da kowa, dan Allah kar ki fara yanzu kin ji ko? Je ki ki lallab'a shi ku shirya,na tabbata a haka zaki samo mana wani ƙarin bayanin da zai taimaka mana koda wajen malam ɗin muka je."

"Babu inda zan je Aunty Naja, baki san yanda nake ji bane idan na gan shi, ji nake kamar na shaƙe shi ya mutu kowa ya huta."

Kallon Mommy Naja tayi ta ga alamun gaskiya a kalaman ta, sai tsoron sabuwar halayyar mommyn ta kama ta, gyad'a kai kawai tayi ta bar ɗakin ta koma nata da tunanin yanda zata kaya zuwa gobe.

Abdul kuwa tinda ya shiga ɗakin shi yake tsananin mamakin halin Mommy na baƙin kishin da bai santa da shi ba,a iya sanin shi Mommy bata da faɗa, me ya shiga kanta take son illata shi akan kishi? Wayar shi ce ta hau ringing, kallon wayar yayi yaga sunan mai kiran ya bayyana balo-balo a jikin wayar, tsaki yaja kafin ya latse kiran,ko maida wayar aljihu bai yi ba aka sake kira, ganin ba zata daina kiran shi bane ya sanya shi ɗauka cikin ƙasa da murya yace,

"Bayan makircin da kike son haɗa min shine kike kirana dik da kin san ina gida ko? Wato so kike ki kashe min aure shine kika shafa janbakin ki a kaya na ko?"

Cikin narke murya Maimoon tace,

"Allah ya tsare ni da raba auren ka My,ban san ya aka yi janbaki na ya shafu a kayan ka ba,wataƙila hakan ta faru ne a lokacin da hankulan mu basu tare damu, Abdussaboor na kira ka ne na sanar da kai ina son ka, ina so ka riƙe alƙawarin da kayi min da gaske, domin ni ba da wasa nake ba,kar ka manta da abinda zai biyo baya a duk sanda ka bijire wa buƙata ta."

"Na ji na gode da saka ni a uku da kike shirin yi ba zan manta ba,kar ki sake kira na ina gida."

Katse wayar yayi ya zauna yaraf a saman gadon shi, kwanta wa yayi rigingine yana kallon fankar cikin d'akin dake tsaye cak bata juyawa saboda sanyin da ake yi a gari, tunanin abinda ya wakana tsanin shi da Maimoon ya fara yi bayan sun gama sheƙe ayar su a hotel.

'Ya akai kina budurwa kika yarda kika sadaukar da kan ki a gare ni? Me yasa ba zaki yi hakuri ki ƙarasa ladan ki na tsare mutuncin ki da kika yi ba har zuwa wannan lokacin ki je gidan mijin ki lafiya?'

Murmushi Maimoon tayi sannan ta zagaye hannayen ta a cikin shi ta kwantar da kan ta a bayan shi tace,

'Tin ina secondary school nake sha'awar yin rayuwa irin ta jin daɗi kamar yanda na ga ƙawaye na nayi,sai dai kashhh na fito a gidan talauci da babu,dan haka a nawa tunanin yawon iskanci ba nawa bane,bani da burin d'akkowa malaman iyaye na magana, ma'ana na samo masu ɗan gaba da fatiha, shi yasa na ƙudurta a raina, ba zan taɓa yin lalata da kowa ba sai wanda na san zai iya aure na koda ya sanni a ƴa mace ne kafin aure.'

Cike da mamaki Abdul ya juya ya kalle ta yace,

'Amma dai wannan wauta taki da yawa take Maimoon,idan kuma kika zubar da budurcin naki abanza ba a aure ki ba fa? Sannan taya akai kika gane ni zan aure ki bayan nayi lalata dake?'

'Tinda muka zo ma'aikatar ku na ji labarin ka a wajen mutanen wajen naku, mahaifin ka sarki ne a garin ku, kana tsananin kare image ɗin garin ku da masarautar ku,naji yanda kowa ke yabon ka a wajen, a lokacin da na ɗora idanu na a kan ka na rasa sukunin zuciya ta,na kamu da son ka a kallon farko da nayi maka,sai kuma na kula da wani yanayi a tattare da kai a lokacin da ka shigo kamfanin, yanayi ne na buƙatuwa irin ta sha'awa.'

'Ban katsi numfashin ki ba, ke da kike cikakkiyar budurwa taya akai kika gane ina tattare da sha'awa?'

Wani Shu'umin murmushi Maimoon tayi kafin ta tashi zaune, wayar ta ta ɗauko ta miƙa masa bayan ta buɗe ta ta shiga gallery ɗin ta, hotuna ne kala-kala na maza da mata tsirara,sai videos na batsa kala-kala,da sauri ya miƙa mata wayar yana binta da kallon mamaki, murmushi ta sake yi sannan tace,

'Da damar ƴan matan yanzu da kake gani babu abinda bamu sani ba,wasun mu ma sun fi wasu matan auren ƙwarewa da kuma yawan saduwa da maza a waje, irina kuma sun san komai lokaci kawai suke jira da wanda suke ganin shine ya dace da su sai su sallama musu kan su, wasu kuma sun san komai amma sun tsare budurcin su har sai sun je gidan auren su sannan ne za su baje kolin su,ƙalilan ne daga cikin ƴan mata a wannan zamanin zaka same su basu san menene rayuwar aure ba, ko nace maka auratayyar ma kanta.'

'To a gaskiya ni dai yanzu bani da niyyar ƙara aure, wannan abun ma da ya faru tsakanin mu akasi aka samu, sannan ban taɓa zaton zan same ki a cikakkiyar budurwa ba da ban kusance ki ba.'

Dariya tayi sosai kafin ta tashi zaune ta janyo handbag ɗin ta,wata camera ƙarama ta zaro ta na juyawa a hannun ta,kallon inda ya yage a jikin jakar ta  Abdul yayi,nan take ya fahimci abinda ya faru, cikin sauri da zafin nama ya tashi dan ya ƙwace camera ɗin ya fasa kowa ya rasa,sai Maimoon ta bashi tsananin mamaki,dan kuwa dambe suka fara yi kamar wasu sa'annin juna da ita, babban abinda ya baiwa Abdul mamaki be wuce yanda ya samu Maimoon da wani irin azababben ƙarfi ba, sai da suka gaji da damben Abdul ya ja ya tsaya dan dole ya yana haki yana kallon ta cikin wani irin yanayi na tashin hankali,zubewa yayi a saman guiwowin shi tare da haɗe hannayen shi waje ɗaya yace,

'Dan girman Allah Maimoon kar kiyi min haka,ki rufa min asiri da ni da iyaye na da iyali na,na jima da tuba daga wannan harkar tsautsayi ne ya sa har na ketare iyakar da ba tawa ba.'

Dariyar rainin hankali Maimoon tayi masa sannan tace,

'Abdussbour kenan, kai a ganin ka haka banza zan zo gare ka? To bari na faɗa maka wata magana, ban fito ba sai da na shirya, cikin maza na tashi,babu irin gwagwarmayar da ban yi ba a rayuwa ta da ka ganni nan, dan haka kar ka sake irin gangancin nan da ni,ka tashi kawai ka shirya ka koma wa iyalin ka, ni da kai mutuwa ce zata raba mu Abdul, sai ka aure ni,idan baka aure ni ba sai na tona maka asiri, sai duniya ta san me kake aikatawa a ɓoye.'

'Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, Maimoon sanin ki bai zame min alkhairi ba, nayi dana-sanin ganin ki a rayuwa ta,kaico na ni Abdussabour,da na sani da na yi hakuri kamar yanda matata ta buƙata na jira bar ta haihu, matata bata gaza ba wajen bani kulawa, nabi ruɗin shaid'an gashi ya kai ni ga halaka.'

'Dik wannan dana-sanin babu inda zai kai ka,ka tashi ka tafi wajen iyalin ka kar suga ka jima,ina mai tunatar da kai ka fara shirin aure na nan kusa, idan ba haka ba nan da sati biyu za ka ga videon ka a social media,zancen ka shine zai yi trending a cikin shekarar nan.'

Jiki babu ƙwari Abdussabour yayi juyi a saman gadon shi tare da share hawayen nadamar da ya gangaro masa, wannan shi ake kira gaba kura baya sayaƙi,idan ya ƙi auren Maimoon asirin shi da mutuncin shi ya tonu ya zube, idan yace zai aure ta Mommy ba zata shafa masa lafiya ba, tayaya zai auri yarinyar data bari yayi zina da ita madadin tayi hakuri ta ci gaba da kare mutuncin ta sai bayan tayi aure? Idan kuma ya aure ta ta ci gaba da neman wasu mazan fa?



**************************

Tin daga harabar gidan har zuwa cikin gidan na Saddiqa a gyare yake fess babu datti ko ɗaya,tsaye take a kitchen ita da khaleesat suna ƙarasa girki kafin dawowar Rouhin nata, cikin sauri ta kalli Khaleesat tace,

"Dan Allah ƙarasa bare ƙwan zan je na yi wanka na dawo,idan kin gama dika kina iya fara cin abincin ni dai kin san sai Rouhi na ya dawo."

"Inyeee masu Rouhi manya, daɗin abun dai muma an kusan kai mu gidan namu Rouhin bare a dinga yi mana yanga da sunan Rouhi."

Dariya suka yi a tare Saddiqa ta wuce tana faɗin,

"Ni dai ban faɗa dan a ji haushi ba, amma idan anji haushi Allah huci zuciyar ƴan mata."

"Inyeee kika sake wani laifin ko? Za mu gauraya dake ne, zaki sake barin wayar ki gidan Ummi ke da mijin ki kiga wanda zai kawo miki har gida."

"Cike da dariya Saddiqa ta ƙarasa shiga ɗakin ta tana faɗin,

"Ohhh ni Saddiqa na shiga uku da gorin nan naki Khaleesat, wai ke magana bata wucewa a wajen ki?"

Dariya kawai Khaleesat tayi ta ci gaba da ɓare ƙwan,tana gamawa ta ƙarasa gyara wajen ta fito da dik abinda ya kamata ta kai saman dinning table, tana zuwa sai ta ajiye komai a inda ya dace sannan ta zuba abincin ta ta koma saman kujera a parlour ta kunna kallo,kallon ta take yi tana cin abincin ta hankali kwance, gefe ɗaya kuma tana danna wayar ta.

Tana nan zaune Saddiqa ta fito sanye da wata doguwar riga mai taushi mara dogon hannu kalar dark green,kanta ya sha ƙananan kitso kamar yanda Munir ke so, hannun ta riƙe da waya sai baza ƙamshi take yi ta samu waje ta zauna a kujerar, kallon ta Khaleesat tayi sannan ta ce,

"A gaskiya Saddiqa kina da kyau sosai ki godewa Allah, sai dai Yah Munir ya fiki kyau kaɗan."

"Son kai ne abun Khalee?"

"Dan Allah ku dena kira na da sunan nan Allah bana sooo."

"To sai kin ce na fi shi kyau zan dena."

"To kin fi shi kyau shi kenan?"

Ƙarar motoci suka ji a gidan nasu, dan haka cike da mamaki suka mike tsaye suka nufi windown dake kallon tsakar gida,Munir suka gani ya shigo a motar shi, sai wata ƙaramar motar da bata kai tashi girma ba dake biye da tashi.

Suna gama shiga gidan suka buɗe marfin mota suka fito a tare, kallon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login